Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ability - A turance tana nufin iyawa.
Misali; Duk abin da aka sa shi yana iyawa don yana da cikakkiyar lafiya.
HAU; Iyawa (Tana nufin ikon yin abu)
Ability to endure hardship or pain - A turance tana nufin dauriya.
Misali; Tanko yana da dauriya.
HAU: Dauriya (Tana nufin juriya)
Abinci - Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa.
Misali; Muna cin abinci sau uku a rana.
ENG; Food/Meal (A turance yana nufin abinci)
Abscess under armpit - A turance tana nufin jambaɗe.
Misali; Jambaɗe ne ya fito mata kuma ya zuba mata zazzaɓi mai zafi.
HAU; Jambaɗe (Tana nufin ƙurajen da ke fitowa a hammata masu zafi sosai)
Abuja Geographic Information System (AGIS) - Hukumar Tsara mahalli Ta Abuja
Abundance, Fortune - A turance tana nufin falala.
Misali; Akwai ɗimbin falala a cikin ambaton Allah.
HAU; Falala (Tana nufin alkhairai da dama)
Abundantly - A turance tana nufin birjik.
Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa.
HAU; Birjik (Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa)
Academic Staff Union Of Polytechnics (ASUP) - Ƙungiyar malaman manyan makarantun fasaha
Academic Staff Union Of Secondary Schools (ASUSS) - Ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandare
Academic Staff Union of Universities (ASUU) - Kungiyar Malaman Jami'a