Category: Juna biyu (ciki)

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin koyar da ilimin rainon ciki (juna biyu) a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hanu.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koya ko koyarwa.

  • Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Yadda Zubar Jini Yake Bayan Haihuwa

    Mahaifar Mace wato “Uterus” a sanda ta ɗauki ciki babu wani guri a jikin halittar ɗan adam da jini ke kai-komo ba tare da ƙaƙƙautawa ba irin wannan gun…. Saboda ƙoƙarin jiki don ganin ya samarwa da abinda ke cikin iska, jini, abinci da kyakkyawan yanayi. Guri ne da ake kira “No go Area” in dai da sunan wargi ne, saboda ko ya hatsari ya faru ana iya shiga uku.

    A duk minti ɗaya na agogo wato sekons 60 sai jini adadin Milimeter 800 zuwa dubu (1liter) ya shiga mahaifa ya fita. Wato dai kwatankwacin ledar pure Water 3 zuwa 4 na jini a duk minti. Shi ko jini baki ɗaya a jikin mutum an yi ƙiyasin ba ya wuce lita 5. Ka ga kenan a minti biyar kacal duk adadin jinin da ke jikin mutum ke shiga ya fita daga cikin Mahaifa. 

    Toh wannan ne yasa ko ya mace ta haihu jini ya ɓalle minti 4 zuwa 5 kacal ta mutu ta gama. Abun ba ya buƙatar ɗaukar lokaci, domin kafin a ankara an yi ta an ƙare. Shi yasa zubar jini bayan haihuwa da ake kira post partum hemorrhage ke kashe mata a karkara da birane ba ji ba gani, domin ko kuna raye a inda manyan asibitoci suke jinkiri kaɗan na abin hawa, ko shawarwarin ya za ai, ko cinkoso a hanya na iya kawo mutuwa ɓagatatan. 

    Toh yanzu Mace masu ciki sun saka kansu cikin wata musiba ta shan wani ruwa da suke wa laƙabi da “RUWAN NAƘUDA” ko a sakaya a riƙa faɗin “RUWAN ADDU’A”. Da ake karɓarwa mata a ba su su sha da sunan naƙuda ta zo musu a gurguje su haihu nan da nan abinda muke kira “PRECIPITATE LABOR.” 

    To alal haƙiƙa ku sani wannan ba wani ruwa ba ne illa ruwan musiba, ruwan guba, ruwan ta-da zaune tsaye, wallahi, wallahi, wallahi duk macen da ke marmarin tafiya lahira a dalilin haihuwa, ko take da burin ta sha da ƙyar tare da ja wa mijinta da iyayen ta asarar manyan kuɗaɗe ba tare da shiri ba, ko take da burin daga haihuwa ɗaya kar ta kuma har abada…

    Toh ta je a ba ta wannan ruwan ta riƙa sha, tunda Allah ya ba ku hankali don ku yi tunani amma sam kun mai da ƙwaƙwalenku tamkar tsumma. Kowanne tarkace yanzu kawowa ake mata su kuma su ɗiba babu lissafi. Shi wancan ruwan wasu muggan sinadarai ake sa mishi masu aiki irin na “Okzitosin” da nan da nan ke sa mahaifa ta fara harbawa tana jijjiga domin juye abinda ke cikinta, tana fisga tana talewa ƙarshe musibar da ake shiga FASHEWAR MAHAIFA yake haddasa wa inda nan da nan Mace kan fita hayyacinta, ta nufi lahira.

    Amma masu ba da irin wannan ruwan wasu ma iyayen yaran ne ke kawo musu. Sun kashe ‘ya’yansu ba tare da sun san su ne suka kashe su ba, sai dai a ce ta haihu amma jini ya ɓalle Allah ya yi mata rasuwa. Karya ne ku kuka kashe ta, kuma akwai shari’a gaban Allah. Kun ba ta abinda ba ku da ilimi kansa, kun ƙi kuma saurarar masana ku ji jan hankalin da suke game da irin wannan muggan al’adun.

    A ƙalla na sami mata uku da suka mutu a wannan tsakanin dalilin shan wannan ruwan naƙudar. Sannan na sami mutum 2 tsakanin nan ‘ƴar shekara 17 da ƴar 21 wanda suka sami fashewar mahaifa, duk da ba su mutu ba sun sha da ƙyar to amma dai hakan na nufin ba su ba kuma ɗaukar ciki ballantana su haihu a duniya, in mahaifa ta fashe ba batu ne a ɗinke ta ba, ta riga ta yi condemn.

    Kuma abin takaici duk jariran nasu sun mutu tun a ciki, shikenan in ba mazajen ƙwarai ba ne shin wa zai zauna da macen da ba zata iya haihuwa ba a irin wannan rikitaccen zamanin namu? Sabuwar amaryar shekara ɗaya a ce ka gane ba ita ba kuma haihuwa dole sai kai shirin kuma sabon aure in kana son haihuwa. 

    Toh wannan ba shi ba ne ma ƙarshen damuwar, ba su ba kuma iya riƙe fitsari, yanzu rayuwarsu za ta dauwama ne da robar fitsari a jika, hanyar kashi ta ɓulle ta dubura ta haɗe da farji. Tsabar wauta da rashin hankali, yarinyar da ko haihuwar fari ba ta yi ba amma da zarar ta sami juna biyu shikenan anta mata aiken abubuwa iri-iri ana ta sha, wannan maganin zaƙi, wannan maganin ciwon mara da dai sauran su.

    Ya kamata idon ya buɗe ku gane me duniya take ciki, kar ki laminci ganganci da rayuwarki. Lallai mu hankalta. Babban abin damuwar har ‘yan boko ko matan da kake ganin suna da ilimi su ma sukan auka cikin irin wannan ɗebe-ɗeben, a haka na sami mace me Masters amma ta je wai an ba ta maganin fibroid a Islamic CHEMIST. An ce idan ta sha zai narke, ƙarshe ga shi fibroid bai narke ba dukkan mararta ta zazzage.

    Dole aka cire mahaifar aka zubar, sannan ba ita ba kuma haihuwa, sannan mafitsararta “Bladder” ta fashe ba za ta gyaru ba, fitsari yanzu ta cikin farjinta yake fita, haka zalik kashi ma wani na fita ta duburarta wani kuma na biyo ta cikin farjinta duk. Yanzu me ya fi wannan tashin hankali, kin je kin kashe kuɗi kin illata kanki a banza da wofi.

    Hakance dai ke faruwa a fannin breast cancer, mace na fama da ciwon nono amma taita biye-biyen masu magunguna a loko suna karɓe mata kuɗi, ba za ta je asibiti ba sai abu ya gama lalacewa nono ya fara wari, in cancer ta gama yaɗuwa inda sai de mutuwa kurum. Don haka Lallai Yan Uwa Mata ku yi hattara, lafiya ta wuce wasa wallahi in kunne ya ji……

    Karanta Yadda Hawan Jini Yake (HYPERTENSION)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hanyoyin Shayar Da Jaririn Da Mahaifiyarsa Ta Rasu

    Hanyoyin Shayar Da Jaririn Da Mahaifiyarsa Ta Rasu

    IDAN MAHAIFIYAR JARIRI TA RASU KUMA BABU HALI NA SIYAN MADARA TA GWANGWANI (FORMULA MILK) ZA KU IYA BIN WAƊANNAN HANYOYIN DOMIN SHAYAR DA JARIRIN:

    1. Samun uwa mai shayarwa: A nemi wata uwa da take shayarwa domin ta taimaka ta shayar da jaririn. Wannan ɗabi’a ce da ta dace da shari’ar Musulunci da al’ada.

    2. Madarar dabbobi: Idan babu uwa mai shayarwa, ana iya yin amfani da madarar shanu ko akuya, wacce aka tafasa ta domin kashe ƙwayoyin cutar da suke cikinta, sa’annan a gauraya ta da ruwa mai tsabta (dilution) domin samun sauƙin narkewarta a cikin jaririn.

    3. Yin dabarun zuwan ruwan nono: Mace tana iya neman izinin mijinta domin ta yi amfani da dabarun da ruwan nononta zai zo (induced lactation), domin ta shayar da jaririn.

    Karanta Dalilan Da Ke Sa Zubar Ruwan Nono Alhalin Babu Ciki Ko Goyo
    Edita@rumasau-kallamu

  • Dalilan Da Ke Sa Zubar Ruwan Nono Alhalin Babu Ciki Ko Goyo

    Dalilan Da Ke Sa Zubar Ruwan Nono Alhalin Babu Ciki Ko Goyo

    Abin da yasa na sake yin wannan rubutun shi ne ganin yawan tambayoyin da ‘yan-uwa mata suke ta yi a kan matsalar a kullum.

    Zubar ruwan nono babu ciki ko goyo yana faruwa ne saboda hauhawar sinadarin prolactin a cikin jikin mace. Akwai wata ƙaramar jaka (gland) wacce take maƙale a jikin ƙasan ƙwaƙwalwa, wacce ake kira “pituitary gland’, ita ce take samar da sinadarin prolactin ɗin.

    Idan jakar tana samar da sinadarin prolactin fiye da yadda jikin mace yake buƙata, to, shi ne hauhawar sinadarin prolactin wanda ake kira “hyperprolactinemia” a likitance. Idan kuma jakar tana samar da sinadarin prolactin ƙasa da abinda jiki yake buƙata, to, shi ne “hypoprolactinemia”.

    Idan kuwa prolactin yana zubowa daidai da halin da jikin mace yake buƙata, to, shi ne “normal physiological prolactin level”. Magana ta gama-gari ita ce, adadin yawan sinadarin prolactin da ake buƙata a jikin mace, bisa ma’aunin ɗakin binciken kimiyya (laboratory), shi ne:

    1. Macen da ba ta da ciki (non-pregnant woman): 25 micrograms per litre (mcg/L).

    2. Macen da take da ciki (pregnant woman): daga 80 zuwa 400 mcg/L.

    3. Macen da take shayarwa: daga 200 zuwa 400 mcg/L.

    NAU’IN RUWAN NONON DA YAKE ZUBO WA MACE SAKAMAKON HAUHAWAR SINADARIN PROLACTIN

    Idan mace tana da matsalar hauhawar sinadarin prolactin, to, ruwan nonon da zai riƙa zubo mata zai kasance kamar haka:

    1. Launi (colour): launinsa zai iya zamowa fari (whitish), ko garai-garai (clear), ko ɗorowa (yellowish).

    2. Kauri (texture): zai iya zamowa maras kauri (watery), ko mai danƙo (sticky).

    3. Yawan zuba (discharge frequency): zai iya zamowa yana zuba a kai-a kai (continuously), ko lokaci-lokaci (intermittently), ko sai an matsa (when nipple is squeezed).

    4. Ɗanɗano (taste): zai iya zamowa mai ɗanɗanon zaƙi-zaƙi (sweetened), ko gishiri-gishiri (salty), ko maras ɗanɗano (tasteless).

    YADDA HAUHAWAR SINADARIN PROLACTIN YAKE HANA MACE ƊAUKAR JUNA BIYU

    Yawanci mace mai hauhawar sinadarin prolactin takan kasa ɗaukar juna biyu. Dalili shi ne sinadarin yana haifar da abubuwa kamar haka:

    1. Hana mace iya saka ƙwan haihuwa (suppression of ovulation): hauhawar sinadarin prolactin yana hana jikin mace zubo da ruwan gonadotropin releasing hormones (GnRH) daga jakar thalamus wacce take cikin ƙwaƙwalwa (hypothalamus).

    Shi kuma GnRH dole sai ya zubo sa’annan jakar sinadarin pituitary wacce take cikin ƙwaƙwalwa za ta zubo da sinadarin luteinizing hormone (LH), wanda yake da matuƙar muhimmanci wajen bai wa mace damar saka ƙwan haihuwa (ovulation) da kuma yin al’ada yadda ya kamata (normal menstrual cycle).

    2. Rikicewar al’ada (irregular menstruation): hauhawar sinadarin prolactin yana haifar da rikicewar al’ada ko kuma ɗaukewarta gaba ɗaya. Hakan zai iya sanya ɗaukar juna biyu ya yi wahala.

    3. Rikita ayyukan jakar ƙwan haihuwa (interference with ovarian function): hauhawar sinadarin prolactin yana hana jakar kwan haihuwa ta yi aiki yadda ya kamata ta fuskar samar da ƙwan haihuwa da kuma yin girmansa.

    4. Rashin samar da yanayi mai kyau a mahaifa (impaired corpus luteum function): koda juna biyu ya samu, kuma ƙyanƙyasasshen ƙwan haihuwa ya shige cikin mahaifa, to, akwai buƙatar kyakkyawan yanayi domin rayuwar ɗan-tayi. Hakan zai yiwu ne idan jikin mace yana samar da sinadarin progesterone isasshe. Shi kuma progesterone ba zai samu ba sai idan halittar corpus luteum tana da kyau.

    A taƙaice, idan mace ta ga ruwan nono yana zubo mata alhalin babu ciki ko goyo, kuma ta daɗe sosai da yin yaye, to, ta je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da daidaiton zubar ruwan sinadarin prolactin ɗinta. Amma akan samu matan da ruwan nononsu ba ya ɗaukewa kwata-kwata, kuma hakan ba ya hana musu ɗaukar juna biyu, sai dai ba su da yawa a cikin mata.

    ABUBUWAN DA SUKE HAIFAR DA HAUHAWAR SINADARIN PROLACTIN

    Su ne:

    1. Tsirowar ƙari a jikin jakar sinadarin pituitary (prolactinomas): wannan ƙari ne amma ba na cancer ba (noncancerous tumour) wanda yake sanya zubar ruwan sinadarin prolactin. Abubuwan da suke haddasa fitowar ƙarin prolactinomas su ne gado, hauhawar sinadarin estrogen, juna biyu, wahalhalun bayan haihuwa, cututtukan jakar sinadarin pituitary.

    2. Laulayin amfani da magunguna (medication side effects): yin amfani da magungunan cututtukan ƙwaƙwalwa (antipsychotics), ko magungunan rage damuwa (antidepressants) ko magungunan hawan jini (antihypertensives), ko magungunan hana tashin zuciya da amai (antinausea), duk suna iya haifar da hauhawar sinadarin prolactin.

    3. Rashin yin aikin jakar sinadarin thyroid yadda ya kamata (hypothyroidism): wannan yana faruwa ne sakamakon yin tiyata a jakar thyroid, ko ƙarancin sinadarin iodine, ko gado, ko laulayin hasken na’urar hoton x-ray, ko nisan shekaru.

    4. Daɗaɗɗen ciwon ƙoda (chronic kidney disease): idan ƙoda ba ta yin aikinta yadda ya kamata na sarrafa sinadarin prolactin, to, akwai yiwuwar ya hauhawa ya haddasa zubar ruwan nono.

    5. Ɗaukar juna biyu da shayarwa (pregnancy and breastfeeding): samun juna biyu da shayarwa suna sanya hauhawar sinadarin prolactin domin samun isasshen ruwan nono ga jariri. Wasu matan sukan yi tazarce kamar yadda na faɗa a sama. Ma’ana, ko da sun yi yaye, to, sinadarin prolactin ɗin ba zai sauka ba. Don haka za su cigaba da ganin zubar ruwan nono har su sake samun wani cikin. Wannan ba matsala ba ne Insha Allah.

    6. Damuwa da kuma ayyukan motsa jiki mai tsanani (stress and excessive physical exercise): idan mace tana yawan shiga cikin yanayin damuwa, to, akwai yiwuwar sinadarin prolactin ɗinta ya hauhawa. Haka nan idan tana yin ayyukan motsa jiki mai yawa.

    7. Hauhawar sinadarin prolactin wanda aka kasa gane asalinsa (idiopathic hyperprolactinemia): akwai lokacin da mace za ta sami hauhawar sinadarin prolactin, kuma duk binciken da za a yi, amma daga ƙarshe sai a kasa gane abinda ya haddasa shi.

    DALILIN DA YASA HAUHAWAR SINADARIN PROLACTIN YAKE DA WUYAR MAGANI

    Mata masu yawa suna yin ƙorafin cewa sun yi amfani da magunguna da yawa har sun gaji, amma matsalar zubar ruwan nono ba ta sake su ba. Lallai warkar da matsalar yana da wahala saboda dalilai kamar haka:

    1. Rashin iya gano ainihin abinda ya haifar da matsar (inability to diagnose the root cause): matuƙar likita bai yi binciken ƙwaƙwaf wajen gano abinda ya haifar da hauhawar sinadarin prolactin ba, to, zai yi wahala a magance ta cikin sauƙi. Za a yi ta magani daban kuma ciwo daban. Ma’ana, ya kamata a bibiyi dukkan abubuwan da na faɗa a sama ɗaya-bayan-ɗaya har a gano tushen matsalar.

    2. Girman ƙarin prolactinomas (tumour size): Idan fitowar ƙarin prolactinomas ne ya haifar da matsalar, to, girman ƙarin zai iya shafar saurin warkewa ko rashin warkewar matsalar. Ma’ana, idan ƙarin ƙarami ne, to, zai fi sauƙin warkarwa. Idan kuwa ya girma, to, sai an dage da shan magani. Ƙila ma sai an yi aikin tiyata.

    3. Amsar da jikin mace yake yi wa magani (medication tolerance): halittar jikin mutane ta bambanta, wani yana da saurin amsar magani, wani kuwa akwai wahalar amsar magani. Magungunan da aka fi yin amfani da su wajen magance zubar ruwan nono su ne bromocriptine ko cabergoline. Jikin mace ya bambanta wajen saurin amsa ko rashin amsarsu.

    Karanta Abubuwan Da Ke Haddasa Rashin Zuwan Al’ada (AMENORRHEA)
    Edita@rumasau-kallamu

  • Zubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu

    Zubar Da Ruwa A Farko Da Kuma Ƙarshen Juna Biyu

    Zubar da ruwa ga farkon ciki da kuma ƙarshen ciki musamman daga wata 8 zuwa haihuwa ba cuta ko matsala ba ce ga mace.

    Lokacin da mace ta samu ciki wasu matan na samun wannan zubar ruwan saboda canje-canje da jikin su ya samu a karon farko, da kuma matan da cikin su ya kusa haihuwa sukan samu wannan alamun na ganin ire-iren waɗannan ruwan a gabansu suna zuba to wannan ba sunanshi da akwai infection ko matsala ba.

    Normal vaginal discharge during pregnancy is called leukorrhea and is thin, white, milky, and mild smelling. Leukorrhea is normal and nothing for you to worry about.

    Sai dai daga lokacin da aka ga ire iren waɗannan ruwa na zuba a tsaya a fahimci kalar su don tantance irin ruwan da ke zuba wanda zai jadda ba na matsala ba ne. Lokacin da aka ga irin wannan ba a buƙatar amfani da Tampons ga mace mai tsohon ciki don kaucewa shigar ƙwayoyin halitta na micro organism.

    Karanta Menene Ƙaiƙayi? (ITCHING)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Shayar Da Jariri Nonon Uwa Zalla (EXCLUSIVE BREASTFEEDING)

    Shayar Da Jariri Nonon Uwa Zalla (EXCLUSIVE BREASTFEEDING)

    Shayarwa aiki ne da Allah SWT ya tsara halittar jikin mace ta riƙa yinta a duk lokacin da ta haihu, domin samar da ingantaccen abinci ga jariri da kuma nuna masa ƙauna. Kadan daga cikin muhimman abubuwan da ya dace mu sani game da shayarwa su ne:

    1. Amfaninta ga jariri (breastfeeding benefits to the baby):

    Shayarwa tana samar da ingantaccen abinci ga jariri daidai da buƙatar jikinsa, domin yin girma yadda ya kamata. Nonon uwa yana ƙunshe da ƙwayoyin halitta masu bayar da kariya ga jikin jariri (antibodies) don su tsare shi daga cututtuka iri-iri. Sa’annan tana kare jarirai daga hatsarin mutuwa farat ɗaya (Sudden Infant Death Syndrome – SIDS).

    2. Amfaninta ga uwa (breastfeeding benefits to the mother):

    Shayarwa tana taimakon jikin mai-jego wajen saurin murmurewa daga ciwon haihuwa (faster postpartum recovery), ta hanyar sanya mahaifarta ta koma yadda take kafin samun juna biyu. Sa’annan tana matuƙar rage hatsarin kamuwa da cututtukan daji na nono (breast cancer), da mahaifa (uterine cancer), da jakar ƙwan haihuwa (ovarian cancer). Bugu da ƙari, tana ragewa mace hatsarin kamuwa da cutar rashin ƙarfin ƙashi (osteoporosis) wanda yakan iya samunta a lokacin ɗaukewar al’ada (menopause).

    3. Ingantacciyar shayarwa ta hanyar sanya jariri ya kama kan nono sosai (establishing good latch):

    Ya kamata uwa tana rungume jaririnta da kyau kuma ta tabbatar kewayen nan mai launin duhu na kan nono (areola) ya shiga cikin bakin jariri a lokacin shayarwa, ba kan nonon (nipples) kawai ba. Idan baki iya ba, to, ki nemi ‘yan uwanki su koya miki. Hakan zai kare mace daga matsalolin tsagewar kan nono (nipples crack).

    4. Shayarwa a kai-a kai (breastfeeding on demand):

    Jarirai sukan sha nono a kai-a kai, don haka uwa ta tabbatar da cewa tana bai wa jaririnta nono a ƙalla bayan duk awa 2 zuwa 3. Idan yana buƙata ma kafin wannan lokacin, to, ta ba shi. Hakan zai kare ta daga matsalolinmu ciccikowar nono (breast engorgement).

    5. Isasshen ruwan nono (breast milk sufficiency):

    Ruwan nono yana taruwa ne gwargwadon yadda mace take ƙoƙarin shayarwa tare da cin wadatacce kuma ingantaccen abinci. Ma’ana, idan mace tana shayarwa akai-akai, to, ruwan nononta zai yi saurin taruwa. Idan kuma ba ta shayarwa akai-akai, to, za ta fuskanci ƙarancin ruwan nono.

    6. Matsalolin shayarwa (breastfeeding challenges):

    Yawancin mace takan fuskanci matsaloli a lokacin shayarwa, kamar, ciccikowar nono, tsagewar kan nono, ƙarancin ruwan nono, ciwon nono, da sauransu. Idan hakan ya faru, to, a je asibiti domin a yi abinda ya kamata.

    7. Matse ruwan nono (breast milk expression):

    Idan nonon mace yana samar da ruwan nono fiye da buƙatar jaririnta, to, za a iya fuskantar matsalar ciccikowar nono, wanda zai haifar da zazzaɓi. Domin kaucewa hakan, ana iya matsewa a cikin mazubi mai tsabta domin ta bai wa jariri a lokaci na gaba. Ga matan da suke zuwa wurin aiki a ofisoshi kuwa, suna barin jariransu a gida, to, shikenan sai a riƙa bai wa jariran ruwan nonon da suka matse. Ana yin matsewar ne da hannu (hand expression), ko da na’urar matsewa (breast pump), wanda ba duk mata ne suka sanshi ba.

    Daga ƙarshe ya kamata musan cewa shayarwa abu ce ta halitta (natural). Idan mace tana yinta bisa ƙa’ida, to, bai kamata ta ji zafi ba. Idan mace tana Shayarwa kuma tana jin zafi to yana nuna cewa akwai matsala, don haka sai a yi ƙoƙarin gane ta kuma a magance ta.
    Karanta Menene Ƙaiƙayi? (ITCHING)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Zubar Jini A Cikin Wata Uku Na Farkon Samun Juna Biyu (FIRST TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Zubar Jini A Cikin Wata Uku Na Farkon Samun Juna Biyu (FIRST TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Idan mace tana da juna biyu, takan sami sauye-sauyen zubar sinadarai (hormones) a cikin jikinta. Wannan zai iya sanya mata zubar jini. Mai yiwuwa ne ta riƙa ganin ɗigon jini ba mai yawa ba a pant ɗinta. Irin wannan jinin bai cika zama matsala ba. Amma idan ya yi yawa sosai, to, ya kamata ta tafi asibiti domin ta ga likita.

    Abubuwan da suke haifar da zubar jini a first trimester sun haɗa da:

    1. Implantation, wato lokacin da ƙyanƙyasasshen ƙwai na haihuwa yake ƙoƙarin maƙalewa a jikin mahaifa.

    2. Cervical polyp, wato zazzagowar mahaifa

    3. Jima’i ko kuma sanya wani abu a cikin farji wanda zai iya haifar da samun rauni ko kujewa a jikin fatar farji

    4. Miscarriage, wato lalacewar ciki

    5. multiple babies, wato juna biyu mai ɗauke da ‘ya’ya fiye da ɗaya

    6. Ectopic pregnancy, wato juna biyun da yake zama a bayan mahaifa maimakon cikin mahaifa

    7. Molar pregnancy, wato cikin karya ba na gaskiya ba

    8. Subchorionic hemorrhage, wato zubar jinin da yake faruwa idan mabiyiya ta rabu da jikin mahaifa

    9. Infection, wato kamuwa da wasu ƙwayoyin cututtuka.

    SANNAN ZUBAR JINI A CIKIN WATA UKU NA BIYU KO KUMA UKUN ZANGO NA ƘARSHEN SAMUN JUNA BIYU (SECOND AND THIRD TRIMESTER HAEMORRHAGE)

    Zubar jini a lokacin da ciki ya shiga second trimester ko third trimester ya fi zama hatsari ga mai juna biyu, domin yana nuna cewa akwai wata babbar matsala da juna biyunta. Abubuwan da suke haddasa shi sun haɗa da:

    1. Cervix problems, wato matsalolin da suka shafi mahaifa kamar kumburi, tsiro, ko samuwar ruwan ciwo a cikin mahaifa.

    2. Placental abruption, wato rabuwar cibiyar jariri daga jikin mahaifa ko kuma rabuwarta daga jikin mabiyiya, da sauransu.

    ZUBAR JINI BAYAN HAIHUWA (POSTPARTUM HAEMORRHAGE)

    Wannan yana nufin zubar jini daga farjin mace bayan ta haihu. Hakan ba zai zama a cikin matsala ba sai idan ya kasance ya yi yawa, kamar a ce tana jiƙa pads guda biyu ko kuma fiye da biyu a cikin awa ɗaya. Abubuwan da suke haddasa shi su ne:

    1. Samuwar ƙari (tear) a farjin mace a lokacin haihuwa ko kuma samuwar rauni a jikin mahaifarta

    2. Fashewar wasu daga cikin jijiyoyin da suke kai jini zuwa cikin mahaifa

    3. Samuwar ƙwayoyin cuta a cikin mahaifa, da sauransu.

    Idan mace ta fuskanci zubar jini a ɗaya daga cikin lokutan da na faɗa a sama, to, ya kamata ta tafi asibiti ne domin a bincika a gane abinda ya haifar mata da matsalar. Daga nan za a ɗauki matakin da ya dace da irin matsalar da take da ita.

    A kowane lokaci ana shawartar mata masu juna biyu da su fara zuwa awo da wuri, kuma su guji shan magani idan ba likita ya ba su ba, domin a can ne za a buɗewa mace file wanda za a riƙa rubuta tarihin matsalarki, aune-aunen da aka yi mata, magungunan da aka ba ta, da kuma nasarori ko akasin haka da aka samu. Kun ga kenan idan maganin ya haddasa wata matsala, to, za a shawo kanta a cikin sauƙi.

    Don karanta Duhun Matse-Matsi [DARKNESS OF INNER THIGH] danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Abin Da Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa (AMNIOTIC FLUID)

    Abin Da Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa (AMNIOTIC FLUID)

    Amniotic fluid ruwa ne dake zagaye da jariri a cikin mahaifa wanda ke taimakawa yaron ya sami balance ta yadda ko faɗuwa mai juna biyu ta yi ta ruf da ciki, cikin ikon Allah shi jariri ba zai san me yake faruwa ba ma ballantana abun ya shafe shi.

    Shi wannan fluid ɗin yakan haɗu da fitsarin da babies ɗin kan yi a cikin mahaifa lokacin da suka kai sati 25weeks sukan kuma fara shan wannan ruwan tun daga sati na 10-11 weeks na ciki, ko lokacin da fatar ƙwayar halittar kumatunsu cikin mahaifa ta fara rufe bakinsu. Dan haka dama sukan sha abinsu tun a ciki.

    Daga lokacin da ciki ya kai sati 20weeks duk wannan ruwan kusan yakan rikiɗe ya zamo fitsarin babies ɗin ya fi yawa. Yayin da ainisin ruwan amniotic ɗin da ke zuwa daga ƙodar baby ɗin ke kasancewa ɗan kaɗan kurum.

    ME YASA SUKE SHA WASU HAR HAKAN YASA SU MUTU?

    Kamar yadda na faɗa ainihin ruwan amniotic fluid dama suna shan abinsu tun a ciki kafin zuwan haihuwa domin shi ne ke ƙara ma huhun su (lungs) ƙwari. Abinda suke sha ya wahal da su yayin haihuwa koma su rasa ransu muna kiransa da (MECONIUM).

    Meconium wato na nufin kashin farko da suke fara yi a ciki yayin artabun naƙuda, idan ya haɗu da ruwan fluid ɗin suka haɗiya shi ke musu illa yake shiga ƙofofin numfashinsu.

    Wanda kamata ya yi sai bayan an haihu za su yi wannan kashin koma kada su yin kwata kwata sai bayan an fara ba su nono. Bisa larura amma idan aka samu doguwar naƙuda musamman haihuwar fari ko kuma matsatsi yayin haihuwa shi ke jawo su yi kashin kuma su sha abinsu musamman yayin da suka ja numfashin farko suka fara fitowa yayin haihuwa.

    Sannan hakan ya fi shafar yaran da suka jima suka ɗau sati 37 zuwa 41 a ciki ko sati 42. Wannan shi ne abinda ke faruwa, kun ga kenan ba abu ne da yake wajibi a a hana faruwarsa ba sai dai ana iya daƙilewa idan ka ba iyalin ƙwarin guiwa zuwa awo tare da kulawa yayin goyon ciki.

    Danna nan don karanta Hatsarin Amfani Da Mayukan Hasken Fata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mutuwar Mata Masu Jego

    Mutuwar Mata Masu Jego

    Duk mai jegon da bayan haihuwa ko da da kwana 1 ne ballantana a ce an kwana uku da haihuwa ta ji alamun zazzaɓi, ko ciwon kai, ko ciwon ƙirji da sauransu. Toh lallai ta sanar a hanzarta kai ta asibiti kar a kuskura! ina maimaitawa kar a kuskura! a ce ai ba komi ta sha paracetamol ko a ce za a nemo Maganin ulcer kurum a ba ta babu komi. Hakan tamkar tallafawa me ƙoƙarin kashe kai ne.

    Sau tari a yanzu akan zo taron suna me jego ba lafiya sosai, amma tai ta juriyar banza saboda cutar da kai, alhalin ƙwayoyin cuta sun sami hanya ta dalilin jinin nifasi da ke fita sun shiga cikin jijiyoyin jininta suna haifar matan da puerperal fever da zai kai ta ga “Puerperal sepsis” yai ta cinta a jika tana zaton abu ne da zai zo ya shige ƙarshe sai gawa.

    Galibi wannan shi ke kashe masu jego in kika cire batun zubar jini bayan haihuwa, musamman bayan kwana 3 da haihuwa zazzaɓin ya fi somawa domin incubation period ɗin kenan na ƙwayoyin cutar, shi yasa wata sai bayan an yi taron suna ana murna kurum a ji an wayi gari wance ta mutu, mutuwa me duka.

    Kada a taɓa ɗaukar hakan da wasa, ko baka da kuɗi ranto ka kai ta asibiti, matuƙar me jego tace ba ta lafiya ƙasa da kwana 40 da haihuwa kar ai wasa.

    Ku kuma ƙananun jami’an lafiya da ke bibiyar rubutuna kodayaushe ku sa wannan cikin kanku, kar me jego tace:-

    – Tanajin kasala,
    – Kanta na ciwo
    – Zazzaɓi
    – Fitar farin ruwa ko jini me ɗoyi
    – Ciwon Mara
    – Zafin fitsari
    – Ko har yau girman cikinta yana nan da sauransa kamar ba ta haihu ba ko kamar da sauran jariri a ciki

    Ku ce za ku ba ta maganin rage zugi kurum ku sallame ta, ko kuwa ku ce za ku yi gwajin Malaria don haka in ya nuna Negative sai dai ku ba ta pain reliever, ko kuma in aka yi kiciɓis ga Malaria positive ku ce iya Malaria ke damunta.

    Kuke buɗe tunaninku sosai for differentials diagnosis, kada a ce komai in ya haɗu da ciwon kai kurum Malaria ko Bp, ko Typhoid ne, duk macen da kuka ji ta yi muku ƙorafin ɗaya ko biyu daga waɗancan alamun na sama kai tsaye ku yi treating ɗinta for puerperal infection muddin me jego ce, domin hakan na da alaƙa da haihuwarta. Mai jego ita ce wadda ba ta wuce kwana 42 da haihuwa ba. Don haka ko da ta yi wata da haihuwa duk da haka tana cikin hatsari har na zubar jini.

    Ya rage naku ku je ku yi biyayya ga manyanku da kuke aiki ƙarƙashinsu, su ilmantar da ku magungunan da alluran da ake amfani da su wajen addressing din matsalar, don ba kowanne antibiotics ake ba su ba, in su ma ba su sani ba toh ku je sahihan journals na obstetrics and gynecology ku yi binkice ku ilmantar da kanku ba wai google ba. Wannan lamari ne da kan zamo Medical Emergency.

    Wannan tasa ko ɓari mace ta yi sai an ba ta magungunan antibiotics, haka ma bayan haihuwa domin riga-kafi koda ƙwayoyin cutar sun maƙale to zai magance su kafin su yi ƙarfin da za su shiga jini tunda ido bai iya ganinsu. AMMA wasu marasa tunanin cikin mata ba sa sha, ko in sun fara sai su bar sha tun kafin ya ƙare, toh masu irin wannan ku kuka da kanku, Domin ba zubar jini ne kurum abin tsoro ba bayan haihuwa.

    In muka kiyaye wannan za mu taimaka wajen rage wasu mace-macen na masu haihuwa.

    Allah yasa mu dace.

    Danna nan don karanta Rashin Kogon Al’aura Ga Mata

    Edita@rumasau-kallamu

  • Cikin Molo (Molar Pregnancy)

    Cikin Molo (Molar Pregnancy)

    Cikin Molo wani nau’in alamun juna biyu ne da wasu cikin mata kan samu kansu da shi wanda kuma a zahiri gaskiya ba ciki ne na haihuwa ba kamar yadda suke tsammani duk da abun ya tattara dukkan alamomin samuwar ciki na zahiri.

    Bisa ƙididdiga a dukkan mata dubu “1000” masu ciki akan sami guda ɗaya “1” ya zamto cikin molo ko cikin ƙarya, wanda 999 su ne ke ɗauke da ciki me ƙunshe da jariri. Viable Pregancy.

    SHIN YA CIKIN YAKE, ME KE JAWO SHI KUMA ?

    Wani cikin ne da ke faruwa sakamakon tangarɗar ƙwan haihuwa wanda wata ƙwayar halitta da ake kira TROPHOBLAST a turance da aikinta samarwa da jariri sinadaran abinci da rayuwa a cikin mahaifa kan rikiɗe ta hau girma a karan kanta ya zamto ta yi girman da ya mamaye cikin mahaifa ta samar da ƙaton tsiro me ƙunshe da ruwa ko tsauri WATO cysts ko TUMOR sakamakon waɗancan ƙwayayen haihuwa marasa rai ko inganci da suka shigo cikin mahaifar mace daga kututar ƙwayaye wato OVARY.

    Wanda wannan yasa a farkon samuwar abun duk wani alamu na ciki mace za ta ji ta fara fuskantarsa kama daga tashin zuciya, zazzaɓi ba me tsanani ba, rashin son warin abu, zubar da miyau, kasala da sauransu. Wani abu ma da za ta yi gwajin ciki na fitsari ko jini kai tsaye za ta ga ya nuna POSITIVE alamun ta samu ciki saboda HcG ɗin is High.

    Kuma zai cigaba da girma kamar yadda ciki ke girma a hankali har a ga tasowar cikin. Shi yasa da yawa in aka ce musu ba ciki ba ne ba sa yadda. Wasu sai a yi ta fama da su su ƙi, har su riƙa kiransa da kwantacce a lokacin da suka ga girman ya dakata. Ko kuma lokacin watannin haihuwa ya zo ya wuce har sun ƙara shekara sai ka ji ana kwantaccen ciki.

    SHIN DUK IRI GUDA NE KO YA RARRABU ?

    Ya kasu rukuni biyu ne kacal; akwai COMPLETE wato me gaba ɗaya, da kuma INCOMPLETE me ragayya.

    RUKUNI NA FARKO [COMPLETE]

    A irin wannan ainihin shimfiɗar cikin mahaifa wato (uterus layer) inda jariri ke kwanciya ciki ya zauna ita kanta shimfiɗar takan rasa ingancinta ma’ana takan tattare ta murmuɗe ta yi tudu da ƙwari, domin daga cikin ƙwayoyin halittun gado chromosomes 46 da Maxa suke saki wato 23 daga mace, 23 wanda ke ba da total na 46.

    Akan samu Chromosome ɗin mace ne kurum zai iya zamowa jariri wato viable egg. Shi MIJIN empty sperm cell ya saki. WANDA tunda kuwa sai da ƙwan namiji ciki zai tabbata amma ga shi sai mace ce ke da normal egg toh irin wannan ke sa zubin shimfiɗar mahaifar ya jirkice shi kuma wancan tumor ɗin na trophoblast sai ya yi amfani da wannan viable egg na macen ya girma ya cika cikin mahaifar mace (uterus). A riƙa ganin kamar ciki gareta. kuma ko yaushe in an duba HCG za a ga high kamar dai mai ciki, yadda dai kuka ji na faɗa a baya.

    RUKUNI NA BIYU [PARTIAL]

    A partial shi kuma cikin 23 pairs ɗin na chromosome MACE tana sakin normal egg tare da 1 pair na chromosome, shi kuma NAMIJIN sai ya saki 2 pairs na chromosome maimakon 1 wato shi kaɗai ya samar da 46pairs maimakon 23pairs wanda in ka haɗa da 23pairs ɗin na matar sun tashi 69 pairs maimakon a sami total na 46.

    Hakan shi ke sa ga cikin ya shiga akwai ciki na gaske ba tumor ba toh amma fa ba zai ta6a rayuwa ya zama cikakken jariri ba, kuma a daidai wannan lokacin ga growth ɗin trophoblast ɗin da ya kusa cika mahaifar mace, don haka nan ma za a yi ta ganin HCG high amma fa ba zai taɓa zama ciki ba.

    Sai dai a PARTIAL ɗin akwai kuma Partial me Normal Karyotype wato chromosome ɗin daidai ne kowa ya samar da 23 ana da total 46 amma kuma ga trophoblast ya samar da tumor kusa da jaririn. To a irin wannan ne yakan girma ya zama ciki a haifi jariri koda kuwa bai da cikakkiyar lafiya.

    A irin wannan ne ake jin hausawa na cewa kwantaccen wance dai ya tashi, duk da cikin kan shafe shekaru. Amma gaskiya ba a cika samun irin wannan ɗin sosai ba, sai dai dama irin wannan tun a ultrasound ake iya bambance shi.

    Domin karanta Cutar Maƙoƙo dannan nan

    ME KE JAWO HAKAN LIKITA ?

    Abubuwan da kan jawo haka sun ƙunshi;

    1. Akwai shekaru musamman macen da ke kusa ko kuma ta haura shekaru 35

    2. Kasancewar mace ta taɓa samun hakan a baya, akwai yiwuwar ƙara maimaitawa

    3. Sai rashin daidaiton sinadaran halitta (hormonal imbalance)

    Wannan matsala musamman a me COMPLETE MOLAR likitoci kan kalle ta a matsayin ɗaya daga cikin cuttukan cancer na mahaifa wato choriocarcinoma. Duk abin da ke iya ƙara girma a karan kansa tabbas ko dai ya zamo cancer ko kuma benign tumor wato wanda ba cancer ba amma in aka bar shi zai iya zama cancer.

    Domin idan har bayan an cire cyst ɗin kuma HCG ya cigaba da tsayawa High akwai zargin ya riga ya zama cancer dole a ɗora mace a kan CHEMOTHERAPY, kuma ana warkar da cancer ɗin cikin ikon Allah in an farga da wuri.

    Idan kuwa aka bar shi to ka san cancer tana iya yaɗuwa zuwa wasu sassan kuma hakan ce za ta faru wanda a ƙarshe mace za ta iya mutuwa a dalilin cancer hanta ko huhu ko hanji alhalin tushen ciwon a mahaifa ne. Wannan tasa da zarar likita yace miki cikin MOLO ne to kar ki ɓata lokaci kurum a cire shi.

    ALAMOMIN CIKIN MOLO

    Alamomin sun ƙunshi;
    Ganin Fitar jini me duhu ta gaba
    Ciwon baya ko mara
    Ganin jini na fita kamar dunƙulen grapes fruits da kuma
    Matsanancin tashin zuciya da amai.

    WAƊANNE GWAJE-GWAJE AKE YI

    Akan yi gwajin jini domin duba hemoglobin level saboda tunanin ƙarancin jini, sannan a kuma duba HCG wato hormone ɗin juna biyu da kuma ultrasound scan.

    MATAKIN ƊAUKA

    1. Kai tsaye bayan tabbatar da molar pregnancy ne abin da ake kira Dayilteshin & kyuritaj wato manuwal bakyum Asfireshan SHI NE abin yi, a cire tissue ɗin baki ɗaya, domin barinsa ba zai taɓa zama jariri ba, dama ba ciki ba ne kuma ko da partial ne wanda ke ƙunshe da ciki shi ma ba girma zai ba.

    Bayan kuma an cire ɗin ba a kuma barin mace ta ɗauki ciki, a ƙalla sai bayan shekara. Saboda ana so a cigaba da auna HCG level ɗin lokaci lokaci har zuwa shekara bayan cire molar ɗin domin idan ya cigaba da zama HIGH kamar de akwai ciki to alama ce ta PERSISTENT GESTATIONAL TROPHOBLASTIC NEOPLASIA wato ya tabbata cancer. Don haka dole a yi maza a fara mata chemotherapy a kashe shi, in ba haka ba za ta yaɗu zuwa sauran organs, kunga ko hakan is deadly.

    2. Ko kuma idan dama mace ba ta da sha’awar ƙara haihuwa tana jin ta gama shi kenan sai a cire mahaifar baki ɗaya kurum. Duk da nan gaba kuma lokacin menopause in estrogen ɗinta ya yi low wasu suna samun hot flashes wato premenopausal symptoms wanda ake musu hormone replacement therapy to amma fa macen da ba ta da mahaifa ita ba za a yi mata wannan ba, domin zai zame mata matsala tunda ya ƙunshi estrogen alhalin ba ta da uterus. Progesterone only method shi ne therapy ɗin da za ta iya amfani da shi.

    Don haka ake son ko yaushe in likita ya tambayi mace wani abu to ba ɓoye-ɓoye ko da dangane da mu’amalar auratayya ne ta faɗa masa gaskiya ba a yi wa likita ƙarya ko da kuwa kina yi wa mijinki shi likita in aka yi masa ƙarya kanki kika cuta.

    Wannan shi ne molar pregnancy a taƙaice.

    Danna nan don karnta Saiƙo Ko Sanƙo

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Zubar Da Miyau Ga Mai Juna Biyu

    Zubar Da Miyau Ga Mai Juna Biyu

    Tsananin zubar da miyau ga mai juna biyu shi ne “ptyalism” ko “hypersalivation” a likitance. Ya fi faruwa a zangon wata 3 na farko (first trimester). Babban abinda yake haddasa shi shi ne sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai, kamar human chorionic gonadotropin (hCG) da oestrogen.

    Amma akwai wasu abubuwan da suma suna kawo shi kamar ƙwarnafi (heartburn), zazzaɓin safe (morning sickness), tashin zuciya (nausea), da shaƙar ƙamshi ko wari na wasu abubuwan da mai juna biyu ba ta buƙatarsu a wannan lokacin.

    Babban maganinsa shi ne tsabtar baki ta hanyar yawan yin brush ko asiwaki, tsabtace abinci, yawaita shan ruwa, yawaita shan abubuwa masu ruwa-ruwa, cin kayan marmari (fruits), da kaucewa wari ko ƙamshin duk wani abin da mai juna biyu ba ta so.

    Idan anyi hakuri, to, ptyalism yakan warkar da kansa.

    Danna nan domin karanta Matsalar Zubar Yawun Bacci
    Edita; Rumasa’u M. Kallamu