Category: Nasihohi

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin samar da nasihohi a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hanu.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa wajan ɗora nasiha ko saukewa

  • Maƙala Mai Taken: Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

    Maƙala Mai Taken: Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

    Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

     Na

     Abu-Ubaida SANI, Ph.D.

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    official@amsoshi.com | ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334

     Citation: Sani, A.-U. (2020, February 24–28). Zamani abokin tafiya: Tasirin kafafen sada zumunta ga tashintashinar Zamfara. Paper presented at the 4th National Conference on Zamfara Kingdom: Social and Political Transformation from the 14th Century to Date, Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Tsakure

     A yau, kafafen sada zumunta sun kasance wani ɓangare na rayuwar al’umma, musamman matasa. Suna da tasiri (mai kyau ko marar kyau ko duka biyu) a ɓangarorin rayuwa daban-daban da suka haɗa da zamantakewa da kasuwanci da ilmi da sana’o’i da mulki da shugabanci da makamantansu. La’akari da haka ne ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin haska fitilarsa domin ƙyallaro ko kafafen na da tasiri a kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara?

    Idan suna da , yaya nauin tasirin yake? Binciken na da manufar (i) bitar yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da (ii) nazartar tasirin kafafen sada zumunta kan waɗannan tashe-tashen hankula. Kasancewar Zamfara ɗaya daga cikin manyan daulolin ƙasar Hausa masu tsohon tarihi. Binciken ya yi amfani da Bahaushen rai domin jan akalarsa.

    An ɗora aikin a kan tunanin Bahaushe mai cewa: “kowane allazi da nasa amanu.” An bi manyan hanyoyi guda biyu domin tattara bayanai. Na farko shi ne hira da aka yi domin samun bayanan nau’ukan tashe-tashen hankulan daga tushe (ganau ko jiyau daga ganau). Na biyu kuwa, an bibiyi kafafen sada zumunta da sauran kafafen sadarwa na yanar gizo (intanet) domin ganin wainar da ake toyawa dangane da batun da ake magana kansa, tare da tattarowa da nazartar bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubuce da suka shafi manufar binciken.

    Binciken ya gano cewa, duk da ɗimbin amfanin kafafen sada zumunta, suna taka rawa kai tsaye ko a kaikaice wajen ruruta wutar tashe-tashen hankular jahar Zamfara. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da kira ga hukomomi da su fara tunanin yin wata huɓɓasa na bibiya da jagorancin al’amuran kafafen sada zumunta.

    Fitilun Kalmomi: Zamfara, Kafafen Sada Zumunta, Tashe-Tashen Hankula

    1.0 Gabatarwa

    Duk da kiran da Abubakar Ladan Zariya ya yi cewa: “Fitina Bacci take ba ta fita,” da kuma tofin Allah wadai da ya yi wa masu tado da ita,[1] wasu kam ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa. A ‘yan shekarun baya-bayan nan, musamman daga wajajen 2013 abin da ya yi sama, an ci gaba da samun tashe-tashen hankula nau’uka daban-daban. Tashe-tashen hankulan sun haɗa da garkuwa da mutane da kai farmaki kan al’umma musamman mazauna karkara da sace-sace.

    Zamfara ƙasar Hausawa ce,[2] wadda kuma tana daga cikin (ƙannai bakwai) banza bakwai. A hirar da aka yi da Bunza, (2019) a gidan rediyon Pride FM na Gusau, ya bayyana ra’ayin cewa: “A yi ƙoƙarin binciko tushen Hausa daga Zamfara.” A bisa wannan dalili, akwai buƙatar gudanar da Bahaushen nazari dangane da yanayin da ƙasar ta tsinci kanta.

    Kamar yadda Bahaushe ya faɗa: “Ruwa ba ya tsami banza.” Dole ne a gano yadda ƙasar al’umma da ke da tarihi na tarbiyya da zamantakewa mai nagarta (halaye da ɗabi’un Hausawa na ƙwarai) ta wayi gari cikin halin tashin hankali . Bincike-binciken da za a gabatar na iya shafar ɓangarori da dama, sannan na iya kasancewa ta fuskoki da dama, duk dai domin a gano:

    1. Mafari ko tushen inda matsalar take domin a yi wa tufkar hanci daga tushe,
    2. Gano tasirin nau’ukan kayayyakin amfanin yau da kullum wurin ruruta lamarin,[3]
    • Ƙoƙarin gano waɗanda ke da hannu cikin tashe-tashen hankulan kai tsaye ko a kaikaice domin shawo kan matsalar.
    1. Nazartar fasali da siga na tashe-tashen hankulan domin ba da hasken kan yadda za a tunkari matsalar.

    Wannan bincike ya ta’allaƙa kan mas’ala ta biyu (ii) da aka zayyana a sama. Binciken ya mayar da hankali wajen nazartar tasirin kafafen sada zumunta a tashe-tashen hankulan na jahar Zamfara. Farfajiyar binciken ba ta wuce jahar ta Zamafara ba. Saboda haka, ko da akwai yanayi makamancin wanda ake magana a kai, ba za a waiwaice shi ba idan dai ya fita daga bagiren binciken.

    1.1 Manufar Bincike

    Babban manufar wannan bincike ita ce nazartar yanayi da matsayin kafafen sada zumunta a tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Kai tsaye aikin zai mayar da hankali kan:

    1. Bitar yanayi da sigar tashe-tashen hankulan jahar zamfara, da
    2. Nazartar rawar da kafafen sada zumunta ke takawa a tashe-tashen hankulan.

    1.2 Ra’in Bincike

    Ƙasar Zamfara na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa masu tsohon tarihi. Wasu daga cikin masana na ganin cewa: “Idan za a lalubo asalin Bahaushe da tushen Hausa, to a neme shi a Zamfara.”[4] A bisa wannan dalili, aikin ba zai je wani wuri daban domin kalen ra’in da zai masa jagora ba. An ɗora aikin kan ragamar tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kowane allazi da nasa amanu.”

    A bisa wannan tunani, kafafen sada zumunta sun kasance hanjin jimina, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Ma’ana ke nan, suna taka rawa iri biyu dangane da tashe-tashen hankulan Zamfara. Suna taimakawa a ɓangare guda, a ɓangare ɗaya kuwa suna ƙara iza wutar matsalar. Idan haka ne kuwa, ya rage ga wannan bincike ya bi dabaru da hanyoyi mafiya dacewa domin tabbatar da wannan ikirari ko ƙaryata shi.

    1.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

    An bi manyan hanyoyi uku wajen gudanar da wannan bincike. Ta farko ita ce bitar ayyuka daban-daban da aka gudanar dangane da tashe-tashen hankula musamman waɗanda suka shafi jahar Zamfara. Wannan ya ba da haske game da yanayin tashe-tashen hankulan.

    Bayan wannan, wata hanya da aka yi amfani da ita wajen tattara bayanai ita ce bibiyar kafafen sada zumuta domin zaƙulo hotuna da bidiyoyi da rubuce-rubuce dangane da batun. An yi ƙoƙarin sakaye sunayen waɗanda suka ɗora ire-iren bayanan a kafafen na sada zumunta saboda dalilai na tsaro.

    Daga ƙarshe kuwa, an yi hirarraki da mutane daban-daban sannan a matakai mabambanta. Yayin waɗannan hirarraki, an yi la’akari da wurin zama da shekaru da ilmin duniya da kuma cuɗanya da kafafen sada zumunta daga ɓangaren waɗanda aka yi hirar da su. Manyan ɓangarorin da hirarrakin suka taɓo su ne:

    1. Tantance ingancin duk wasu bayanai da aka samu daga kafafen sada zumunta, da
    2. Samun bayanai game da yanayin tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da
    • Samun bayanai dangane da tasirin kafafen sada zumunta kan tashe-tashen hankulan jahar Zamfara, da kuma
    1. Tantance bayanai da aka samu daga hirarrakin.[5]

    1.4 Bitar Matsayin Kafafen Sada Zumunta A Zamantakewa

    A duniyar yau, kafafen sada zumunta sun zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. Kusan za a iya cewa, duniyar mutane ba za ta iya rayuwa ba sai da su. Dalili kuwa shi ne, rayuwar mutane da dama ta dogara kacokan kan ire-iren waɗannan kafafe. Nan ne cinsu, nan ne shansu![6] A rahoton da Clement, (2019: 2) ya fitar, masu amfani da kafar Whatsapp a wata kaɗan sun kai kimanin biliyan guda da miliyan ɗari biyar (1,005,000,000). Binciken da Jayasekara, (2015) ya gudanar ya nuna cewa, ana samun ƙaruwar masu amfani da kafafen sada zumunta matuƙa.

    Masana da manazarta da dama sun yi bincike da rubuce-rubuce game da tasirin kafafen sadarwa a zamantakewa.[7] Siddiqui & Singh sun bayyana cewa:

    Now a day’s social media has been the important part of one’s life from shopping to electronic mails, education and business tool. Social media plays a vital role in transforming people’s life style. Siddiqui & Singh, (2016: 71)

    Fassara

    A yau, kafafen sada zumunta sun zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan’adam tun daga kan sayayya da tura saƙonni da ilimi har zuwa kasuwanci. Kafafen sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa dangane da salon rayuwar mutane.

    Lallai wannan batu haka yake, domin kuwa ko a ƙasar Hausa akwai mutane da dama da suka raja’a matuƙa kan kafafen na sada zumunta. Akwai muhimman ɓangarorin rayuwa da waɗannan kafafe suka fi shafa. Sun haɗa da:

    1. Sada zumunta
    2. Tattaunawa a matakin ɗaiɗaiku ko ƙungiyoyi
    • Kasuwanci da cinikayya
    1. Ilimi da karantarwa

     

    • Tun farko dai waɗannan kafafe an samar da su ne domin sada zumunta. Misali, Facebook da aka samar a wajajen 2004, ya kasance huɓɓasa ne na ɗalibin Jami’ar Harvard mai suna Mark Zuckerberg. Ya ƙirƙire shi ne a matsayin kafar sada zumunta tsakanin ɗaliban makaranta. Sannu a hankali ɗaliban wasu makarantu na daban suka fara amfana da shi.[8] A shekarar 2006 ne kuma aka fitar da shi a matsayin kafar sada zumunta da duniya gaba ɗaya za ta iya amfani da shi (Baruah, 2012: 4; Clement, 2019: 2). A zuwa yau, Facebook ke kan gaba duk cikin kafafen sada zumunta. Wasu daga cikin fitattun kafafen sada zumunta bayan shi sun haɗa da:
    • Instagram
    • Twitter
    • Whatsapp
    1. A ɓangare guda kuwa, ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da kuma ma’aikatu na amfani da waɗannan kafafe wajen tattaunawa. A tattaunawar da aka yi da Babban Mai Kula da Ayyuka (Senior Vendor Manager) na kamfanin Amsoshi Digital Services[9], ya bayyana cewa:

    Ta hanyar kafafen sada zumunta ne kamfani ke samun damar tattaunawa alhali kowa yana gidansa… Matsalar da aka fi fuskanta ita ce, har yau an bar Hausawa a baya a wannan fanni. Ko da tattaunawa za a yi, sun fi ganewa da Whatsapp kawai da Facebook, watakila saboda sun fi sauƙin shaani. (Arabi, 2019)

    Ko ba komai, kafafen na tallafa wa kamfanoni wajen sauwaƙa kuɗaɗen zirga-zirga (don zuwa tarurruka). A maimakon tafiye-tafiye domin ganawa, akan tattauna ne kawai ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

    1. Ana amfani da kafafen sada zumunta wajen kasuwanci. A wannan ɓangare matan Hausawa ma ba a bar su a baya ba wajen morar wannan dama. Kafafen sun taimaka wajen ba wa mata damar gudanar da kasuwanci a natse, ba tare da dole sai sun fita waje domin kasa haja ba. A maimakon hakan, suna kasa hajar ne bisa iska a kafafen sada zumunta. Waɗanda suka yaba, za su tuntuɓa ta waɗannan kafafen. A hirar da aka yi da Malama Sa’adatu Umar Ɗandare, ta bayyana ra’ayinta game da matsayin kafafen sada zumunta kamar haka:

    A nawa kasuwanci, kafafen sada zumunta su ne jigon kasuwa saboda kayan da duk zan saya ta intanet zan gan su, kuma ta nan zan sayar da su. (Ɗandare, 2019)

    Shi kuwa Malam Muhammad Zulyadain[10] yana ganin ai rayuwa ma kacokan ba ta yiwuwa a yau sai da kafafen sada zumunta.[11] A ɓangaren kasuwancinsa, ya ce:

    Yanzu kusan kasuwanci ya koma yanar gizo kama daga manya har ƙananan kasuwanci… Kaso mafi yawa (ɓ75%) na abokan huldar kasuwancina muna haɗuwa ne a kafafen sadarwa. (Zulyadain, 2019)

    1. Tuni kafafen sada zumunta suka zama wani fili na koyo da koyarwa. Ko bayan rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da odiyo-odiyo na ilmi da ake yaɗawa ta kafafen, akwai shafuka da zauruka da ake buɗewa na musamman domin karantarwa. Karatun kuwa yakan shafi ɓangarorin rayuwa daban-daban. Sun haɗa da addini da kimiyya da kiyon lafiya da ilmin intanet da ilmin kwamfuta da ilmin zamantakewa da ilmin kasuwanci. Wasu daga cikin fitattun makarantun da ake da su kan kafafen sada zumunta sun haɗa da:
    2. Hausa Musical Institute
    3. Makarantar Malam Bambadiya
    4. Zauren Markazus Sunnah

    2.0 Tashe-Tashen Hankula A Zamfara

    A shekarun baya, tun kafin shekarar 2007, Zamfara ta kasance cikin ruwan sanyi.[12] A wancan lokaci, akan samu ƙananan laifuka ne kawai irin su sace-sace ko rashin jituwa tsakanin al’umma da kan kai ga faɗa da dai makamantansu.[13]

    Aminu, (2020)[14] ya bayyana cewa: “A wancan lokaci, babban aikin ta’addanci da ke wakana shi ne faɗa tsakanin matasan shiyar gabas da na yamma.” Faɗan na yin tsananin da har yakan kai ga samun munanan raunuka ko ma rasa rayuka. Wani nau’in aikin ta’addanci da ake samu wanda kan kai ga munanan raunuka ko rasa rai shi ne bangar siyasa.

    Daga wajajen 2008 ne kuma aka samu ɓullowar tashe-tashen hankula cikin nau’uka daban-daban da suka haɗa da:

    1. Fashi da makami
    2. Satar shanu
    • Garkuwa da mutane
    1. Hare-hare (Almustapha, 2020; Aminu, 2020; Ibrahim, 2020)[15]

    Tsakanin 2008 zuwa 2019 an samu rashe-rashen rayuwa da salwantar dukiyoyi sakamakon waɗannan tashe-tashen hankula. Duka waɗannan ayyuka akan danganta su ne da Fulani. Binciken ya ci karo da bayanan da ke tabbatar da cewa, tushen tashe-tashen hankulan ya samu tsira ne a sakamakon fansa da Fulanin suka ƙuduri ɗauka game da rashin adalci da suke ganin an yi masu. Wannan ya kasance ta fuskoki biyu:

    1. Bayan an fara samun yawaitar fashi da makami, wasu daga cikin jami’ai ‘yan sa kai sun danganta abin da ayyukan Fulani. Daga nan ne suka ɗauki mataki kan Fulanin da suke zargin na da hannu cikin fashi da makamin. A hirar da aka yi da Almustapha, (2020) da Ibrahim, (2020) sun tabbatar da cewa, ɗaya daga cikin shuwagabannin Fulanin ya taɓa bayyanawa ƙarara cewar sun kai wasu hare-haren ne a matsayin ɗaukar fansa. Daga cikin garuruwan da aka kai wa waɗannan hare-hare na ɗaukar fansa akwai Kizara da ke ƙaramar hukumar Gusau da ‘Yargaladima da ke ƙaramar hukumar Maru da kuma wasu ƙauyukan yankin Ɗ
    2. Aminu, (2020) ya bayyana a hirar da aka yi da shi cewa, wasu daga cikin masu hannu cikin tashe-tashen hankulan sun yi iƙirarin bin hanyar sakamakon karya masu alƙawari da aka yi. Sun bayyana cewa, ‘yan siyasa sun masu alƙawura goshin zaɓen 2007 (yayin da ‘yan siyasar suka ɗauke su a matsayin ‘yan bangar siyasa). Bayan zaɓe kuwa, sai aka yi abin da Bahaushe ce ke cewa: “An ci moriyar gangan, an ya da goronta!” Ko ma dai yaya abin yake, to “da walakin goro a miya,” domin kuwa “ruwa ba ya tsami banza.”
    • Wasu daga cikin masu riƙe da makaman na ikirarin cewa, an ƙwace gonakan da suke noma an mallaka wa ‘yan siyasa. Hakan ya samar masu da takunkumin tattalin arziki da dole sai sun nemi mafita. Idan laila ta ƙiya sai a koma basha.
    1. Wasu kuwa na kukan cewa, burtalan[16] da suke bi aka mayar gonaki. Shiga gonakan kuwa ya kasance laifi da ke janyo hukunci ga duk wanda ya aikata. Wannan ya sa makiyayan suka kasance cikin wahala. Da tura ta kai bango, sannan tafiya ta yi tafiya, sai hannun agogo ya juya.
    2. Akwai kuma masu ikirarin cewa, an fara samun yawaitar tashe-tashen hankulan ne tun lokacin da aka fara sace wa Fulanin yankin dabbobinsu. A wannan lokaci, ɓarayin shanun ɗauke da makamai na far ma ƙauye tare da kwashe shanu masu adadi da yawa. Dabbobin kuwa na daga cikin kaso mai tsoka daga ɓangaren tattalin arziki wanda makiyayan suka dogara a kai domin rayuwa.[17]

    A ɓangare guda kuwa, akwai masu yi wa tashe-tashen hankulan kallo na daban. Dangane da musabbabinsu, tashe-tashen hankulan, binciken ya ci karo da ra’ayoyi da suka haɗa da:

    1. Akwai waɗanda ke da fahimtar cewa, ummulhaba’isin waɗannan fitintinu shi ne albarkatun ƙasa (musamman zinare)[18] da Allah ya azurta ƙasar Zamfara da shi. Hakan ne ta sa ake ta ƙirƙirar tashe-tashen hankula domin kore mazauna ƙauyuka daga muhallansu. Hakan zai ba da damar haƙar zinaren hankali kwance.
    2. Wasu kuwa, musamman malaman addinin Musulunci, na da fahimtar cewa tashe-tashen hankulan jarabawa ce daga Ubangiji. Suna faruwa ne sakamakon gurɓacewar halayyar mutane. Kai tsaye sukan danganta shi da ayyukan tsafe-tsafe da ake gudanarwa, musamman waɗanda suka shafi wasa da Alƙur’ani mai tsarki.[19]

    Lokacin da tashe-tashen hankulan suka yi tsamari musamman daga wajajen 2016, mazauna wasu ƙauyuka sun yi gudun hijira zuwa garuruwan da ke kusa da su. Daga nan ne kuma labaran tashe-tashen hankulan suka mamaye duniyar intanet. Hotuna da bidiyoyi da rubutattun labarai game da su, duk suka mamaye kafafen sada zumunta. Ibrahim, (2019) a hirar da aka yi da shi ya tabbatar da cewa, adadin mutanen da suka yi gudun hijira na da yawa sosai. Ya ce:

    Wasu daga cikinsu sun samu taimako daga mutanen gari. Wasu sun ɗauki haya. Wasu kuwa sun zauna a cikin makarantu. Wasu kuma an ba su wurare aro sun zauna. (Ibrahim, 2019)

    Hukumomi sun yi ta bin hanyoyi daban-daban domin shawo kan lamarin. Daga cikin har da ƙoƙarin neman sulhu da ƙusoshin tashe-tashen hankulan. A wajajen ƙarshen 2019 zuwa farkon 2020 ne aka samu sulhun da ya kai ga raguwar tashe-tashen hankulan. Sulhun ya kasance wani yunƙurin samar da zaman lafiya na gwamnatin da aka zaɓa a shekarar 2019.

    3.0 Gurbin Kafafen Sada Zumunta a Tashe-Tashen Hankulan Zamfara

    Kafafen sada zumunta suna taka rawa iri biyu dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. A ɓangare guda suna taimakawa ta wasu fuskoki da suka shafi faɗakar da jama’a dangane da abubuwan da ke faruwa tare da miƙa ƙoƙon bara na neman addu’o’i daga al’ummu na kusa da na nesa, da makamantansu. A ɗaya ɓangaren kuma, kafafen sada zumuntar suna ƙara wa wuta karmami. Sukan yi hakan ta fuskar ruruta zance da yaɗa jita-jitan ƙarya da cusa tsoro a zukatan mutane.

    A gaskiya tasirin kafafen sada zumunta game da tashe-tashen hankulan zamfara nau’i biyu ne. Suna amfanarwa a gefe guda. A gefe guda kuwa cutarwa suke yi…[20] (Maikwari, 2019)

    A taƙaice dai, kafafen na sada zumunta sun zama hanjin jimana, wato akwai na ci akwai na zubarwa. An raba rawar da kafafen sada zumuntar ke takawa dangane da tashe-tashen hankula a Zamfara zuwa manyan rukune biyar kamar haka:

    Jad. 1: Manyan Nau’ukan Tasirin Kafafen Sada Zumunta a Kan Tashe-Tashen Hankula a Zamfara

      Masu Kyau Marasa Kyau
    1. Faɗakarwa Ta da Hankali
    2. Ƙoƙon Bara Yaɗa Ayyukan Ta’addanci
    3. Bunƙasa Adabi

    3.1 Faɗakarwa

    Faɗakarwa kalma ce mai kinin ma’ana da nusarwa ko nusatanwa ko tunatarwa. Bunza, (2013: 2) ya ba da ma’anar wannan kalma da cewa: “Faɗakarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwarsu.”[21] Kafafen sada zumunta na faɗakar da al’ummomi na kusa da na nesa dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara ta fuskoki kamar haka:

    1. Bayanai dangane da abubuwan da ke faruwa a daidai wata rana sannan daidai wani lokaci na saurin watsuwa ta kafafen sada zumunta. Wannan na taimaka wa al’umma wajen guje wa faɗawa yankunan da abin ya shafa.[22]
    2. Ana tura nau’ukan faɗakarwa daban-daban na yadda mutane za su guje wa faɗawa cikin tarkon waɗannan masu ta da hankula. Wannan ya shafi labarai na yadda wasu suka faɗa tarkon masu ta da hankulan, wanda hakan na matsayin hannunka mai sanda da darasi ga mai karanta labarin. Ko da ma dai an ce, “Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.” Wasu lokuta kuma kai tsaye ake kawo bayanai kan abubuwa da ya kamata mutane su kiyaye.
    • Akwai faɗakarwa da ta shafi jan hankali al’umma musamman matasa daga nisanta kansu daga ire-iren waɗannan tashe-tashen hankula. Wannan na iya kasancewa ta fuskar wa’azantarwa da nuna illolin shiga cikin ire-iren ayyukan.

    3.2 Ƙoƙon Bara

    Ƙoƙon bara salon magana ne da ke ɗaukar ma’anar miƙa koke domin neman wani biyan buƙata.[23] Masana da marubuta daban-daban sun yi rubuce-rubuce kan bara musamman a ƙasar Hausa. Wasu daga cikinsu sun haɗa da Karofi, (1980) da Bashir, (1991) da Sarkin Gulbi, (2007).[24] Ƙoƙon bara a wannan bincike na nufin kai koke da zimmar neman agaji.

    Rubuce-rubuce da ake ɗorawa dangane da halin da al’umma kan shiga a lokacin tashe-tashen hankulan na zaman ƙoƙon bara. Mutanen da ke cin kare da rubuce-rubucen (da ma maganganu da ake turawa ta odiyo), a ƙalla sukan taimaka da addu’a. A wasu lokutan kuwa, ire-iren rubucen na jefa ɗimbin tausayi a zukatan al’umma. Wannan ya sa masu gudun hijira daga cikin waɗanda abin ya shafa sukan samu tallafi a garuruwa da ƙauyukan da suka yi hijirar zuwa gare su. Nau’ukan tallafin da suke samu sun haɗa da:

    1. Matsuguni
    2. Abinci
    • Tufafi
    1. Kuɗi
    2. Abubuwan buƙatun yau da kullum kamar sabulu da omo da makamantansu.

    Hoto 1: Rubutaccen Labarin Tashe-Tashen Hankulan Jihar Zamfara da kan Waz’af

    Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Whatsapp ranar 29 ga watan Disemba, shekarar 2019.

    A wajajen watan Disemba na shekarar 2018, na kasance ganau ba jiyau ba dangane da wannan lamari. A unguwar Sabon Gari da ke Damɓa a Gusau ta Jahar Zamfara, akwai mutane kimanin 18 da suka taso daga ƙauye bayan zaman can ya masu tsauri. Mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.

    Ɗaya daga cikinsu ta san wani dattijo a nan Damɓa. A bisa haka, sai suka tare gidansa. Dattijon mai ƙaramin ƙarfi ne matuƙa. Bisa wannan dalili, sai ya garzaya masallacin da ke kusa da su ya kai kukansa. Al’ummar wannan masallacin ne ta ɗauki nauyin ci da shansu har ranar da suka bar Damɓa. A kullum liman na neman taimakon kuɗin abincinsu na wannan rana. Mu kuma mamu mu bayar.[25]

    A hirar da aka yi da Ibrahim, (2019) da Maikwari, (2019) an samu bayanai dangane da wuraren da ‘yan gudun hijira suka zauna. A yayin zaman nasu, sun samu tallafi da kulawar jama’a. Wasu daga cikin wuraren su ne:

    1. Makarantun gwamnati musaman firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo[26]
    2. Sakateriyoyin wasu ƙananan hukumomi[27]
    • Shaguna da rumfuna a kasuwanni
    1. Tashoshi
    2. Gidajen jama’a
    3. Masallatai

    3.3 Bunƙasa Adabi

    Wani abin jan hankali dangane da adabi shi ne, ba sai yanayin lumana ko yadda zuciya ke so ke samar masa abinci ba. A maimakon haka, sau da dama mummunan yanayi ko ƙunci ko tashin hankali ko dai wasu abubuwa na ƙi na samar da tubalan ginin sabbin falsafofi a duniyar adabi. Tashe-tashen hankulan Jahar Zamfara sun taka rawar gani wajen samar da ƙirƙire-ƙirƙiren adabi da suka haɗa da waƙoƙi da karuruwan magana musamman na zamani.[28]

    Jad. 2: Waƙoƙi da Aka Samu a Sakamakon Tashe-Tashen Hankulan Jahar Zamfara

    Sunan Waƙa Mawaƙi Nau’in Waƙa
    Bazamfariya Dr. Aliyu U. Tilde Rubutacciya
    Waƙar Kidnafas[29] Abdulhamid M. Sani Rubutacciya
    Yau ga Allah Muka Koma Waƙar Zamani[30]
    Zamfara Babu Lafiya Sagir Yusuf Rubutacciya

     

    Haƙiƙa waɗannan waƙoƙi sun kasance ci gaba ga adabin Hausa musamman ɓangaren waƙa. Ko baya ga haka, sun taimaka wajen jawo hankalin al’umma musamman domin dogewa bisa addu’o’i da gyara halaye da zamantakewa, duk dai domin samun sauƙin lamarin.

    Jad. 3: Sabbin Karuruwan Magana da Aka Samu a Sakamakon Tashe-Tashen Hankulan Jahar Zamfara

    Sabuwar Karin Magana Tsohuwar Karin Magana
    Ba da ni ba, neman aure a Ɗansadau Ba da ni ba gaɗa a maƙabarta/hurumi
    Ba kanta, an sace mai garin Ɗansadau
    Ana Maiduguri sai ga Zamfara Ana kukan targaɗe sai ga karaya
    Ana Boko Haram sai ga kidnafas Ana kukan targaɗe sai ga karaya
    Ritaya sa! An tura ɗansanda dejin Ɗansadau
    Duk kun raba mini hankali, an ce da ɗansanda ya baro Borno ka koma Ɗansadau Duk kun raba mini hankali, an ce da rago sha hura ka tafi gona
    Ta nan muka fara, ɗan Borno ya ga Bazamfare Ta nan muka fara, kuturu ya ga mai ƙyasfi

    Madogara: Hirarraki[31]

    A jadawali na uku da ke sama, an ga jerin misalan karuruwan magana da suka samu sakamakon tashe-tashen hankulan a jahar Zamfara. Wasu daga cikin an yi amfani da tsoffin karuruwan magana ne wajen samar da su. Wato an kwaikwayi falsafar da ke cikin tsoffin karin maganar ne domin ƙirƙira su.

    3.4 Ta Da Hankali

    A cikin wannan bincike, ta da hankali na nufin jefa tsoro ko firgici ga zukatan al’umma. Binciken ya gano cewa, ɗaya daga cikin illolin kafafen sada zumunta dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara shi ne jefa tsoro da zaman ɗar-ɗar a zukatan al’umma na kusa da na nesa. Abin lura a an shi ne, kafafen watsa labarai sukan tace sahihancin labari kafin fitar da shi. Ko bayan nan ma, sukan ba da labarai ta salo da sigar da ba za su kasance masu ta da hankalin al’umma ba.

    A ɓangare guda kuwa, labaran da ake yawo da su ta kafafen sada zumunta ba tatattu ba ne. Wasu ma na ƙarya ne. Wasu lokutan jita-jita ce ma tsura ake rurutawa. Saboda haka, labaran da ke fita daga kafafen sada zumunta sun fi muni da ta da hankali.[32] Wannan rashin kwanciyar hankali ga masu karanta labaran na faruwa ta fuskoki da dama. A ƙasa an kawo misalan wasu daga cikin hotuna da aka ci karo da su waɗanda za su iya ta da hankulan masu gani.

    Hoto 2: Hoto Mai ta da Hankali da aka Ɗola a Fesbuk

    Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Fesbuk.[33]

    A hirar da aka yi da malaman makarantar da ake ikirarin wannan abu ya faru, sun bayyana cewa labarin ba haka yake ba. Abu makamancin haka ya faru, amma ba yadda aka kawo labarin ba. An kawo wannan labari a Fesbuk cikin sigar da zai iya janyo ƙiyayya da rikici irin na addini. Ko bayan haka, hoton kansa ya kasance mai ta da hankali.

     Hoto 3: Gawarwarki da yawa da aka jejjera su cikin rami guda

    Madogara: An ɗauko wannan hoto daga Fesbuk.[34]

    Hoto 4: Hotunan gawarwaki a kwakkwance

    A hirar da aka yi da Maikwari, (2019) ya bayyana cewa:

    A yanzu haka akwai guruf-guruf da aka buɗe a kafafen sada zumunta musamman Whatsapp waɗanda suke yaɗa farfagandar ƙarya sakamakon ƙin jinin gwamnati mai ci da suke yi. Kullum sukan ƙago labaran da ke nuna ana samun daɗuwar tashe-tashen hankula. Yayin da aka bincika, wani lokaci sai a tarar sunayen ƙauyukan da suka zayyana babu su kwata-kwata ma a jahar Zamfara. (Maikwari, 2019)

    Idan kuwa haka ne, lallai matsalar ta kai inda ta kai. Dole ne kuma gwamnati da sauran hukumomi waɗanda abin ya shafa su tashi tsaye domin daidaita sahun amfani da kafafen sada zumunta.

    3.5 Yaɗa Ayyukan Ta’addanci

    A duk lokacin da mutane (musamman yara) ke kallon ayyukan ta’addanci, zuciyarsu tana ƙara bushewa ne da ƙeƙashewa. Sannu a hankali tausayin da suke ji zai riƙa raguwa. Za a kai gacin da kwata-kwata nau’ukan ta’addancin ba sa wani tasiri irin na sanya tausayi ko jin ƙai a zukatansu.

    A ɓangare guda kuwa, yana koya wa yara hanyoyin aikata rashin gaskiya daban-daban. Daga cikin nau’ukan abubuwan da ke ƙunshe a kafafen sada zumunta waɗanda kuma ke da alaƙa da ta’addanci akwai:

    1. Hotuna da bidiyoyi da labarai a kan makamai da yadda ake sarrafa su.
    2. Hotuna da bidiyoyi na makamai da yadda ake safarar su.
    • Hotuna da bidiyoyi da labaran kashe-kashe.
    1. Hotuna da bidiyoyi da labarai game da ayyukan ta’addanci da aka aikata irin su fashi da makami da sata da garkuwa da mutane da makamantansu.

    A ƙasa an kawo ‘yan misalai waɗanda aka tattaro daga kafafen sada zumunta.

    Hoto 5: Bindigogi da Alburusai a Fesbuk

    Madogara: An ɗauko wannan hoto ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.

    A hoto na 5 da ke sama, za a ga hoton bindigogi da kuma alburusai. A ƙasar Hausa an saba ganin yadda yara ke kwaikwayon wasa da bindigogi waɗanda suke haɗawa da kara ko ‘yan itatuwa. Masu wayo daga cikinsu suna amfani da fayif da ƙaramin katako ko falanki da ashana domin yin bindigar wasa wadda take ƙara. Duka waɗanan na faruwa ne sakamakon kallace-kallacen hotuna da bidiyoyin nau’ukan bindigogin da kuma yadda ake sarrafa su. A bisa wannan dalilai, kai tsaye ire-iren hotunan nan na da tasiri a kan tarbiyya da falsafar yara masu tasowa.

    Hoto 6: ‘Yan Bindiga na Shirin Kai Hari

    Madogara: An ɗauko wannan bidiyo ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 2020 daga Fesbuk.

    An sanya wannan bidiyo ne da sunan ‘yan bindigar Jahar Zamfara ne ke shirin kai hari. Sai dai bincike ya nuna cewa, labarin ba gaskiya ba ne. Hasali ma, ba a Nijeriya aka ɗauki wannan bidiyo ba.

    4.0 Sakamakon Bincike Da Shawarwari

    Tun wajajen shekarar 2008 aka fara samun ƙaruwar tashe-tashen hankula a Jahar Zamfara. A lokacin bai yi ƙamari ba, domin bai wuce faɗa tsakanin zauna-gari-banza na unguwanni da kuma sace-sace ba. Ƙaruwar fashi da makami da satar shanu ya buɗe wani sabon babin tashe-tashen hankulan. A wajajen shekarar 2012 zuwa 2013 ne lamarin ya yi ƙamari sosai musamman bayan ƙaruwar garkuwa da mutane da kuma hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa ƙauyuka.

    A ɓangare guda kuwa, wannan bincike ya gano cewa, kafafen sada zumunta sun kasance ruwa biyu dangane da tashe-tashen hankulan jahar Zamfara. Kai tsaye alfanunsu sun haɗa da:

    1. Faɗakar da al’umma domin su farga tare da guje wa faɗawa cikin tashe-tashen hankulan ta kowace fuska. Wannan ya haɗa da ɗaukar makami, ko kuma garaje da rayuwa wajen faɗawa cikin haɗarin tashe-tashen hankulan.
    2. Taimakawa wajen neman tallafin addu’o’in samun zaman lafiya da ma samun tallafi nau’uka daban-daban kamar yadda aka lissafa a ƙarƙashin 3.2 da ke sama.
    • Suna kuma taimakawa wajen bunƙasa adabin Hausawa musamman abin da ya shafi waƙoƙi da karuruwan magangannu.

    A ɓangare guda kuwa, kafafen na sada zumunta suna da illolin da suka haɗa da:

    1. Ta hanyarsu ne ake yaɗa jita-jita da labaran ƙarya marasa tushe. Wasu labaran na ƙara ruruta lamari tare da jefa ƙiyayya da gaba da rikicin addini da ƙabilanci a zukatan al’umma.
    2. Labarai da bidiyoyi da hotuna da ake sanyawa na sukan kasance masu ta da hankalin al’umma. Wannan na faruwa musamman da yake ba tacewa ake yi ba ballantana a yi tunanin waɗanda suka dace a sanya da waɗanda ba su dace ba.

    Dangane da waɗannan, binciken an ba da shawarar cewa:

    1. Gwamnati ta tashi tsaye tare da fitar da wasu tsare-tsare da dokoki na musamman da za su lura da yadda ake tafiyar da al’amuran kafafen sada zumunta a Nijeriya. Wannan na iya kasancewa ta sigar samar da yarjejeniya ta musamman da kamfanonin da hukumomin da ke lura da kafafen sada zumuntar. Za a iya bin matakan rufe asusu da ma bin wasu hanyoyin hukunci na daban ga masu yaɗa labaran ƙarya, musamman waɗanda ke ta da hankula.
    2. Malaman addini da na makarantun boko su rinƙa faɗakarwa game da illolin yaɗa labaran ƙarya da ta da hankula da kuma jefa ƙiyayya tsakanin ‘yan ƙ
    3. A samu tarurrukan ƙara wa juna sani a matakai daban-daban da za a tattauna tare da samun gudummuwar malaman ilmi da manazarta game da hanyoyi da matakan da za a tunkari matsalar. Gwamnati a matakai daban-daban tare da haɗin guiwar makarantu (musamman jami’o’i) su jagoranci tafiyar.

    5.0 Kammalawa

    Tunanin Bahaushe na “kowane allazi da nasa amanu” na ƙunshe da ƙamshin gaskiya. Binciken nan ya ci karo da hakan yayin da ya ci karo da amfani da kuma illolin kafafen sada zumunta yayin da yake nazartar tasirin kafafen ga tashe-tashen hankulan jahar Zamfara.

    Matsayin kafafen sada zumuntan sun kasance hanjin jimana, wato “akwai na ci, akwai na zubarwa.” Ya rage ga mahukunta da gwamnatoci da sauran waɗanda abin ya shafa, da su yi wata huɓɓasa domin amfanuwa da kyawawan manufofin kafafen, tare da samar da matakai da hanyoyin da za a zage tsirin illolinsu.

    Manazarta

    Baruah, T. D. (2012). Effectiveness of Social Media as a tool of communication and its potential for technology enabled connections: A micro-level study. In International Journal of Scientific and Research Publications. Volume 2, Issue 5, Pp. 1-10, ISSN 2250-3153.

    Bashir, L. (1991). “Bara a Ƙasar Hausa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Clement, J. (2019). Daily active users of WhatsApp Status 2019. Retrieved on 3rd January, 2020 from: https://www.statista.com/statistics/730306/whatsapp-status-dau/.

    Jayasekara, A. H. D. (2015). Facebook users and undergraduates (Specially reference to Selected Universities in Sri Lanka ). In the International Journal of Scientific Research and Innovative Technology, Vol. 2, No. 5 , Pp. 78-85. ISSN: 2313-3759.

    Karofi, D. S. (1980). “Mabarata: Tasirinsu da Gudummawarsu a Kan Adabin Hausa.” Kundin digiri na (nawa?) wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

    Korkmaz, M., Celebi, N. & Yucel, A. S. (2014). Practical review of the place of social networks in our daily life and their effect on today’s youth. International Journal of Academic Research Part B; 6(1), Pp. 250-261. DOI: 10.7813/2075-4124.2014/6-1/B.35.

    Owusu-Acheaw, M. & Larson, A. G. (2015). Use of Social Media and its Impact on Academic Performance of Tertiary Institution Students: A Study of Students of Koforidua Polytechnic, Ghana. In Journal of Education and Practice. Vol. 6, No. 6, 2015 ISSN 2222-1735 (Paper), ISSN 2222-288X (Online), Pp. 94-101.

    Sarkin Gulbi, A. (2007). “Nazari Kan Al’adar Bara a Ƙasar Sakwkato.” Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Siddiqui, S. & Singh, T. (2016).Social Media its Impact with Positive and Negative Aspects. In International Journal of Computer Applications Technology and Research. Vol. 5, Issue 2, Pp. 71 – 75, ISSN:- 2319–8656.

    Umar, A. B. (2013). Waiwaye Adon Tafiya: Faɗakarwa a Cikin Ƙagaggun Labaran Hausa. An cirato ranar 28 ga watan Disamba, 2019 daga: https://www.amsoshi.com/ 2018/03/waiwaye-adon-tafiya-fadakarwa-cikin.html.

    Kafafen Intanet da Aka Ziyarta

    https://www.statista.com/statistics/273563/number-of-facebook-employees/

    https://www.amsoshi.com/

    Waɗanda Aka Yi Hira da Su

    Suna Wurin Zama Sana’a Ƙiyasin Shekaru
    Almustapha, Aliyu Gusau Aikin Gwamnati 50 – 60
    Aminu, Ibrahim Gusau  Aikin Kamfani 40 – 50
    Ɗandare, Sa’adatu Umar Kebbi Sayar da atamfofi (Kasuwanci) 20 – 30
    Gobir, Yakubu Aliyu (Ph. D) Sakkwato Koyarwa a jami’a 50 – 60
    Hassan, Nasiru Gusau Koyarwa a sakandare 40 – 50
    Ibrahim, Aliyu Gusau Aikin Gwamnati 50 – 60
    Ibrahim, Faruk Gusau Kasuwancin man fetur da gas (Manajan gidan man fetur na Zayaz Resource) 30 – 40
    Maikwari, Haruna Umar Gusau Koyarwa a kwaleji 30 – 40
    Zulyadain, Muhammad Kano Kasuwancin tufafi da kayan kwalliya 20 – 30

    Rataye

     Bazamfariya ta Dr. Aliyu U. Tilde

    Ta’ala mun kira ka,

    Gida Naija da Makka,

    Na bene har na bukka,

    Yakini babu shakka,

    Ga komi kai iyawa.

     

    Ka shaida mun bara’a,

    Ga duk wani mun yi a’a,

    A saɓo ba mu ɗa’a,

    Muna roƙonka sa’a,

    Gabanin mui cikawa.

     

    Tsaro yau yai gazawa,

    A Hausa da tausayawa,

    A kullum ba lafawa,

    Da yaɗon ɗan kabewa,

    Da sauri ba tsayawa.

     

    A Zamfara anka fara,

    Abin sanda da gora,

    Ya ƙarfafa babu lura,

    Da iska har da ƙura,

    Ya kai kan Sakkwatawa.

     

    Ƙasar Gandi da Isa,

    Da ke da natso da hirsa,

    A yau an tashi rusa,

    Ginin Usumanu ƙusa,

    Da Gwamna Bafarawa.

     

    Suna nan yammacinmu,

    A Birnin Gwari namu,

    Zubairu yana kiranmu,

    Mu kai ɗauki dukkanmu,

    Da sauri ba tsayawa.

     

    Kasar Dikko ya jawo,

    Ta’adda na ta yawo,

    A ɗauke mutum a kawo,

    Kuɗaɗe kan ya dawo,

    Ga dangi ba ragawa.

     

    A Daura sunka sabka,

    Magaji yana a garka,

    Da ƙarfi sunka ɗauka,

    Ya sa Sarki ya koka,

    A tashi a zam kulawa.

     

    Bare hanyar Abuja,

    Farin kaya da soja,

    Da manya masu maja,

    A tsorace babu ko ja,

    A jirgi za su zowa.

     

    Muhammadu sai ka miƙe,

    Ka ɗau ɗamara ka tamke,

    Da R.P.G. da sulke,

    Ta’adda duk ka banke,

    Ka himmata ba gazawa.

     

    Nasiha ce na ba shi,

    Da A’i uwargidan shi,

    Su ɗau kibiya da mashi,

    A kullum babu fashi,

    Ka dage gun matsawa.

     

    Burutai kar ka zauna,

    Ka ɗauki igwa ka auna,

    Ga tungar masu ɓarna,

    Ka watse duk ka ƙona,

    Su tuba su bar mayawa.

     

     

    Sa’an nan ga Sadiƙu,

    Yana ta jiran kiranku,

    Ya ɗau jirgi ya bi ku,

    Ya ba ku tsaro samanku,

    Da bom ba dakatawa.

     

    Na bi ku ina kirari,

    Ina baiti da sauri,

    Kumama babu ƙwari,

    Da daji ya yi ƙauri,

    Na kwanta ban ɗagawa.

     

    Da malammai a baya,

    Tsayayyu masu raya,

    Dare duka ba ritaya,

    Da farko har nihaya,

    Ijaba sui biɗowa.

     

    Arewa ina kiranmu,

    Mu taru a dunƙulenmu,

    Mu nemi tsaron ƙasarmu,

    Amana har da ilmu,

    Sana’a sai yabawa.

     

    Talauci bai yi kyau ba,

    Yana kawo musiba,

    Da kunci ga anoba,

    Da jari babu riba,

    Kasa duk tai macewa.

     

    Talauci in ya zauna,

    Da kafirci da ɓarna,

    Suna biye ba lumana,

    Ɗabi’u duk su ƙona,

    Mutunci yai ficewa.

     

    Ƙalau muke ko husuma,

    A jaki ko a Homa,

    Idan an ce mu koma,

    Ka sa mu tuna da Kalma,

    Mu yi ta wajen cikawa.

     

     

    Salamatun da tsira,

    Ga Annabi sa ka ƙara,

    Iyaye duk ka tara,

    A haula har mu dara,

    Dawaman ba gushewa.

     

    Da tammat zan tiƙe ta,

    Bazamfariya kiran ta,

    Watan azumi na yi ta,

    Da fuska biyu gare ta,

    Wajen mai bincikawa.

    Dr. Aliyu U. Tilde 19 May 2019

    WAƘAR KIDNAFAS

    Abddulhamid M. Sani

    (Malumman Matazu)

     

    Allah da sunanka nake farawa,

    Kai kay yi loto kullum yake juyawa,

    Kai ne ka raya Allahu kai ka matarwa,

    Ka halicci fajir sannan kayo Mumnawa,

    Zan so ku ji ni ya al’umarmu mutane.

     

    Kafin na fara na yo salati farko,

    Wurinsa Manzo Shalele da aka aiko,

    Duk Annabawa shi ne ya zam cikamakko,

    Sannan iyalai sahabihi nai anko,

    Ban ƙin na sanya nagargaru a mutane.

     

    Yau firgici ne ya mamaye yankinmu,

    Tsoro a kullum daɗo yake jama’armu,

    An sace mata an sace har yaranmu,

    Masu kuɗinmu an sace sarakanmu,

    Abin takaicin wai gwamnatin jama’a ne.

     

    Cikin gidanka a zo a ɗau maka mata,

    Koko ɗiyanka a bi su har makaranta,

    Waninmu fsinja yana kan mota,

    Yau al’umaru muna cikin firgitta,

    Halin ƙasarmu na garkuwa da mutane.

     

    Sam baabu imani wurin kidifawa,

    In sunka sata wasu waya suka yowa,

    Kuɗi miliyya su ce abin fansowa,

    Allah tsare mu kaidinsu mun roƙawa,

    Su al’umar da ke garkuwa da mutane.

     

    Wasu cikinmu in sun yi garkuwa das su,

    Nau’i da nau’i azaba suke gunsu,

    Duka da yunwa su gaggalabaita su,

    Har izgilanci kidifawa ke yi gunsu,

    Sharri gare su ‘yan garkuwa da mutane.

     

    Daji su ɗaure ruwa ya ƙare kansu,

    Sanyi na hunturu a kai na wasunsu,

    Can daga baya za su kira ikhwansu,

    Kuɗi a kawo koko su hallaka su,

    Wayyo ni wayyo wai gwamnatin jama’a ne!

     

    Kare suke ci ba babbaka yankinmu,

    Abin takaici wai shugaba kuma ɗanmu,

    Mun raina himmar da ake wurin kare mu,

    Wai sulhu za ai da masu kakkashe mu!

    Anya hukuma aikinta kare mutane?

     

    Abin takaici ne ƙwarai kui duba,

    Wai a hakan ne ake faɗin ci gaba,

    Ƙalubale ne gare mu wannan babba,

    Dukkan musifa yaye mana Wahhaba,

    Duk kar ka ware har garkuwa da mutane.

     

    Ni sha’írin nan ‘yar shawarata ga ta,

    Wurin hukuma ni ma gudummuwata,

    Tsayin daka ku yi don kare al’ummata,

    Jami’an tsaronmu ciki da maha’inta,

    Ku sanya lura cikinsu kun gaggane.

     

    Bora da mowa kul kar ku wawware su,

    In kun ka gano tabbas ku hukunta su,

    Wurin hukuncin kul kar ku bambanta su,

    ‘Yar shawarata ƙin garkuwa da mutane.

     

    A sa idanu sosai ga infomansu,

    Jami’an tsaro na sirri a alkinta su,

    Dama cikakka a ba su sui aikinsu,

    ‘Yan sanda soji a ba su duk ƙarfinsu,

    Don daƙilewar ‘yan garkuwa da mutane.

     

    Mu ‘yan ƙasa kau gare mu shawarata,

    Aikin alkhairi mu yi mu nuna a yi ta,

    Har addu’o’i mu rinƙa yi gun bauta,

    Kamun ƙafa na duk matsalar Allah kyauta,

    Babbar musifa ta garkuwa da mutane.

     

    Ko ƙyas bayani in mun ji kar mu rufe ta,

    Mu kai rahoto ga jami’ai su bahasta,

    In mun yi wannan Allahu za ya tsayatta,

    Allahu amsa duk matsalar ga ta kwanta,

    Babbar musifa da ta damu dukka mutane.

     

     

    Ashirin da iyu two thousand eighteen yin ta,

    A shekarar da “Musabbabi” ma nai ta,

    Wata na Maris don ba ni son in manta,

    A tsakkiyarda muke cikin firgitta,

    Birni da ƙaye yin garkuwa da mutane.

     

    Ni wanda nai ta Abdulhamid Malumma,

    Abba ga Hafsat ni ne Uban Fatimma,

    Jihar Katsina birninmu mai alfarma,

    Garin Matazu a nan kuma nake zamma,

    Allah taƙaita a daina kama Mutane.

    ALHAMDULILLAH

    [1] Allah wadaran mai tado ta,

    Da waɗanda suke daɗa jawota,

    Allah ka hane mu da tashin ta…

    (Abubakar Ladan Zariya, Waƙar Haɗin Kan Afirka)

    [2] Wannan ba ya nuna cea ba za a samu wasu ƙabilu na daban bayan Hausawa ba. Abin da kawai ake nufi shi ne, mafi rinjayen al’umma da al’adu da cikar tarihi na garin duk na Hausa da Hausawa ne.

    [3] Waɗannan sun haɗa da wayoyin salula da kwamfutoci da ababen hawa da makamai da makamantansu.

    [4] Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na da wannan ra’ayi. Ya kafa hujja da cewa, duk yankin da mawaƙa da sauran masu zalaƙar harshe suka yawaita, to zai iya kasancewa tushen wannan harshe a tarihance. Ya bayyana haka a hirar da aka yi da shi a gidan rediyon FM Zamfara, a watan Oktoba, shekarar 2019.

    [5] Wato ana ƙara tabbatar da bayanan da aka samu daga wani mutum ko wasu mutane ta hanyar tambayar wasu mutane na daban.

    [6] A shekarar 2019, kafar intanet ɗin nan mai suna Sitatista da ke adana bayanai dangane da kafafen intanet ya fitar da ƙididdigar ma’aikatan Facebook. Ya bayyana cewa, a shekarar 2018, ma’aikatan sun kai dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya da biyar (25,105).

     

    [7] Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun haɗa da na Baruah, (2012) da Korkmaz, Celebe & Yucel, (2014) da OwusuAcheaw & Larson, (2015) da Siddiqui & Singh, (2016).

    [8] Makarantun da suka fara amfani da kafar sun haɗa da Columbia da Yale da Stanford (Clement, 2019: 2).

    [9] Kamfani ne da ya shahara wajen ayyukan fassara da tafintanci da bincike (da makamantansu) cikin harsuna da al’adun Afirka. Don ƙarin bayani, a duba https://www.amsoshidigitalservices.com/

    [10] Shi ne ke da kamfanin Dayn’s Collection.

    [11] “Toh gaskiya yanzu kusan za a iya cewa kafar sadarwa ta zamo wani sashi na rayuwa. Kamar yadda muka sani cewa rayuwa yanzu ba za ta yiwu babu ita ba.” (Zulyadain, 2019)

    [12] A lokacin babu tashe-tashen hankula da suka shafi garkuwa da mutane da salwantar rayuwa da dukiyoyi.

    [13] An kira su ƙanana ne kasancewar ba sa cikin nau’ukan miyagun ayyuka da ke ta da hankalin al’umma da jan hankalin duniya (musamman idan ba su yawaita ba).

    [14] Ya faɗi haka a hirar da aka yi da shi ranar Alhamis, 23 ga watan Fabarairu, shekara ta 2020 a ƙofar gidansa.

    [15] A hirarraki da aka yi da su, duk sun tabbatar da wannan batu.

    [16] Burtali na nufi hanyar da ake bi da dabbobi musamman zuwa kiwo. Takan kasance marar ciyawa saboda tattakawa da dabbobi ke yi yau da gobe.

    [17][17] Ɗaya ɓangaren tushen tattalin arzikin nasu shi ne noma.

    [18] Akwai albarkatun zinari a yankunan ƙananan hukumomin Maru da Zurmi da Maradun. An fi samun sa ƙaramar hukumar Maru, musamman yankin Ɗansadau.

    [19] Daga kimanin shekarar 2017 zuwa 2019 an tsinci Alƙur’anai da aka jefa a masai kimanin kashi huɗu ko sama da haka.

    [20] Daga cikin amfanin kafafen na sada zumunta da ya lissafo akwai: (i) Samar da bayanai da (ii) Neman addu’a daga al’umma da (iii) Neman agaji daga al’umma da kuma (iv) Sanar da duniya abin da ake ciki wanda hakan ke sanya gwamnati ƙara mayar da hankali kan lamarin. Ya kuma bayyana rashin alfanunsu da suka haɗa da: (i) Yaɗa labaran ƙarya da (ii) Ta da hankalin al’umma,

    [21] Za a iya samun ƙarin bayani dangane da ma’anar faɗakarwa cikin ayyukan Gusau, (2008) da Usman, (2008).

    [22] Gobir, (2019) ya labarta yadda wata ‘yar uwarsa ta so kawo ziyara tare da halartar buki daga Adamawa zuwa Sakkwato. Yayin wannan tafiya, dole sai an wuce ta cikin jahar Zamfara. Kasancewar ta samu bayanai game da tashe-tashen hankulan, cikin sauƙi suka yanke shawarar rashin zuwanta shi ya fi kwanciyar hankali.

    [23] An gina wannan salon magana daga ƙoƙon bara na ainihi wanda shi ne mai bara ke miƙawa domin karɓar abin sadaka.

    [24] Sarkin Gulbi, (2007: 23) ya bayyana ma’anar bara da cewa: “… wata hanya ce ta roƙon jama’a da wasu mutane kan bi bisa waɗansu dalilai don neman abin da suka ci ko suka sha ko suka yi sutura ko ma suka ajiye don biyan wasu buƙatu na rayuwa.

    [25] A wancan lokaci, babban abin da ya ba ni ƙarfin guiwa tare da karkata zuciyata wajen mayar da hankali kan wannan taimako shi ne labaran waɗannan tashe-tashen hankula da nake karantawa a waya. Duk da a cikin mamun akwai dattawa da suke ta’ammuli da rediyo, matasa irina na da yawa, waɗanda kuma wayoyin hannunmu su ke matsayin rediyonmu. A intanet muke samun labaran yau da kullum.

    [26] Misali, Government Girls Secondary School Kotorkoshi da Government Day Secondary School Mada da sauransu.

    [27] Misali, Sakateriyar ƙaramar hukumar Tsafe

    [28] Karin maganar zamani shi ne nau’in karin maganar da ake ƙirƙira a zamanin yau. Mafiya yawancin ire-iren karuruwan maganar suna da tsoffin karuruwan magana makamantansu.

    [29] A wasu baitukan waƙar, sha’irin ya ba da shawara ga hukuma da sauran al’umma baki ɗaya dangane da yadda za a shawo matsalar waɗannan tashe-tashen hankula. Yana cewa:

    Ni sha’írin nan ‘yar shawarata ga ta,

    Wurin hukuma ni ma gudummuwata,

    Tsayin daka ku yi don kare al’ummata,

    Jami’an tsaronmu ciki da maha’inta,

    Ku sanya lura cikinsu kun gaggane.

     

    Bora da mowa kul kar ku wawware su,

    In kun ka gano tabbas ku hukunta su,

    Wurin hukuncin kul kar ku bambanta su,

    ‘Yar shawarata ƙin garkuwa da mutane.

     

    A sa idanu sosai ga infomansu,

    Jami’an tsaro na sirri a alkinta su,

    Dama cikakka a ba su sui aikinsu,

    ‘Yan sanda soji a ba su duk ƙarfinsu,

    Don daƙilewar ‘yan garkuwa da mutane.

     

    Mu ‘yan ƙasa kau gare mu shawarata,

    Aikin alkhairi mu yi mu nuna a yi ta,

    Har addu’o’i mu rinƙa yi gun bauta,

    Kamun ƙafa na duk matsalar Allah kyauta,

    Babbar musifa ta garkuwa da mutane.

     

    Ko ƙyas bayani in mun ji kar mu rufe ta,

    Mu kai rahoto ga jami’ai su bahasta,

    In mun yi wannan Allahu za ya tsayatta,

    Allahu amsa duk matsalar ga ta kwanta,

    Babbar musifa da ta damu dukka mutane.

    [30] A nan ana nufin waƙar da aka rera a situdiyo.

    [31] An samu waɗannan bayanai sakamakon hirarraki da aka yi da Aminu, (2019), Almustapha, (2019) da Hassan, (2019).

    [32] Babban misali a nan shi ne, ko da ayyukan ta’addanci kafefen watsa labarai za su nuna, sukan tabbatar da cewa sun kauce nuna wasu ɓangarororin. A kafafen sada zumunta kuwa, akan sanya kowane irin labari ko odiyo ko bidiyo. Sau da dama akan ci kawo da bidiyo na yadda ake yanka mutane ƙarara, ko kuma ake sassara su gunduwa-gunduwa. Akan samu lokuta da kamfanin Fesbuk ke bayyana wasu daga cikin bidiyoyi ko hotuna da ake ɗorawa a matsayin masu ta da hankali (violent).

    Wani lokaci har takan cire su. Misali, akwai bidiyon da aka ɗora ɗauke da bayani a sama (wanda wannan bincike ba zai kawo bayani ko bidiyon ba saboda dalilai na tsaro) inda wanda ya ɗora bidiyon da kansa yake nuna ba kowa zai iya kallo ba “Amma fa sai mai ƙarfin zuciya.”

    [33] An ɗauko shi ranar 29 ga watan 12, shekarar 2019. https://www.facebook.com/search/photos/?q=killings%20in%20zamfara&epa=SERP_TAB

    [34]An ɗauko shi ranar 29 ga watan 12, shekarar 2019.

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken: Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Kunya Take

    Yadda Kunya Take

    “Kunya tana kawo dukkan alheri” (Manzon Allah SAW)

    Kunya wata ɗabi’a ce da take hana mutum aikata rashin ɗa’a ga Allah ko ga mutane. Kunya ɗabi’a ce da Allah ya yi umarni da shi tun tale-tale ba a addinin musulunci kaɗai ba, duk addinai kunya abu ne da aka yi umarni da shi, kuma abu ne mai kyau.

    Wannan ya sa Manzon Allah SAW yace: “Yana daga cikin abinda mutane suka gada daga kalaman hikima na Annabawa magabata – shi ne – Idan ba ka jin kunya, toh ka aikata abinda ka ga dama” Allah Ta`ala ya ba mu labarin wasu `yanmata da Annabi Musa ya shayar da dabbobinsu lokacin da ya bar Masar ya nufi Madyana a cikin suratul ƙasas.

    Wannan ƙissar an kawo ta a littafin Linjila ta Annabi Isa (AS) a wannan ƙissar an nuna yadda waɗannan ‘yanmata ko ɗaya daga cikinsu take ta jin kunya lokacin da za ta ta kai Annabi Musa AS wurin mahaifinsu ta yadda tana tafiya amma tana jin kunya.

    A addinin musulunci wanda yake addinin ne da bai bar komai ba mai kyau sai da ya yi umarni da shi, sannan duk wani abu mummuna ya yi hani da shi, ya yi umarni da jin kunya. Manzon Allah SAW ya ce “ Kunya tana daga cikin imani”.

    Kunya a addini ta kasu kashi biyu:

    Kunyar Allah; wanda shi ne mutum ya rinƙa ganin girman Allah ta yadda ba zai aikata wani abinda ya saɓa wa umarnin Allah ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba. Idan mutum yana jin kunyar Allah to, ba zai aikata abinda Allah ya hana shi ba ko ya ƙi aikata abinda Allah ya umarce shi ba, saboda ya san Allah yana ganinsa. Wannan zai sa ya rinƙa ganin girman Allah.

    Kunyar mutane; wannan tana ƙasa da wancan na farkon. Kunyar mutane tana hana mutum aikata abinda ya ga dama a cikin rayuwar yau da gobe a cikin mutane. Zai hana shi aikata abinda Allah ba ya so. Ba wai don mutum ya ƙi aikata wani abu dan tsoron Allah ba, sai dan kunyar mutane. A’a, Bahaushe ya ce: ana barin halal don kunya. Abinda ake nufi shi ne, wani abin ba saɓa wa Allah ba ne, amma a al’adance ba daidai ba ne, idan dai addini bai wajabta shi ba, toh mutum zai iya bari don kunyar mutane. Wannan shi ma abu ne mai kyau.

    Manzon Allah SAW da kansa an rawaito cewa yana da tsananin kunya kamar yadda budurwa take da kunya. An san yadda budurwa- a da- su ke da kunya. Shi yasa Manzon Allah SAW ya ce idan aka tambayi budurwa kan maganar aure, toh shirunta shi ne amsa. Wannan ya nuna irin kunyar da budurwa take da shi ba zai ba ta dama ta amsa kai tsaye ba.

    Haka aka rawaito ce wa Sayyidina Uthman RA yana da tsananin kunya. Manzon Allah SAW ya ce: har Mala’iku suna jin kunyar Sayyidina Uthman. Manzon Allah ya ce shin ba zan ji kunyar wanda mala’iku suke jin kunyar sa ba.

    Nana Aisha RA an rawaito tana cewa: Da aka binne Manzon Allah SAW a ɗakinta da Sayidina Abubakar, tana iya cire kayanta ko mayafinta idan ta shiga ɗakinta, saboda mijinta ne da mahaifinta, amma da ka binne Sayyidina Umar a ɗakin sai ta ce sai na daina cire kayana ko mayafina a ɗakin saboda ina jin kunyar Sayyidina Umar. Duk da ba a raye yake ba, yana kabarinsa, amma tana jin kunya cire mayafinta a inda aka binne shi.

    Ba a musulmi ba kaɗai, har cikin waɗanda ba musulmi ba ana samun masu kunya saboda ɗabia’a ce mai kyau. A tarihin babban malamin nan Sir Issac Newton, ana faɗin cewa mutum ne mai kunya sosai da kamun kai, har ta kai ba ya son magana sosai a gaban jama’a.

    A mata kuma akwai irin su Isabella Clara Eugenia (1566 – 1633) duk da cewa mai mulki ce sosai, amma mace ce mai kunya da kamewa sosai. Akwai Maria Sibylla Merian (1647 – 1717) wadda tana daga cikin mata kaɗan da suka shahara a ɓangaren kimiyya a wacan lokacin, amma ta zaɓi gudumawarta ya fito fili ba ita ba, saboda ta fifta kunya, kamun kai da mutunci.

    Ga su ire iren Sarauniya Alexandra(1844 – 1925), matar Sarki Edward VII, `yar sarakai ce daga ƙasar Denmak, kuma matar basarake amma ba ta jefar da kunya, mutunci da kamun kai ba. Da waɗannan ɗabi`u ake gane ta duk inda ta shiga a Ingila alokacin duk da ba ta yawan fita jama`a.

    An kawo waɗannan ne don a nuna kunya ba addinin musulunci ne kaɗai ya yi umarni da ita ba, har ma sauran addinai da al`ummu daban daban. Kuma abu ne da mutane suke ƙaunar mai wannan sifar, da kuma yaba masa.

    Kunya ba ƙauyanci ba ne, ba kuma rashin wayewa ko gaɓanci ba ne, a a, ɗabi`a ce mai kyau. Manzon Allah SAW ya ga wani mutum yana yi wa ɗan`uwansa faɗa kan cewa ya faye jin kunya. Sai Manzon Allah SAW ya ce masa: ƙyale shi, kunya ba abinda take kawowa sai alkhairi” wannan ya nuna mana kunya alheri ce, ba kauyanci ba ne ko rashin wayewa. Kuma rashin kunya ba wayewa ba ne kuma ba wayo ba ne ko birnanci.

    A wannan zamanin musamman na Social Media, matasa da yawa sun tsame kansu daga jin kunya, musamman mata, waɗanda su ya kamata su kasance kan gaba wurin nuna wannan ɗabi`a kyakkyawa. Abubuwa na baɗala, lalacewa da rashin albarka duk sun yawaita a tsakanin matasa, ba don komai ba sai rashin wannan ɗabi`a ta kunya.

    Manzon Allah SAW ya yi gaskiya da ya ce “Wanda ba ya jin kunya ya aikata abinda ya ga dama” saboda rashin kunya da matasa ba ji yanzu, ya sa suke ta tsula tsiyar su a Social Media. Mata suna nuna tsaraici a fili, ana maganganun batsa, da baɗala, kai har ta kai ka ga ana nuna fasiƙanci a fili.

    Waɗanda suke waɗannan ayyukan na ashsha ba sa jin kunyar kowa, shi yasa suke abin da suka ga dama. Ka ga budurwa da ake sa ran za a same ta mai tsananin kunya amma ta fito duniya tana nuna tsaraicinta a fili ko tana magaganun batsa. Ba abinda ya jawo haka sai rashin kunya.

    Ci gaban zamani da ilimin zamani ba su ne suke ba da gudunmawa wurin ƙaruwar rashin kunya ba kaɗai, ga misalai nan da yawa na mata da maza wanda sun kai wani matsayi na karatun zamani amma sun kame kansu, suna da kunya da mutunci. Sannan a hannu guda kuma wasu ko bihim ba su sani ba, amma fitsara da sheɗanci ya zama musu abin tutiya.

    Manzon Allah SAW ya ce kunya ba ta kawo komai sai alkhairi, duk mai kunya toh zai ga sakamakon kunyarsa, ita ɗabi`a mai kyau ba ta faɗuwa ƙasa banza kuma tana da amafani. Akwai tagomashi mai yawa a nan duniya da kuma lahira. Kunya ba za ta bar mutum ya saɓa wa Allah ba, kunya ba za ta bar mutum ya wulaƙanta ba, kunya tana jawo wa mutum ɗaukaka da daraja.

    Rashin kunya takan sa mutum ya saɓa wa Allah, rashin kunya takan sa mutum ya wulakanta, takan jawo ƙasƙanci, taɓewa, da na sani da nadama. Manzon Allah SAW ya ce: “kunya tana da ga cikin Imani” duk mai kunya yana da imani, mara kunya shi kuma akasin haka. Imani kuwa ba inda yake kai mutum sai ɗa’a, ɗa’a kuma aljanna take kai mutum kai tsaye. Allah ka sa mu dace. Amin.

    Danna nan don karanta Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

    Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

    Sahabi Aliyu R.A ya faɗa ga Jabir ɗan Abdullahi R.A cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu huɗu; Addini, da Malami, da mai yin aiki da ilimin sa, sai Jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani, da kuma Mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyar sa.

    Marigayi Sheikh Dr.  Ahmad Bamba ya faɗa mana cewa ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskatar sa a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne. Saboda haka a  cewar sa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a a har ma da sani gami da riƙo na abinda bai gaskata ba.

    Rayuwa irin ta Dr Ahmad madubi ce ga ɗaukacin al’ummar musulmi. Shi mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martaba irin ta Annabi Muhammad s.a.w.

    Mai kimanin shekaru 82 da haihuwa, wanda ya rasu a yau Jummu’a 7/1/2021, Marigayi Dr Ahmad Bamba ya shafe ɗaukacin rayuwar sa wajen nema da kuma bayar da sani. Ya shafe sama da shekaru 20 yana ɗaukar darasi a Madina, masallacin Annabi Muhammad s.a.w.

    Sannan ya fassara Littafin Muwaɗɗa wallafar Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen larabci zuwa harshen Hausa, baya da karantarwar sa ga manyan littattafai irin su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunnani Darimi, da makamantan su duk a cikin harshen Hausa.

    Tabbas, rasuwar sa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar musulmi musamman Hausawa.Ya zo a cikin littafin ‘Al ilmu Huwal Imamu’ na Shekh Ibrahim Nyasi cewa Hanyar aljanna ta na hannun mutane guda huɗu; Malami, da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi. Shi Malami idan ya kasance mai gaskiya ne cikin zuciyar sa, tabbas Allah zai azurta shi da Hikima.

    Duk kuwa wanda aka bai wa Hikima alal haƙiƙa an ba shi gagarumar baiwa a nan duniya da gobe lahira kamar yadda yadda ya zo a cikin littafin Allah Alqurani. An tambayi Ɗan Mubarak cewa su wanene mutane?, sai yace ‘Malamai’, sai aka ce masa su wanene sarakuna?

    Sai yace masu gudun duniya, sai aka ce su wanene ƙasƙantattu?, sai yace masu cin duniya da addini. Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma. Abdul-Aswad yana cewa babu wani abu wanda yafi Ilimi ɗaukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da Malamai ke yin hukunci a garesu.

    AHNAF R.A yana cewa Malamai sun kusa kasancewa iyayen giji.. dukkan ɗaukakar da ba a ƙarfafe ta da ilimi ba, ƙarshen ta ƙasƙanci ce. Annabi Muhammad s.a.w ya faɗa cewa “Malamai, su ne magada Annabawa” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi)

    Allah Ta’ala kuwa ya faɗa cewa “Iyaka dai masu jin tsoron Allah su ne Malamai” (Suratul Fathi, 28). Babu buƙatar zafafa yabo ga marigayi Mallam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa ba ne a zamanin rayuwar sa, amma shi ne wanda ya jaddada Sunnah a ƙasar Hausa bayan da ta ɗauko dusashewa.

    Shi mutum ne wanda yake son Allah da Manzon sa, wanda yake tarbiyantar zukatan bayin Allah a kan bautar Allah ta tsanin manzon sa Annabi Muhammad s.a.w da mayar da lamurra a gareshi, kuma mutum ne maras kwaɗayi, mai darrajanta ilimi da darrajanta kansa, gami da faɗar gaskiya walau ga shuwagabanni ko ga mabiyansu.

    Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar musulunci, tushen darajar sa kuwa bai wuce ga riƙon sa ga sunnar Annabi Muhammad s.a.w ba, da tsantsenin sa kai kace shi ne Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri. Haƙiƙa, rayuwar sa ta kasance abar koyi ga al’ummar musulmi.

    Wani sashen masana sun faɗa cewa An fifita Imam Hasanul Basri a kan sauran Tabi’ai, saboda abubuwa guda 5;-

    1. Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.

    2. Ba ya hanuwa ga barin wani aiki face ya fara hanuwa daga gareshi.

    3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abinda Allah ya hore masa zai ba shi.

    4. Ya kasance tana wadatuwa da ilimin sa ga barin neman wani abu a wajen mutane.

    5. Ya kasance ciki da wajen sa duk ɗaya ne.

    Tabbas, duk waɗannan siffofi guda biyar sun tabbata ga Marigayi Shekh Ahmad Ibrahim Bamba. Ga shi kuma ya samu cikawa irin tasa.. da fatan Allah ya rahamshe su duka amin.

    Abdullah bin ‘Amr Ibnul ‘Ash ya ruwaito daga Annabi Muhammad s.a.w cewa “Lallai, Allah ba ya ɗauke ilimi daga hanawar sa ga bayin sa. Sai dai yana ɗauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakan mutane za su gushe, sai mutane su naɗa wawayen mutane a shugabanci. Sannan idan aka tambaye su, sai su yi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma su yi asara.” (Al-Bukhari da Muslim suka ruwaito).

    Kaicho da rashin babban masani Dr Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama ba ce. Tabbas, kowanne mai rai zai ɗanɗana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dr Ahmad ya koma ga mahaliccin sa, kowannen mu lokaci yake jira domin komawa zuwa ga Allah. Don haka ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa, da neman ilimi, da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.

    Da fatan Allah ya gafartawa Dr Ahmad Ibrahim Bamba, Allah ya tallafi bayan sa amin.

    Danna nan don karanta Cin Zarafin Ƙananun Yara Da Kariya A Bisa Haka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta II

    September 12, 2024

    ƁANGARE NA II: HANYOYIN SADA ZUMUNTA

    Musamman a wannan ƙasar Najeriya hanyoyin sada zumunta sun fara ɓulla ne daga shekara ta dubu biyu (2000) lokacin da aka fara amfani da wayar hannu mai amfani da layin waya.

    Da farko wayoyin da ake amfani da su, wayoyi ne da ba sa ɗauke da manhajar hanyoyin sada zumunta, da yawan mutane a lokacin ba hanyoyin sada zumunta ne a gaban su ba, kawai abinda su ka fi yi shi ne buga waya da amsa kira.

    Za a iya ce wa mafiya wayancin waɗannan hanyoyi ba a samar da su ba, balle ma a saka su a matsayin manhaja a wayar hannu. Misali, manhajar sada zumunta na 2go wasu ɗalibai na jami`ar Witwatersrand Johannesburge, suka ƙirƙire shi a 2007.

    Brian Acton da Jan Koum su ne suka ƙirƙiri manhajar Whatsapp a shekara ta 2009, Facebook kuma Nick Clegg, Sheryl Sandberg, Sean Parker, Mark Zuckerberg suka ƙirƙira a 2004 a Massachuset ƙasar Amurka. Twitter kuma a shekarar 2006 aka ƙirƙire shi, amma sai 2012 aka ƙaddamar da shi wanda Jack Dorsey, Noah Glass, Biz Stone da Evan Williams su ka ƙirƙira.

    Twitter (2006), Tiktok( 2016), Telegram (2012). Kafinsu akwai wasu hanyoyin na wasiƙu da sada zumunci kamar su hotmail, yahoomail (1997) da gmail (2004) da sauransu amma ba a samun su a manhajar wayar hannu. Waɗancan su ne aka fi sani a nan, amma akwai dubbansu suna nan ana ta amfani da su yau a faɗin duniya.

    A nan kasar, musamman a yankin mu na Arewa, da yawa daga cikin masu amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta ba su san waɗannan manhajoji ba sai kusan shekarar 2010 yau shekara goma sha –biyar ke nan. Sannan da yawa da ga cikin mutane ba su san babban dalilin samar da waɗannan manhajojin ba, balle su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

    Matasa na cikin `yan gaba dai gaba dai wurin amfani da waɗannan manhajojin. Ƙaramin misalin da zan bayar shi ne a cikin mutane miliyan hamsin (50M) da suka yi amfani da 2go a nahiyar Afrika miliyan 13 suna Najeriya kuma sama da kashi casa`in (90%) matasa ne.

    Wannan hasashe haka yake har yau a ko ina, matasa su ne kan gaba wurin amfani da waɗannan hanyoyi musamman a ƙasashe masu tasowa. Wannan ya na faruwa ne sakamakon rashin aikin yi da zaman banza da matasa suke fama da shi a ƙasashe masu tasowa wanda ci bayan tattalin arziki ke sabbaba shi.

    A yau ana ganin samari marasa aikin yi suna yin duk abinda za su yi dan su sami kuɗin da za su sayi data dan su sami damar amfani da waɗannan manhajoji na sada zumunta. Misali, Facebook idan mutum ba shi da data, idan kuma ba lite yake amfani da shi ba, toh a akwai abinda ake cewa “free mode” kwai za ka ga rubutu, amma hotuna ko bidiyo ba za su bayyana ba, sannan ba zai baka damar bin hanyar da za ka sami labari ba ko wani bayani ba wato “link”.

    Sau da yawa wannan yana hana mutane fahimtar asalin abinda aka yaɗa ko aka wallafa, sannan ya kan sa mutum ya yi sharhi na goyon baya ko akasin haka, ko ma ya yaɗa abinda ba shi ne ba.

    Abu mai mahimanci na gaba shi ne, mutane suna shiga abin da ba su da ilimi a kai. Wannan shi ne dalilin yin wannan rubutun. Sau da yawa babban malami zai yi bayani na ilimi mai zurfi a kan wani abu mai mahimmanci da ya shafi addini, a yaɗa shi ta hanyoyin sada zumunta, kwatsam sai ka ga wani matashi, ko wani ɗan tasha bai san dama ko hagu ba a kan abinda ya shafi ilimin addini, kawai sai ya ce wannan babban malamin nan “ƙarya” ya keyi, ko zai ci gyaran malamin.

    Ba don komai ba, kawai wannan hanya ta ba shi dama ya ga ko ya ji abinda wannan babban malamin ya faɗa. Wani babban abin takaicin shi ne shi, wannan matashi ko ɗan tashan ba zai iya kawo wata hujja na ilimi ba, sai soki-burutsu, jahilci da hayaniya.

    Misali ɗaya daga cikin misalai masu yawa shi ne mas`alar mutum ya ce ya saki matarsa da wasa ko da kuwa a shirin wasan kwaikwayo ne. Manyan malamai kamar Dr. Bashir Aliyu Umar, oon da Prof. Umar Sani Fagge sun yi fatawa a kan ce wa duk wanda ya aikata haka matarsa ta saku.

    Suka kafa hujja da hadisin Manzon Allah SAW ingantacce. Amma aka samu wasu waɗanda ba su wani abu na ilimin addini, kai wasu ma `yan tasha ne, suka rinƙa surutai na jahilci da rashin ladabi ga malamai da malanta da ƙoƙarin ƙaryata hadisin Manzon Allah SAW da molon ka.

    Ba abinda ya ba su wannan damar sai waɗannan hanyoyi na sada zumunta wanda suke ganin ilimi kamar abin banza da arhan malanta. Idan aka duba a baya za mu ga mas`aloli na addini, malamai da tsarekunsu su suke tattauna cikin girmamawa ta hanyar rubuce – rubucen ilimi.

    Amma yanzu saboda waɗannan hanyoyin na zamani sai a ci mutuncin malami, a zage shi, a faɗi munanan maganganu game da shi, ba tare da an kawo wata hujja ko wata magana ta ilimi ba saboda ba abin da za a iya faɗa da rashin ilimi.

    Sannan abu na biyu, wannan ya ba da dama kowa ya ga cewa zai iya zama malami saboda yawan yaɗuwar ilimin kayauta kuma cikin sauƙi. Kowa zai iya zama malami dare ɗaya. Wanda kuma ba haka ba ne, kuma ba ma zai yiwu ba.

    Abu na uku, waɗannan hanyoyin sun bai wa wasu `yan dagajin mutane damar yin sojan gona, su mai da kansu malamai, su tsoma baki a cikin abinda ya shafi ilimi, da ma faɗin duk abinda suka ga dama. Jahilai kuma suna nan birjik followers, masu sharing da masu like.

    Daga ƙarshe, waɗannan hanyoyin sun ba da gudumawa wurin yaɗuwar ilimi da wayar wa mutane kai game da addini, sannan a gefe ɗaya kuma sun ba da damar raina malamai da ilimi, rashin ganin girman ilimi da mahimmancinsa. Malamai sun zama ba komai ba, sannan malanta ta zama arha.

    Duk wanda baya ganin wanɗanda suke riƙe da tushen addininsa, (ilimi) da girma ta yaya zai ga girman addininsa? Gimama malamai yana daga cikin abinda zai sa mutum ya san daraja da girman addininsa.

    Whatsapp: 08039290267

    Karanta Malamai, Malanta Da Hanyoyin Sada Zumunta A Yau (1)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kira A Kan Haɗin Kai

    Kira A Kan Haɗin Kai

    ‘Yan Najeriya muna cikin wani muhimmi lokaci. Wata mummunar fahimta tana shiga cikin al’ummarmu, tyana canza yadda muke kallon ‘yan-uwanmu da kuma rage darajar kanmu da ƙaunar ‘ƴan’uwanta da ta kasance tana bayyana mu.

    Dole mu dakata mu yi wa kanmu wata muhimmiyar tambaya: a cikin rayuwarmu ta yau da kullum don neman abinci da ci gaba, shin mun taɓa tunanin addinin manomi wanda ya noma shinkafar da muke ci? Shin muna tambayar addinin likitan da ya rubuta maganin da ya ceci rayuwarmu? Idan muka buɗe famfo, shin muna tunanin ko injiniyan da ya tsara tsarin ruwan yana da aƙidarmu?

    Amsar ba ta da shakku, ’A a’. Ba mu yi haka ba. Muna saye, muna ci, kuma muna rayuwa, muna dogaro ga juna a cikin hanyar da ba a iya rabuwa. Rayuwarmu ta yau da kullum shaida ce mai ƙarfi game da haɗin kanmu.

    To, me yasa, a wasu fannonin rayuwa, muka ƙyale a raba mu? Me yasa muke tallata bambance-bambancen addini alhali kuwa tarihinmu na gaba ɗaya ya faɗi wani labari daban?

    Mun yi yaƙi don ‘yancin kanmu tare, a matsayin mutane ɗaya tare da manufa guda. Mun zauna tare a cikin ajujuwa, muna koyo daga malamai ɗaya, muna mafarkin makoma guda ga Najeriya. Muna ciniki tare, muna murna tare, muna makoki tare.

    Wannan rarrabuwa ba hanya ba ce ta Najeriya. Guba ce da ke raunana mu da kuma hana mu ci gaba. Duk gidan da ya rabu da kansa ba zai iya tsayawa ba, balle ya ci nasara a rayuwa.

    Hanyar Ci Gaba: Komawa ga Ƙimar Mu Na Gaba ɗaya

    Don maido da girmanmu, dole ne mu zaɓi haɗin kai da juna. Ga yadda za mu iya farawa:

    1.  Yi Bikin Asalin Mu Guda: Ganin kanmu a matsayin ‘yan Najeriya—’yan’uwa maza da mata na al’umma ɗaya. Imaminmu wani ɓangare ne na asalinmu, ba makami da za a yi amfani da shi a kan maƙwabci ba.

    2.  Ƙarfafa Tattaunawa: Ƙarfafa tattaunawar addini a cikin al’ummominmu. Bari shugabannin mu na addini su yi wa’azin soyayya da haƙuri. Lokacin da muka yi hira, muna rushe ganuwar tsoro da rashin fahimta.

    3.  Mai da hankali kan Manufofi Guda: Talauci, jahilci, da rashin ingantaccen tsaro wannan ba sa bambanta tsakanin Musulmi da Kirista. Waɗannan su ne abokan gabanmu. Kamata ya yi mu karkatar da ƙoƙarinmu don yaƙar waɗannan, maimakon yaƙi da juna. Ci gabanmu gaba ɗaya ya dogara da ƙoƙarinmu gaba ɗaya.

    4.  Maido da Maganar Mu: Dole ne mu ƙi maganganun da ke neman raba mu. A shafukan sada zumunta da kuma a cikin al’ummominmu, mu zama jakadun zaman lafiya, muna raba labarun haɗin kai da abota waɗanda suka fi yawan labarun rikici.

    Najeriya ƙasa ce mai girma, mai albarka da ɗimbin albarkatun ɗan adam da na halitta. Ƙarfinmu yana cikin hadin kai. Kada mu ƙyale rashin fahimta ya canza mana tunani. Muna buƙatar juna don rayuwa da ci gaba.

    Mu zaɓi hanyar ‘yan-uwanta. Mu zaɓi hanyar haɗin kai. Mu zaɓi hanyar Najeriya ɗaya.
    A Haɗe Muke Da Ƙarfi, A Rabe Muke Da Rauni.

    Karanta Yaushe Ne Kwanakin Layya Suke Ƙarewa?

    Edita@rumasau-kallamu

  • Amfanin Haƙuri

    Amfanin Haƙuri

    Haƙuri: Shi ne danne zuciya a kan wani abu mara kyau, wanda ya baƙantawa mutum zuciya.

    Haƙuri yana da matuƙar amfani ga mutane, kamar yadda ya zo a cikin littafin Sheikh Abdulrahim bin Ahmad Alkadhi mai suna “Daƙa’ikul khabar” shafi na 17 babi na goma sha biyu yace, labari ya gangaro cewa wanda aka jarabce shi da wata masifa, sai ya yaga tufafin sa ko ya bugi ƙirjin sa (to hukuncin wanda ya aikata haka) kamar (wanda) ya riƙi makami ne zai yi yaƙi da Allah (Subhanahu wata’ala).

    Sannan kuma an ruwaito daga Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) yace wanda ya ɓalle ƙofa ko ya yaga tufafin sa ya yi da wata masifa ta same shi ko ya bugu wajan zaman sa ko ya sare bishiya ko ya yanke gashin kan sa (saboda tsanani masifar da ta same shi), to za a gina masa gida na wuta a kan kowane gashi (wanda ya cire), sa’annan kuma Allah ba zai karɓi aikin sa na farilla ba ko na nafila matuƙar yana kan wannan hali.

    Har ila yau, Allah zai ƙuntata ƙabarinsa, kuma zai tsananta yi masa hisabi, sannan kuma dukkanin mala’ikun da suke sama da ƙasa za su dunga tsine masa, haka kuma za a rubutawa laifuffuka guda dubu a gare shi, sannan zai tashi a cikin ƙabarin sa tsirara.

    Haka kuma, wanda ya karya gefan jikin sa, saboda wata masifa, to Allah zai karya addinin sa, idan kuma ya bugi ko ya mari kumatun sa ko ya azabtar da fuskar sa, to Allah (Subhanahu wata’ala) ba zai kalle shi ba da rahmar sa ba ranar alƙiyama.

    Bugu da ƙari, kuma ya zo a cikin shafi na 18, babi na goma sha huɗu a cikin wannan littafin yace Sayyadina Aliyu bin Abu-ɗalib (karramallahu wajhahu) yace “haƙuri ana yin sa ne ta hanyoyin guda uku; na farko yin haƙuri a kan yi wa Allah biyayya, na biyu yin haƙuri a kan saɓawa Allah, na uku haƙuri a kan wata masifa wacce ta samu mutum.

    Saboda haka, duk wanda ya yi haƙuri a kan yi wa Allah biyayya, to Allah zai ba shi daraja guda ɗari, sa’annan kuma ko wace daraja yawanta ta kai tsakanin sama da ƙasa.

    Wanda kuma ya yi haƙuri a kan saɓawa Allah, to Allah zai ba shi daraja guda ɗari shida ranar lahira, haka kuma kowace dajara yawan ta ta kai faɗin sama da ƙasa, wanda kuma ya yi haƙuri a kan wata masifa wacce ta same shi, to Allah zai ba shi lada ba tare yi masa hisabi ba (ranar lahira).

    Karanta Tarihin Farfesa Abdallah Uba Adamu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Bet9ja Cacar Zamani

    Bet9ja Cacar Zamani

    Wata nau’i ce ta caca da ake yin ta ta yanar gizo, mutum za ya yi rijista da bet9ja, ya buɗe account, ya sa kuɗi gwargwadon yadda zai shiga, sa’annan sai ya canka tsakanin ‘yan wasa da za su buga ƙwallo, ya ayyana cewa wane cikin minti kaza misali za ya sa ƙwallo kaza a raga, ko kuma wane zai jefa ƙwallo kaza, ko club kaza shi ke da galaba ko nasara.

    Idan zaɓinsa ya tabbata zai iya cin dubu 100 a Naira 200 da ya shiga, wannan kuwa ita ce haƙiƙanin caca da Allah (SWT) ya haramta, wadda ta ƙunshi abubuwa kamar haka:

    1- Garari, rashin tabbas, ko ya ya ƙanƙantar kuɗin da za a ka sa.
    2- Cin dukiyar mutane ba tare da wata wahala, ka sa 200 ka kwashe dubu 100, a banza.
    3- Haifar da gaba da ƙiyayya da hana salla da ambaton Allah (SWT), kamar yadda Allah (SWT) ya bayyana.

    A yau matasa ganin wannan banzar ta sa suka yawaita cikinta, tunaninsu ya kau daga hanin Allah (SWT) ga caca, a halin shiga cikinta zai janyo wa ma’abocinta matsaloli da dama kamar:

    1- Saɓa wa hani na Allah (SWT), domin Allah ya yi umarni da a nesanci caca.
    2- Birgima da cuɗanya cikin datti da ƙazanta ta Shaiɗan, bal Allah (SWT) ya ce: “Datti ne daga aikin Shaiɗan”.
    3- Rashin rabautuwa duniya da lahira, domin Allah (SWT) ya ce: “Ku nesance su domin ku samu rabauta”.
    4- Za ya samu matsala ta adawa da ƙiyayya da yan’uwansa.
    5- Za ya samu matsala ta ƙaranta yin salla da zikiri ko ma ya daina
    6- Kamar yadda ma’abocin sa zai:
    a- Sangarce a harkar neman halaliya da lalaci saboda ya ga banza.
    b- Zai haifar masa da damuwa da jinyar gangar jiki dss.

    Allah ya tsare mu.

    As-Sheikh Dr. Isa Garba Nayaya
    11/12/2020

    Karanta Shigowar Nufawa Ƙasar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025

    Fassarar Huɗubar Juma’a daga Masallaci mai Alfarma 7th February 2025

    Mai Huɗuba: Sheikh Dr. Abdullah Awwad

    Mai Fassara: Dr Usman Muhammad Ahmad

    Shugaban Shashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗubar Masallaci Mai Alfarma: Sheikh Dr. Abdullah Awwad 12/06/1446H

    HUƊUBA TA FARKO

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Masa, muna neman taimakonSa da gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunammu da munanan ayyukammu, duk wanda Allah Ya shiryar, to, babu mai ɓatar da shi, kuma duk wanda Ya batar, to babu mai shiryar da shi.

    Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa.

    (Ya ku waɗanda kuka ka yi Imani, ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kusa Musulmi)

    (Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga shi, kuma ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su, kuma ku ji tsoron Allah Wanda kuke yi wa juna magiya da Shi, kuma ku kiyaye yanke zumunci, lallai Allah Mai kula da ku ne)

    (Ya ku waɗanda kuka yi Imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacce take daidai, Zai kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubbanku, kuma duk wanda ya yi ɗa’a ga Allah da ManzonSa, to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)

    Bayan haka:

    Lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi sharrin lamura su ne ƙirƙirarru, kuma kowane ƙirƙirarren abu bidi’a ne, kuma kowace bidi’a ɓata ce.

    Bayan haka:

    Ya ku mutane! Lallai Allah Wanda hikimarSa ta ɗaukaka, Ya halicce ku ne domin ku bauta Masa, kuma Ya kallafa muku ayyukan da za ku iya, don haka, ku aikata su. Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa, da nisantar abin da ya hana da manyan zunubai, kuma ku yi la’akari da abin da ke cikin Alƙur’ani mai girma na ababen lura.

    Haƙiƙa Allah ya saukar da shi a gare ku don ku bi shi, domin lallai yana daga cikin mafi girman tanadi na samun tsira, saboda abin da yake ƙunshe da shi na farillai da mustahabbai da halacci da haramci da wa’azozi da jan kunne, to me ya sa zukata ba sa bin umarninsa, kuma ba sa barin abin da ya hana kuma ya tsawatar, kuma ba sa jin tsoron wanda ya san bayyane da boyayye cikin ayyukan bawa, da sirrikansa da kuma zahirinsa!

    Haƙiƙa gafala ta yi musu katutu, kuma sha’awace-sha’awacen zukata sun kautar da su daga lura da ababen suka saɓa musu, sai su ka ji daɗin ɗanɗanon ɓarnarsu, kuma suka jahilci ɗacin sakamako da za a musu a lokacin mutuwarsu, don haka, sai suka doge a kan saɓonsu, ba su ji tsoron yini da za a damƙe su ta ƙafafunsu da makwarkwarɗarsu ba.

    Ranar da za a ninka azaba ga wanda ya bar salla kuma ya tozarta ta, wanda ya yi sakaci game da lamarin zakka kuma ya ƙi ba da ita, wanda ya keta alfarmar watan Ramadana ya sha azumi a cikinsa, wanda ya jinkirta faralin Hajji alhalin yana da ikon yi kuma ba tare da wani uzuri ba.

    Ranar da za a shayar da mashayin giya da ruwan ɗiwa, a kwankwaɗa masa abin da zai ɗanɗani kaito da kuɗarsa da shi daga ruwan mugunyar ‘yan wuta. Ranar da za a sako harasan wuta ga mazinata da fajirai, kuma a dake su da bulalunta ta gabansu da bayansu.

    Maciyin riba kuma ya ci daga bishiyar zaƙƙum, lallai zina da cin riba ba su taɓa bayyana a cikin wasu mutane ba face sai sun sauko wa kansu da azabar Allah, muna neman tsarin Allah daga fushinsa da azabarsa, kuma azzalumai za su wanzu a cikin iska mai tsananin zafi da kuma tafasasshen ruwa, da kuma inuwa ta turnuƙun hayaƙi.

    Ku saurara! Lallai duk wanda ya shagala da kansa, to, ba zai samu lokacin aibata waninsa ba, kuma duk wanda gazawarsa ta dame shi, to, idanuwansa za su makance daga ganin gazawar waninsa da abin da yake aikatawa, don haka, ku kame harsunanku daga keta mutuncin mutane- Allah ya muku rahama- saboda lallai Allah Yana kusa da harshen duk wani mai magana, kuma duk wanda ya keta mutuncin ɗan’uwansa kuma ya cutar da shi da magana ko da aiki, to, Allah Shi ne Abokin husumarsa.

    Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: ((Waɗanda suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyananne)).

    Babban malami Ibnu Usaimin Allah Ya masa rahama ya ce: “Wato suna jifansu da abin da ba su aikata ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage, wato ƙarya. Ƙage kuma, shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da bai tare da shi; don haka ne ma lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tambaya game da yi da wani, sai ya ce: “Shi ne ka ambaci ɗan’uwanka da abin da yake ƙi”. Ya ce: Ya Manzon Allah! Idan ɗan’uwana yana tare da abin da nake faɗi fa? Ya ce: “Idan yana tare da abin da kake faɗi, to haƙiƙa ka ci namansa, idan kuma ba ya ɗauke da shi, to, haƙiƙa ka masa ƙage”. Muslim ne ya rawaito.

    Sannan Allah Ya masa rahama ya cigaba da cewa: Kuma cutar da Mumini yana kasancewa da magana da kuma aiki, kuma hanyoyinsa na da yawa, lallai waɗanda suke cutar da muminai ba tare da sun yi laifin komai ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage wa kawunansu, kuma shi ne ƙarya, da kuma laifi bayyananne, shi ne uƙuba mai girma, Allah Ya amintar da mu”. A nan maganarsa ta ƙare, Allah Maɗaukakin Sarki Ya masa rahama kuma Ya saka masa da alheri bisa hidimarsa ga Musulunci da Musulmi.

    Ya Ubangijinmu, Ka sanya harsunanmu su kasance masu tsarki, zukatanmu su kasance masu ƙaunar muminai. Ya Ubangijinmu, Kada Ka sanya ƙiyayyar waɗanda suka yi imani a cikin zukatanmu. Ya Ubangijinmu, lallai Kai Mai tausayawa ne, Mai jinƙai.

    Ya Allah Ka tsare mu daga son zuciya, da kuma bin zuciya mai yawan umarni da mummuna, sannan Ka tsare mu daga shaiɗan la’ananne. Ku ji tsoron Allah, ya ku bayin Allah! Kuma ku yi gaggawar yin amfani da damar da aka ba ku matuƙar tana nan. Ku ci gaba da ingantattun ayyukanku muddin ana karɓar su, kuma ku kakkaɓe kawunanku daga aikata laifi matuƙar igiyar rayuwa bata katse ba.

    Kuma ka rage buri, ya kai wanda ya ruɗu, domin rayuwa gajeriya ce. Ka tsarkake aikinka ga Allah domin Mai duba aikin Mai gani ne, kuma ka bar kusakuranka, domin lissafin mai tsauri ne. Kuma ka gyara laifukanka ta hanyar tuba, domin makoma ta yi maka daɗi.

    Imam Ahmad -Allah Ya yi masa rahama, da Imamul Bukhari Allah Ya yi masa rahama a cikin “Al-Adabul-Mufrad”, da kuma Albaihaƙi da isnadi mai kyau, sun rawaito daga Abdullahi bin Amr Allah ya yarda da su: cewa Annabi tsira da amincina Allah su tabbata a gare shi ya ce:

    (Ku yi jinƙai, za a jiƙanku, ku yi gafara, za a gafarta muku. Kaicon waɗanda suke zama kamar masakin magana. Bone ya tabbata ga masu dogewa da yin abin da suka sani cewa mummuna ne). Ma’anar “Masakin magana”: su ne waɗanda suke sauraron magana amma ba sa fahimtar ta, kuma ba sa aiki da ita.

    A’uzubillahi minash shaiɗanir rajim, bismillahir Rahmanir Rahim: (Sai ka yi bushara ga bayina () Su ne waɗanda suke sauraron magana kuma su bi mafi kyawun ta, Waɗannan ne waɗanda Allah ya shiryar, kuma waɗannan su ne ma’abota hankula).

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da kuma dukkan Musulmi, don haka, ku nemi gafaranSa, lallai Shi Mai yawan gafara ne kuma Mai jinƙai.

    HUƊUBA TA BIYU

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai ɗorewa tare da wanzuwarSa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo da ba ya ƙarewa sai idan Ya nufa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo na dindindin, ba abin da zai samu wanda ya faɗe shi sai yardarSa. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo dauwamame a kowane ƙiftawar ido da numfashin abu mai rai.

    Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayensa da Sahabbansa da waɗanda suka bi shiriyarsa kuma suka yi kira irin kiransa.

    Bayan haka:

    Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmi don ku rabauta, ku fargar da kawunanku daga gafala, kuma ku bi hanyar tsira, idan ba ku aikata haka ba kuka tasaya, to fa ku sani cewa shi ajali tafiya yake da ku, kyawawan ranaku na wucewa, ita mutuwa kuma tana farke a farfajiyarku, kuna nufin samun duniya Shi kuma Allah Yana nufin Lahira.

    Ya ku bayin Allah!

    Ku yawaita salati da sallama ga mafakar mutane a babbar matsaya ranar Alƙiyama, Annabinmu kuma mai cetonmu Muhammadu tsira da amincin Allah mai yawa su tabbata a gare shi da Alayensa.

    Ya Allah ka ƙara yarda da Halifofi shiryayyu da sauran Sahabbai gaba ɗaya, da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Ya Allah Ka amfanar da mu da son su, kuma Ka tashe mu cikin tawagarsu, kuma kada Ka karkatar da mu daga bin tafarkinsu da hanyarsu ya Mafi karamcin masu karamci. Ya Allah! Ka ƙarfafa Musulunci da Musulmi, Ka ɗaukaka Kalmar gaskiya da Addini da falalarka.

    Ya Allah! Ka ƙarfafa Shugabanmu kuma Majiɓincin lamuranmu da gaskiya da yin daidai da dace, Ka yi riƙo da hannunshi ga ayyukan nagarta da taƙawa, Ka azurta shi da mashawarta nagari, Ka ɗaukaka AddininKa da kalmarKa da shi, Ka sanya shi ya zama mai taimako ne ga Musulunci da Musulmi, kuma Ka haɗa kan Musulmi da shi a kan gaskiya da shiriya ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah! Ka datar da shi da Yarimansa da ‘yanuwansa da mataimakansa zuwa gaskiya da shiriya da kuma duk abin da yake akwai gyara ga al’umma da ƙasa a cikinsa, Ka saka musu da alheri saboda kulawarsu da Masallatai biyu masu alfarma da daraja, da kuma duk abin da suke gabatarwa saboda cigaban Musulunci da Musulmi.

    Ya Allah! Ka datar da masu jagorancin Musulmi ga yin aiki da Littafinka da Sunnar Annabainka Muhammadu – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Ka sanya su su zama rahama ga bayinKa Muminai, Ka haɗa kansu akan gaskiya ya Ubangijin talikai, Ka kuma datar da duk jagororin Musulmi ga duk abin da yake gyara ne ga Ƙasa da mutanen.

    Ya Allah! Ka saki labulan suturtawarka akan ƙasarmu da kuma dukkan ƙasashen Musulmi. Ya Allah! Muna kamun ƙafa da yardarKa kada Ka yi fushi da mu, kuma muna kamun ƙafa da amincinKa kada Ka yi mana uƙuba, kuma muna nema tsarinka daga azabarKa, ba mu iya kaiwa matuƙa wurin yaɓonKa kamar yadda Ka yabi kanKa.

    Ya Allah! kada ka yi mana azaba da munanan ayyukanmu, kuma kada Ka kama mu da abin da wawayen cikinmu suka aikata, Ka isar mana duk wani abin da ya dame mu, kuma Ka kasance Mai ƙarfafawa da ba da nasara a gare mu.

    Ya Allah! Lallai mu muna roƙon Ka farin ciki da zai lulluɓe zukatanmu da ‘yantuwar Masallacin Ƙudus daga hannu Yahudawa ‘yanƙwace, Ya Allah Ka jefe su da kibiyarKa da ba ta kure, Ka saukar musu da uƙubarKa mai tsanani, ya Majiɓincin masu rauni, ya Ma’boci ƙarfi mai tsanani! Ya Mai gudanar da giragizai! Ya Mai rusa rundunonin maƙiya! Ka saukar wa ‘yanta’adda azaba mafi tsanani, Ka sanya su abin ɗaukar izina ga masu hankali.

    Ya Allah! Muna roƙon Ka farin ciki saboda samun nasarar Musulmi a kan abokan gabansu azzalumai. Ya Allah! Lallai mu muna roƙon gafararKa, saboda lallai Kai Ka kasance Mai yawan gafara ne, don haka Ka saukar mana da ruwan sama mamako, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Ka saukar mana da ruwan sama, ya Allah! Lallai mu wata halitta ce cikin halittunKa, don haka kada Ka hana mu falalarKa saboda zunubanmu.

    Ya Allah! Ka karɓa daga gare mu lallai Kai Mai ji ne kuma Masani, kuma Ka karɓi tubarmu lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai tsausayi. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Mazanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Danna nan don karanta Addu’ar Shiga Masallaci

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Nasiha A Kan Mata

    Nasiha A Kan Mata

    MATA 10 WAƊANDA  ALLAH YA TSINE MUSU: –

    ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
    1. Mata masu tsaga fuskokinsu. –

    ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ

    2. Mata masu aske gashin gira. –

    ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
    3. Mata masu kankare hakori (wushirya). –

    ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
    4. Mai ‘karin gashi da wadda ake ƙara mata gashi. –

    ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺯﻭﺟﻬﺎ
    5.Matar da mijinta ya yi fushi da ita. –

    ﺍﻟﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺕ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ
    6. Mata masu shigar maza.

    ﺯﻭﺍﺭﺍﺕ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
    7. Mata masu yawan ziyartar kabur-bura (maƙabarta).

    – ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺎﺕ
    8. Mata masu kururuwa akan mamaci. –

    ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ
    9. Mata masu auren kashe wuta. –

    ﻛﺎﺳﻴﺎﺕ ﻋﺎﺭﻳﺎﺕ ﻣﺘﺒﺮﺟﺎﺕ
    10. Mata masu bayyana tsiraicinsu.

    Ka da ku manta TSINUWA ita ce nisanta daga rahamar Allah!
    ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ” ﻳﺎﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺗﺼﺪﻗﻦﻭﺃﻛﺜﺮﻥ ﻣﻦ ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭﻓﺈﻧﻲﺭﺃﻳﺘﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ ” ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
    Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘Yaku taron mata! ku yi sadaƙa, kuma ku yawaita neman gafara (Istigifari) Allah ya gafarta Mana.

    Danna nan don karanta Abin Da Ya Kamata Mu Sani

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

  • Nasiha A Kan Rayuwa

    Nasiha A Kan Rayuwa

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi Yana cewa, “Ku yi ƙoƙarin danne abubuwa guda uku a cikin ranku, da rayuwarku.”

    1. Fushi
    2. Sha’awa
    3. Maganganunku.

    Ku himmatu wajen aikata abubuwa biyu:

    1. Ayyukan alhairi.
    2. Abokai na gari.

    Ku ci moriyar abubuwa uku:

    1. Ƙarfi
    2. Lokaci
    3. Lafiya.

    Ku nemi abubuwa uku:

    1. Gafarar Allah
    2. Ilimi
    3. Hikima.

    Allah ya ba mu ikon kiyayewa.

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu

    Domin karanta Nasiha danna nan