Category: Ilimin Kasuwanci

Mun samar da wannan ɓangaren ne, domin samar da ingantaccen ilimin kasuwanci a sauƙaƙe a cikin harshen Hausa tare da masana fannin. Za ku iya kai wa gare su ta hanyar amfani da kwamfutoci ko wayoyin hannu cikin sauƙi.

WikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa domin koyo ko koyarwa.

  • Jagoran Noman Waken Soya

    Jagoran Noman Waken Soya

    Gabatarwa

    Waken soya yana daga cikin amfanin gonar da aka ɗauka a matsayin abinci; wanda ake shukawa kuma ake sarrafawa a kowace nahiya. Ana samun nasarar shuka waken soya a jihohi masu yawa na Nijeriya ta hanyar amfani da iri ɗan kaɗan ko kuma kayan aiki.

    Danna nan domin dauko cikakken littafin

    Noman waken soya ya bunƙasa sakamakon amfani da yake da shi ga jikin ɗan Adam, da kuma amfani ga tattalin arziƙi, da yawan sarrafa shi a gidaje. Shi ginshiƙi ne wajen samun man girki, ana samun kashi 18 zuwa 22 na man girki a cikin ƙasa. Yana kuma ƙunshe da shi 40 zuwa 42 na sinadarin gina jiki.

    Hoto Na farko: Waken Soya

    Yanayi Da Ake Buƙata Wajen Noman Waken Soya

    • Yanayi da nau’in ƙasa yana da tasiri wajen haɓakar waken soya. Waken soya yana yi sosai a Arewacin Nijeriya, inda yawan ruwan sama ya wuce mili-mita ɗari bakwai (700mm) zuwa dubu ɗaya (1000mm).
    • Waken soya tsiro ne mai son gajeren yini sannan furensa yana buƙatar gajeren yini. Ana iya shuka shi a gona wadda ma’aunin PH ɗin ƙasar ya fara daga 4.5 zuwa 5.5. Ba a shuka waken soya a ƙasa mai tsakuwa ko gona mara nagarta domin zai sa shukar ta tsiro cikin rauni.
    • Yana buƙatar yanayi mai zafi, tsakanin yanayin zafi 22 oc zuwa 35 oc.

    Aikace-aikacen Da Ake Buƙata Domin Noman Waken Soya

    Gyaran Gona

    • Sharar gona; Za a cire dukkan ciyawa a filin, sannan a shirya gadon-shuka da hannu ta hanyar amfani da fatanya ko wani kayan aiki da aka maƙalawa shanu ko kuma motar gona (tarakta).
    • Kasar da aka gyara da kyau na sanya shukar fita da kyau da rage haɗarin ciyawa. Za a iya shuka a kan kunya ko a gyararren fili.
    Hoto Na Biyu: Gyaran Gona Da Tantan

    Zaɓar Irin Shuka

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Zaɓaɓɓun irin shuka

    • Ka zaɓi irin da ya dace da yankin da kake noma.
    • Zaɓen irin waken soya ya danganta ne ta wajen lura da lokacin nunar sa, da jure fari da cututtuka.
    • Lokaci shi ma abin lura ne wajen zaɓen irin da ya dace da yankuna, a lura da iri mai zuwa da wuri ba mara saurin zuwa ba a guraren da suke da ƙarancin ruwa.
    Hoto Na Uku: Wanke Iri da Gyaran sa
    • A wanke iri da sinadarin (Fungiside kamar Captain, Apron plus) a yi amfani da fakiti ɗaya ga kilo takwas (8kg) na iri kafin a shuka domin kariya daga ƙwayoyin cututtuka dake cikin ƙasa.
    • A yi amfani da irin shuka mai inganci na kalar da aka zaɓa. A guji irin da ya tsage ko wanda ya samu illa, a yi amfani da iri wanda bai wuce watanni 12, ba domin samun tsirao mai kyau.
    Hoto Na Hudu: Iri Mara Kyau
    • Zaɓi iri mai kyau don shuka sannan a tabbatar da babu ƙwari a cikin sa. Kada a sayi irin shuka a gama-garin kasuwa, domin babu tabbacin kyawun sa ko tsirar sa.

    Shuka

    Lokacin shuka waken soya: Waken soya yana yi sosai a lokaci mai faɗi, idan gurin yana da danshi; kwanakin shukar da aka amince da su domin shuka waken suya a yankuna daban-daban na Nijeriya su ne aka gabatar a Tebur na Ɗaya (1).

    Tebur na Ɗaya: Lokutan da aka amince don shuka waken soya a Nijeriya

    S/N YANKI Lokuntan da aka tabbatar don shika
    1. Arewa ta Tsakiya Farko kan Yuni zuwa farkon Yuli
    2. Arewa maso Yamma Tsakiya Yuni zuwa farkon  Yuli
    3. Sudan savanna/Arewacin-Arewa Satin farko da na biyu na Yuli (1-2) weeks)
    • Kada a yi shukar wuri, saboda tsoron fari kan iya jawo yankwanewar shukar da kuma buƙatar sake shuka (kofi).

    Yawan Irin Shuka

    • Kimanin kilo 50-70 (Tiya 20-28) ake buƙata domin samun yawan tushe da ya kai (444,444) a cikin kadaɗa ɗaya na waken soya.

    Tazara Tsakanin Shuka

    • A shuka waken soya da hannu ko da injin shuka sannan a shuka kwaya 3 zuwa 4 a rami; a tazara sentimeta saba’in da biyar (75cm) tsakanin kunya da kunya, sannan sentimeta goma (10cm) tsakanin tushe da tushe.
    Hoto Na Biyar: Yadda Ake Shukan Waken Soya

    Sa Takin Zamani

    Taki da ake saka wa Waken Soya.

    • Ya danganta ne daga gwajin ƙasa. Waken soya a matsayin sa na amfanin mai gululai a sauyarsa zai iya samar wa kansa sinadarin nitrogen ta hanyar jawowa daga sararin sama.
    • Sinadarin phosphorus ne wanda waken soya ya rasa sosai. Don haka, sai a zuba takin phosphorus daidai don haɓakar yabanya. A zuba takin (SUPA) (3 x 50 kg bags) haɗe da ƙarin 2 x 50 bags na takin kamfa NPK (15:15:15).
    • Yawan takin da aka aminta a zuba wa gonar waken soya:

     Tebur na biyu: Yawan taki da za a saka wa Waken Soya

    S/n Yawan Taki (Kg/Ha)
    1 Buhu biyu da rabi na (NPK(15:15:15)
    2 Buhu uku na SSP (SUPA)

    Noma

    Feshin Maganin Ciyawa:

    Noman farko zai fara ne a sati na biyu (2) bayan shuka; sannan noma na biyu a sati na biyar zuwa na shida (5-6).

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Feshin Maganin Ciyawa:

    Magungunan kashe ciyawa in an yi amfani da su da kyau, suna aiki sosai wajen magance ciyawa. Akwai maganin ciyawa na waken soya da za a iya fesawa kafin tsirowar shi da kuma bayan tsirowar shuka. Idan an yi amfani da maganin kashe ciyawar, to noma ɗaya ake buƙata bayan sati biyar zuwa shida (5 -6); a goran magani a yi amfani da maganin kashe ciyawa kamar yadda aka yi bayani.

    Ƙwari da Hanyoyin Magance su;

    Za a iya magance kwarin waken soya ta hanyer feshi ɗaya na (CYPERMETRIN) Di-mechecate 10EC; a adadin 100ml a cikin lita goma sha biyar (15) na ruwa.

    Tuge Waken Soya:

    Waken soya yana isa tugewa ne a watanni uku zuwa huɗu bayan shuka; sannan yana buƙatar girbi da wuri domin kaucewa asarar yawan amfani.

    Za a iya girbe waken soya a lokacin da ya kai matakin da ƙwari ba za su addabe shi ba; sanda danshi (yawan ruwa) dake cikinsa ya kai tsakanin kashi 14-16%.

    Ayyukan da ake yi bayan tuge waken soya

    Bugu da Shiƙa:-

    • A buge waken soya da hannu ko da injin da zarar ya bushe sosai, ba tare da ɓata lokaci ba.
    • An yarda a yi bugu da hannu a ƙananan gonaki. Wannan ya ƙunshi sanya waken soya a buhu da kuma bugun shi da sanda. Sannan za a sheƙe shi don a fitar da kwayar daga raugar.
    • Ana iya amfani da inji wanda zai buge ya kuma cire datti cikin sauƙi.
    Hoto Na Shida: Bugu Da Shiƙa Da Hannu
    Hoto Na Bakwai: Amfani Da Injin Casa

    Ajiya

    • Ana ajiye waken soya ne a lokacin da ruwan da ya kai cikin ƙwayar yake kashi goma 10% ko ƙasa da haka.
    • Ana iya gane bushewar ƙwayar waken soya ne sanda aka kasa gatsa shi da haƙora ko fasa shi da ‘yan yatsu, don ajiya daga wata 6 zuwa 12 sannan kuma domin dogon ajiya fiye da shekara.
    • Kada a ajiye waken soya a ƙasa, a sa itace ko katako idan za a ajiye shi a cikin suto ko rumbu.
    • Kada a jingina shi da bango wajen ajiya.

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Domin karatna cikakken bayani a kan Jagoran Noman Masara danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tuwon Masara danna nan.

  • Yadda Ake Noman Wake

    Yadda Ake Noman Wake

    Wake muhimmin abinci ne wanda yake da matuƙar amfani a jikin mutane da dabbobi. Akwai manyan kasuwanni da ake sayar da wake, kuma manoma suna sarrafa harawar wake don sayarwa a lokacin rani don samun kuɗin shiga da kimanin kashi ashirin da biyar cikin ɗari (25%).  

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Wake na taka muhimmiyar rawa wajen samar da sinadarin takin Nitrogen ga amfanin gona (kamar masara, gero da dawa); idan ana sauya abin da aka shuka bayan damina uku zuwa huɗu da wake ko waken soya, musamman a sauran wurare. Wake baya buƙatar a yawaita masa takin zamani, sabo da sauyi na inganta ƙasar gona. Wannan ƙasida na bayyana mana dabarun noman fari da jan wake da nufin taimakawa masu noman waken don riba.

    Hoto na farko: Gonar wake

    Gyaran Gona

    • Ka yi sassabe da sharar gona kafin damina, sannan in damina ta faɗi, ka yi feshin maganin ciyawa glyphosate (round-up) wanda aka fi sani da Randon adadin lita huɗu (4) a faɗin hecta ɗaya.
    • Bayan sati biyu, sai a yi kaftu, ko kuma haro ko a yi huɗa, daga bisani sai a yi shuka.

    Gonar da ta dace a Noma Wake

    • Lokacin damina, ana iya noman wake a nau’o’in ƙasa masu yawa, amma zai fi kyau a gonakin tudu, wuri mai yashi-yashi kuma mai tsanewa da wuri.
    • In kuma da rani ne, za a noma waken, sai a sami gona a kusa da wurin da za a sami isasshen ruwa. (Wato korama ko dam ko rijiya mai ruwa).

    Yanayin da Wake yake Buƙata

    • Ana iya noman wake a lokacin damina da lokacin rani, muddin akwai yanayin zafi kimanin awa 28-30 a dare da rana a lokacin noman wake.
    • Wake yana yabannya mai kyau a wuraren da ake samun ruwan sama da ya kai kamar kimanin ma’aunin 500-1200mm a shekara.
    • Amma saboda sabbin irin wake da aka samu, yanzu ana noma wake a wurare masu samun ƙarancin ruwan sama kamar ƙasa da ma’auni 500mm a shekara.      
    • Wake yana jure fari, kuma ana iya noma shi a gona mai yashi ko kuma saimon gona

    Zaɓen Irin Wake don Shuka                                                                  

    • Ka zaɓi irin waken da ya fi dacewa da yanayin gonarka, ana zaɓen irin waken ne bisa la’akari da yawan kwanakin da yake ɗauka a gona kafin ya nuna da kuma yawan buhunan da yake bayarwa a hecta ɗaya, da jure ƙarancin ruwa, da jure wa ƙwari da cututtuka.
    • Kuma a yi lakari wajen zaɓen irin wake ta lura da launinsa da kuma girman ƙwayarsa.

    Adadin Irin da Ake Buƙata

    • Ka yi amfani da kilo (12-25) sha biyu zuwa ashirin da biyar na irin wake a hecta ɗaya.
    • Wannan ya danganta ga kalar irin waken, girman ƙwayar waken da tsarin noman shi
    • Ana buƙatar irin wake mai yawa idan waken mai yaɗo ne?
    • Ba a buƙatar iri da yawa indai waken mai yaɗo ne.

    Wanki da Gyaran Iri don Shuka

    • A wanke irin wake kafin shuka, gyara irinka, kafin shuka kuma a yi amfani da maganin wanke iri mai inganci saboda cututtukan dake cikin irin ko cikin ƙasa. Cututtuka da tsuntsaye suna kai hari ga wake kafin ya tsira da bayan ya tsiro.
    • Maganin wanke irin ya haɗa da MASHAL 2 percent APRON STAR, ALL STAR, DRESS FORCE SEED PLUS e.t.c. yi amfani da gram 10 domin wanke kilo 2-5 na iri.
    • Ka wanke hannunka da kyau da sabulu da ruwa bayan wankin iri da shuka.

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Shukar Wake:

    • A lokacin damina, kada ka yi gaggawar shuka wake don kada ya nuna a tsakiyar damina, kuma kada ka yi jinkiri sosai don gujema matsalar ɗaukewar ruwan sama da wuri.
    • Abu mai muhimmanci wadda za ka yi la’akari da shi, shi ne, ka gane lokacin da ruwan saman ya fara da kuma tsawon lokacin da yake ɗaukewa da kuma tsawon lokacin da waken yake ɗauka kafin ya nuna.
    • Mafi yawan waken da yake yaɗo da mai girma a tsugune suna lura da faɗuwar rana kafin su fara fure.

    Tazarar Shukar Wake

    • Ana shuka wake mai yi a tsugune a tazarar kimanin 50cm a tsakanin kunya da kunya da kuma tazarar kimanin 20cm a tsakanin shuka da shuka. Wake mai yaɗo ana shuka shi a tazarar 75cm tsakanin kunya da kunya, 50cm tsakanin tushen wake zuwa wani tushen.

    Zurfin Shukar Wake

    • Ana shuka wake a adadin zurfi na 2.5cm zuwa 5cm. Shukar farin wake fiye da zurfi na 5cm zai haifar da jinkiri wajen tsirar sa.
    • Idan ya yi zurfi sosai yana iya ruɓewa ko ya tsiro ɗaiɗai.

    Adadin Takin da Wake Yake Buƙata

    • Noman wake ba ya buƙatar taki mai yawa.
    • Ya kamata a yi amfani da takin NPK 15;15;15, kowace hecta ɗaya a sa mata buhun taki biyu a lokacin huɗan gonan ko takin SUPA SSP 30kg bayan shuka.

    Magance Ciyawa da Wuta-Wuta

    • A nome ciyawa aƙalla sau biyu. Noma na farko makonni biyu bayan shuka, sannan noma na biyu makonni huɗu zuwa biyar bayan shuka.
    • A iya amfani da maganin ciyawa wajen magance ciyawa a gonar farin wake
    • Wuta-wuta tana kawo illa sosai a gonar wake, takan fita a tushen waken ta dankwafe shi, ta hana shi fitowa ko girma, ganyensa ya rinƙa bushewa, kuma ya daina ‘ya’ya.
    • Saboda haka, ya kamata a cire wuta-wuta tun tana ’yar ƙaramar yabanya, kafin ta yi fure kuma yana da kyau a shuka wake mai jure wa wuta-wuta.
    Hoto na biyar: Wuta-wuta a gonar wake

    Kwarin Wake da Maganinsu

    • Matsalar ƙwarin wake su ne babban ƙalubale a kan harkar noman wake a Nijeriya. Ƙwarin sun kasu kashi uku:
    Hoton na shida: Tsutsar wake

    1. Ƙwari masu lalata ganyen wake kafin fure/huda.

    2. Ƙwari masu lalata wake a lokacin fure/huɗa.

    3. Ƙwari masu lalata wake bayan ya saki ‘ya’ya.

    Dabarun Magance Kwari a Gonar Wake

    • Wake yana buƙatar feshi sau biyu ko sau uku ya danganta ga yanayin ɓarnar ƙwari a gonar.

    Feshin farko: Ka yi feshin farko a tsakanin kwana talatin (30); ko talatin da biyar (35) bayan shuka lokacin da wake zai fara fure.

    Feshi na biyu: Ka yi feshi na biyu kwana goma bayan feshin farko a lokacin da waken yake fure.

    Feshi na uku: Ka yi feshi na uku idan ya zama dole, kwana goma da yin feshi; na biyu idan akwai mummunan farmaki daga ƙwarin wake MAIKOT (MARUCA) da kuma ƙwaro mai tsotse kalaben wake.

    Roron Wake

    • Ka yi roron waken a lokacin da ‘ya’yan waken suka bushe.
    • Wake mai zuwa da wuri da kuma wanda baya yaɗo, ana roro sau ɗaya.
    • Wake mai yaɗo kamar kanannaɗo a kan yi roro sau biyu ko sau uku.
    Hoto na bakwai: Roron Wake

    Ajiyar Wake

    • Ka ajiye wake a mazubin da iska bata shiga kamar duro ko buhun leda ko jarka
    • Ka ajiye tsabar waken ta hanyar jera su a buhu mai leda a ciki ko kuma ta hanyan ninka buhuna uku.

    Ajiyar Wake Na Lokaci Mai Tsawo

    • Ka yi amfani da maganin ƙwari mai suna samanda gari (Phostoxine). Ka lulluɓe maganin da tsumma ko takarda mai laushi wato (Toilet paper) ƙwaya ɗaya ko biyu sannan ka saka a cikin buhun wake mai nauyin kilo ɗari (100kg).
    • Kada ka yi amfani da, ko ka sayar da tsabar waken da aka cuɗanya shi da maganin ajiya har sai bayan wata shida.
    • Ka tabbata da tsaftar ma’ajiya, kuma duk sati biyu ka duba ko za a sami wani canji a yanayin ajiyar waken.

    Danna na domin dauko cikekken littafin

    Domin karanta cikakken bayani a kan Jagoran Noman Shinkafa A Najeriya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Noma A Najeriya danna nan.

  • Jagoran Noman Masara A Nijeriya

    Jagoran Noman Masara A Nijeriya

    Gabatarwa

    Masara tana ɗaya daga cikin amfanin gonar da aka fi nomawa a Najeriya. Ita ce ta fi sauran amfanin gona yawan faɗin ƙasa da ake noma ta. Noman masara yana ƙara bunƙasa a Najeria sakamakon ƙaruwar fasaha da dabarun noma. Masara ita ce abinci mafi muhimmanci ga jama’a, dabbobi da masana’antu a Najeriya.

    Sama da manoma miliyan hamsin (50m) ke noman masara da kuma mutane miliyan casa’in a wajen sarrafa ta da amfani na yau da kullum.

    Yanayin Da Masara ke Buƙata

    • Masara tana buƙatar yanayin mai ɗumi
    • Matsakaicin yanayin zafi = 20 zuwa 35 0C
    • Masara ba ta son yanayin zafi ya yi ƙasa da 30 0C
    • Yawan ruwan sama da masara ke buƙata = Mili-mita ɗari biyar zuwa ɗari tara

    Aikace Aikacen Noman Masara

    • Ka zaɓi wurin da ba ya riƙe ruwa kuma mai nagarta.
    • Ka kaucewa wuri mai tudu da kwari mai riƙe ruwa
    Hoto na Ɗaya: Wurin da ya dace da noman Masara
    • Sassaɓe gonarka kuma ka ƙona sharar
    • Ka yi kaftu sannan harrow da tantan ko shanun huda
    • Ka ja kunnyoyi da tazarar 75cm tsakanin kunya da kunya.

    Gyaran Gona

    Zaɓin Irin Shuka

    • Ka zaɓi ingantaccen Iri.
    • Ingantaccen iri yana jure wa cututtuka da ƙwari.
    • Ingantaccen iri yana bayar da amfani mai yawa
    Hoto na huɗu: Irirrikan Masara

    Yawan irin da zai shuka Kadada ɗaya

    • Kilo giram 15-20 ake buƙata don shuke kadada ɗaya.

    Wankin Iri

    • A wanke iri kafin shuka da maganin da ake kira Apron plus ko ire-iren shi.
    • A wanke iri daidai lokacin da za a yi shuka.
    • Fakiti ɗaya na Apron plus (10g) za a wanke kilo 3 na irin masara.

    Shuka:

    Lokacin Shuka

    • An fi so a yi shuka lokacin da ruwan sama ya kankama, misalin ƙarshen watan Mayu zuwa sati biyu na watan Yuni. (Karshen watan biyar zuwa sati biyu na watan shida).

    Yadda Za A Yi Shuka

    • Shuka iri ƙwaya ɗaya a rami mai zurfin santi-mita uku zuwa biyar (3-5cm).
    • Tazara tsakanin tushe da tushe a santi-mita ashirin da biyar (25cm) zai bada tushe 53,200 a kadada.
    Hoto na biyar: Yadda ake shukan Masara

    Nome Ciyawa

    Noma Da Fartanya:

    • Noman farko sati 2 zuwa 3 bayan shuka
    • Noma na biyu sati 5 zuwa 6 bayan shuka

    Maganin Ciyawa:

    • Lasso GD                                  Lita 4 zuwa 5 a kadada ɗaya (4-5 lts/ha)
    • Atrazine   Liquid                        Lita 4 zuwa 5 a kadada ɗaya (4-5 lts/ha)
    • Atrazine powder                        Kilo giram 1.5 zuwa 3 a kadada ɗaya (1.5-3kg/ha)
    • Primagram                                  Lita 3 a kadada ɗaya (3lts/ha)
    • Zuba gwangwanin madara biyu zuwa biyu da rabi (2-2.5) na magani a gorar feshi (CP 15) sai ka zuba ruwa lita 15.
    • Fesa magani kwana 1 zuwa 2 da shuka
    • Fesa magani yayin da gonar take da lema

    Hoto na shida: Yadda ake feshin maganin ciyawa.

    Sa/Zuba Taki

    • Ana saka wa masara taki sau biyu (Sati 2 da Sati 4 – 6) bayan shuka
    • Sa Taki na farko Kamfa (NPK):

    Idan 15:15:15 = buhu 8 a kadada ɗaya

    Idan 20:10:10 = buhu 6 a kadada ɗaya

    • Sa Taki na biyu mai gishiri (UREA):

    Urea 46:0:0 = buhu 2 a kadada ɗaya

    • Ka saka gram 8 na NPK (Kimanin marfin Coca-Cola)
    • Ka tona rami a kusa da tushen masarar (8-10 cm).
    Hoto na bakwai: Yadda ake sa taki a Masara

    Ban-ƙasa

    • Ka yi ban-ƙasa sati 6 bayan shuka ko da garmar hannu ko ta shanu.
    • Ban-ƙasa yana hana masara ta kwanta, kuma yana rufe jijiyoyin masara.
    • A kula kada a yi wa masara illa lokacin ban-ƙasa.
    Hoto na takwas: Ban-ƙasan Masara da shanun huda

    Ƙwari da Cututtuka

    • Ƙwari da cututtuka suna rage samun amfani a gonar masara.
    • Shuka da wuri tare da wanke irin masara suna taimakawa wajen rage illar ƙwari da cututtuka.
    • Ana son canja amfani a gona bayan shekaru ana shuka masara.
    • Maize borer = Yana shiga karar masara ko goyonta
    • Grass moth = Yana cinye masara tun tana ƙarama har ta girma.
    • Rootworm beetle = Yana cin jijiyar masara har ta kai ga faɗuwa
    • Maize flea beetle = Yana saka cuta mai suna(bacterial leaf blight).

    Cututtukan Masara

    • Maize smut = Tana kama goyon masara sai ta samar da ɓangaren da babu ƙwayar masara
    • Maize rust = Tana saka wani ɓangaren ganyen masara ya zama kamar ya yi tsatsa.
    • Maize anthracnose Tana saka ruɓewar ganye da karan masara.

    Hanyoyin Magance Cututtukan Masara

    • Yin shuka a kan lokaci tare da wanke iri yana rage haɗarin cututtuka
    • Shuka ingantaccen iri mai jure cututtuka
    • Kada a shuka masara tsawon lokaci a gona ɗaya
    • Sharan gona da gyaran gona mai kyau, yana taimakawa wajen rage haɗarin cututtuka a masara
    • A yi amfani da maganin ƙwari da ya dace.

    Girbi

    • Idan za a yi amfani da masara ɗanya: Sai a girbe ta lokacin da ta yi ƙwari kimanin kwanaki (55-70) bayan shuka.
    • Amma idan ana buƙatar hatsi ne: Sai a bari sai ta bushe sosai, ta yanda za a iya ɓamɓare ta da hannu ko da injin casa.

    Ajiyar Masara

    • A shanya masara ta bushe kafin a ajiye.
    • A yi amfani da magungunan ajiya irin su: Actellic 2 % DP, Phosoxin da sauransu.
    • Actellic 2 % DP = giram 300 zuwa 500 a buhu mai nauyin kilo giram 100.
    • Phosoxin = Saka ƙwaya biyu a kowane buhu mai nauyin kilo giram 100.
    • A yi ajiya a wuri mai samun iska.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Jagoran Noman Farin Wake danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tsaba Da Wake danna nan.

  • Jagoran Noman Shinkafa A Nijeriya

    Jagoran Noman Shinkafa A Nijeriya

    Gabatarwa

    Shinkafa ta kasance ɗaya daga cikin amfanin gona mai matuƙar tasiri da kawo kuɗin shiga ga manoma a Nijeriya. Ta samar da ayyukan yi ga mutane sama da miliyan goma sha biyar (15million) a harkar nomanta da kasuwancinta a Nijeriya. Buƙatar shinkafa ƙara bunƙasa take a kowace shekara a Nijeriya.

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Hoto na Farko: Yabannyar Shinkafa.

    Yanayin da Shinkafa ke Buƙata domin Samun Amfani mai Yawa

    • Da rana shinkafa na buƙatar yanayin zafi kimanin ma’aunin digri 30°C
    • Amma da daddare shinkafa na buƙatar yanayin zafi kimanin ma’aunin digiri 20°C
    • Shinkafa na buƙatar yanayin zafi kimanin ma’aunin digri 16 – 200C lokacin (ɗaukar ciki) da ta sa bunini da ƙwaya.
    • Amma tana da buƙatar yanayin zafi kimanin ma’aunin digri 18 zuwa 320C lokacin da ƙwayar ta take nuna.
    • Idan ma’aunin yanayin zafi ya wuce kimanin digri 350C to lallai zai shafi saka ƙwayar shinkafa.

    Aikace-aikacen Noman Shinkafa

    Zaɓan Gona:

    • Ita shinkafa ana iya noma ta a kowace irin ƙasa. Manomi ya zaɓi fili shimfiɗaɗɗe, wanda ba tudu ba gangare; sannan ya kasance mai riƙe ruwa kuma da ƙasa mai ƙarfi da kyau.
    Hoto na biyu: Gyaran gona da Tantan
    • Manomi ya sassaɓe ciyayi da tushe-tushe, ya kwashe su a tsakanin watan Nuwamba zuwa Fabrairu; sannan ya yi haro da hannu ko da motar gona wato Tantan (Tarakta) kafin shuka.

    Zaɓen Irin Shuka:

    • Zaɓi irin da ya dace da gonarka,  kuma wanda kasuwa ke buƙata. Idan kana shakka to ka tuntuɓi malamin gona na kusa da kai ko ma’aikatar gona; ko kuma kamfanin iri domin samun irin da ya dace da gonarka, kuma wanda kasuwa ke buƙata.

    Wankin Iri:

    • Wankin Iri na kare shuka daga cututtuka da ƙwari, sannan yana sanya fitar tsiro da kyau. Ana cakuɗa mudu 4 ko kilo hudu (4) na iri da fakiti ɗaya (10g) na Apron Star 50 DS domin wanke iri.
    Hoto na Huɗu: Wankanken Irin Shuka na Shinkafa.

    Shuka:

    • Za a iya noma shinkafa har sau uku cikin shekara guda, kuma a gona ɗaya idan akwai ruwa kamar haka.
    • Fabrairu, Maris, Afrilu da Mayu
    • Mayu, Yuni, Yuli da Agusta
    • Agusta, Satumba, Oktoba da Nuwamba
    • A shuka kilo 50-60 a kadaɗa ɗaya idan shukar kai tsaye ce, ko kilo 80 a kadaɗa ɗaya idan yafi za a yi.
    • A shuka ƙwayar shinkafa  biyar ko shida (5-6) a rami mai zurfin sentimeta biyu zuwa huɗu (2-4cm). Kar ya wuce sentimeta biyar (5cm). Sannan a shuka ta a tazarar sentimeta ashirin da biyar (25cm) tsakanin tushe da tushe da kuma layin shuka zuwa layin shuka.
    • Idan dashe za a yi: Ana yin dashe bayan kwana 21 da yafi ko kuma sanda ta fara ganye biyu zuwa shida (2-6) na girma.
    • A dasa silin tsiro 2-3 a rami a bisa tazarar 20cm tsakanin layi, sannan ko sentimeta sha biyar zuwa ashirin  (15-20cm) tsakanin shuka.

    Sa Takin Zamani:

    • Amfani da takin gargajiya yana da tasiri a gonar shinkafa wajen haɓaka amfani. Shinkafa tana buƙatar sinadarin Nitrogen sosai.
    • Ana sa takin kamfa buhu huɗu (4) a kowace hekta bayan kwana 10-14 da shuka ko dashe.
    • Ana sa mata urea buhu 2 bayan sati 6 da shuka ko dashe lokacin da za ta fara ƙunsa ciki.
    Hoto na Bakwai: Takin Kamfa

    Magance Ciyawa:

    • Ciron Ciyawa Ko Noma: Yana da mahimmanci manomin shinkafa ya yi noma ko ciron ciyawa a tsakanin sati 2 zuwa 3 bayan shuka ko dashe da kuma kafin ta fara fitar da kai.
    • Yadda Ake Amfani Da Maganin Ciyawa A Gonar Shinkafa: Idan manomi zai yi amfani da maganin hana ciyawa fitowa, ya yi amfani da butachlor lita 5 a kowace hecta, amma kar ya wuce kwana  biyu da shuka shinkafar ko ya yi amfani da STOM 500e ko OXADIAZON (RONSTAR) lita 3 a hecta 1 wanda ya zaɓa cikin su.
    Hoto na Takwas: Feshin maganin Ciyawa

    Magance ƘKwari da Cututtuka:

    • Ƙwari: Ƙwari da cututtuka da dama suna addabar gonar shinkafa, don haka ya zama dole manomi ya sanya ido; kuma ya ɗauki mataki da zarar ya ga ƙwari ko wata cuta a gonar shinkafarshi. Ta hanyar yin amfani da magunguna da kuma dabarun noma na zamani domin samun amfanin gona mai yawa da kuma kaucewa asara.

    Don Cikakkiyar Kariya daga Cututtukan Shinkafa sai:

    • A yi amfani da ingantaccen irin shuka.
    • A tabbatar da wanke irin kafin shuka.
    • A tabbatar da tsabtar gonar.
    • Da zarar an ga alamar cuta a tushen shinkafa, tuge ta kafitar daga gonar ka
    • A yi amfani da ingantattun magungunan cututtuka da na ƙwari (misali benlate ….)

    Girbi

    • Shinkafa tana isa girbine idan tsabar tayi ƙarfi; sannan ta canja launi zuwa ruwan ƙwai ko ruwan ƙasa (Yellow/brown) Kimanin kwanaki 30-45 bayan fure. A wannan lokaci lemar dake jikinta ya kai kamar zuwa kasha ashirin da huɗu cikin ɗari (24%).
    Hoto na Tara: Shinkafa da tanuna

    Ajiya a cikin ɗaki ko rumbu

    • Ana buƙatar Shinkafar da za a adana ta bushe sosai, ta kai ma’aunin kashi goma cikin ɗari ko ƙasa da haka na laimar dake jikinta.
    • Rumbun (Store) ya kasance a tsaftace kuma a bushe kafin a ajiye shinkafar.
    • Ana buƙatar wajen ajiya a suto ya kasance kar a ajiye shi kai tsaye a ƙasa, kuma ya kasance an raba shi da ƙasa, a ɗora shi a kan katako ko itace.
    • Rumbu ya kasance babu ramukan ɓeraye, sannan kar a jingina shi da bango.

    Yawan Amfani da Manomi kan Iya Samu:

    • Manoma na samun kimanin buhu (40-60) a gonanakin fadama ko kuma buhu (30-50) a gonakin tudu.
    • Amma saboda bunƙasar fasaha ta noman zamani, manoma suna samun kimanin buhu 73 a gonar fadama, da kuma yawan buhuna kimanin 37 a gonakin dake tudu mai faɗin kadaɗa ɗaya.

    Danna nan domin dauko cikekken littafin

    Domin karanta cikakken bayani a kan Jagoran Noman Waken Soya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tuwon Shinkafa danna nan.

  • Yadda Ake Turaren Sikari

    Yadda Ake Turaren Sikari

    Kayan Haɗawa

    Ruwan turare (alcohol)

    Yara-yara gwangwani 1

    Sikari kwano

    Kala

    Filabo

    Madarorin Turare 5

    Yadda Ake Haɗawa

    A juye Sikari a cikin mazubi. A juye Yara-yara, a sa madarorin turare 5. Sai a sa kala, a yi ta juyawa har sai ko’ina ya haɗe jikinsa sosai.

    Shi ma wannan turare a cikin garwashi ake sawa a turara ɗaki da shi.

    A ƙarshe dai amfani da turare ya kewaye dukkan ƙasashe. Haka kuma da sauran jihohi. Ya Kuma cancanci a ce yana ciki kasafin wata-wata na kowanne mai gida. Gidanka ƙamshi Kuma jikin matarka ƙamshi. Haka zai sa wa ma’aurata natsuwa da samu gamsuwa da juna. Duba yadda ake haɗaɗɗiyar humra.

    Littattafai da aka duba:

    Taron ƙara wa juna ilmi.

    Hikimomin Kulawa da Mai gida.

    Mu Koyi Sana’a.

    7th Nuwanba, 2015,
    Gidan Mumbayya, kano.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Turaren Ɗaki Na Musamman danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman danna nan

  • Noma A Najeriya

    Noma A Najeriya

    Aikin Noma a Najeriya reshe ne na tattalin arziki a Najeriya; yana ba da aikin yi ga kusan kashi 30% na yawan jama’ar har zuwa shekarar 2010. Ana canza sashen ta hanyar kasuwanci a ƙananan matakan matsakaita da manya.

    Fitar da abinci ya kai sama da kashi 70 na GNP na Najeriya a lokacin da aka samu ‘yanci; bayan shekaru ashirin da biyar, ya kusan zama koma baya ga kayan abinci wanda ya kai sama da kashi 50 na shigo da kayayyaki.

    Fitar da abinci ya ragu bayan samun ‘yanci; duk da cewa yankuna da dama na Saharar Afirka, sun kasance masu amfani; kuma suna iya samar da abinci, ta yadda kowane mai abinci ya fita; sai aka shigo da hatsi sama da sau bakwai.

    Saboda haka Gwamnatin Najeriya ta inganta yin amfani da takin gargajiya ba a cikin 1970s.

    A shekarar 1990, an gano hekta miliyan 82 daga cikin fadin ƙasar na kusan hekta miliyan 91 da ake nomawa. Kashi 42 na yankin da ake nomawa an yi noma. Mafi yawan wannan ƙasar an noma ta ne a ƙarƙashin tsarin daji na daji; inda ake barin ƙasa ba aiki na wani lokaci; don ba da damar sake sabunta halittar ƙasar.

    An rarraba kadada miliyan 18 a matsayin makiyaya ta dindindin, amma tana da damar tallafawa noman. Yawancin hekta miliyan 20 da gandun daji da dazuzzuka suka mamaye; suna da imanin cewa suna da damar noma.

    Riƙe kayan aikin gona ƙanana ne, kuma sun watse; kuma ana gudanar da noma da kayan aiki masu sauƙi. Babban noma ba na kowa bane. Aikin noma ya ba da gudummawar 32% ga GDP a 2001.

    Kayan Amfanin Gona

    Manya kayan amfanin gona sun haɗa da wake, shinkafa, dawa, da kashu, da rogo; da koko, da gyada, da danƙo, da soɓo, da masara (masara), da kankana, da gero, da dabino, da filawa; da shinkafa, da roba, dawa, da waken soya, da ayaba, da dawa.

    A da, Najeriya ta yi fice wajen fitar da man gyaɗa da na dabino. Amma tsawon shekaru yawan fitar da wannan kayan ya ragu. ‘Yan shekarun baya kamfanonin Najeriyar na gida sun fara fitar da; gyaɗa, kashu, kanwa, ganyen zogale, Ginger, koko da dai sauransu.

    Kayayyakin aikin gona na ƙasar sun faɗa cikin manyan kungiyoyi biyu; noman kayan abinci da ake samarwa don amfanin gida; da kuma fitarwa zuwa kasashen waje. Kafin yaƙin basasar Najeriya, ƙasar ta wadata kanta da abinci; amma ta ƙaru sosai bayan shekarar 1973.

    Gurasar da aka yi da alkama ta Amurka ta maye gurbin amfanin gona na gida; a matsayin abinci mafi arha mafi sauƙi. Tsakanin 1980 da 2016, samar da Yam ya ƙaru daga sama da tan miliyan 5 zuwa tan miliyan 44.

    Domin karanta cikakken bayani akan Jagoran Noman Masara A Nijeriya ko Jagoran Noman Shinkafa A Nijeriya danna nan

  • Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman

    Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman

    Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura . Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:
    Icen Sandal
    Ice, Hawi
    Icen Gab-Gab
    Icen Durot
    Da dai Sauransu.

    Ana yin turare na soyawa kuma ana yin na jiƙawa. Ya danganta da buƙatar mutum.

    Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe .

    KAYAN TURAREN WUTA
    Icen Hawi
    Matan Arewa
    Farce
    Misik
    Alhaji Abdullahi
    Salamalekum
    Sasorabia
    20 fragrances
    Madara turare ( 8)

    YADDA AKE HAƊAWA
    Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa. A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.

    Littattafai da aka duba:

    Taron karawa juna ilmi.

    Hikimomin Kulawa da Mai gida.

    Mu Koyi Sana’a.

    7th Nuwanba, 2015,
    Gidan Mumbayya, kano.

  • Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Humra.

    Yadda Ake Haɗaɗɗiyar Humra.

    Humra turare ne na ruwa da ake shafawa a jiki. Mafi yawa mata su suka fi amfani da ita. Amma turare ne na Maza da mata duka . Humra ana yin ta kaloli daban-daban. Akwai Fara, baƙa da jar humra. Humra na bambanta ne saboda irin kayan haɗi. Da kuma turaruka. Wasu na amfani da turaruka masu arha. Wasu Kuma suna sa turaruka masu ƙamshi mai daɗi da tsada.

    KAYAN HUMRA
    Scenario 1
    Garin farce
    Garin sandal
    Garin kaninfari
    Misik
    Madara turare :
    Anfal
    Sultan
    Black SS
    Arabi’an oudh

    YADDA AKE HAƊAWA
    Za a bude roba Scenario (Ruwan hada turare ) a juye a mazubi. Sai a juye garin farce Wanda aka gyara shi, aka soya. Da garin sandal, da garin kaninfari. A daka Misik da Ambur A juya sosai .
    Sai a samu turaruka masu ƙamshi mai daɗi. Kala hudu, shida ko dai dai ƙarfi a sa. Wato azuba madara turare Anfal, sultan, da Black SS da Arabian Oudh. Sai a juya su haɗe sosai. A juye a cikin kwalabe / robobi turare.

    Kamshi na daga cikin abubuwa dake ƙara wa mutane daraja. Kamshi na ƙara soyayya. Yana da kyau mata da maza mu zama masu tsafta da ƙamshi.

    Litattafai da aka duba
    Khadija Mar’atussaliha
    Amina Yusuf Gwamna

    Lacca
    Mu Koyi sana’a
    Birnin kudu Jigawa