Author: Khadija Yusha’u (Amira)

  • Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Biskit Cikin Sauƙi

    Abubuwan da ake bukata

    • Fulawa   2cups
    • Bota  1/2cup
    • Baking powder 1tspn
    • Icing sugar 1,1/2
    • Gishiri 1tspn
    • Milk 1tspn

    Yadda ake haɗawa

    A tankaɗe fulawa a kwano daban.

    Sai a zuba mata icing sugar a ciki.

    Sannan a zuba gishiri da baking powder a ciki.

    Sai  a zuba bota a ciki a juya su har sai sun haɗe jikin su.

    Sai a zuba madara a kai a cigaba da cakuɗa su har sai sun haɗe jikin su.

    Sai a sa a kan faranti a bubbuɗa shi.

    Sannan a kawo abu mai faɗi amman rawun dai-dai girman da ake so.

    Domin karanta yadda ake yogurt ko ice cream custard danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Shekara Nawa Shugaban Halitta Ya Yi Azumin Ramadan A Rayuwarsa?

    Shekara Nawa Shugaban Halitta Ya Yi Azumin Ramadan A Rayuwarsa?

    Amsa: Ya yi azumin Ramadan ne na tsahon shekara tara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan A Cikin Azumin Ramadan Na Shekaru Tara Da Ya yi, Sau Nawa Ya yi Azumi Talatin, Sau Nawa Ya yi Azumi Ashirin Da Tara? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Yadda Ake Yogurt

    Yadda Ake Yogurt

    Yogurt yana da matuƙar amfani a jikin ɗan Adam, a binciken masana sun gano yogurt na kariya daga kamuwa daga cutar daji(cancer), ciwon zuciya da makamantan su.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Madarar gari
    Ruwa
    Nono
    Filebo

    Yadda ake haɗawa:

    A ɗora ruwa a kan wuta ya tafasa

    Sai ki zuba madarar gari a kwano daban, ki zuba mata ruwa ki kwaɓa ta

    Sai ki juye a kan tafashasshen ruwan dake kan wuta

    A bar shi ya yi kamar minti biyar a kan wutar yana tafasa

    Sanna a sauke a bar shi ya ɗan sha iska, sai a zuba nono cokali biyu a kai, amma kar a juya.

    A bar shi ya yi awa takwas a ajiye.

    domin sanin yadda ake boga ko biredin kwakwa danna nan

  • Mulkin Soja Da Jamhuriyya Ta Uku (1983-1999)

    Mulkin Soja Da Jamhuriyya Ta Uku (1983-1999)

    Juyin mulkin soja da aka yi a 1983 ya faru ne a bikin sabuwar shekarar. Haɗin gwuiwar wasu manyan hafsoshin sojojin Nijeriya ne, suka yi haɗin gwuiwa, kuma hakan ya haifar da kifar da Jamhuriyar Nijeriya ta biyu da kuma sanya Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa. Juyin mulkin soja na Muhammadu Buhari jim kaɗan bayan sake zaɓen shugaban ƙasa a 1984 ana ganin sa a matsayin wani ci gaba mai kyau. Buhari ya yi alƙawarin manyan gyare-gyare, amma gwamnatinsa ba ta yi kyau sosai fiye da wanda ta gabata ba. An hamɓarar da gwamnatinsa da wani juyin mulkin soja a 1985.
    An hambarar da Janar Buhari a shekarar 1985, bayan juyin mulkin soja, a ƙarƙashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida, wanda ya kafa Majalisar Rundunar Sojojin Ruwa kuma ya zama shugaban sojoji da kwamandan sojoji a manyan hafsoshin sojojin. A 1986, ya ƙafa Ofishin Siyasar Najeriya a 1986 wanda ya ba da shawarwari ga sauyawa zuwa Jamhuriyar Nijeriya ta Uku.
    A cikin 1989, Babangida ya fara yin shirye-shirye don sauyawa zuwa Jamhuriyar Nijeriya ta Uku. Ya ba da izinin kafa jam’iyyun siyasa, sannan ya ƙirƙiro da tsarin jam’iyyu biyu, tare da Social Democratic Party (SDP) da Babban Taro na National Republican Council(NRC) gabanin babban zaben shekarar 1992 Ya buƙaci dukkan ‘yan Nijeriya da su shiga dukkan ɓangarorin, waɗanda marigayi Cif Bola Ige ya ambata da “hannayen kuturu guda biyu.” -A sashe biyu ɗin sun kasance shawarwarin ofishin Siyasa ne.
    A watan Nuwamba 1991, bayan da aka gudanar da ƙidaya, Hukumar Zabe ta Kasa (NEC) ta sanar a ranar 24 ga Janairun 1992 cewa duka majalisun dokoki biyu na babban taron ƙasa da na shugaban ƙasa za a yi a ƙarshen shekarar. An karɓi wani tsari na jefa ƙuri’a, wanda ake kira zaɓi na A4. Wannan tsari ya ba da shawarar cewa duk wani ɗan takarar da yake buƙatar wucewa ta hanyar karɓar duk zaɓaɓɓun mukamai daga Ƙaramar Hukuma, Gwamnatin Jiha da kuma Tarayya.
    Babangida ya tsira daga yunƙurin juyin mulkin Nijeriya na 1990, sannan ya jinkirta sake komawa ga alkawarin da aka yi wa dimokiradiyya zuwa shekarar 1992. Zaɓen shugaban ƙasa na 1993 da aka yi a ranar 12 ga Yuni, na farko tun bayan juyin mulkin soja a 1983. – ya nuna ‘yan takarar Moshood Abiola da Babagana Kingiɓe na Social Democratic Party (SDP) sun kayar da Bashir Tofa da Slyvester Ugoh na babban taron Jam’iyyar National Republican (NRC) sama da miliyan biyu da dubu ɗari uku.
    Ko yaya, Babangida ya soke zaɓen? Wanda ya haifar da zanga-zangar fararen hula da suka rufe ƙasar cikin makonni. A watan Agusta na 1993, Babangida daga ƙarshe ya cika alkawarinsa na miƙa mulki ga gwamnatin farar hula, amma ba kafin naɗa Ernest Shonekan, shugaban gwamnatin rikon kwarya, An ɗauki tsarin mulkin Babangida a matsayin mafi cin hanci da rashawa, kuma yana da alhakin ƙirƙirar al’adar cin hanci da rashawa a Nijeriya.
    A ƙarshen shekarar 1993, gwamnatin wucin gadi ta Shonekan, ta taƙaice a tarihin siyasar ƙasar nan a cikin juyin mulkin soja a shekarar 1993, ƙarƙashin jagorancin Janar Sani Abacha, wanda ya yi amfani da ƙarfin soja wajen daƙile ci gaba da tashin hankalin farar hula. A 1995, gwamnati ta rataye masaniyar muhalli Ken Saro-Wiwa kan zarge-zargen kashe-kashen da ya yi wa dattawan Ogoni hudu.
    An gabatar da ƙarar ne a ƙarƙashin dokar Alien Tort Statute a kan Royal Dutch Shell da Brian Anderson, shugaban kamfanin na Shell na Nijeriya, sun yanke hukunci, ba tare da yanke hukunci ba a yayin da Shell ke ci gaba da musanta alhakin. Da yawa  miliyan dala asusun da aka gano zuwa Abacha an gano su a 1999.
    Wannan tsarin mulki ya kawo ƙarshe a shekarar 1998, lokacin da azzalumin sarki ya mutu a cikin gari. Ya saci kuɗaɗe don kashe asusu a bankunan yammacin Turai sannan ya sha alwashin shirya juyin mulki ta hanyar kamewa da karɓar janar da ‘yan siyasa. Wanda ya gaje shi,shi ne Janar ABDULSALAM ABUBAKAR, ya amince da sabon tsarin mulki a ranar 5 ga Mayu 1999 wanda ya ba da damar gudanar da zaɓuka masu yawa.

     

  • Nau’ikan Abinci 5 Da Ya Kamata A Kauracewa Kafin Kwanciya Bacci

    Nau’ikan Abinci 5 Da Ya Kamata A Kauracewa Kafin Kwanciya Bacci

    1. Naman kaza: Naman kaza da sauran danginsa suna hana barci mai dadi, matukar aka ci kafin barci. Wannan na faruwa ne, saboda narkewar abinci a jikin dan Adam na ɗaukar lokaci ya yin barci. A maimakon ɗan Adam ya yi barci mai daɗi, jikinsa zai maida hankali ne wajen narkar da abincin.
    2. Kayan kwalam masu sukari: Wannan a bayyane yake, duk da mutane da yawa na cin irin wadannan abincin kafin su kwanta. Wannan ba abin da ya dace ba ne, don kuwa suna ɗaukar lokaci kafin su narke a jiki. A maimakon jikin mutum ya samu sauki da hutu yayin kwanciyar barcin, sai ya yi ta kokarin narkar da abincin wanda hakan zai hana barci mai nagarta.
    3. Shayin Coffee: Duk da kuwa abin sha ne, yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya kamata a guda kafin a kwanta. Wannan kuwa za a iya danganta shi ne da sinadarin ‘caffeine’ da ke ciki wanda ke hana barci.
    Amma kuma, idan mutum na da burin kin barci, toh zai iya shan coffee don wannan aikin. Abin kiyayewa a nan kawai shi ne, kada ya zama mutum ya saba, don akwai matsalolin da ke akwai dangane da sabo da shan sinadarin caffeine.
    1. Abinci mai yaji: Duk yadda mutum ke son abinci mai yaji, zai fi idan aka ci da safe ko da rana amma a kiyaye da dare. Abinci mai yaji kan jawo tashin zuciya, idan aka ci da dare kuma hakan yakan hana nagartaccen barci.
    2. Abinci mai maiƙo: A shawarce abinci mai maiko abin gudu ne da daddare ,don samun lafiya mai inganci. Maiƙon dake ƙunshe a abincin nasa ciki ya fitar da ‘acid’ wanda yake kawo tashin zuciya. A don haka ne idan ana bukatar barci mai nagarta tare da gudun tashin zuciya da safe, sai a guji abinci mai maiko da dare.
    Domin sanin menene nutrion dannan nan
  • Yadda Ake Madarar Youghurt

    Yadda Ake Madarar Youghurt

    Yadda Ake Madarar Youghurt

    Abubawan da ake bukata

    • Madara kofi huɗu
    • Ruwa kofi huɗu
    • Sukari kofi
    • Flavor mai ƙamshin madara cikin cokali.
    • Corn starch kofi ɗaya
    • Culture rabin cokali

    Yadda ake hadawa:

    1. Da farko za a kwaɓa madarar (ta gari) da sukari da corn starch sai a zuba ruwan sanyi a kai.
    2. Daga nan sai a tafasa ruwan zafi a zuba a kai, idan an ɗan daɗe sai a juya shi, har sai an tabbatar babu ƙulalai ko kaɗan a ciki.
    3. A murje haɗin ya zama ruwa, sannan a bar shi ya huce ya zama da ɗumi.
    4. Kafin ya yi sanyi sosai, sai a zuba culture a ciki.
    5. Bayan an sa culture, sai a rufe a bari ya yi awa takwas zuwa 12, ko ma ya kwana.
    6. Idan aka buɗe shi, sai a zuba sukari da flavor sai a motsa.
    7. Idan yogurt din ya haɗu sai a sa a fridge a bar shi ya yi sanyi.
    8. Daga nan sai a sha shi yadda ake so.

    Karin haske:

    Za a iya amfanin da madarar gari ko ta ruwa wajen haɗa yogurt na gida.
    Idan da madarar gari za a yi amfani, to yadda na yi bayani haka za a yi.
    Idan kuma da madarar ruwa ce, to a dafa madarar sannan a ɗiga mata culture, a rufe na tsawon awa takwas koh sha biyu.
    Wannan shi ne yadda ake yin yogurt a gida daki-daki.
    Za ku kuma iya sha da fura ko a kankare kwakwa a ciki yogurt din a sha
  • Yadda Ake Stuffed Meat

    Yadda Ake Stuffed Meat

    A yau za mu koyi yadda ake stuffed meat.

    Stuffed meat abinci ne da ake yin sa daga nama, yana da matuƙar daɗi musamman ma wajen karin kumallo na safe ko tarbar baƙi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Nama me girma
    • Kakide (kitse)
    • Butter
    • Tumatur
    • Jan tattasai
    • Green pepper
    • Albasa
    • Nama sala sala masu kauri
    • Kayan ƙamshi
    • Citta

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A wawwanke cikin naman nan a yi aljihu biyu abar kasan naman kar a yanka shi.
    2. A ɗumama butter a soya tumatu a yanka tattasai duka a cire ‘ya’yan a soya da albasa.
    3. A zuba naman nan sala-sala a ciki a zuba maggi da kayan ƙamshi.
    4. A zuba kwatan naman nan da hadi a aljihu daya, kwata a daya aljihun sannan a zuba rabi a saman.
    5. A nannaɗe a ɗaure a sa abu me nauyi a danne.
    6. Asa a gwangwanin baking a gasa ana zuba kakide a hankali har ya gasu.
    7. A barbaɗa kayan yaji a kai in ana so.

    A ci da daɗi.

    Domin sanin Yadda Ake Bandashe danna nan

  • Yadda Ake Bandashe

    Yadda Ake Bandashe

    A yau za mu koyi yadda ake bandashe.

    Bandashe abinci ne da ake yin sa daga gurasa, yana da sauƙin sarrafawa da daɗin ci, musamman ma a wajen karɓar baƙi da wuraren taruka.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Gurasa mai gishiri
    • Dakakken ƙuli-ƙuli
    • Albasa
    • Tumatir
    • Mai

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A sami gurasa a saka ta a cikin ruwan ɗumi, ta yi kamar sakan biyar a ciki sai a cire.
    2. A tsanar da ita, ko kuma a turara ta, abin da dai ake so shi ne, gurasar ta yi laushi sosai.
    3. Sai a zuba mai gaba da bayanta, sai ki kawo ƙuli-ƙuli a barbaɗa, shi ma gaba da baya; sai ki yanka tumatir da albasa da cocomba, idan ana so ma har kabeji ana iya sawa a kai.
    4. Idan ana buƙata ana iya kara mai, domin ya ji, a tabbatar ƙuli-kulinki ya ji magi; ba sai an zo ana ƙarawa a kai ba, ba zai taɓa yi ba.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasar Oven danna nan

  • Yadda Ake Gurasar tanderun Nasara (OVEN)

    Yadda Ake Gurasar tanderun Nasara (OVEN)

    A yau za mu koyi yadda ake gurasar tanderun Nasara (Oven).

    Abubuwan da ake buƙata

    • Fulawa
    • Yis
    • Kantu/riɗi
    • Sikari
    • gishiri

    Yadda ake haɗawa

    1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
    2. Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
    3. Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin
    4. Sai a tabbatar an kunna (oven) din ya yi zafi sosai, sai a kawo tiren gashi a shafa masa bota.
    5.  Sai a kawo kwaɓin a cura, a kuma fakada, sai a saka a cikin tiren gashi,
    6. Idan an saka duka, ko kuma iya yadda zai dauka, sai a mayar da tiren cikin (oven) din a rufe.
    7. Zai ɗauki kamar minti goma sha biyar, zuwa minti ashirin kafin ta yi. Ko kuma da an fara jin ƙamshi to ta yi, sai ki cire.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasar Tukunya danna nan

  • Yadda Ake Gurasar Tukunyar Ƙarfe

    Yadda Ake Gurasar Tukunyar Ƙarfe

    A yau za mu koyi yadda ake gurasar tukunya, gurasar tukunya abinci ne da ake yin sa daga fulawa, gurasa na da sauƙin sarrafawa da sauƙin ajiya.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Fulawa
    • Yis
    • Kantu/riɗi
    • Sikari
    • gishiri

    Yadda ake haɗawa

    1. A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
    2. Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
    3. Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin.
    4. Sai a sami tukunyar ƙarfen mai ƙwari, a ɗora ta a kan wuta, idan ta yi zafi sosai, sai a zare itatuwan a bar garwashin, saboda ka da gurasar ta kone.
    5. Sai a cura gurasar a faɗaɗa ta, a saka cikin tukunyar,
    6. Idan an gama, sai a kawo murfi a rufe. Idan ta yi, za a ji ta fara ƙamshi.

    Domin sanin Yadda Ake Gurasa Tanderu danna nan