Yadda Ake Stuffed Meat

0
377

A yau za mu koyi yadda ake stuffed meat. Stuffed meat abinci ne da ake yin sa daga nama, yana da matukar daɗi musamman ma wajen karin kumallo na safe ko tarbar baƙi.

Abubuwan da ake buƙata

 • Nama me girma
 • Kakide (kitse)
 • Butter
 • Tumatur
 • Jan tattasai
 • Green pepper
 • Albasa
 • Nama sala sala masu kauri
 • Kayan ƙamshi
 • Citta

Yadda ake haɗawa

 1. A wawwanke cikin naman nan a yi aljihu biyu abar kasan naman kar a yanka shi.
 2. A ɗumama butter a soya tumatu a yanka tattasai duka a cire ‘ya’yan a soya da albasa.
 3. A zuba naman nan sala-sala a ciki a zuba maggi da kayan ƙamshi.
 4. A zuba kwatan naman nan da hadi a aljihu daya, kwata a daya aljihun sannan a zuba rabi a saman.
 5. A nannaɗe a ɗaure a sa abu me nauyi a danne.
 6. Asa a gwangwanin baking a gasa ana zuba kakide a hankali har ya gasu.
 7. A barbaɗa kayan yaji a kai in ana so.
A ci da daɗi.

Domin sanin yadda ake bandashe danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Banɗashe
Labarin na GabaYadda Ake Gas Meat
Babbar Dalibar addini, wacce ta karanci abin cei da lafiyar sa (food and nutrition) da kuma kwararriyar mai hada abin ci da kuma koyar da aikin hannu