Category: Tarihi

Mun samar da wannan ɓangaren ne domin samar da dukkanin Tarihi a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa wajan ɗora Tarihi ko saukewa

  • Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru

    Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata kaza da ta ce za ta yi aure, sai zakaru suka yi ta zuwa neman aurenta. Duk zakaran da ya zo, sai Kaza ta ce ba ta son sa. Wani tace ya yi gajarta; wani ta ce ba shi da gashi; wani ta ce bai iya cara ba. Wani kuma idan ta raina shi, sai ta ce ba shi da sirdi, ko kuma ya yi tsawo, ko ba shi da kyaun fuska.

    Haka dai ta rinƙa korar su. Sai wata rana Muzuru ya sami labarin halin Kaza, da kuma buƙatar iyayenta na su aurar da ita. Shi ke nan, sai Muzuru ya yi shigar manyan mutane, watau ya sanya babbar riga da hula, ya kuma kawo rawani ya naɗa. Bai tsaya ko’ina ba sai gidan su Kaza. Ya kira Kaza, ta fito tana wani yauƙi.

    Da ta gan shi da shiga irin ta kamala, sai ta sanar da iyayenta cewa yanzu ta sami mijin aure. Iyayenta suka yi ƙoƙarin hana ta, amma ba ta ji maganarsu ba. Daga ƙarshe dai aka ɗaura musu aure da Muzuru. Ranar da za a kai amarya gidan mijinta, sai abokan Muzuru suka rinƙa yin wata waƙa suna cewa:

    “Kaka ga abinci ya shigo mai daɗi, Kayau-kayau.”

    Shi kuma ango yana cewa: “Ku kawo mini abincin nan in ci, In yi maganin kwaɗayi.” Sai Muzuru ya ɗauki allo, wai zai yi karatu, amma sai ya rinƙa cewa: “In jingina allona, In ci Kaza.” Da kowa ya watse, sai ko Muzuru ya cabke Kaza. Tun tana kuka, Kwayat!, Kwayat!!, har aka ji shiru ya gama murɗe wuyanta, ta mutu. Saboda tun fari ba ta ji maganar mahaifanta ba, ba wanda ya yi ƙoƙarin ceton ta daga damƙar da mijinta ya yi mata. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Girman kai rawanin tsiya.
    • Kowa ya ɗebo da zafi, bakinsa.
    • Mai rabon shan duka, ba ya jin kwaɓa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can ƙasar Turu, an yi wani mutum mai ’ya’ya mata biyu. Allah ya yi su kyawawa. Ga haske, in ka gan su kamar taurari. Ɗaya daga cikin ’yammatan ba ta fita ko da ƙofar gida. Amma ɗayar takan zauna a ƙofar gida, kuma duk wani saurayi da ya zo, sai ta ce za ta kira masa ’yar’ uwarta.

    Ana nan, ana nan, sai wata rana wani dodo ya rikiɗa ya koma saurayi, ya je gidansu. Sai ya tarar da yarinyar nan da kan zauna a ƙofar gida, ya yi mata sannu; ita kuma ta mayar masa. Sai ya ce: “Kai amma yarinyar nan na yaba da kyaunki.” Sai ita ko ta ce masa: “Ai da ka ga ’yar’uwata da ba za ka yi mini magana ba, balle ma ka ce ina da kyau.”

    Dodo ya sami gangara, sai ya ce: “To, ko za ki kira mini ita?” Sai yarinyar ta shiga ta yi wa ’yar uwarta magana. Ita kuma ta tambaye ta: “Da wa ya yi kama?” Sai ta ce: “Ya yi kama da mahaifiyarmu.” Da ta ji haka sai ta ce: “A a, ai babu wani saurayi da ya isa ya gwada kansa da mahaifiyata. Ba zan je ba.”

    Daga nan mai zama a bakin ƙofa ta je ta ba mutumin haƙuri. Ba tare da ya nuna fushi ba, ya kama hanya ya yi tafiyarsa. Amma saboda nacinsa, kullum sai ya je gidan, yana ƙoƙarin ganin yarinyar. Sannu a hankali har yarinyar nan mai tsayawa a waje ta gayawa mahaifinsu halin da mutumin nan yake ciki na tsananin ƙaunar da yake yi wa ‘yaruwarta.

    Da mahaifinsu ya ji bayaninta, sai yace: “Duk sanda ya zo ki shigo ki gaya mini. Can kuwa sai ga mutumin. Nan da nan ta yi masa bayani cewa: “ka jira in yi wa sanar da mahaifinmu cewa ka iso. Mahaifin yaran ya fito, suka gaisa da baƙon, ya kuma sanar da shi cewa yana so ne ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, wato wadda take cikin gida.

    Sai baban yaran yace masa ya jira yana zuwa. Ya shiga gida. Da shigarsa, sai ya ɗauki yarinya ya sa ta a cikin rumbu. Sai ya kira mutumin yace: Ga wannan rumbu ka kai wa kakannin yarinyar a garinsu. mutumin nan ya ɗauki rumbu, ya kama hanya. Yana cikin tafiya sai ya yi tun tuntuɓe ya faɗi; yarinyar da ke cikin rumbun ma ta faɗo.

    Da yarinyar ta ga mutumin sai tace: “sannu kawu” Sai mutumin ya ce: “Ashe ke ce a ciki?” Da ta lura a daji suke, sai ta gudu ta tasamma gida. Washe-gari sai mutumin ya koma gidansu yarinyar, ya tambayi labarinta, to amma kafin ya je, mahaifinta ya tambaye ta abin da ya farutsakaninta da mutumin, ta kuma gaya masa yadda mutumin ya yi tuntuɓe ya faɗi, da yadda ta yi masa sannu bayan ta faɗo daga rumbu.

    Da mahaifinta ya ji haka sai ya ce: “Ai ko nai kamata ki yi masa sannu ba da ya faɗi. “Sai ya sake sa ta a cikin rumbu, ya sake ɗora wa mutumin. Mutumin ya kama hanya, sai ya sake yin tuntuɓe a cikin daji, ya faɗi. Yarinya ta mance da abin da mahaifinta ya gaya mata, sai ta yi masa sannu.

    Shi kuwa ya kama ta, ya fyaɗa da ƙasa, ya mueɗe mata wuya, nan take ko haurawa ba ta yi ba. Daga nan sai ya ɗauki gawar ya jefa a cikin jakarsa. Ya ajiye jakar a gindin wata bishiya, ya tafi neman itacen da zai yi tsire da gawar, ya gasa. Ashe duk abin da suke yi wata tsohuwa tana ganinsu, sai ta yi sauri ta cire gawar yarinyar ta jidi duwatsu ta zuba masa a cikin jakar, ta gudu da gawar, ba ta tsaya ko ina ba sai gidan mahaifin yarinyar nan.

    Ta kai masa gawar ‘yarsa. Da dodo ya samo itacen, ya ɗauki jakarsa ya je inda zai gasa yarinyar nan ya ci nama, sai ya juye duwatsu a tukunya ya hura wuta, ba tare da ya san duwatsu yake dafawa ba. Can da ya ji dutse ya fashe sai ya ce: “Yawwa wannan ƙwaƙwalwarta ce ta fashe. Sai ya ɗebi fasasshen dutse ya cinye.

    Da tsohuwa ta kai gawar sai ta ce da iyayenta: Ku duba abinda kuka sa aka yi wa ‘yarku.

    Mahaifin yarinyar ya yi wa tsohuwa godiya, suka yi sallama ta tafi. Tsohuwa na tafiya, sai uban ya ƙone gawar yarinyar, ya zuba tokarta a cikin mararaki, ya zuba ruwa, sai ya rataye mararakin nan; sannu a hankali ruwan tokar ya fara ɗigowa daga mararaki. Da ya ɗigo, sai yace: “Wannan hannun Sirandi ne.” Can kuma idan ruwa ya sake ɗiga sai yace: “Wannan kuma ƙafarta ce.”

    Da haka dai, kafin wani lokaci yarinyar nan ta haɗu tsaf ta miƙe. Washe-gari kuma sai Dodon nan ya sake zuwa ƙofar gidansu yarinyar. Da mai zama a ƙofar gida ta gan shi, sai ta shiga gida da gudu ta gaya wa mahaifinta cewa ga fa mutumin nan ya sake zuwa. Sai mai gidan ya fito. Da suka gaisa sai ya tambayi baƙon wa kuma ya zo nema.

    Shi kuwa ya ce ya zo ne yana neman wannan yarinyar da ta gudu ta shiga gida, wai ya aura. Sai mahaifinta ya gaya wa baƙon nan cewa ai yarinyar ta yi miji tuntuni. Sai bai komai ba ya tafi abinsa. Bayan ’yan kwanaki aka ɗaura wa yarinyar aure ta tare. Da mutumin ya sake dawowa sai aka ce masa yarinyar ta bar gidan.

    A nan take sai ya kife. Can cikin dare kuma sai ya rikiɗa, ya je inda yarinyar take ya ce zai kashe ta. Sai yarinyar ta nemi mijinta da ya kuɓutar da ita daga hannun wannan azzalumi. Amma sai mijinta yace ai shi ba ya ganin komai. Washe-gari sai ya je ya sami mahaifin yarinyar nan ya ce masa ya lura dai matarsa tana ganin aljanu, saboda haka ya dawo da ita, ba ya auren, ya sake ta.

    Da uban ya ji haka, sai ya tambaye ta abin da ta gani. Ta gaya masa duk yadda suka yi da Dodo. Sai baban yarinyar ya ba ta wata kyanwa, ya ce: “Idan har mutumin nan ya sake zuwa zan ce masa zan haɗa shi da ke ku je gidansa. Idan har ya rikiɗa ya zama wani abu, sai ki ce masa idan da gaske yake to ya rikiɗa ya koma wani ƙaramin abu, kamar ɓera.

    Idan ya zama ɓera, sai kawai ki cinna masa kyanwar nan ta cinye shi. ”Rannan da mutumin ya dawo, sai uban yarinyar nan yace: “Zan ba ka ɗiyata, amma sai ta je da kai ta ga gidanka.” Sai mutumin ya ce: “Ta fito mu tafi.” Nan da nan yarinya ta naɗe tabarmarta, ta saka kyanwa a ciki yadda ba zai gan ta ba, ta fito suka tafi.

    Suna isa kusa da gidansa, sai ya zama Giwa, sai ya ɗauki yarinyar ya kawo ta kusa da tukunya, amma ba ta tsorata ba, sai yarinyar ta ce: “In da gaske kake kana rikiɗa, to ka rikiɗa ka koma wani abu ƙaramin gani.” Nan da nan ya zama bushiya. Da ta ga haka sai ta yi tsaki ta ce: “Wannan ai ka yi rikiɗar kaya ce kurum. Ina so ka rikiɗa ka zama abin da ba shi da kaya.”

    Yana jin abin da ta faɗa, sai ya rikiɗa ya zama ɓera. Kamar walkiya, sai yarinyar nan ta saki kyanwa. Nan take kuma kyanwa ta kama ɓerar nan ta lanƙwame. Jim kaɗan sai kawai dawaki da jakuna da raƙuma da sauran kayayyakin alatu masu ɗimbin yawa suka bayyana.

    Nan da nan ta kwashe su ta ɗora wa raƙuman nan da shanu da jakuna da ta mallaka, ta zaɓi wata taguwa ta haɗa mata sirdi, ta hau, ta kora sauran dabbobin da ta yi wa laftun dukiya, ba ta tsaya ko’ina ba sai a gidansu. Da babanta ya gan ta da wannan dukiya mai tarin yawa, ga shi ta durƙusa ta gaishe shi, ta kuma yi godiya ga Allah saboda ya raba ta da wannan bala’i, sai ya yi matuƙar murna. Ita da mahaifanta da ’yan’uwanta suka ci gaba da morar wannan dukiyar hankali kwance. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Girman kai rawanin tsiya.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango shi ba.
    • Karen bana, maganin zomon bana

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kare Da Kura

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kare Da Kura

    Tatsuniyar Kare Da Kura

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Kare da wata Kura a Dajin Saidawa. Suna ganin juna amma daga nesa, har dai yau da gobe suka saba, sai suka ƙulla abota. Kare yana da ’ya’ya bakwai, Kura kuma tana da’ya’ya biyar. Sai wata rana suka ce za su je daji dakan wake. Sai suka shirya suka fita.

    Suka yi ta tafiya har suka isa wurin dakan wake, suka kama aiki. Can sai Kare ya ce wa Kura: “Gara ki jeki ɗora mana sanwar kalaci. Ina ganin wake da shinkafa ya kamata ki
    dafa. ”Kura na jin haka ta ce: “Gaskiyarka, Kare.” Kura ta je ta kama ’ya’yan Kare, ta zuba su a tukunya, ta ɗora sanwa.

    Daga nan ta koma wurin aiki. Da Kare ya ga ta koma, sai ya tambaye ta: “Kin ɗora sanwa ne?” Kura ta ce masa: “E, na ɗora. Ai yau fa za mu ci daɗi.” Daga nan sai
    Kura ta kama waƙa tana cewa:

    “Mu yi daka da wuri mu tafi,

    ’Ya’yan Kare suna shan wuta,

    Hum tiri hum.”

    Da Kare ya ji abin da take cewa, sai ya ce: “Kura bari inje in duba mana sanwa ko wuta tana ci.” Kura kuma ta ce wa Kare: “Idan ka je kar ka buɗe tukunyar; ka iza wutar kawai ka dawo.” Sai Kare ya ce: “To, na ji.” Kare na isa murhu ya tarar wutar ta mutu; ko zafi ma sanwar ba ta fara yi ba.

    Sai ya buɗe tukunyar domin ya ga abin da Kura take dafa musu. Kare na buɗewa sai ya ga ’ya’yansa suna mutsulniya a cikin ruwa. Bai yi wani ɓata lokaci ba, sai ya fitar da su. Nan da nan ya kamo ’ya’yan Kura ya sa a cikin tukunyar nan, ya nemo guma-guman itace ya haɗa wuta; ya ɗora tukunya a kan murhu.

    Sai ya kai ’ya’yansa ya ɓoye a kan wata bishiya. Da ya koma wurin aiki inda Kura ke jiransa, sai ta tambaye shi: “Ka gyara itacen dai ko?” Ba tare da ya nuna mata abin da ya yi ba, sai kawai ya ce da ita: “E, na gyara, ƙanwar Zaki, surukar Damisa, kanwar Giwa!” A cikin murnar kirarin da Kare ya yi wa Kura da kuma zaton za ta ci naman ’ya’yansa, sai ta ci gaba da rera wannan wakar:

    “Mu yi daka da wuri,

    Kafin rana ta kai tsakiya,

    ’Ya’yan Kare sun sha wuta,

    Sun kusa nuna.

    Hum tiri hum.”

    Sai Kare ya fara tasa waƙar yana cewa:

    “Ka juye nawa ’ya’yan

    Ka bar na an’uwana.”

    Sai Kura ta ce: “Wace irin waƙa ce haka Kare?” Sai Kare ya ce: “Sanda kike yin taki waƙar, na yi magana ne?” Da jin wannan tambaya tasa sai ta yi shiru. Suka ci gaba da gyaran wake, har suka gama. Bayan sun gama aiki, sai Kura ta ce wa Kare: “Je ka ka ɗebo wake da shinkafa daga cikin tukunya mu ci.”

    Sai Kare ya je ya ɗebo musu; ita tana zaton naman ’ya’yan Kare ne. Kura ta ci nama, ci irin na ƙeta da haɗama, har ta rage da nufin za ta kai wa ’ya’yanta. Sai Kare shi ma ya ce zai kai wa ’ya’yansa abin da ya rage. Da ta ji maganar Kare, sai ta fashe da dariya, amma ba ta yi wa Kare bayanin dalilin dariyarta ba.

    Shi kuma bai tambaya ba. Suka tafi, kowa da nufin ya kai wa ’ya’yansa nama. Lokacin da Kura ta isa raminta, sai ta tarar saura ɗanta ɗaya. Sai ta koma da gudu ta tambayi Kare, “Ina ’ya’yana?” Sai Kare ya ce: “Da kika ɗora ’ya’yana a kan wuta za ki dafa, na tambaye ki ne?”

    Sai Kura ta bi Kare da gudu za ta kashe. Da Kare ya ga haka sai ya ce da ’ya’yansa: “Ku miƙo mini igiya.”Suka jeho masa, ya kama, ya haye bishiyar. Da Kura ta kasa hawa bishiyar, sai ta ce wa Kare: “Za mu haɗu da kai.” Sai Kare ya ce: “Gobe ma zan je ɗaukar itace.” Sai Kura ta tafi abinta.

    Washe-gari sai Kare ya ɗauki damin itace. Yana cikin tafiya sai ya hangi Kura tana zuwa. Sai ya shiga cikin itacen, yana mirginawa. Da Kura ta je kusa da itacen sai ta ce:

    “Itace mai mirginawa!

    Itace mai mirginawa!!

    Ba ni hanya, ina neman Kare.”

    Sai itace ya mirgina ya kauce, Kura ta wuce. Da Kura ta yi nisa, sai Kare ya fito ya ɗauki itace ya tafi zarafinsa. Da Kura ta komo sai ta sami Kare a kan bishiya, sai tace: “Kare jiya ka yi mini ƙarya, ka ce min za ka je ɗaukar itace, amma ban gan ka ba.” Sai Kare ya ce: “Jiya ba ki haɗu da wani itace yana murginawa ba?

    ”Kura ta ce: “Na haɗu da shi mana.” Sai Kare ya ce: “A garinku kin taba jin an ga itace yana murginawa shi kaɗai?” Sai Kura ta ce: “To, gobe ina za ka?” Sai Kare ya ce: “Gobe zan je in ɗebo ruwa.” Kura ta tafi, tana tunanin yadda za ta gama da Kare idan gari ya waye. Washe-gari sai Kare ya ɗauki tulunsa, ya je ɗaukar ruwa.

    Sai ya hango Kura ta doshi rafin da yake. Sai ya shiga cikin tulunsa yana murginawa. Da Kura ta je kusa da tulun sai ta ce:

    “Tulu mai mirginawa,

    Tulu mai mirginawa.

    Matsa mini in wuce, Domin ina neman Kare.”

    Sai Tulun ya mirgina, Kura ta wuce. Da Kare ya auna, ya san Kura ta yi nisa, sai ya fito ya ɗauki ruwansa ya tafi. Daga baya kuma Kare da Kura suka haɗu, yana baya-baya da ita. Sai Kura ta ce: “Kare, ka yi min ƙarya.” Shi kuwa sai ya mayar mata da jawabi cewa, “Ba ki haɗu da wani tulu mai mirginawa ba?

    Ai ni ne a cikin tulun.” Kura ta ce ta gamu da shi, ta sake tambayar sa cewa: “To gaya mini inda za ka gobe domin in sami damar gamawa da kai kowa ya huta.” Sai Kare ya harari Kura, ya yi mata kallon raini, ya ce: “Zan je su, watau kamun kifi a gulbin yamma da Dajin Saidawa.”

    Washe-gari Kare da ’ya’yansa suka je su. Can sai suka ga Kura ta tunkari inda suke. Sai Kare ya ce wa ’ya’yansa duk su faɗa ruwa su buɗe haƙoransu. Har shi ma suka faɗa suka buɗe haƙoransu. Kura tana isa a gaɓar gulbi, sai ta ga haƙoran Kare da ’ya’yansa, sai tsoro ya kama ta. Sai ta ce wa ’yarta:

    “Kilatanda! kilatanda!!

    Baya baya ba ta.” Duk ta yi ’yan dube-dubenta ba ta ga Kare ba. Haka Kura ta gaji ta tafi. Da Kare ya ga lallai Kura ta tafi ba ta da nufin komawa bakin gulbi nemansa, sai ya fito da ’ya’yansa. Daga nan suka bar dajin nan domin kada wata rana tsautsayi ya sa Kura ta halaka shi da ’ya’yansa. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • In za ka gina ramin mugunta ka gina gajere, ba ka sani ba ko kai ne za ka faɗa.
    • Rama cuta ga macuci ibada ce.
    • Duk inda ka kai da wayo wani ya fi ka.
    • Cin dare ɗaya kumburin ciki.
    • Wankan wuta sau ɗaya a kan yafa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata mai ciki. Sai wata rana ta shirya za ta yi balaguro. Tana tafiya a cikin daji, sai naƙuda ta kama ta. Sai ta raɓa a ɗan wani wuri ta haihu. Ta ɗauki jinjirin ta kama hanya tana tafiya, ko za ta tarar da wani gida ta huta. Sai ko ta tarar da wani gida a tsakar dokar daji ta shiga.

    Ashe gidan nan na Dodo ne. Sai ko mai jegon nan ta ga ruwa a gidan, ta ɗiba ta yi wanka da shi, ta wanke ɗanta, ta dafa abinci. Sai ta hau kan ɗakin Dodon, ta zauna ta ci abincin da ta dafa. Sai ta ga wata wuƙa a gidan Dodo, ta kuwa ɗauke ta, ta hau kan ɗakinsa ta zauna.

    Can Dodo ya dawo daga farauta, sai ko tsoro ya kama ta, sai ta tsunkuni jaririnta, har ya saki zawayi saboda jin zafi. Zawayin kuwa ya zubo a tafin hannun Dodo yayin da yake zaune a gindin ɗakin yana hutawa, sai ya lashe, ya ko yaba da daɗin abin da ya lasa, sai
    ya ce: “Wannan ai miya ce da gauta.”

    Da ya ɗaga kansa domin ganin daga inda wannan abin daɗi yake zo masa, sai ko suka yi arba da matar nan. Sai ta sake tsunkunin ɗanta, ya yi wata irin ƙara. Da Dodo ya ji, sai ya tsorata, ya shiga daji a guje, ya kira sauran dabbobin dawa domin su zo su ga wata irin halitta da bai saba ganin irinta ba, wai yana so su kore ta daga gidansa.

    Dabbobin suka cika gidan Dodo, to amma ba wanda ya shiga saboda tsoro. Suka ce Giwa ta shiga, ta ƙi; aka ce Raƙumin Dawa, ya ko yarda ya shiga. Da ya kunna kansa ya shiga sai ko matar ta riƙe kan. Da sauran dabbobin suka ga ya jima bai fito ba, sai suka tambaye shi abin da ya riƙe shi. Sai ya ce: “Dodo ne ya riƙe mini wuya.”

    Ita kuwa matar sai ta sa wuƙar ta fara yankan wuyan Raƙumi. Tun suna tambayar Raƙumin Dawa yana magana, har ya kasa magana. Jim kaɗan sai suka ga ya faɗi matacce, ba kai a jikinsa. Ganin haka fa duk suka tarwatse da gudu; Dodo mai gidan ne kuwa a kan gaba. Duk bishiyar da ya ci karo da ita sai ya tuge ta don gudu.

    Da matar ta ji ba sauran motsin dabbobin nan, sai ta sauƙo goye da ɗanta ta kama hanya, ba ta tsaya ko’ina ba sai gidan mijinta. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Banza ta kori wofi.
    • Taron tsintsiya ba shara.
    • Dabara ta fi ƙarfi.
    • Yuyu banza, ƙwaƙƙwara ɗaya ya fi amfani.
    • Dabara ɗaukar ɗaki.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Sarki Kunkuru, wanda matarsa ta haifi ɗa namiji. Sai ya tara Kunkurayen garin ya sanar da su cewa matarsa ta haifi ɗa. Ya bayyana cewa duk wanda ya san sunan yaron, zai ba shi ’yarsa aure. Sai wani Kunkurun ya je bakin rafi ya ɓuya. Lokacin da ’yar Sarki da ƙawayenta da kuyangi suka je ɗaukar ruwa, sai Kunkurun ya faɗa cikin tukunya ɗaya daga cikin kuyangin, ya ɓuya.

    Bayan ’yar Sarki da jama’arta sun koma gida, kuma wadda ya shiga tukunyarta ta ajiye ruwan, sai Kunkurun nan ya fito, ya ɓuya a bayan ƙyauren ɗakin Sarki. Da Sarki ya shiga gida, sai ya kira matarsa mai jegon jaririn nan da aka haifa, ya ce: “Kin ba Kuturin nono ya sha?”

    Kunkurun da ke maƙe yana jin su, kuma ya ji sunan yaron Kuturin. Sai uwar ta ce da Sarki: “A a, ina dai shirin ba shi yanzu.”Can da Kunkurun da ke bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya ji ƙafa ta ɗauke, sai ya fito, ya gudu. Washe-gari sai Sarki ya tara Kunkuraye, ya tambaye su ko akwai wani da ya san sunan jaririn gidansa.

    Duk wurin aka mutu a ka, ba wanda ya yi magana, sai Kunkurun nan da ya yi dabararl aɓewa a bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya nuna alamar yana da magana. Sai Sarki ya ba shi dama, ya tambaye shi sunan yaron. Nan take kuwa Kunkurun nan ya ce: “Ai sunansa Kuturin.” Sai Sarki ya ce: “Haka ne kuwa, ba shakka.”

    Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sarki ya cika alkawari, watau aka ɗaura wa ’yarsa aure da wannan talakan Kunkuru da ya faɗi sunan jaririn gidansa daidai. To, amma kuma yarinyar ba ta son Kunkurun da aka ba ta, amma kuma ba ta nuna masa ba. Wata rana ’yar Sarki da mijinta suna hira, sai ya yi suɓur-da- baka ya gaya mata dabarar da ya yi har ta kai ya aure ta.

    Bayanin da ya yi mata ya ɓata mata rai, domin da ma ba ta son sa. Amma fa ba ta nuna masa tana cikin ɓacin rai ba. Washe-gari sai tace da mijinta tana son zuwa ganin gida. Sai mijinta Kunkuru ya amince, amma ya ce kar ta daɗe ta dawo da wuri. Da ta isa gida, sai ta gayawa mahaifinta yadda mijinta ya yi har ya ji sunan ƙanenta, wanda kuma a sakamakon haka ya aura masa ita.

    Da Sarki ya ji bayaninta, sai ya ce mata ta koma gidan mijinta, ya san abin da zai yi. Sai ta koma. Wata rana sai Sarki ya tara duk Kunkurayen da ke fadamu da yake iko da ita, ya ce musu ya yi baƙo, kuma duk wanda ya gaya masa sunan baƙon, to zai ba shi rabin garinsa. Bayan Sarki ya gama jawabi, jama’arsa duk sun koma gida, sai ya umarci dogarai da su shiga fakon duk wanda zai zo ya shiga gidansa, su kama shi.

    Da dare ya yi, sai ga Kunkuru surukin Sarki ya doshi ƙofar shiga gidan Sarki, yana sanɗa. Bai san ana ganin sa ba. Yana shiga zauren farko, sai ko dogaran Sarki suka yi wuf suka cafke shi, suka ɗaure.Da gari ya waye, sai aka kai shi gaban Sarki. Nan da nan labari ya bazu, duk gari aka shiga mamakinsa da jin haushinsa.

    Daga bisani Sarki ya sa aka yanke masa hannaye da ƙafafu, aka kai shi bayan gari aka jefar. Yana cikin halin azabar ciwo a daji, sai Ƙadangare ya zo wucewa. Da Kunkurun nan ya gan shi sai ya kira shi, ya roƙe shi ya ba shi aron ƙafafuwansa, domin ya je kasuwa. Sai Kadangare ya girgiza kai, ya ce: “A a, ba zan iya ba ka aron ƙafafuwana ba.”

    Can kuma Maciji ya zo wucewa, sai Kunkurun nan ya ce da shi: “Maciji, maciji ɗan’uwa, ka ba ni aron ƙafarka mana in je kasuwa, idan na dawo in ba ka kayanka.” Sai Maciji ya yarda ya ba shi, ya ce masa amma fa ya dawo da wuri. Kunkuru ya sa ƙafafuwa ya kama hanya, amma fa bai dawo da wuri ba kamar yadda ya yi wa Maciji alƙawari.

    To a kan haka shi ya sa duk sanda yake cikin tafiya, da ya ji motsi sai ya yi sauri ya maƙe ƙafafuwansa da hannayensa, saboda yana zato Maciji ne ya biyo sawun ƙafafunsa. Wannan rashin dawo masa da ƙafafun da Kunkuru ya ara ne ya sa kowa yanzu yake ganin Maciji yana jan ciki ba ƙafafu. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karya fure take ba ta ’ya’ya.
    • Kayan aro ba ya rufe katara.
    • Mayaudari ƙarshensa asara da nadama da jin kunya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata da mijinta, ba su taɓa haihuwa ba. Sai ’yan gaza gani a garinsu suka shiga cewa ita juya ce ba mai haihuwa ba. Irin waɗannan maganganu kuwa sukan dame ta. Wata rana tana dawowa daga gona, sai ta ga wani jariri a gindin gamji. Sai ta ɗauke shi, ta goya, ta tafi da shi gida. Da mijin ya shiga gida, sai ta gaya masa ta haihu a gona.

    Ya yi murna, amma fa da ’yar shakka. Bayan mako guda aka raɗa wa jariri suna Tabi. Daga nan sai ta shiga zaman jego a gida, ta yi kwana arba’in tana cin kaji. Bayanta cika arba’in, sai ta gaya wa mijinta tana buƙatar yarinyar da za ta taimaka mata wajen renon yaron. Mijin kuma ya nemo mata.

    Ashe yaron nan ba mutum ba ne, aljani ne, amma ba su sani ba. Kullum idan mai gidan da matar za su je gona, sai yaron yace: “Iya ki zo mini da ɓera; baba ka zo mini da fara.” Kuma da zarar sun fita daga gidan, sai yaron ya rikiɗa ya zama babban mutum. Tuni kuma ya ja kunnen yarinyar, ya ce mata: “Idan kika gaya wa mutanen nan abin da nakan yi bayan sun tafi gona, to zan kashe ki.”

    Shi ke nan, kullum sai ya sa ta shiga rumbu, ta ɗebo hatsi yasa ta shiga niƙawa, yana yi mata kiɗa da gurmi. Ga waƙar da yakan yi airin wannan lokaci: “Kai Ɗan Tabi, Kai Ɗan Tabi, Ɗan mai gajerar fuska, Wagga mata ba ta haifi ɗa ba, Sai ka sa ta sami Tabi. Tabi, Tabi na me ye?” Da zaran ya ƙintaci iyayen sun kusa komowa gida, sai ya rikiɗa ya koma yaro, kamar yadda suka san shi, ya sa yarinyar ta goya shi.

    Idan suka dawo sai su ba shi ɓeran da farar da suka kamo masa. Kowacce rana sai sun kawo masa ɓera da fara. Ana nan, a kwana a tashi, sai suka lura yarinyar tana ramewa, amma ba su san abin da ke damun ta ba. To, ashe wata tsohuwa maƙwabciyarsu tana ganin duk abin da yake faruwa tsakanin yarinyar nan da ɗan aljanin nan.

    Sai wata rana ta kasa jurewa, ta kira mijin da matar tace da su: “Ku yi kamar za ku gona, sai ku ɓuya a gidana, ku gaabindayaronku yakan yi.” Washe-gari da sassafe suka je gidan tsohuwa, suka sa idonsu a ƙafar danga, suka shiga jira. Jim kaɗan kuwa yaron ya rikiɗa, ya zama babban mutum. Suna gani ya ɗauki yarinya ya jefa ta cikin rumbu. Suna gani ta miƙo masa hatsi, ta fito ta fara niƙa masa.

    Sai ya bugi cikinsa, riga ta fito. Da ya sake bugawa, sai ga hula. Da ya buga a karo na uku, sai ga gurmi. Nan take ya fara kaɗa gurmi yashiga yin wannan waƙar: “Kai Tabi, Kai Ɗan Tabi, Ɗan mai gajerar fuska, Ka ga mata ba ta haifi ɗa ba, Sai ta sa ma ɗa suna Tabi, Tabi na meye.” Sai mijin ya tambayi tsohuwar yadda za su yi.

    Tsohuwar tace da su: “Yanzu ku koma gida; gobe za mu je gidan mai magani.” Washe-gari suka yi kamar sun je gona, suka nemo ɓera da fara suka kai wa yaron. Sai yaron ya ce: “Mama, yau ba ku je gona ba.” Sai ta ce masa sun je, sun gaji shi ya sa ba su samo masa ɓera da fara masu kyau ba. Sai yaron ya ce ba zai ci ba, amma gobe idan sun je gonar su zo masa da fara da ɓera masu kyau.

    Washe-gari suka je wurin tsohuwa ta raka su wurin mai duba. Suka gaya masa duk abin da ake ciki. Ya duba, ya gano cewa yaron nan fa ba mutum ba ne. Da suka tambayi mai duba yadda za su rabu da yaron nan, sai ya ce to su je su sami baƙin rago mai farar ƙafa da gyaɗa da riɗi a soye, da ƙwarya da garin dawa, sai su tafi da su bakin rafi.

    Duk wanda aka aika, to idan ya tafi kada ya sake dawowa, ya je ya hau wata bishiya. Sai suka je, suka nemo duk abin da aka ce, suka kai. Ɗan duba mai magani ya ce su je su ɗauko yaron, su je bakin rafi da shi. Suka sa yarinya mai goyonsa ta goya shi suka ce za su je bakin rafi kamun kifi. Sai ta goya shi, suka tafi.

    Da suka je bakin rafi, sai ɗan duban ya ce ya kamata a fara dafa abinci kafin a kama kifi. Ashe wai suna yi wa Tabi wayo ne, sai matar ta yi kamar za ta hura wuta sai ta ce: “Af, mun yi mantuwa. Mun manta auduga da dutsen hura wuta.” Sai suka cewa yarinyar ta sauke goyon, ta je ta ɗauko musu dutsen hura wutar.

    Sai ta sauke yaron, ta je, ta hau kan bishiya. Da suka ji shiru, sai suka ce tsohuwa ta bi sawun yarinyar ta duba ko lafiya. Ita ma ta je shiru. Sai mijin shi ma ya bi tsohuwa, shi ma shiru. Sai matarsa ta bi sawunsa. Daga ƙarshe dai kowa ya tafi, suka bar yaro da ɗan duba. Shi ma mai duba sai ya yi wa yaro dabara ya tafi ya bar shi. Da yaro ya ji shiru, sai ya yi ta kiran su, amma ina, sai ya ce: “Wato mutanen nan suna so su ci amanata ne.”

    Sai ya juye gyaɗa da riɗi a cikin aljihunsa. Idan ya ɗiba sai ya watsa a bakinsa, sai yace wannan ƙafar wane ne, yana ta bin sawunsu, har ya isa gindin bishiyar da suka hau. Yana ɗaga kansa, sai ga su gaba ɗaya kan bishiyar. Dukansu tsoro ya kama su. Sai ya ce: “Yanzu haka za ku yi min? Na kwanta a gindin bishiya ina hutawata kika zo kika ɗauke ni, kuma yanzu za ki ci amanata? Ki sani idan Allah bai ba ki ɗa ba, to ba wanda zai iya baki shi. Ku sauko ku tafi na yafe muku. Amma nan gaba kada ku ƙara tsintar ɗa, ku ce za ku riƙe.” Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Abin da Allah bai ba ka ba, babu wanda ya isa ya ba ka shi.
    • Zaƙin nema ba ya kawo samu.
    • Tsintattar kyanwa ba ta mage.
    • Idan za ka yi fatan samun ɗa, yi fatan samun nagari.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗankucaka

    Tatsuniyar Ɗankucaka

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Ɗankucaka ya fita kiwon ragonsa a bayan gari. Ya yi wa rago talala don kada ya shiga gonakin mutane ya yi ɓarna. Bayan la’asar sai ya koma ya kunce ragon, ya hau ya kama tafiya. Da ya isa kusa da gidan Kura, sai rago ya yi kuka. Da Kura ta ji kukan rago sai ta fito da gudu ta kira Ɗankucaka. Da ya je sai tace: “Yaya sunanka ne?” To daman kuwa Ɗankucaka wani hatsabibin yaro ne.

    Wasu ma kan yi masa ganin aljani. Sai ya ce da Kura: “Sunana Ɗankucaka.” Kura ta tambaye shi: “To, Ragon na sayarwa ne?” Sai Ɗankucaka ya ce: “E, na sayarwa ne.” Sai Kura ta ce: “Nawa ne kuɗinsa?” Sai Ɗankucaka ya ce: “Ba da kuɗi za a saya ba; sai dai a yi kokowar kwana bakwai.

    Kuma kokowar a kan dutse nake yinta.” Jin haka sai Kura ta yi dariya ta ce: “Mutanen ƙwarai ma ba su ce za su yi kokowa ba, sai kai Ɗankucaka!” Tana gama faɗin haka sai kawai ta kama Rago ta kashe, ta ɗauki gangar jikinsa ta kai gida suka sha gara ita da ’ya’yanta.

    Washe-gari sai Ɗankucaka ya je wurin Kura suka tafi kokowa. Suka kama kokowa; can Kura ta kayar da Ɗankucaka. Lokacin da za su rabu kowa ya tafi gida, sai Kura ta ce: “Banda wawa, maimakon ka karɓi kuɗi sai ka zaɓi duka?” Ɗankucaka dai bai ce da ita uffan ba. Washe-gari ya sami Kura suka tafi dutsen da suke yin kokowa.

    Gaga-gaga, Kura ta sake kada Ɗankucaka. Da za su rabu kowa ya tafi gidansa sai Kura ta kalli Ɗankucaka ta ce: “Gara ka haƙura da kokowar nan haka, don za ka rasa ranka.” Ɗankucaka dai bai ce komai ba. A ranar kokowarsu ta ukun ma Kura ta kayar da shi. Amma a rana ta huɗu, sai Ɗankucaka ya ɗaga Kura ya doka ta a kan dutse.

    Kayen kuwa ya kiɗima ta. Sai ta ce da shi: “Kai aboki menene haka?” Ɗankucaka ya ce mata: “A lokacin da kika ƙwala ni da ƙasa na yi magana ne?” Kura ta ce: “A a, a gaskiya ba ka yi magana ba.” Da Kura ta isa gida daga fagen kokowarta da Ɗankucaka, sai tace da ’ya’yanta: “Duk wanda ya zo nema na gobe ku ce na yi tafiya, ba zan dawo ba sai bayan kwana biyar.”

    Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura domin ta fito su tafi kokowa. Ashe ta shiga rumbu ta ɓuya, amma ’ya’yanta suka ce tayi tafiya. Ɗankucaka ya ce: “Na ji ta yi tafiya; amma daman tace idan na zo in ɗauki rumbu in tafi da shi.” Sai ’ya’yan suka ce: “To, ɗauki mana.” Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya ɗauki rumbu.

    Sa’adda ya je bakin ƙofa, sai ya yi wurgi da rumbun. Kura ta buge ƙugunta; ba ta san sanda ta ce: “Wayyo!! Mene ne haka aboki?” ba. Da Ɗankucaka ya ji haka sai ya ce: “Na gaji ne saboda nauyinki; ina hutawa ne. Ashe kina nan, kika ƙi fitowa mu je kokowa?” Tun da an gane, kan dole ta yarda suka je fagen kokowar.

    Da suka kama kokowa kici-kici, sai ya ɗaga Kura sama, ya yi juyi da ita, sannan ya maka ta a kan doron dutsen nan. Kayen ya kai kaye, kuma jikinta ya yi tsami fiye da kullum. A rana ta shida sai Kura ta ɓuya a cikin zana. Da Ɗankucaka ya biya mata domin su tafi fagen fama, sai ya ce ya je ne ya ɗauki zana.

    Ba tare da wani musu ba ’ya’yan Kura suka ba shi zanar da uwarsu ta maƙe a ciki. Da ta lura ya je bakin ƙofa, sai ta ji tsoron kada ya yi jifa da ita. Sai tace: “Abokina daure ka ajiye ni a hankali, kada ka yi jifa da ni irin na jiya.”Da Ɗankucaka ya ji maganarta sai ya ce: “Ashe kina nan?” Ba su zame ba sai a wurin kokowarsu.

    Ɗankucaka ya sake yi wa Kura mummunan kayen da bai taɓa yi mata kamarsa ba; duk kanta ya farfashe. Da ta isa gida, sai ta gudu daga gidanta, ta tafi gidan kawunta. Tana isa sai ta tarar da ɗan kawunta mai suna Goshi. Ta tambaye shi: “Goshi, ina babanka?” Sai yaron ya ce: “Babana yana nan, amma kin san ba a tashinsa daga barci sai da wani babban dalili, kuma idan ana son ya tashi sai an nemi zugazugai an sa a ƙarƙashinsa, an haɗa wuta kamar ta maƙera.

    Zafin wannan wuta ne zai tayar da shi.” Yana gama yi mata bayani ta ce: “Goshi, abin da ya kawo ni fa babban abu ne.” Goshi ya dubi Kura ya ce: “Wane abu ne kuwa wannan?” Sai Kura ta gaya masa yadda suka yi da Ɗankucaka, kuma ta nuna masa kanta, duk ta ji ciwo. Sai Goshi ya ce: “Ai idan dai wannan ne, ai ko ni zan yi miki maganinsa.”

    Shiga gida a shafa miki magani.” Goshi ya koma bakin ƙofa ya zauna, yana jiran ya ga wanda zai zo. Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura, ya tambayi ’ya’yanta inda take; suka ce masa ta yi tafiya. Sai ya fita ya fara bin sawun Kura, har sawunta ya kai shi gidan kawunta.

    Da ya isa, sai ya tarar da Goshi a kofar gida. Sai ya tambaye shi: “Kura tana nan ne?” Goshi ya sanar da shi Kura tana nan, kuma ya tambaye shi: “Me ya faru ne?” Ɗankucaka ya ce masa: “Ina son ta zo mu je mu ƙarasa kokowarmu ne.” Ba tare da tunani ba, Goshi ya ce: “Na sayi kokowar. Mu je ka yi da ni.”

    Sai Ɗankucaka ya ce: “A kan dutse muke yi fa.” A cikin fushi Goshi ya ce da Ɗankucaka: “Ko a kan ƙarfe ne na karɓa.” Suka tafi. Da fara kokowa Ɗankucaka ya Ɗaga Goshi ya danƙara da ƙasa. Goshi ya ji zafin kayen nan ƙwarai. Shi ma ya zabura, ya ɗaga
    Ɗankucaka, ya maka shi da ƙasa kan dutsen nan. Kayen ya razana Ɗankucaka.

    To amma sai suka ci gaba da fafatawa. Can Ɗankucaka ya sake kayar da Goshi. Da ya ga Goshi a ƙasa, sai yace: “Dutse buɗe.” Dutse ya tsage, Goshi ya faɗa ciki.” Goshi ya yi wa dutse magana, wani hayaƙi ya turnuƙe, sai ga Goshi ya fito. Suka sake kama kokowa. Da Goshi ya yi wani gwauron numfashi, ya cicciɓi Ɗankucaka, ya yi sama da shi ya maka shi da ƙasa a kan dutsen nan, bai ko shura ba ya mutu.

    Goshi ya ɗauki Ɗankucaka ya je gida, ya feɗe shi, ya dafa suka cinye namansa, amma ya shanya fatarsa. Ba a ba Kura naman Ɗankucaka ba, saboda yaminsa ya fi nata ƙarfi. Bayan ’yan kwanaki sai kitsen fatar Ɗankucaka da ke rataye ya fara narkewa yana ɗiga ƙasa.

    Aka gaya wa Kura duk kwaɗayin da zai kama ta, kada ta kuskura ta taɓa fatar. Kwanci-tashi, wata rana Kura ta zo wucewa sai ta ga mai yana ɗiga daga jikin fatar nan, sai ta ce: “Ga daɗi, amma an ce kada in ci. Amma bari in taɓa kaɗan.” Sai ta sa harshe ta lashi man. Nan da nan wasu dogayen farata masu kaifi da tsini suka bayyana a jikin fatar, suka datse harshen Kura.

    Zafi ya kama ta. Sai ta ƙwala ihu. Da Goshi ya ji haka, sai ya fito ya ce: “Me ya faru?” Sai ta ce: “Fatar nan ce ta yi farata, ta kama ni za ta kashe.”Da ya ji haka sai ya gane Kura dai ta taɓa man da ke ɗiga ne. Daga baya sai Goshi ya ɗinka jaka da fatar Ɗankucaka.

    Wata rana zai fita farauta sai ya ba Kura jakar ta rataya domin ta raka shi. Suna cikin tafiya sai jaka ta yi farata. Faratan suka kama Kura. Sai ta ƙwala ihu. Sai Goshi ya karɓi abinsa ya riƙe, suka shiga daji. A cikin dajin, sai Goshi ya ce: “Wuta, wuta daji!” Daji ya kama da wuta.

    Ɓeraye da gafiyoyi da sauran ƙananan dabbobi suka fito. Sai Goshi ya dube su ya ce: “Duk ku gasu.” Nan da nan suka gasu. Ya ce: “Tuwo fito.” Sai ga tuwo masaki-masaki. Sai Goshi ya ce da Kura: “Fara ci.” Kura ta ce: “A a, kai dai fara. Ai kai ne babba.”
    Sai Goshi ya fara cin naman nan da tuwo. Kafin a ƙifta idanu, ya cinye komai. Mamaki ya kama Kura.

    Sai ta tambaye shi: “Yaya ka cinye duka ba ka rage mini ba?” Sai ya ce: “Ai ke ce ba ki yi magana ba.” Daga ƙarshe dai haka suka kama hanyar gida. Shi a ƙoshe, Kura na jin yunwa. A kan hanya ne suka je bakin wani rafi. Sai Goshi ya dubi ruwan ya ce: “Kifaye ku zo ku taru in kama.” Nan take kifaye suka taru.

    Ya ba Kura dama ta kwashi kifaye ta ci. Ta ƙi, wai shi ne babba. Shi kuwa sai ya kama kifayen ya cinye su baki ɗaya, ko ƙaya bai bari ba. Haka suka ci gaba da tafiya. Sannu a hankali suka isa daidai wata kuka mai ’ya’ya da yawa, amma ba abin kaɗo su. Sai Goshi ya ce da Kura ta ba shi cinyarta ɗaya ya kaɗo ’ya’yan kukar da ita.

    Tun kafin ta yi magana sai ya fizge mata cinya ɗaya, ya jefa, ’ya’yan kuka suka zubo birjik. Ya sha kukar nan ta yi masa karo. Ya ɗauki cinyar Kura ya maƙala mata, ta zauna kamar ba a taɓa cire ta ba. Mamaki da tsoro suka rufe Kura. Da haka dai suka isa gida. Washe-gari sai Kura ta je ta sami abokinta Kurege, ta ce da shi: “Yau za mu je farauta, amma kar ka ɗauki gayan tuwo.”

    Amma Kurege da wayonsa ya ɗauki gayan tuwo ya jefa a jakarsa. Sai Kura ta ce kar ya ɗauki fartanya. Amma sai Kurege yasa ƙaramin magirbi a cikin jakarsa. Ta ce ko dutsen hura wuta kada ya ɗauka. Amma duk abin da ta ce kada ya aikata, sai da ya yi. Suna isa daji Kura ta ce: “Wuta, wuta daji. Daji bai kama da wuta ba. Da ta yi ta gaji, sai ta ce da Kurege, “Mene ne abin da za mu yi?”

    Sai ya ce da ita: “Ko da yake kin hana in zo da dutsen wuta, na zo da wani da na gani a jakarki.” Ta yi murna. Suka yi ƙyastu da dutse, wuta ta tashi a daji. Kura ta ce da ɓeraye su fito, amma ko gashi ba su gani ba. Ta nemi shawarar Kurege. Shi kuwa ya tuna mata: “Ai kin ce kada in zo da magirbi.” Kura ta ce: “Je ka ɗauko mana.”

    Don kada ya wahala, sai ya fito da wanda ke cikin jakarsa. Kura ta amsa, ta yi ta tonon ramukan ɓeraye, amma ba su samu da yawa ba. Ta ce da ɓeraye su gasu, amma ba abin da ya faru. Ta rasa yadda za ta yi. Amma sai Kurege ya taƙaita musu wahala, ya fito da dutsen ƙyastu, ya buga shi, wuta ta kama. Da haka dai har duk abubuwan da ta ce kada ya ɗauko daga gida suka yi amfani.

    Ba tare da wata-wata ba, Kura ta kama nama da ci. Kurege dai bai ce komai ba. Amma idan ya faki idonta, sai ya ɗauki gasasshen ɓera ya jefa cikin jakarsa. Da haka ya tara abinda zai je gida da shi, ko da yake ba ta bari ya ci ba. Duka abubuwan da Goshi ya yi sanda ya fita farauta da Kura, sai da ta yi irinsu tare da Kurege. Amma shi yana fakar idonta ya ɓoye irin abubuwan da ta riƙa ci tana hana shi, har suka isa bishiyar kuka.

    Da suka je bishiyar kuka, sai Kura ta ce wa Kurege: “Ka kwanta in cire cinyarka in jeho mana kuka da ita.” Sai Kurege ya ce: “Haba Kura. Haka bai dace ba.” Sai Kura ta fusata ta ce: “Ka yarda da abin da na ce, in ka ƙi kuwa in kashe ka, in ciri cinyar in yi abin da nake so da ita.” A kan dole Kurege ya kwanta, ta tuge cinyarsa, ta jefi kuka da ita.

    Sai cinyar ta maƙale. Da Kurege ya ga haka sai ya fara ƙaraji, yana hargowa. Can dai ya yi sa’a, iska ta kaɗa cinyar ta faɗo. Kura ta ɗauko cinya wai za ta maƙala wa Kurege. Idan ta sa nan, sai ta ƙi zama, ta ce ta yi yawa ne. Sai ta riƙa cin naman cinyar da nufin rage mata girma, domin ta yi daidai.

    Da haka har cinyar tarage saura kaɗan; sai ga Goshi. Kukan Kurege ne ya jawo shi. Sai
    ya tambayi abin da ya sa Kurege kuka. Kurege ya yi masa bayani. Goshi ya tambayi Kura nata bayanin. Kura ta ce Kurege ya faɗi gaskiya. Sai Goshi ya yi wuf ya cafke Kura, ya kashe ya cinye. Daga nan kuma ya nemo wata cinya ya maƙala wa Kurege, ta zauna. Da
    aka sa wa Kurege cinya, sai ya tashi, ya ruga a guje bai sake komowa kusa da inda ya saba haɗuwa da Kura ba. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Azzalumi a ƙarshensa jin kunya ko wahala.
    • Kura dirungu sha duka.
    • Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Furera Da Gungume

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya sunanta Furera. Wata rana ita da ƙawayenta suka je daji neman itace, sai ta ga wani gungume tace za ta ɗauka, amma suka hana ta. Ta kafe faufau ita sai ta ɗauka. Ta ɗauka, ta tafi da shi gidansu. Ya zamana a gidan suna dadabbobi da yawa, kamar shanu da tumaki da awaki da jakai, har ma da alfadari.

    Furera ta ajiye gungume a tsakar gida. Can sai gungume ya kama waƙa yana cewa:

    “Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci.”

    Wannan abu ya ba Furera mamaki, sai ta je ta yi wa babanta irin waƙar da gungume ke yi. Sai mahaifinta ya ce: “Ki ba shi kaza ya ci.”Furera ta kama kaza ta ba gungume. Da aka ɗan jima kuma gungume ya sake komawa kan waƙarsa:

    “Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci

    Nama, Furera nama, in ci.”

    Furera ta garzaya ga mahaifinta ta ce: “Baba, baba, ka ga gungumen nan ya sake cewa in ba shi nama.” Mahaifinta ya ce: “Ki ba shi akuya.” Furera ta ba shi, ya lankwame nan take. Da haka ɗaya bayan ɗaya har dabbobin gidan suka ƙare, iyayen Furera kuwa suka gudu don kada gungumen yace zai cinye su.

    Gungume kuma ya sake waƙar neman nama, amma ba sauran dabbobi a gidan, sai Furera. Ta rasa yadda za ta yi. Gungume kuwa maitarsa ta motsa, sai kawai ya mirgina inda Furera take, ya haɗe ta, ya cinye. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Mai rabon shan duka, sai ya sha.
    • In ajali ya zo, ko babu ciwo sai a tafi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can wata ’yar unguwa da ke dab da wani tsauni, an yi wasu’yan biyu, Awa da Dawi. Tun suna yara mahaifiyarsu ta rasu, suka ci gaba da taimakon juna. To, amma shi Dawi hatsabibin yaro ne, kuma duk sanda ’yar’uwarsa Awa ta dafa abinci, sai ya cinye. Kullum ana haka har ta kai sai da ta tona rami domin ta riƙa ɓoye rabonta na abincin a ciki, amma sai ya tono ya cinye.

    Wata rana Dawi ya ce da Awa: “Ni fa na gaji da zaman garin nan. Ina so ki goya ni mu yi ƙaura mu je mu zauna a wani gari inda za mu sami kwanciyar rai.” Bayan Awa ta yi ɗan tunani, sai ta amince, ta goya shi, kuma ta ɗauki ’yan tarkarcensu a ka, suka kama hanya.

    Suna cikin tafiya sai Awa ta ce: “Na ga inda za mu tafi yana da nisa kuma ga shi ina jin yunwa.” Can sai Dawi ya hango wani ɗaki a gefen hanya, ya ce su shiga ciki. Da suka shiga, sai suka tarar da abinci a ciki. Dawi ya ce: “To ga shi Ubangiji ya ji kukanmu, ai sai mu ci.”

    Ba da wata-wata ba sai Awa ta yarda. Suka cinye abincin nan duka, duk da yake ba su san mai shi ba. Suka sha ruwa, suka sake kama hanya. Suna tafiya har suka isa wani
    gari. Dawi ya ce: “Albishirinki, ni fa ina da wata dabara.” Awa ta ce: “Kawo ta mu gani.” Sai kawai Dawi ya tara yaran garin nan ya ce shi fa ɗan dabo ne, kuma zai yi wasanni iri-iri domin ya ɗebe musu kewa.

    Daga nan sai ya ce a kawo turmi, domin ya yi musu wasan daka mutum irin yadda ake yi a garinsu. Dawi ya fara shiga turmi, yara suka daka shi, kuma ya fito jiki lafiya lau. Wani daga cikin yaran ma ya shiga, aka daka shi, amma sai ya fito da jikinsa jina-jina. Da yaran suka ga haka, sai wasu daga cikinsu suka tsere.

    Sauran da suka tsaya kuwa, sai suka riƙa shiga turmi ɗaya bayan ɗaya ana laƙada su, suna fita jiki a kumbure. Da mutanen garin suka ga abin da yake faruwa da yaransu, haushi ya kama su, suka yi ca a kan Awa da Dawi. Dawi ya ce da su: “Don Allah ku dakata.

    Idan kun yi haƙuri, za ku ga abin mamaki.” Mutanen suka tsaya, suna jira su ga abin da Dawi zai yi. Sai ya yi wani irin siddabaru na hatsabiban yara, nan take duk yaran da aka yi wa rauni a turmi suka warke sarai. Mamaki ya kama jama’a, suka ce sai shi da Awa su zauna a garin nan tun da suna da abin mamaki da asiri haka.

    Suka yarda. Suka zauna a garin. Dawi da Awa suka girma, ya zama sadaukin matashi. Awa kuma ta zama kyakkyawar mace, son kowa. Dawi ya kama noma da farauta. Ya tara dukiya mai yawa kamar ba maraya ba. Ita kuma ta zauna da shi suna cin duniyarsu.

    Mutanen gari suka yi wa Dawi laƙani: “Dawi Mai Turmi.” Shi kuma yakan ce: “In da mai son mu daka shi ya zo.” Duk sanda ya faɗi haka sai a bushe da dariya, labarinsa ya bazu a duniya. Shi yasa ma kuke jin duriyarsa a taskar tatsuniyoyi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.
    • Tausasa wa ɗan’uwa shi ma wani jari ne.
    • Kar a yi saurin yanke hukunci ga abin da ba a san haƙiƙaninsa ba.
    • Arziƙi a ƙafa yake.
    • Motsi ya fi zama

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wani mutum ne yana zaune da matarsa a cikin talauci a wani ɗan ƙauye, babu cin yau balle na gobe. Wata rana sai ya je gona ya ga wata busasshiyar bishiya, ya hau ya fara sara da gatarinsa domin neman abin zaman gari. To akwai wani dutse mai kogo kusa da gonar.

    Sai kwatsam, ga wasu mutane su goma sha biyu riƙe da kwari da baka sun fito daga ciki. Da fitowarsu sai suka zauna suka ci abinci, suka tafi. Amma kafin su bar wurin sai da suka faɗi wani abu kamar haka: “Kalja sum sum, Kalja sum sum, Kalja sum sum.” Da faɗin haka sai mutumin ya ga ƙofar kogon dutsen ta rufe.

    Sai dai ya ga kamar ɗaya daga cikinsu ya manta da wani abu sai yace: “Buɗe sum sum, Buɗe sum sum, Buɗe sum sum.” Sai ƙofar kogon ta buɗe, ya shiga ya ɗauko wata batta daga ciki; ya fita, suka kama hanyarsu. Bayan sun tafi, sai mutumin ya matsa kusa da dutsen domin ya kashe kwarkwatar idonsa.

    To, tun da ya ji abin da suka faɗa, sai shi ma ya faɗa, ƙofar kogon kuma ta buɗe, sai ga ruwa. Ya sake cewa: “Kalja sum sum,” wata ƙofar ta buɗe, sai ga wuta. Bai fasa ba dai, ya sake faɗa, wata ƙofar ta buɗe, amma a wannan wuri sai kawai ya ga ƙyalƙyali irin na zinariya. Ga kuma tarin zinariyar mai ɗinbin yawa, abin gwanin ban mamaki, har ma da tsoro.

    Can gefe kuma tarin azurfa ne kamar ba iyaka, ga kuma kuɗi a wani ɓangaren kamar duk kuɗin duniya baki ɗaya aka tara a can saboda yawansu. Mutumin nan ya shiga ya ɗebi dukiya iya yadda zai iya ɗauka, ya ɗora a ka, yana riƙe da gatarinsa ya kama hanyar gida, amma fa duk sai da ya tabbata ya rufe duk ƙofofin kogon nan da ya buɗe.

    Yana isa gida matarsa ta tarye shi da murna kamar dai yadda takan yi kullum idan ya je neman abinci ya dawo. Mutumin da gaggawa kuma a cikin murna ya nuna wa matarsa zinare da kuɗi da azurfar da ya samo. Matar kuma a guje ta je ta aro ma’auni a wajen maƙwabta suka auna zinaren.

    Ba da saninsu ba ashe akwai ɗan guntun zinaren ya maƙale a ma’aunin da suka mayar masu. Masu ma’auni suka ajiye, har dare ya yi. Sai ga wani abu ya haske musu ɗaki, suka yi ta mamaki. Da gari ya waye suka shiga bincike, suka gano ashe zinare ne a jikin ma’auni da maƙwabta suka ara da maraice.

    Daga nan suka aiki ɗayansu ya je ya tambayi mutumin inda ya samo zinariya. Ya dai matsawa mutumin sai ya nuna masa inda ya samo domin shi ma ya je ya ɗebo. A kan tilas mutumin nan ya tasa ƙeyarsa suka tafi. Da suka isa, sai mutumin ya gaya wa maƙwabcinsa abinda ake cewa ƙofofin kogon dutsen nan su buɗe.

    Daga nan fa sai ya tafi gida abinsa. Maƙwabci ya faɗi abin da mutumin ya gaya masa, sai nan da nan ƙofofin suka buɗe. Sai ga dukiya, kamar ta fi wadda mutumin farko ya fara gani jiya. Maƙwabci ya lafci dukiya iyakar son ransa, to amma da ya zo fita sai ya rikice, ya rasa abinda zai faɗa ƙofar kogo ta buɗe.

    Jim kaɗan sai mutanen nan goma sha biyu suka dawo daga inda suka je. Suka shiga kogon, sai kawai suka tarar da maƙwabci. Ganin ya kwashi dukiya ba tare da izininsu ba, sai suka kama shi suka yanka, suka ajiye gawarsa a gefe. Washe-gari da mutumin ya ji ana cewa maƙwabcinsa bai dawo gida ba, sai ya koma dajin nan, ya jira sai da mutanen nan suka fito suka tafi, ya je ya buɗe kogo, ya shiga.

    Da shigarsa sai ya tarar da gawar maƙwabcinsa a gefe, mutanen nan sun yanka ta gunduwa-gunduwa. Ya tattara gaɓobin, ya zuba a mangala, ya kama hanyar gida. Sai ya ɗebi zinariya, ya je wurin shugaban dogarai ya ce da shi ɓarayi sun tare su, har suka kashe mishi ɗan’uwa, saboda haka ya ce masa: “Don Allah ga ladan zinariya nan ka sake haɗe min shi, domin a rufe shi a haɗe.”

    Sarkin Dogarai ya haɗa mutum, amma tun kafin a ɗauke shi a tafi da shi wurin binnewa ra, sai mutanen kogo suka je gidan Mai Gari suka ce wani mutum ya sayi saniyarsu bai biya ba, amma ya mutu an kawo gawarsa gidan Sarkin Dogarai. Sarki ya bincika aka tabbatar da haka; aka kawo gawar, suka ce a ba su.

    To, dama suna so a ba su gawar ne domin su cinye, Sarki ya hana. Yasa Sarkin Dogarai ya ba mutumin nan gawar maƙwabcinsa, aka binne ta bisa al’adar garinsu. Mutanen kogo suka haƙura, shi kuwa matalaucin nan da ya sami dukiya a dare ɗaya, ya yi ta cin
    duniyarsa shi da matarsa. Amma kuma duk sanda ya ga matalauta yakan taimake su da kuɗi da abinci da jari domin su yi sana’a. Sai mutan ƙauyen suka sa masa suna Mai sa’a. Kurunkus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mahaƙurci mawadaci.
    • Wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa.
    • Kuɗi masu gidan rana.
    • Duk wanda ya haƙura da kaɗan Allah zai wadata shi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Jika Da Kaka

    Edita@rumasau-kallamu