Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Sarki Kunkuru, wanda matarsa ta haifi ɗa namiji. Sai ya tara Kunkurayen garin ya sanar da su cewa matarsa ta haifi ɗa. Ya bayyana cewa duk wanda ya san sunan yaron, zai ba shi ’yarsa aure. Sai wani Kunkurun ya je bakin rafi ya ɓuya. Lokacin da ’yar Sarki da ƙawayenta da kuyangi suka je ɗaukar ruwa, sai Kunkurun ya faɗa cikin tukunya ɗaya daga cikin kuyangin, ya ɓuya.
Bayan ’yar Sarki da jama’arta sun koma gida, kuma wadda ya shiga tukunyarta ta ajiye ruwan, sai Kunkurun nan ya fito, ya ɓuya a bayan ƙyauren ɗakin Sarki. Da Sarki ya shiga gida, sai ya kira matarsa mai jegon jaririn nan da aka haifa, ya ce: “Kin ba Kuturin nono ya sha?”
Kunkurun da ke maƙe yana jin su, kuma ya ji sunan yaron Kuturin. Sai uwar ta ce da Sarki: “A a, ina dai shirin ba shi yanzu.”Can da Kunkurun da ke bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya ji ƙafa ta ɗauke, sai ya fito, ya gudu. Washe-gari sai Sarki ya tara Kunkuraye, ya tambaye su ko akwai wani da ya san sunan jaririn gidansa.
Duk wurin aka mutu a ka, ba wanda ya yi magana, sai Kunkurun nan da ya yi dabararl aɓewa a bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya nuna alamar yana da magana. Sai Sarki ya ba shi dama, ya tambaye shi sunan yaron. Nan take kuwa Kunkurun nan ya ce: “Ai sunansa Kuturin.” Sai Sarki ya ce: “Haka ne kuwa, ba shakka.”
Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sarki ya cika alkawari, watau aka ɗaura wa ’yarsa aure da wannan talakan Kunkuru da ya faɗi sunan jaririn gidansa daidai. To, amma kuma yarinyar ba ta son Kunkurun da aka ba ta, amma kuma ba ta nuna masa ba. Wata rana ’yar Sarki da mijinta suna hira, sai ya yi suɓur-da- baka ya gaya mata dabarar da ya yi har ta kai ya aure ta.
Bayanin da ya yi mata ya ɓata mata rai, domin da ma ba ta son sa. Amma fa ba ta nuna masa tana cikin ɓacin rai ba. Washe-gari sai tace da mijinta tana son zuwa ganin gida. Sai mijinta Kunkuru ya amince, amma ya ce kar ta daɗe ta dawo da wuri. Da ta isa gida, sai ta gayawa mahaifinta yadda mijinta ya yi har ya ji sunan ƙanenta, wanda kuma a sakamakon haka ya aura masa ita.
Da Sarki ya ji bayaninta, sai ya ce mata ta koma gidan mijinta, ya san abin da zai yi. Sai ta koma. Wata rana sai Sarki ya tara duk Kunkurayen da ke fadamu da yake iko da ita, ya ce musu ya yi baƙo, kuma duk wanda ya gaya masa sunan baƙon, to zai ba shi rabin garinsa. Bayan Sarki ya gama jawabi, jama’arsa duk sun koma gida, sai ya umarci dogarai da su shiga fakon duk wanda zai zo ya shiga gidansa, su kama shi.
Da dare ya yi, sai ga Kunkuru surukin Sarki ya doshi ƙofar shiga gidan Sarki, yana sanɗa. Bai san ana ganin sa ba. Yana shiga zauren farko, sai ko dogaran Sarki suka yi wuf suka cafke shi, suka ɗaure.Da gari ya waye, sai aka kai shi gaban Sarki. Nan da nan labari ya bazu, duk gari aka shiga mamakinsa da jin haushinsa.
Daga bisani Sarki ya sa aka yanke masa hannaye da ƙafafu, aka kai shi bayan gari aka jefar. Yana cikin halin azabar ciwo a daji, sai Ƙadangare ya zo wucewa. Da Kunkurun nan ya gan shi sai ya kira shi, ya roƙe shi ya ba shi aron ƙafafuwansa, domin ya je kasuwa. Sai Kadangare ya girgiza kai, ya ce: “A a, ba zan iya ba ka aron ƙafafuwana ba.”
Can kuma Maciji ya zo wucewa, sai Kunkurun nan ya ce da shi: “Maciji, maciji ɗan’uwa, ka ba ni aron ƙafarka mana in je kasuwa, idan na dawo in ba ka kayanka.” Sai Maciji ya yarda ya ba shi, ya ce masa amma fa ya dawo da wuri. Kunkuru ya sa ƙafafuwa ya kama hanya, amma fa bai dawo da wuri ba kamar yadda ya yi wa Maciji alƙawari.
To a kan haka shi ya sa duk sanda yake cikin tafiya, da ya ji motsi sai ya yi sauri ya maƙe ƙafafuwansa da hannayensa, saboda yana zato Maciji ne ya biyo sawun ƙafafunsa. Wannan rashin dawo masa da ƙafafun da Kunkuru ya ara ne ya sa kowa yanzu yake ganin Maciji yana jan ciki ba ƙafafu. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Karya fure take ba ta ’ya’ya.
- Kayan aro ba ya rufe katara.
- Mayaudari ƙarshensa asara da nadama da jin kunya.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare
Edita@rumasau-kallamu









