Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani ƙauye wai shi Wake-Wake, kusa da Dajin Aljanu, inda aka yi wata mata mai ’ya’ya biyu, mace da namiji. Wata rana sai mahara suka kai wa ƙauyen Wake-Wake hari. Maharan kuma suna da yawan gaske kuma sun fi zaratan Wake-Wake yawa da tarin makamai.
Faɗa ya ƙaure, aka yi musu kaca-kaca, ko’ina sai gawarwakin mutanen Wake-Wake ake gani a yashe. Mata da tsofaffi da ƙananan yara suka ruɗe, hankalinsu ya tashi, gigita ta yawaita. Da uwar yaran nan ta ga maharan sun hallaka jama’ar garin masu yawa, sai ta suri ’yarta domin ta kare ta daga ’yan harin.
Da namijin ya ga haka sai ya ce: “Iya ni ba za ki kare ni ba? Ni ne fa idan na girma zan kula da gonarki, in gina miki gida kuma in tara miki shanu da sauran dukiya.” Sai uwar ta saki ’yar, ta ɗauki namijin. Da budurwar ta ga haka sai ta ce: “Haba Iya, ki kula da ni domin ni ce mai yi miki wanke-wanke da ɗaukar ruwa da shara, in taya ki girki da dai sauran ayyukan gida.
Idan ba ki kula da ni ba, mahara suka kashe ni, wa zai taimake ki?” Da mahaifiyarta ta ji haka, sai ta ajiye namijin, ta ɗauki yarinyar suka ɓuya inda mahara ba za su gan su ba. Da namijin ya ga haka, sai ya shige cikin ganyen kabewar da ta yi yaɗo, ya ɓuya, ko motsi ba ya yi.
Numfashinsa ma ba ya ɗaga cikinsa domin gudun kada a ga alamun mai rai a mafakarsa. Can sai ga maharan sun zo wucewa ta kusa da inda ya ɓuya, sai ɗaya daga cikinsu ya ce da sauran: “Kai baraden fama mu duba cikin ciyawar nan, na ji ƙanshin mutum.”Sai Jarmai, watau jagoransu ya ce: “Kai dai wawa ne, yaya mutum zai ɓuya a nan?
Mu yi gaba mazajen fama.” Sai maganar Jarmai ta janye hankalinsu, ba su duba ba. Yaro dai ya haye hatsarin shan kaifin barandamin barade. Da yaron nan ya tabbatar maharan sun tafi, sai ya fita daga maɓoyarsa. Yana cikin tafiya sai ya ga bishiyar Buwaila. Sai ya faɗa ta da sara.
Da sara ya fara ratsa bishiya sai ta ce: “Kai yaro, me za ka yi da ni ne idan ka sare ni?” Ko tsorata bai yi ba, sai ya ce: “Zan ci ne idan na sara, yunwa da ƙishirwa sun dameni.” Da bishiya ta ji haka, sai tausayi ya kama ta ta ce: “Zaga ta hannun dama za ka ga tukwane biyar, ɗaya ta abinci, ɗaya ta ruwan sha, ɗaya ta ruwan wanka, ɗaya ta wurin bayan gida, ɗayar kuma ta wurin barci.”
Murna ta kama yaro ya ce da bishiya: “To, na gode.” Bayan ya ci ya ƙoshi, ya sha ruwa, ya yi wanka, sai ya zauna ya huta. Bishiya dai ta yaba da hankalinsa har dai suka saba. Yau da gobe dai har mutanen gari suka gane dangantakar yaro da bishiyar, sai suka yi masa laƙabi da Ɗan Buwaila.
Ana nan, ana nan, sai wata rana bishiyar ta ce da Ɗan Buwaila: “Ya kamata ka mallaki dukiyar kanka saboda halin yau da gobe.” Sai ya ce: “Gaskiyarki, duk abin da kika yi mini na gode.” Can sai wata saniya da ke kiwo ta biyo ta kusa da bishiyar, sai bishiyar ta ce da Ɗan Buwaila, “Bugi cikin saniyar nan ka ga abin mamaki.”
Da ya bugi cikin saniya sai ga shanu masu yawan da ba zai misaltu ba, garke-garke suna tuɗadowa, sai ta ce: “Duk waɗannan shanu fa naka ne.” Bayan wani lokaci, wasu mutanen garin su Ɗan Buwaila suka fara zunɗe suna cewa: “Ta yaya wannan yaro zai fi Sarki dukiya?” Wasu daga cikinsu suka ce: “A sare bishiyar kowa ma ya huta.”
Kamar da wasa, sai aka yi gayya, aka sare bishiyar. Ɗan Buwaila ya zamanto maraya ba inda zai je neman shawara. A nan ne fa ya kama kuka. Can sai wata jijiyar bishiyar ta ce da shi: “Daina kuka Ɗan Buwaila, ɗauke ni ka ɗasa.” Da ya ɗasa jijiyar sai ko bishiyar Buwaila ta tsiro ta girma, wanda bai sani ba ma ba zai ce an taɓa sare wata bishiya a wurin ba.
Da mutanen garin suka ga haka, sai suka sare wannan sabuwar bishiyar, suka shiga gari da ita. Sai wani ɓangore na jikin bishiyar ya ƙubuta ya je ya sami Ɗan Buwaila ya ce da shi: “Yanzu dai mutanen garin nan sun gama da ni, gara ka bar garin nan, in ba haka ba kuwa za su kashe ka.”
Sai Ɗan Buwaila ya ce: “To.” Sai ɓangorin bishiyar ya ce da shi: “Ka ɗauki wannan ɓangori nawa ka tafi da shi duk inda za ka, kuma ka tafi da shanunka sun ishe ka zaman duniya. Kuma ka buga wannan ɓangorin a tsakiyar shanun, za su cure su zama ɗaya. Idan ka je garin da za ka zauna sai ka bugi saniyar da ɓangorin yawansu zai komo.”
Shi ke nan, Ɗan Buwaila ya shiga tsakiyar shanu ya yi abin da ɓangorin bishiyar ya umarce shi sai shanun suka ɓata, sai saniya ɗaya tak, ya kama hanya. Yana cikin tafiya da saniyarsa ɗaya, har ya kai wani gari ya yi tambaya, aka nuna masa gidan Sarki, ya kuma isa ya yi gaisuwa a fada, sai ya sanar da Sarki buƙatarsa ta neman izinin zama a garinsa.
Sarki ya yi murna, ya ce da shi: “Ai mu haka muke so jama’armu ta ƙaru.” Ya sa aka gina wa Dan Buwaila gida. Bayan ’yan kwanaki Ɗan Buwaila ya zama ɗan gari, sai ya bugi saniyar da ɓangoren bishiyar nan, sai yawan shanunsa ya komo. Nan da nan kuwa ’yan tsegumi suka ce da Sarki: “Bai dace a ce wani a garin nan ya fi ka dukiya ba.”
Hassada da sara da suka da haɗa rigingimu dai suka yi yawa, har ta kai fadawa suka ba Sarki shawarar cewa: “Lallai Sarki ka yi wani abu don a ƙure ƙaryar yaron nan domin ya bar garin nan.” Sai Sarki ya yarda, amma fa ba domin ransa yana so ba. Sai ya ba da irin ƙwarya ya ce: “Ku ba shi a ce ya shuka yau kuma ta fito ta girma, ta yi ’ya’ya, ya fafai, a kawo mini duka a yau.”
Da Ɗan Buwaila ya gaya wa ɓangorin bishiyar Buwaila sai ya ce da shi: “Ba komai, totse ni a ƙasa.” Da ya totse shi, sai ya ga idanu da baki sun fito masa, sai ya ce: “Idan ka je gaban Sarki ka tambaye shi wai ban da shi akwai wani Sarki a garin nan ne? Idan an ce babu, sai ka ce, to saboda me za a ce a kai wa Sarki mai daraja ruwa a cikin ƙwarya mai ɗaci?”
Ɗan Buwaila ya je fada, a gaban Sarki ya yi yadda ɓangorin ya gaya masa. Sai Sarki ya ce: “Kana da gaskiya, yi tafiyarka.” Amma duk da haka masu suka ba su daina ba.Sai wasu kuma suka zuga Sarki wai a kai wa Ɗan Buwaila rago a ce ya sa shi ya haihu. Idan ya kasa, an ƙure shi ke nan, daga nan sai a kore shi daga garin.
Sai Ɗan Buwaila ya gaya wa ɓangorin bishiyar; sai ya ce masa: “Ka je fada gaban Sarki kana kuka. Idan ya ce me ya sa kake kuka, ka ce masa an aiko maka cewa babanka yana naƙuda zai haihu. Idan suka ce ba su taɓa jin namiji da haihuwa ba, sai ka ce da su: ‘Ashe kun san ragon nan ma ba zai haihu ba ke nan.”
Da safe ya ja rago har ƙofar fada ya ɗaure shi, ya shiga sai gaban Sarki, ya faɗi ya yi gaisuwa, yana kuka. Da Sarki ya ga hawaye a fuskarsa, sai ya ce: “Lafiya Ɗan Buwaila?” Sai ya ce da Sarki: “Ka daɗe mai duniya, adali, an aiko mini ne cewa mahaifina yana can yana naƙuda zai haihu.”
Da fadawa suka ji haka, musamman ma masu yi masa hassada a gaban Sarki sai suka ce: “Ƙarya yake yi, yaya namiji zai yi naƙuda? Ai maza ba sa haihuwa.” Sarki dai bai ce komai ba, amma sai Ɗan Buwaila ya yi farat ya dubi Sarki yace: “To, Mai martaba sun ce maza ba sa haihuwa, amma an aiko mini rago an ce lallai in sa shi ya haihu.
Ta yaya zan sa rago ya haihu?” Da Sarki ya ji haka sai ransa ya ɓaci, domin fadawansa sun sa ya yi kuskure. Sai Sarkin ya ce: “To, idan haka ne kuwa ina so wane da wane daga cikin fadawana su bar mini ƙasata. Suna nema su haɗa ni rigima da jama’a.” Nan take aka yi waje da su aka kai su can iyaka da ƙasar Wake-Wake.
Kan tilas suka bi hanyar shiga Dajin Aljanu da ke kusa da Wake-Wake. Bayan kamar wata biyar da yin haka, sai Ɗan Buwaila ya nemi yardar Sarki domin ya je Wake-Wake ya zo da mahaifiyarsa da ’yar’uwarsa, su zauna tare. Sai Sarki ya ce da shi: “An ba ka izinin, idan ka dawo kuma zan aura maka ɗaya daga cikin ’ya’yana.”
Sai ya yi godiya, ya koma gidansa, ya shirya, ya kama hanyar garinsu Wake-Wake. Ɗan Buwaila ya je ya kawo mahaifiyarsa da ’yar’uwarsa, Sarki kuma ya cika alƙawarin da ya yi masa na aurar masa da ’yarsa, suka zauna cikin farin ciki da jin daɗi, domin ya zama surukin Sarki, babu wani algungumi da zai sake sukar sa a gare shi. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Haƙƙin iyaye ne su kula da ’ya’yansu maza ne ko mata.
- Hassada ga mai rabo taki.
- Mahaƙurci mawadaci.
- Nuna jarunta da gwagwarmaya don neman kyakkyawar makoma.
- Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.
- Mai arziki ko a ƙwara ya sayar da ruwa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Darajar Neman Sani
Edita@rumasau-kallamu










