Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wasu mata su biyu, Bushiya da Komayya. Suna da’ya’ya samari su biyu. Ɗaya sunansa Ɗanbushiya, ɗayan kuma Ɗankomayya. Yaran nan sun yi kama da juna sosai, kuma sun shaƙu da juna. Komai iri ɗaya ake yi musu, kamar tufafi da sauran abubuwa makamantansu.
Kwanci tashi, rannan sai ciwo ya kama Bushiya. Jikinta kuma ya ba ta cewa ciwon nan na ajali ne. Saboda haka, sai tace da Komayya ta kula da Ɗanbushiya idan ta rasu. Sai Komayya tace da ita: “Haba, ai abin da aka yi kina nan, shi ne za a yi ko a bayan ranki.” Bayan kamar kwana biyu da yin wannan magana, sai Bushiya ta ce ga garinku nan.
Kamar da man abin da Komayya ke jira kenan, sai kawai ta shiga matsa wa Ɗanbushiya lamba, sai kace daga sama ya faɗo. Wannan tsangwamar da Komayya ke nunawa Ɗanbushiya tana damun Ɗankomayya. Kullum idan ta zo ba su abinci, sai ta nuna son kai, amma kuma Ɗankomayya sai yaƙi ci idan ba tare da Ɗanbushiya ba ne.
Ta rasa yadda za ta yi ta sami galaba a kan Ɗanbushiya. Wata rana Ɗankomayya ya fita, Ɗanbushiya kuma yana gida, sai ta kira wani wanzami da zai wuce ta ce ya yi wa Ɗanbushiya shasshawa a fuska. Wanzami ya kama Ɗanbushiya ya yi masa tsaga, ya tafi. Can kuma Ɗankomayya ya dawo, ya ga an yi wa Ɗanbushiya tsaga.
Sai ya dube shi ya ce: “Wa ya yi maka tsaga?” Ɗanbushiya ya ce: “Iya ce.” Washe-gari da safe Ɗankomayya ya ce Ɗanbushiya ya raka shi kasuwa. Sai ya raka shi. Shi ma ya nemi wanzami, ya ba shi lada, aka yi masa tsage irin na Ɗanbushiya. Suka koma gida. Da Komayya ta ga ɗanta da shasshawa, sai ta kama Ɗanbushiya da duka, ta ce shi ne ya yi wa ɗanta.
Da ta gaji da bugunsa, sai ta rabu da shi. Washe-gari, sai ta aiki ɗanta wata unguwa nesa da garinsu. Kafin ya dawo, sai ta ja Ɗanbushiya zuwa gindin wata kuka, da ke da rijiya a gindinta, ta sa shi ya hau ya tsunko mata ganyen kuka. Ya hau, ya fara sauke kuka, amma sai ta rinƙa cewa ba ta son irin kukar da yake sarowa, tana nuna masa rassan da ke saman rijiyar nan, wai irinsu zai saro.
Yana bin kukar da take nuna masa har ya ƙure reshen kukar, ya suɓuto daga sama, ya faɗa rijiya. Bayan raunukan da ya ji, ya kuma karye a ƙafafuwansa biyu. Da ta ga halin da ya shiga, sai ta ce: “Ai gara haka. Ina ma mutuwa ka yi kowa ya huta.” Tana gama wannan magana sai ta bar wurin, ta tafi gida.
Da ɗanta ya dawo, sai ya nemi ganin abokinsa, Ɗanbushiya. Uwar ta ce masa ya fita yawo. Ɗankomayya ko ya ƙi cin abinci, yana jira sai Ɗanbushiya ya dawo su ci tare. Da ya ga jinkirin ya yi yawa, sai ya fita nemansa, yana tafiya, yana rera wannan waƙa:
“Amale, amale Raƙumin dawa,
A nan gari na duniya,
Ina kake ne, Ɗanbushiya?”
Sai ya ji shiru. Ya ci gaba da zagaya gari yana waƙa, amma shiru. Can da ya bi ta bayan gidansu, sai ya ji an karɓa masa waƙar: “Ga ni a nan Ɗankomayya, Ga ƙafafuna sun rugurguje, Ga bakina ya murguɗe, Ga ni babu idon ganin gari.” Da ya ji Ɗanbushiya ya mayar masa da waƙa, sai ya je bakin rijiyar.
Da ya leƙa ya ga ɗan’uwansa a cikin rijiyar nan, sai ya shiga, ya fito da shi. Ya kai shi, maɗora suka ɗora shi. Ya yi jinya, ya warke sarai. Da Komayya ta ga ya warke, sai ta ce su koma gida. Jin haka Ɗankomayya ya yi ƙeme-me ya ce shi kam ba zai je gidan ba. Shi da Ɗanbushiya suka yanke shawarar shiga daji, suka zaɓi wuri, suka gyara, suka gina ɗakuna, sai suka yi zamansu a can.
Sannu a hankali, mutane suka rinƙa zuwa, har dai wurin nasu ya zama babban gari. Yau da gobe, suka yi arziki. Sai Ɗankomayya ya shawarci Ɗanbushiya cewa ya kamata shi ya zama Sarki, shi kumaya yi masa Waziri. Haka kuwa aka yi. Aka kafa masarauta har sai
da gawurtarsu ta kai, ba mai ganin su sai in sun ba da izini.
Ana nan, kwanci-tashi, sai wata rana wata mace ta je wurin Komayya ta ba ta labarin garin nan da irin arzikin da Sarki da Waziri suka mallaka. Ta ce mata kuma sunan garin Bushiya da Komayya. Sai jikin Komayya ya ba ta ko Ɗanbushiya da Ɗankomayya ne, saboda haka sai ta sha alwashin sai ta je garin, ta gano wa idanunta abin da ke can.
Ta shirya, ta bi fatake ranar kasuwar garin. Ba ta tsaya ko’ina ba sai a ƙofar fada. Ta ce ta zo gai da Sarki. Dogarawa suka yi mata iso. Ta shiga cikin mazaunin Sarki da ke tsakiyar fadarsu. Sarki Ɗanbushiya ya tarye ta da fara’a da girmamawa, to amma sai
Wazirinsa Ɗankomayya ya ce da dogarawa: “Me ake yi da maƙiyi?”
Dogarawa suka ce: “Kisa ko ɗauri.” Sai Ɗankomayya ya ce a fita da ita a aika ta lahira, domin ƙila ta zo ne ta aika da su can. Gara kuwa ya gama da ita kafin ta ƙara yi musu illa. Har yau ɗin nan, ba wanda ya san wannan mata da Waziri ya sa aka kashe. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Rama cuta ga macuci ibada ce.
- Maciyin amana ƙarshensa halaka.
- Ginin da Allah ya yi ba wanda ya isa ya rusa shi.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Maibaiwa Da Dodanniya
Edita@rumasau-kallamu










