Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wata yarinya mai hankali da tsananin biyayya ga iyayenta; ba ta saɓa wa umarninsu. Wannan biyayya da take yi waiyayenta, ta sa ƙawayenta na kishi da jin haushinta. Ana nan, sun rasa yadda za su yi da ita, sai wata rana aka tura su saran itace dajin da ke bayan garinsu.
Da ƙawayen nan suka ga suna cikin daji tare da ita, sai suka tali ɓawon kargo suka ɗaure ta da shi, suka tafi suka bar ta a ɗaure a daji. Can da almuru, sai ga Zaki zai wuce. Yarinyar nan da ta ga Zaki sai ta ce: “Yaya Zaki, idan ka dawo daga farautar da za ka ka, ka biyo ta nan ka kwance ni.”
Zaki ya dube ta, idanunsa da alamun tausayi, ya ce: “To, sai na dawo ɗin.” Da Giwa ta zo wucewa, ita ma suka yi haka da ita. Haka dai ta yi da duk namun dajin da ke wucewa. Dukkansu baki ɗaya, in ban da Kura, ba wanda bai ce zai kwance yarinyar ba idan ya dawo daga farauta ko kiwo.
Da yarinyar ta ce da Kura in ta dawo ta kwance ta, sai Kura ta ce: “Ni kam, cinye ki zan yi.” A nan take Kura ta cinye yarinyar nan ta koma gida. Da Zaki ya dawo daga farautarsa, bai ga yarinya ba; Giwa ma haka. Rashin ganin yarinya ya sa Zaki ya yi tunga a daidai da inda ya bar ta kuma ya rinƙa tsayar da duk dabbar da ta dawo daga farauta ko kiwo.
Wuri ya cika da dabbobin daji, amma ba a ga Kura ba. Sai aka tambayi Zaki ko a kira Kura ne? Jin haka Zaki ya ce: “To, wane ne zai je?” Kurege ya yi farat ya ce: “Manyan Dawa, ni zan je.” Zaki ya amince. Kurege na isa ƙofar ramin Kura ya ce da ita:
“Yau an samo babban nama za a raba, amma Zaki ya ce ba za a raba naman ba sai kina nan.
Shi ya sa ya ce in zo in kira ki.” Kura tana ɗoki ta ce: “Mu tafi, Kurege.” Suka kama hanya, har suka isa. A fusace Zaki ya tambaye ta: “Ke Kura, ina yarinyar da take nan?” A tsorace Kura ta ce: “Ai ni yau sam ban zo wurin nan ba.” Nan take Zaki ya umarci kowacce dabba ta tsallaka wani rami. Nan da nan suka fara.
Duk dabbar da ta je tsallaka ramin sai ta ce: “Ga abin da na ci, daga ɗan tsuntsu sai ciyawa, sai kayan ciki, sai hanji, hak!” Duk dabbar da ta faɗi haka, idan ba ta yi ƙarya ba, sai ta tsallake ramin nan lafiya. Sannu a hankali abu ya zo kan Kura. Ba ta faɗi yadda sauran suka faɗa ba. Sai ta ce: “Kun ga abinda na ci, hak! daga abin ciki sai hanji.”
Tun kafin ta gama rufe baki, da tace, “Hak!” sai ga yarinya ta faɗo. Nan take sauran dabbobin suka kama Kura da bugu. Kafin yarinyar nan ta gama farfaɗowa saboda wuyar da ta sha a cikin Kura, tuni an kashe Kura. Sauran dabbobin nan suka yi wa yarinya goma ta arziki.
Zaki ya sa aka raka ta har garinsu da dukiya mai tarin yawa. Yanzu haka mutanen ƙauyen suna ta tururuwa gidan mahaifan yarinyar, suna taya ta murna. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Na gari na kowa, mugu sai mai shi.
- Hasada ga mai rabo taki ce.
- Mai aikata alheri zai ga kyakkyawan sakamako.
- Mai aikata sharri zai ga mummunan sakamako.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗanbushiya Da Ɗankomayya
Edita@rumasau-kallamu










