Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru

    Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata kaza da ta ce za ta yi aure, sai zakaru suka yi ta zuwa neman aurenta. Duk zakaran da ya zo, sai Kaza ta ce ba ta son sa. Wani tace ya yi gajarta; wani ta ce ba shi da gashi; wani ta ce bai iya cara ba. Wani kuma idan ta raina shi, sai ta ce ba shi da sirdi, ko kuma ya yi tsawo, ko ba shi da kyaun fuska.

    Haka dai ta rinƙa korar su. Sai wata rana Muzuru ya sami labarin halin Kaza, da kuma buƙatar iyayenta na su aurar da ita. Shi ke nan, sai Muzuru ya yi shigar manyan mutane, watau ya sanya babbar riga da hula, ya kuma kawo rawani ya naɗa. Bai tsaya ko’ina ba sai gidan su Kaza. Ya kira Kaza, ta fito tana wani yauƙi.

    Da ta gan shi da shiga irin ta kamala, sai ta sanar da iyayenta cewa yanzu ta sami mijin aure. Iyayenta suka yi ƙoƙarin hana ta, amma ba ta ji maganarsu ba. Daga ƙarshe dai aka ɗaura musu aure da Muzuru. Ranar da za a kai amarya gidan mijinta, sai abokan Muzuru suka rinƙa yin wata waƙa suna cewa:

    “Kaka ga abinci ya shigo mai daɗi, Kayau-kayau.”

    Shi kuma ango yana cewa: “Ku kawo mini abincin nan in ci, In yi maganin kwaɗayi.” Sai Muzuru ya ɗauki allo, wai zai yi karatu, amma sai ya rinƙa cewa: “In jingina allona, In ci Kaza.” Da kowa ya watse, sai ko Muzuru ya cabke Kaza. Tun tana kuka, Kwayat!, Kwayat!!, har aka ji shiru ya gama murɗe wuyanta, ta mutu. Saboda tun fari ba ta ji maganar mahaifanta ba, ba wanda ya yi ƙoƙarin ceton ta daga damƙar da mijinta ya yi mata. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Girman kai rawanin tsiya.
    • Kowa ya ɗebo da zafi, bakinsa.
    • Mai rabon shan duka, ba ya jin kwaɓa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can ƙasar Turu, an yi wani mutum mai ’ya’ya mata biyu. Allah ya yi su kyawawa. Ga haske, in ka gan su kamar taurari. Ɗaya daga cikin ’yammatan ba ta fita ko da ƙofar gida. Amma ɗayar takan zauna a ƙofar gida, kuma duk wani saurayi da ya zo, sai ta ce za ta kira masa ’yar’ uwarta.

    Ana nan, ana nan, sai wata rana wani dodo ya rikiɗa ya koma saurayi, ya je gidansu. Sai ya tarar da yarinyar nan da kan zauna a ƙofar gida, ya yi mata sannu; ita kuma ta mayar masa. Sai ya ce: “Kai amma yarinyar nan na yaba da kyaunki.” Sai ita ko ta ce masa: “Ai da ka ga ’yar’uwata da ba za ka yi mini magana ba, balle ma ka ce ina da kyau.”

    Dodo ya sami gangara, sai ya ce: “To, ko za ki kira mini ita?” Sai yarinyar ta shiga ta yi wa ’yar uwarta magana. Ita kuma ta tambaye ta: “Da wa ya yi kama?” Sai ta ce: “Ya yi kama da mahaifiyarmu.” Da ta ji haka sai ta ce: “A a, ai babu wani saurayi da ya isa ya gwada kansa da mahaifiyata. Ba zan je ba.”

    Daga nan mai zama a bakin ƙofa ta je ta ba mutumin haƙuri. Ba tare da ya nuna fushi ba, ya kama hanya ya yi tafiyarsa. Amma saboda nacinsa, kullum sai ya je gidan, yana ƙoƙarin ganin yarinyar. Sannu a hankali har yarinyar nan mai tsayawa a waje ta gayawa mahaifinsu halin da mutumin nan yake ciki na tsananin ƙaunar da yake yi wa ‘yaruwarta.

    Da mahaifinsu ya ji bayaninta, sai yace: “Duk sanda ya zo ki shigo ki gaya mini. Can kuwa sai ga mutumin. Nan da nan ta yi masa bayani cewa: “ka jira in yi wa sanar da mahaifinmu cewa ka iso. Mahaifin yaran ya fito, suka gaisa da baƙon, ya kuma sanar da shi cewa yana so ne ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, wato wadda take cikin gida.

    Sai baban yaran yace masa ya jira yana zuwa. Ya shiga gida. Da shigarsa, sai ya ɗauki yarinya ya sa ta a cikin rumbu. Sai ya kira mutumin yace: Ga wannan rumbu ka kai wa kakannin yarinyar a garinsu. mutumin nan ya ɗauki rumbu, ya kama hanya. Yana cikin tafiya sai ya yi tun tuntuɓe ya faɗi; yarinyar da ke cikin rumbun ma ta faɗo.

    Da yarinyar ta ga mutumin sai tace: “sannu kawu” Sai mutumin ya ce: “Ashe ke ce a ciki?” Da ta lura a daji suke, sai ta gudu ta tasamma gida. Washe-gari sai mutumin ya koma gidansu yarinyar, ya tambayi labarinta, to amma kafin ya je, mahaifinta ya tambaye ta abin da ya farutsakaninta da mutumin, ta kuma gaya masa yadda mutumin ya yi tuntuɓe ya faɗi, da yadda ta yi masa sannu bayan ta faɗo daga rumbu.

    Da mahaifinta ya ji haka sai ya ce: “Ai ko nai kamata ki yi masa sannu ba da ya faɗi. “Sai ya sake sa ta a cikin rumbu, ya sake ɗora wa mutumin. Mutumin ya kama hanya, sai ya sake yin tuntuɓe a cikin daji, ya faɗi. Yarinya ta mance da abin da mahaifinta ya gaya mata, sai ta yi masa sannu.

    Shi kuwa ya kama ta, ya fyaɗa da ƙasa, ya mueɗe mata wuya, nan take ko haurawa ba ta yi ba. Daga nan sai ya ɗauki gawar ya jefa a cikin jakarsa. Ya ajiye jakar a gindin wata bishiya, ya tafi neman itacen da zai yi tsire da gawar, ya gasa. Ashe duk abin da suke yi wata tsohuwa tana ganinsu, sai ta yi sauri ta cire gawar yarinyar ta jidi duwatsu ta zuba masa a cikin jakar, ta gudu da gawar, ba ta tsaya ko ina ba sai gidan mahaifin yarinyar nan.

    Ta kai masa gawar ‘yarsa. Da dodo ya samo itacen, ya ɗauki jakarsa ya je inda zai gasa yarinyar nan ya ci nama, sai ya juye duwatsu a tukunya ya hura wuta, ba tare da ya san duwatsu yake dafawa ba. Can da ya ji dutse ya fashe sai ya ce: “Yawwa wannan ƙwaƙwalwarta ce ta fashe. Sai ya ɗebi fasasshen dutse ya cinye.

    Da tsohuwa ta kai gawar sai ta ce da iyayenta: Ku duba abinda kuka sa aka yi wa ‘yarku.

    Mahaifin yarinyar ya yi wa tsohuwa godiya, suka yi sallama ta tafi. Tsohuwa na tafiya, sai uban ya ƙone gawar yarinyar, ya zuba tokarta a cikin mararaki, ya zuba ruwa, sai ya rataye mararakin nan; sannu a hankali ruwan tokar ya fara ɗigowa daga mararaki. Da ya ɗigo, sai yace: “Wannan hannun Sirandi ne.” Can kuma idan ruwa ya sake ɗiga sai yace: “Wannan kuma ƙafarta ce.”

    Da haka dai, kafin wani lokaci yarinyar nan ta haɗu tsaf ta miƙe. Washe-gari kuma sai Dodon nan ya sake zuwa ƙofar gidansu yarinyar. Da mai zama a ƙofar gida ta gan shi, sai ta shiga gida da gudu ta gaya wa mahaifinta cewa ga fa mutumin nan ya sake zuwa. Sai mai gidan ya fito. Da suka gaisa sai ya tambayi baƙon wa kuma ya zo nema.

    Shi kuwa ya ce ya zo ne yana neman wannan yarinyar da ta gudu ta shiga gida, wai ya aura. Sai mahaifinta ya gaya wa baƙon nan cewa ai yarinyar ta yi miji tuntuni. Sai bai komai ba ya tafi abinsa. Bayan ’yan kwanaki aka ɗaura wa yarinyar aure ta tare. Da mutumin ya sake dawowa sai aka ce masa yarinyar ta bar gidan.

    A nan take sai ya kife. Can cikin dare kuma sai ya rikiɗa, ya je inda yarinyar take ya ce zai kashe ta. Sai yarinyar ta nemi mijinta da ya kuɓutar da ita daga hannun wannan azzalumi. Amma sai mijinta yace ai shi ba ya ganin komai. Washe-gari sai ya je ya sami mahaifin yarinyar nan ya ce masa ya lura dai matarsa tana ganin aljanu, saboda haka ya dawo da ita, ba ya auren, ya sake ta.

    Da uban ya ji haka, sai ya tambaye ta abin da ta gani. Ta gaya masa duk yadda suka yi da Dodo. Sai baban yarinyar ya ba ta wata kyanwa, ya ce: “Idan har mutumin nan ya sake zuwa zan ce masa zan haɗa shi da ke ku je gidansa. Idan har ya rikiɗa ya zama wani abu, sai ki ce masa idan da gaske yake to ya rikiɗa ya koma wani ƙaramin abu, kamar ɓera.

    Idan ya zama ɓera, sai kawai ki cinna masa kyanwar nan ta cinye shi. ”Rannan da mutumin ya dawo, sai uban yarinyar nan yace: “Zan ba ka ɗiyata, amma sai ta je da kai ta ga gidanka.” Sai mutumin ya ce: “Ta fito mu tafi.” Nan da nan yarinya ta naɗe tabarmarta, ta saka kyanwa a ciki yadda ba zai gan ta ba, ta fito suka tafi.

    Suna isa kusa da gidansa, sai ya zama Giwa, sai ya ɗauki yarinyar ya kawo ta kusa da tukunya, amma ba ta tsorata ba, sai yarinyar ta ce: “In da gaske kake kana rikiɗa, to ka rikiɗa ka koma wani abu ƙaramin gani.” Nan da nan ya zama bushiya. Da ta ga haka sai ta yi tsaki ta ce: “Wannan ai ka yi rikiɗar kaya ce kurum. Ina so ka rikiɗa ka zama abin da ba shi da kaya.”

    Yana jin abin da ta faɗa, sai ya rikiɗa ya zama ɓera. Kamar walkiya, sai yarinyar nan ta saki kyanwa. Nan take kuma kyanwa ta kama ɓerar nan ta lanƙwame. Jim kaɗan sai kawai dawaki da jakuna da raƙuma da sauran kayayyakin alatu masu ɗimbin yawa suka bayyana.

    Nan da nan ta kwashe su ta ɗora wa raƙuman nan da shanu da jakuna da ta mallaka, ta zaɓi wata taguwa ta haɗa mata sirdi, ta hau, ta kora sauran dabbobin da ta yi wa laftun dukiya, ba ta tsaya ko’ina ba sai a gidansu. Da babanta ya gan ta da wannan dukiya mai tarin yawa, ga shi ta durƙusa ta gaishe shi, ta kuma yi godiya ga Allah saboda ya raba ta da wannan bala’i, sai ya yi matuƙar murna. Ita da mahaifanta da ’yan’uwanta suka ci gaba da morar wannan dukiyar hankali kwance. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Girman kai rawanin tsiya.
    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango shi ba.
    • Karen bana, maganin zomon bana

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kare Da Kura

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kare Da Kura

    Tatsuniyar Kare Da Kura

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Kare da wata Kura a Dajin Saidawa. Suna ganin juna amma daga nesa, har dai yau da gobe suka saba, sai suka ƙulla abota. Kare yana da ’ya’ya bakwai, Kura kuma tana da’ya’ya biyar. Sai wata rana suka ce za su je daji dakan wake. Sai suka shirya suka fita.

    Suka yi ta tafiya har suka isa wurin dakan wake, suka kama aiki. Can sai Kare ya ce wa Kura: “Gara ki jeki ɗora mana sanwar kalaci. Ina ganin wake da shinkafa ya kamata ki
    dafa. ”Kura na jin haka ta ce: “Gaskiyarka, Kare.” Kura ta je ta kama ’ya’yan Kare, ta zuba su a tukunya, ta ɗora sanwa.

    Daga nan ta koma wurin aiki. Da Kare ya ga ta koma, sai ya tambaye ta: “Kin ɗora sanwa ne?” Kura ta ce masa: “E, na ɗora. Ai yau fa za mu ci daɗi.” Daga nan sai
    Kura ta kama waƙa tana cewa:

    “Mu yi daka da wuri mu tafi,

    ’Ya’yan Kare suna shan wuta,

    Hum tiri hum.”

    Da Kare ya ji abin da take cewa, sai ya ce: “Kura bari inje in duba mana sanwa ko wuta tana ci.” Kura kuma ta ce wa Kare: “Idan ka je kar ka buɗe tukunyar; ka iza wutar kawai ka dawo.” Sai Kare ya ce: “To, na ji.” Kare na isa murhu ya tarar wutar ta mutu; ko zafi ma sanwar ba ta fara yi ba.

    Sai ya buɗe tukunyar domin ya ga abin da Kura take dafa musu. Kare na buɗewa sai ya ga ’ya’yansa suna mutsulniya a cikin ruwa. Bai yi wani ɓata lokaci ba, sai ya fitar da su. Nan da nan ya kamo ’ya’yan Kura ya sa a cikin tukunyar nan, ya nemo guma-guman itace ya haɗa wuta; ya ɗora tukunya a kan murhu.

    Sai ya kai ’ya’yansa ya ɓoye a kan wata bishiya. Da ya koma wurin aiki inda Kura ke jiransa, sai ta tambaye shi: “Ka gyara itacen dai ko?” Ba tare da ya nuna mata abin da ya yi ba, sai kawai ya ce da ita: “E, na gyara, ƙanwar Zaki, surukar Damisa, kanwar Giwa!” A cikin murnar kirarin da Kare ya yi wa Kura da kuma zaton za ta ci naman ’ya’yansa, sai ta ci gaba da rera wannan wakar:

    “Mu yi daka da wuri,

    Kafin rana ta kai tsakiya,

    ’Ya’yan Kare sun sha wuta,

    Sun kusa nuna.

    Hum tiri hum.”

    Sai Kare ya fara tasa waƙar yana cewa:

    “Ka juye nawa ’ya’yan

    Ka bar na an’uwana.”

    Sai Kura ta ce: “Wace irin waƙa ce haka Kare?” Sai Kare ya ce: “Sanda kike yin taki waƙar, na yi magana ne?” Da jin wannan tambaya tasa sai ta yi shiru. Suka ci gaba da gyaran wake, har suka gama. Bayan sun gama aiki, sai Kura ta ce wa Kare: “Je ka ka ɗebo wake da shinkafa daga cikin tukunya mu ci.”

    Sai Kare ya je ya ɗebo musu; ita tana zaton naman ’ya’yan Kare ne. Kura ta ci nama, ci irin na ƙeta da haɗama, har ta rage da nufin za ta kai wa ’ya’yanta. Sai Kare shi ma ya ce zai kai wa ’ya’yansa abin da ya rage. Da ta ji maganar Kare, sai ta fashe da dariya, amma ba ta yi wa Kare bayanin dalilin dariyarta ba.

    Shi kuma bai tambaya ba. Suka tafi, kowa da nufin ya kai wa ’ya’yansa nama. Lokacin da Kura ta isa raminta, sai ta tarar saura ɗanta ɗaya. Sai ta koma da gudu ta tambayi Kare, “Ina ’ya’yana?” Sai Kare ya ce: “Da kika ɗora ’ya’yana a kan wuta za ki dafa, na tambaye ki ne?”

    Sai Kura ta bi Kare da gudu za ta kashe. Da Kare ya ga haka sai ya ce da ’ya’yansa: “Ku miƙo mini igiya.”Suka jeho masa, ya kama, ya haye bishiyar. Da Kura ta kasa hawa bishiyar, sai ta ce wa Kare: “Za mu haɗu da kai.” Sai Kare ya ce: “Gobe ma zan je ɗaukar itace.” Sai Kura ta tafi abinta.

    Washe-gari sai Kare ya ɗauki damin itace. Yana cikin tafiya sai ya hangi Kura tana zuwa. Sai ya shiga cikin itacen, yana mirginawa. Da Kura ta je kusa da itacen sai ta ce:

    “Itace mai mirginawa!

    Itace mai mirginawa!!

    Ba ni hanya, ina neman Kare.”

    Sai itace ya mirgina ya kauce, Kura ta wuce. Da Kura ta yi nisa, sai Kare ya fito ya ɗauki itace ya tafi zarafinsa. Da Kura ta komo sai ta sami Kare a kan bishiya, sai tace: “Kare jiya ka yi mini ƙarya, ka ce min za ka je ɗaukar itace, amma ban gan ka ba.” Sai Kare ya ce: “Jiya ba ki haɗu da wani itace yana murginawa ba?

    ”Kura ta ce: “Na haɗu da shi mana.” Sai Kare ya ce: “A garinku kin taba jin an ga itace yana murginawa shi kaɗai?” Sai Kura ta ce: “To, gobe ina za ka?” Sai Kare ya ce: “Gobe zan je in ɗebo ruwa.” Kura ta tafi, tana tunanin yadda za ta gama da Kare idan gari ya waye. Washe-gari sai Kare ya ɗauki tulunsa, ya je ɗaukar ruwa.

    Sai ya hango Kura ta doshi rafin da yake. Sai ya shiga cikin tulunsa yana murginawa. Da Kura ta je kusa da tulun sai ta ce:

    “Tulu mai mirginawa,

    Tulu mai mirginawa.

    Matsa mini in wuce, Domin ina neman Kare.”

    Sai Tulun ya mirgina, Kura ta wuce. Da Kare ya auna, ya san Kura ta yi nisa, sai ya fito ya ɗauki ruwansa ya tafi. Daga baya kuma Kare da Kura suka haɗu, yana baya-baya da ita. Sai Kura ta ce: “Kare, ka yi min ƙarya.” Shi kuwa sai ya mayar mata da jawabi cewa, “Ba ki haɗu da wani tulu mai mirginawa ba?

    Ai ni ne a cikin tulun.” Kura ta ce ta gamu da shi, ta sake tambayar sa cewa: “To gaya mini inda za ka gobe domin in sami damar gamawa da kai kowa ya huta.” Sai Kare ya harari Kura, ya yi mata kallon raini, ya ce: “Zan je su, watau kamun kifi a gulbin yamma da Dajin Saidawa.”

    Washe-gari Kare da ’ya’yansa suka je su. Can sai suka ga Kura ta tunkari inda suke. Sai Kare ya ce wa ’ya’yansa duk su faɗa ruwa su buɗe haƙoransu. Har shi ma suka faɗa suka buɗe haƙoransu. Kura tana isa a gaɓar gulbi, sai ta ga haƙoran Kare da ’ya’yansa, sai tsoro ya kama ta. Sai ta ce wa ’yarta:

    “Kilatanda! kilatanda!!

    Baya baya ba ta.” Duk ta yi ’yan dube-dubenta ba ta ga Kare ba. Haka Kura ta gaji ta tafi. Da Kare ya ga lallai Kura ta tafi ba ta da nufin komawa bakin gulbi nemansa, sai ya fito da ’ya’yansa. Daga nan suka bar dajin nan domin kada wata rana tsautsayi ya sa Kura ta halaka shi da ’ya’yansa. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • In za ka gina ramin mugunta ka gina gajere, ba ka sani ba ko kai ne za ka faɗa.
    • Rama cuta ga macuci ibada ce.
    • Duk inda ka kai da wayo wani ya fi ka.
    • Cin dare ɗaya kumburin ciki.
    • Wankan wuta sau ɗaya a kan yafa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken: Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

    Maƙala Mai Taken: Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

    Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a Sikelin Manazartan Ƙarni Na 21

     Daga

     Dr. Adamu Rabi’u Bakura

    Department of Languages and Cultures

    Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Email: arbakura62@gmail.com

    Phone: 08064893336

     

    Da

     

    Abu-Ubaida SANI

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    official@amsoshi.com | ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334

    Citation: Bakura, A. R., & Sani, A.-U. (2024, May 3–6). Gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a sikelin manazartan ƙarni na 21. Paper presented at the International Conference on the Life and Songs of Alhaji Sa’idu Faru, Department of Languages and Cultures, Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria.

    Tsakure

    Masana suna la’akari da waɗansu alƙaluma yayin ayyana makaɗan Hausa a ƙarƙashin wani rukuni na musamman daga cikin tarin rukunonin makaɗa da ake da su a farfajiyar adabi da al’adun Hausawa. Waƙoƙin fada na daga cikin shahararrun rukunonin waƙoƙin baka. Wani abin lura shi ne, akan samu makaɗan da ke ƙarƙashin wannan rukuni da suke sauya sheƙa ko su kasance jemagu sakamakon tasirin zamani ko waɗansu dalilai masu alaƙa da tattalin arziki ko waninsa.

    Binciken nan yana da manufar bitar rayuwa da waƙoƙin Alhaji Sa’idu Faru domin ganin ko ya sauya sheƙa ko kuma ya kasance makaɗin sarauta kaifi ɗaya na tsawon zamanin kiɗansa? An yi amfani da dabarun ƙalailaice waƙoƙin makaɗin da kuma yin hira da masana a wannan fanni a matsayin hanyoyin tattara bayanai.

    Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa, Sa’idu Faru ya tabbata makaɗin sarauta na yankan shakku, domin kuwa dukkannin waƙoƙinsa ba su fita daga da’irar sarauta da masarauta ba. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da nuna dacewar tattarawa da kundace waƙoƙin wannan shahararren makaɗi domin gudun salwantar su.

    Fitilun Kalmomi: Kiɗa, Waƙa, Waƙoƙin Fada, Waƙoƙin Sarauta, Makaɗan Fada, Makaɗan Sarauta

    1.0 Gabatarwa

    Allah ya arzurta mawaƙan Hausa da ɗimbin hikima da basira tare da fasahar sarrafa harshen Hausa wajen ƙaga waƙoƙi. Wannan ne ya sa sukan rera waƙoƙin da suka danganci fannonin rayuwar ɗan’adam daban-daban.

    A sakamakon haka ne masana da manazarta adabin Hausa suka karkasa makaɗan zuwa azuzuwa ta la’akari da rukunonin al’ummar da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa. Masana kamar Bello (1982) da Yahaya (1983/85) da Mashi (1986) da Gusau (1996) sun raba mawaƙan zuwa rukuni-rukuni gwargwadon fahimtarsu, ta la’akari da abubuwa kamar haka:

    • Muhallin waƙoƙinsu
    • Kayan kiɗansu
    • Jigogin waƙoƙinsu

    Hasali ma kowane rukunin da makaɗan ke yi wa kiɗa da waƙa akwai kayan kiɗan da suka keɓanta da su wajen sarrafawa a yayin da suke aiwatar da sana’arsu ta waƙa. Bello (1982) da Ibrahim (1985) da Gusau (1996) sun raba mawaƙan Hausa ta la’akari da muhallin waƙoƙinsu, kamar haka:

    • Mawaƙan sarauta/Fada
    • Mawaƙan jama’a
    • Mawaƙan Sana’a
    • Mawaƙan ban dariya
    • Mawaƙan sha’awa

    Wannan aiki ya karkata kan binciko gurbin Makaɗa Sa’idu Faru a cikin makaɗan fada. Makaɗan fada sun shahara wajen luguden kalmomin Hausa ta fuskar salo, raha, ƙaƙale, yabo, zambo, habaici, shaguɓe, zuga da adana tarihi, da sauransu. Sukan sauya falsafar da suka gada kaka da kakanni sakamakon sauyawar zamani da ire-iren sauye-sauyen da ke wanzuwa a tsarin sarauta da raguwar ƙarfin ikon sarakunan ƙasar Hausa.

    Wannan ya sa wasu makaɗan suka zama bigi-sa-bigi-taiki domin neman tara abin duniya. Fahimtar haka ne ya sa wannan muƙalar ta yi azamar ɗora waƙoƙin Ɗan’umma Uban Kiɗi bisa sikelin bin diddigin gano ko makaɗin ya sauya sheƙa sakamakon sauyawar zamani, ko kuwa yana kamilin makaɗan sarauta har ya karɓa kiran Ubangijinsa?

    2.0 Bitar Muhimman Batutuwa

    2.1 Kiɗa

    Kiɗa Bahaushiyar kalma ce wadda Hausawa suke kiran ta kiɗaa. Kalmar tana cikin jerin kalmomi na suna jisin maza. Jam’in kalmar kuwa shi ne kaɗe-kaɗe. A wani karin harshen kuwa sukan ce kiɗe-kiɗe. Kalmar tana ƙunshe da ma’ana kamar haka:

    • Buga ganga ko kalangu da abin bugawa.
    • Bugun ƙwarya ko goge ko garaya da hannu ko da makiɗi ko da wani abu, kamar yadda Kano, (2006 p. 243) ya bayyana.

    Garba, (1990 p. 89) cewa ya yi kiɗa na nufin: “Yin amfani da abubuwa don ta da amo iri daban-daban.” A wata ma’anar kuwa cewa ya yi kiɗa na nufin, “Fasahar tsara amo na muryar mutum ko daga abubuwa ko duka a haɗe.” Yayin da aka dubi waɗannan ma’anonin za a iya cewa, kiɗa yana nufin buga wani abu a kan wani domin samar da wani amon sauti da ka iya jan hakalin mai saurare.

    2.2 Waƙa

    Kalmar waƙa tana cikin jerin kalmomin suna jinsi mace. Jam’inta kuwa waƙoƙi ko waƙe-waƙe. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Magana wadda akan rera da baki, aka tsara bisa wani zubi na musamman” kamar yadda Garba (1990 p. 152) ya nuna. Shi kuwa Kano, (2006 p. 466) ya bayyana ta da ma’anar, “Tsararriyar magana da ake rerawa a kan kari ko rauji.”

    Waƙa a bisa ma’anarta, tana nufin furta abin da ke cikin ƙwaƙwalwa. Sau da yawa akan ji Bahaushe na cewa:

    1. Na waƙa yi masa dukan fitar arziki.
    2. Na sha waƙa zuwa aikin Hajji.
    3. Na waƙa masa farashin kayan.
    4. To, Allah ya sa ba waƙa ba ce.

    A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali , Bahaushe kan ce:

    1. Ai na zaci waƙa ce.
    2. Ya matse sauti kamar mai waƙ
    3. Zaƙin murya sai ka ce zabiya.

    Ta wata fuskar kuwa, waƙa takan kasance wata magana wadda akan rera da baki, wadda kuma aka tsara bisa wani zubi na musamman.

    Dangane da ma’anar waƙa ta ɓangaren adabi kuwa, za a ga masana adabin baka da dama sun ba da ma’anarta a wurare mabambanta gwarwadon fahimtarsu. Daga cikin masanan, Gusau (1984 p. 3) cewa ya yi:

    Waƙar baka ita ce wani saƙo cikin zance na azanci da ake rerawa ba faɗa kurum ba, ta cikin hikima da fasaha da zaɓaɓɓun kalmomi, waɗanda suka dace da saƙon. Kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa, dangane da sautin murya da kiɗa da amshi da gaɗa da taɓi ko zabiyanu mai saka zuciya jin daɗi.”

    Shi kuwa Umar (1987 p. 7) ya bayyana ma’anar da cewa:

    Waƙa ita ce nau’in sarrafaffen harshe da ake gabatarwa da sigar gunduwoyin zantuttukan da ake kira baitoci ko ɗiyoyi, waɗanda ake ginawa a kan kari ƙayyadadde, kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.

    Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni da masana suka bayyana, za a ga cewa, suna ƙoƙarin nuna cewa, waƙa na nufin tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da hikimar sarrafa harshe da ake rerawa gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman.

    2.3 Waƙoƙi Fada

    Su ne wasu manazarta kan kira da waƙoƙin sarauta. Waƙoƙi ne da ake yi wa duk wani da ya jiɓinci jinin sarauta ko aka ba shi wani matsayi na musamman a majalisar sarki, inda ake taro domin gudanar da mulkin al’umma cikin tsari irin na gargajiya. Masu aiwatar da waɗannan waƙoƙin su ake yi wa laƙabi da makaɗan sarauta ko mawaƙan sarauta.

    Ta fuskar ma’ana kuwa, Gusau (1988 p. 165) cewa ya yi:

    Waƙoƙin baka na fada su ne waɗanda makaɗa na musamman ke gudanarwa ga sarakunan gargajiya da iyayen ƙasa da hakimai da dagatai da masu unguwanni da ‘ya’yan sarakuna da fadawa da masu riƙe da da muƙaman sarauta da sauran ƙungiyoyin da suka jiɓinci sarauta.

    Waƙar fada na zuwa ne a rere cikin sautin murya da daidaita shi, wanda ya sa take zuwa gutsure-gutsure (gunduwa-gunduwa) tare da maimaita gindinta a tsakaninsu. Kowane gutsure kammalalle ne ga kansa, amma wani zubin ma’anarsa takan cika ta tumbatsa har ta tsallaka ga gutsuren da ke bi masa. Gutsuren nan ne ake kira ɗan waƙa, jam’insa kuwa, ɗiyan waƙa.

    Ana iya cewa, waƙar fada shiryayyen zance ne mai zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaitawa da ake yi wa wanda ya shafi sarauta domin a yabe shi, ko zuga shi ko kambama shi tare da fito da shi fili kowa ya san shi. Takan ƙunshi nakasa (aibanta) abokan hamayyar wanda ake yi wa waƙar ta hanyar yi musu zambo da habaici da shaguɓe da nuna hushi da tsoratarwa da firgitarwa da sauransu.

    2.3.1 Wanzuwar Waƙar Fada

    Ana kyautata zaton an soma waƙa ne a farfajiyar doron duniya a daidai lokacin aka ƙirƙiro farauta da samuwar addinin gargajiya. Gusau (1988 p. 167) ya nuna cewa, waƙa ta ƙara bunƙasa da haɓaka sanadiyyar yaƙe-yaƙe da bayyanar sana’o’i da wasannin motsa jiki da wasu lamurran da suka jiɓimci al’adun gargajiya. Masanin ya nuna cewa, a farfajiyar ƙasar Hausa farauta ta kasance daɗaɗɗiyar sana’a da aka fara aiwatarwa. Hasalima an sami waƙoƙin da suka dangance ta.

    Ana cikin irin wannan yanayi ne, sai sarautun gargajiya suka bayyana sakamakon taruwar al’ummar Hausa tsangaya-tsangaya. Wannan ya faru ne tun daga lokacin da suka kafa mazaunai don samar da wurin zama na dindindin, domin samun damar gudanar da sana’ar noma da kiwo da wasu abubuwan inganta rayuwa tare da kare kai daga farmakin namun daji.

    Ana kyautata zaton daga lokacin ne aka soma yi wa sarki waƙoƙi gajeru. Bayan bunƙasar waɗannan tsangayoyin mazaunin farko zuwa ƙauyuka da garuruwa da birane, sai yaƙe-yaƙe suka haddasu a tsakaninsu, domin ƙoƙarin tabbatar da mulkin danniya. Ana cikin irin wannan yanayi ne yaƙe-yaƙen ƙabilanci suka wakana a tsakanin ƙabilu da Hausawa domin son mulki da iko da kuma shugabanci na sarakuna da ke mulkin su, ko kuma don neman faɗaɗa ƙasa ta mulki domin ta zama babbar daula.

    Sakamakon irin waɗannan yaƙe-yaƙe da suka auku ne ya wanzar da samuwar wasu masu rauni da ke da kishin al’ummarsu; waɗanda ba su da ƙarfin karawa da dakarun yaƙi. Su ne suka dinga amfani da hikimarsu da basirarsu da zalaƙarsu wajen gudanar da kirari na yabon sarakunansu tare da zuga jarumansu domin ƙara musu ƙwarin guiwar fatattakar abokan adawa.

    A wani ƙaulin kuma, Gusau (1988 p. 167) ya nuna cewa, makaɗan da suka rinƙa yi wa sarakunansu guntayen waƙoƙi tun kafin a fara yaƙe-yaƙe ne suka cigaba da koɗa sarakunansu a fagen daga tun kafin a fita yaƙi ko bayan an dawo.

    A wani ƙaulin kuwa an bayyana cewa, a lokacin da ake kaɗa wasu kayan kiɗan yaƙi kamar: Tambari da kurya, sai Ɗanma’abba ya rinƙa aiwatar da kirari tare da zuga sarkinsu. Daga irin haka ne ‘Yanma’abban suka samu sukunin ɗinka ganguna da ƙudurin in an tafi yaƙi ko bayan an dawo su dinga cicciɓa sarki da jama’arsa.

    Hasali ma tare da su ake zuwa yaƙin. Ko an samu ɓacin rana, ba za a kashe su ba, sai dai su bi sarkin da ya samu nasara su dinga yi masa waƙoƙi suna zuga shi kan bajintarsa (Gusau, 1988 p. 168). A sakamakon haka ne wasu ƙasashe suka samu damar mallakar tamburran abokan hamayyarsu. Misali, kamar yadda ake hasashen cewa irin haka ne ya haifar da Gumawa suka mallaki tamburran Zamfarawan Anka.

    A tsakanin shekarar 1910 zuwa 1915 a daidai lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare aka daina kiɗan yaƙi, kamar yadda Gusau (1988 p. 170) ya nuna. Daga nan sai makaɗan suka koma ga aiwatar da waƙoƙin ga sarakuna suna yabon su ta hanyar bayyana musu irin bajintar da kakanninsu suka nuna a fagen fama.

    Wannan salon kiɗan shi ne ake yi wa laƙabi da kiɗan fada ko kuma a ce kiɗan sarauta ko na iko ko mulki. Hasali ma shi ne ya maye gurbin kiɗan yaƙi. Daga lokacin ne sarki kan gayyato mawaƙi ya yi masa waƙa a inda zai yabe shi, ya kuma zuga shi, kana kuma ya kushe abokin gabarsa. Yayin da mawaƙi ya gama rera waƙoƙinsa, sai sarkin ya yi masa gagarumar kyauta ta ƙasaita.

    A sakamakon wannan, mawakin yakan ji yana ƙaunar sarkin. Soyayyarsa takan sa ba wanda yake yi wa waƙa sai sarkin. Sakamakon haka ne sarakuna suka samu damar mallakar makaɗa da mawaƙa a fadojinsu, har suka zama makaɗan fada, kamar yadda Gusau (1988 p. 170) ya bayyana.

    2.3.2 Musabbabin Yin Waƙoƙin Fada

    Akwai abubuwa da dama da suka sabbaba ƙaga kiɗan fada. Ire-iren waɗannan abubuwan sun ƙunshi, nuna buwaya (gagara) da rinjaye (fifiko) da dawwama cikin samun nasara da galaba a kan maƙiya da soyayya da kyauta da sauransu.

    Sakamakon irin waɗannan abubuwa da mazaje suka keɓanta da su ne, ke sa a shirya musu waƙoƙi domin ƙara zuga su tare da fito da martabarsu da kwarjininsu a idon jama’a. Misali, ga abin da Malamin Kiɗa Sa’idu Faru ke bayyana wa Sarkin Kiyawa na Ƙaura Alhaji Abubakar, a inda yake cewa:

    Ni kiɗin yaƙi nay yi ma Abu na Isau,

    Ba ni son kana zaunawa banza,

    Ka ɗauki takobi da bindigogi da bakukuwa.

    Ba mu sansani sai bakin Tsabre,

    Kano da Katsina hak Kwantagora,

    Duk riƙon Namoda na, shi na ac can,

    Garba ka amshe riƙon duk da Umaru,

    Umaru yab bam ma.

    (Sa’idu Faru: Gwabron giwa na Shamaki, Baba Ubangandu)

    2.3.3 Makaɗan Fada/Sarauta

    Su ne makaɗan da ke yi wa sarakuna waƙa kawai. Ba kasafai suke yi wa sauran jama’a waƙa ba. Sun fi mayar da hankalinsu a kan uwayen gidansu. Sarakuna su ne iyayen gijinsu. A sakamakon haka, ba sa yi wa kowa waƙa sai da izinin sarkinsu. Wannan na faruwa musamman kasancewar sarakunan ne suke ɗaukar ɗawainiyarsu, kuma sun fi kowa ganin ɗaukaka da darajar sarakunansu. Makaɗa da dama da ke cikin rukunin farko na makaɗan sarauta suna da wannan falsafar a cikin zukatansu. Misali, Mu’azu Na’alalo cewa ya yi:

    Darajar kaza gashinta,

    Darajar makaɗi sarkinai,

    (Gital, 1984) a cikin Abba da Zulyadaini (2002)

    Haka shi ma Jankiɗi ya ce:

    Jumirin kwaram a kwana ana tafiya sai goga,

    Jaki bai kai nan ba,

    ‘Yan yara masu kurin waƙa ku bar wargi,

    Ma’ana ba ta zama ɗai ba.

    Ni ba ni kiɗin iska sai ga sarkina.

    Idan aka dubi waɗannan ɗiyan waƙa, mawaƙan fada suna nuni da cewa, yi wa sarakuna waƙa ya fi kome martaba, don haka suna kallon yi wa talaka waƙa kamar aikin banza ne. A ɓangaren sarakunan da ake yi wa waƙar kuwa, sukan ɗauki ɗawainiyarsu da ta iyalansu tun daga muhallinsu, har abin da za su ci da kuma suturarsu. Sa’idu Faru ma ya nuna yadda ubangidansa ke ɗauke da lalurarsa a cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Misali, ga abin da yake cewa:

    Sarki zamaninka na ruhwa,

    Na ta da kaina,

    Kowag gane ni da Daudu,

    Ya san sarki garan gawurtacce.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Abubakar Sarkin Kiyawan Ƙaura)

    A nan za a fahimci cewa, makaɗin na ishara ne da cewa shi makaɗin sarauta ne, don haka ne sarkinsa ke ɗauke da buƙatunsa.

    Haka kuma ya fito fili ya na bayyana wa al’umma cewa, shi ne kawai makaɗin sarauta da ya rage a wannan zamanin. Sauran makaɗa sun koma makaɗan jama’a sakamakon juyin zamani. Ga abin da yake cewa kamar haka:

    Sa’idu Faru ka waƙar iko,

    Komai kaj jiya ƙarya a kai,

    Sa’idu Faru ka waƙam mulki,

    Komai kaj jiya ƙarya a kai.

    (Sa’idu Faru: Turakin Kano Amadu)

    2.3.4 Rabe-Raben Makaɗan Sarauta

    A wannan rukuni na makaɗan sarauta (makaɗan fada) za a tarar cewa Gusau (1996) ya kasa su zuwa ɓangarori biyu. Kashi na ɗaya (1) da na biyu (2). Jerin makaɗan da suka faɗo ƙarƙashin kaso na farko su ne:

    1. Abdu Kurna
    2. Abubakar Akwara
    3. Alhaji Muhammadu Sarkin Taushin Katsina
    4. Aliyu Ɗandawo
    5. Buda Ɗantanoma
    6. Ibrahim Gurso
    7. Ibrahim Narambaɗa
    8. Idi Ɗangiwa Zuru
    9. Jibo Maituru
    10. Muhammadu Dodo Maitabshi
    11. Muhammadu Inyaga
    12. Salihu Jankiɗi

    Kashi na biyu kuwa ya ƙunshi makaɗan da suka haɗa da:

    1. Alhaji Ɗankurma Maru.
    2. Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun.
    3. Alhaji Sa’idu Faru
    4. Alhaji Sa’idu Maidaji Sabon-Birni
    5. Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo
    6. Muhammadu Ango Maitabshi
    7. Muhammadu Maidamma Sarkin Taushi
    8. Sarkin Taushi Muhammadu Ɗanbunguɗu
    9. Umaru Maisa’a Tubali

    2.3.5 Alaƙar Makaɗan Fada Da Sarauta

    Makaɗan fada na ɗaya daga cikin rukunin al’umma da sarakuna ke ɗauke da lalurorinsu na yau da kullun. Sarki yakan zama ubangidan makaɗi, shi yakan ɗauki lalurar cinsa da shansa, ya yi masa gida ya ba shi gona, ya kuma rinƙa yi msa sutura tare da iyalansa. Haka kuma yakan ba shi kuɗaɗen ɓatarwa.

    Sarki yakan amince wa makaɗinsa fiye da sauran fadawansa. Yakan zauna tare da shi su yi hira cikin sakin fuska sosai da zaman amana da taimakon juna. Shi kuma makaɗin zai dinga girmama sarkin da mutunta shi tare da yi masa ladabi da biyayya tamkar yadda al’ummar fada ke yi masa.

    A al’ada, makaɗin fada bai fita waje ya yi wa wani sarki ko jinin sarauta waƙa, sai da izinin ubangidansa. Yayin da ya je waƙa gun wani, zai nuna wa sarkinsa duk nau’in abin alherin da aka yi masa. Wani lokaci, yana iya bayyana masa a cikin sigar waƙa.

    3.1 Siffofin Makaɗan Sarauta Da Matsayin Sa’idu Faru

    Makaɗan sarauta suna da waɗansu siffofi da suka fi alaƙantuwa da su. Sun haɗa da:

    1. Makaɗin sarauta shi ne wanda kan samu wani basarake ya zauna a wajensa ya kasance ubangidansa da zai rinƙa yi masa yammaci (kiɗa daren Juma’a) ko daren salla. Sukan bi sarki a duk lokacin da zai fita rangadi (kewayar gundumar da ke ƙarƙashin mulkinsa).
    2. Sukan nemi izinin ubangidansu kafin su tafi yawon kiɗa gidan wani sarki ko alƙali ko bafade ko wani mai arziki da ke ɗasawa da ubangidansu.
    3. Akasarinsu sun gadi kiɗa da waƙa irin na sarauta idan aka cire Aliyu Ɗandawo Shuni, wanda ya kasance ɗan wani shahararren malami da aka yi a can Shuni ɗin da ake kira da suna Modibbo Aliyu, Kamar yadda Gusau (1984) ya nuna.
    4. Sun fi kowane Bahaushe sanya tufafin gargajiya, wato sanya manyan riguna da wandunan buje da taguwoyi masu manyan hannaye. Sukan kuma naɗa rawani. Suna riƙe wannan al’ada ce saboda irin wannan suturar sarakuna kan ba su. Abin la’akari shi ne, sarakuna ba sa rabuwa da sanya manyan suturu komi gumi ko zafi. Hasali ma sarki ba zai fito gidansa ba rawani a kansa ba. shi ya sa makaɗan sarauta suka riƙe wannan ɗabi’a domin kare martaba da alfarmar sarauta. Shi ya bambanta su da sauran makaɗa da mawaƙan ƙasar Hausa.

    Duban ire-iren waɗannan siffofi da aka ambata a sama da la’akari da irin sigar yanayin shigar Alhaji Sa’idu Faru za ka tabbatar shi cikakken makaɗin sarauta ne. A lokacin rayuwarsa ba ka raba shi da shiga irin ta iyayen gidansa.

    3.2 Kayan Kiɗan Makaɗan Fada Da Gurbin Sa’idu Faru

    Ta sigar kayan kiɗa kuwa, makaɗan sarauta sun sha bamban da sauran makaɗa da mawaƙan baka na ƙasar Hausa. Haka kuma sun kasu kashi-kashi dangane da kayan kiɗan da suke amfani da su, da nau’o’in waƙoƙin da kuma uwa-uba irin garuruwan da suke zaune da kuma inda suka ƙaurato. Ta fannin kayan kiɗa, za a iya kasa su zuwa kashi uku kamar haka:

    1. Masu kaɗe-kaɗe
    2. Masu bushe-bushe
    3. Bambaɗawa (masu kirari) (Ibrahim, 1983 p. 2).

    Ta wannan haujin kuwa, Alhaji Saidu Faru yana cikin sahun makaɗan fada da ke amfani da kayan kiɗa dangin na sarauta. Su ma kayan kiɗan sarauta sun karkasu kamar haka:

    (i) Tafshi

    (ii) Kotso[1]

    (iii) Jauje

    (iv) Tambari

    (v) Banga

    Waɗannan kayan kiɗa akan yi amfani da su wajen tsima sarki ta hanyar kambama shi da magabatansa.

    Kashi na biyu kuwa sun ƙunshi abubuwan busawa ne da suka danganci:

    (i) Algaita

    (ii) Kakaki

    (iii) Ƙaho

    (iv) Farai

    Waɗannan kayan busa suna ba wa talakawa labari ne cewa, sarauta tana nan daram ta kafu. Suna kuma jawo hankulan masoya sarki da cewa su zo su ji abin da za a faɗa game da masoyinsu.

    3.3 Sauya Sheƙar Makaɗan Sarauta Zuwa Na Jama’a

    Sauye-sauyen ubangida ga makaɗan fada yakan faru ne a zamanin da sarakuna ke da ƙarfin ikon gudanar da al’amuran tafiyar da ragamar mulkin al’ummominsu, kafin mulkin Jamhuriya ta farko. A waɗansu lokuta makaɗa na sauya ubangidansu, musamman saboda dalilai kamar haka:

    1. Yayin da ubangida (sarki) ya karɓa kiran Mahaliccinsa.
    2. Yayin da aka fitar da shi daga sarautarsa.
    3. Yayin da ya daina yi wa makaɗinsa alheri.

    4.1 Nau’o’in Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Sa’idu Faru ya yi wa sarakuna da jinin sarauta waƙoƙi da dama waɗanda shi ma kansa bai san adadinsu ba saboda yawansu. Hasali ma, dukkan waƙoƙin shi ne ya ƙaga su da kansa. Shi ba kamar sauran makaɗan sarauta ba ne da ke maimaita waƙoƙin da mahaifansu suka aiwatar ba. A ƙasa an kawo waɗansu sarakuna da hakimai da uwayen ƙasa da ya yi wa waƙa:

    1. Sarkin Yamman Faru Ibrahim
    2. Sarkin Yaƙin Banga Sule
    3. Sarkin Kiyawan Ƙaura Abubakar Garba
    4. Sarkin Gabas Na Mafara Muhammadu
    5. Sarkin Musulmi Abubakar III
    6. Sarkin Yawuri Alhaji Muhammadu Tukur
    7. Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami
    8. Sarkin Kano Ado Bayero
    9. Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
    10. Sarkin Gabas Shehu Uban Ƙasar Talata Mafara
    11. Turakin Kano Amadu
    12. Muhammadu Muhammadu Maidabo Tudun Falale
    13. Alhaji Muhammadu Mode, Ɗan Alin Birnin Magaji
    14. Sarkin Zamfaran Zurmi, Suleiman Muhammadu Sambo
    15. Sarkin Zazzau Alhaji Dr. Shehu Idris, da sauransu

    Ta fuskar waƙoƙin da ya yi wa ubangidansa kuwa, ya yi wa Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo waƙoƙi da dama. Abin da hannaye suka samu nasarar dafawa su ne:

    1. Farin cikin Musulmi duk kai muka taƙama yau,

    Muhammadun Muhammadu ɗan Abdu mai darajja.

     

    1. Sai na zo in yi mai kiɗi in ƙaro ilmi,

    Mamman Bajinin Magaji mai takakkay yaƙi.

     

    1. Farin cikin Musulmin Duniya, mai martaba na Abubakar,

    Ci fansa Alhaji Macciɗo.

     

    1. Kana shire Baban Yan Ruwa,

    Na Bello Jikan Ɗanfodiyo.

     

    1. Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,

    Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

     

    1. Shugaban sahun gabas riƙa ƙwarai,

    Muhammadun Amadu Uban Zagi.

     

    1. Hattara Bajinin gidan Bello Jikan Hassan maganin wargi.

     

    1. Ya yi Sarki daidai wada mai yanzu yar riƙa,

    Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai dubun bara.

    1. Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.

     

    1. Hattara mai martaba Bello ɗan Bubakar,

    Sarkin Kudun Hausa.[2]

    Yayin da aka kwatanta Alhaji Musa Ɗankwairo a matsayinsa na mawaƙin sarauta kuma Sarkin kiɗan ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu, da Alhaji Sa’idu Faru, za a iya cewa, Ɗanƙwairo ya canza sheƙa sakamakon juyin zamani.

    Hasali ma ana hasashen cewa, tun waƙar Shirya Kayan Faɗa ba wata waƙa da ya sake yi wa ubangidansa. A madadin haka, sai ya karkata ga yin waƙoƙin jama’a da suka ƙunshi ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da malamai da tajirai. Wannan ne ya sa mafi yawan waƙoƙinsa suka zama na gama-gari. Misalan waƙoƙin sun haɗa da ta:

    1. Alhaji Shehu Kangiwa
    2. Kanal Umaru Muhammad
    3. Alhaji Ahmadu Aruwa
    4. Alhaji Kabiru Mado
    5. Alhaji Ali na Malan Bawa
    6. Alhaji Garba A.D. Kano
    7. Alhaji Garba Nadama
    8. Alhaji Ahmad Muhammad
    9. Alhaji Bala Maiyafe
    10. Malan Lawal Ƙalarawi
    11. Alhaji Bala Salisu
    12. Alhaji Sikofiyo
    13. Alhaji Bature Dogon Tela
    14. Alhaji Ibrahim Maganinta
    15. Waƙoƙin Faɗakarwa
    16. Waƙoƙin Jam’iyyun Siyasa

    Ta la’akari da jerin waɗannan waƙoƙin, za su iya kawar da Ɗanƙwairo daga cikin sahun mawaƙan sarauta. Ta fuskar Sa’idu Faru kuwa, babu waƙar da ya aiwatar da za ta iya fitar da shi daga cikin sahun makaɗan sarauta.

    4.2 Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    Kasancewar Sa’idu makaɗin sarauta ne na asali, bai sake juyin zamani da kwaɗayin tara abin duniya ya ruɗe shi ba. Shi ya sa ya tsaya wajen gina waƙoƙinsa a kan turakun da iyaye da kakanni suka assasa tushensu tun farkon fara kaɗe-kaɗen fada (sarauta).

    Binciken masana kamar Gusau (1996 p. 121) ya tabbatar da cewa, Makaɗa Sa’idu faru ba ya yi wa kowa waƙa sai sarki da wanda ya kasance jinin sarauta. Waƙar farko da ya fara aiwatarwa ita ce ta Sarkin Yamman Faru Ibrahim. Gindin waƙar shi ne:

    Bi da maza ɗan Joɗi na Iro,

    Iro magajin Shehu da Bello.

    Hasken hitila ba ɗai da wata ba,

    Tauraro haskenka subahin,

    Dawaya kora ɗimau na wakili,

    Uban sarkin zagi Bello na yari.

    Ruwa da kada ɗibgau na Magaji,

    Sai tsohon wawa ka shigar su.

    (Gusau, 1996 p. 119).

    Tun daga wannan waƙar sai ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi. Yana cikin irin wannan yanayi ne, Allah cikin ikonsa da baiwarsa ya sada shi da Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar na III, wanda ya sarauci ƙasar Talata Mafara daga 1953 zuwa 1956, kamar yadda Talata Mafara (2007 p. 17) ya nuna. Ya fara yi wa Sarkin Kudu Macciɗo waƙoƙi a daidai lokacin da yake riƙe da muƙamin Ubanƙasar Talata Mafara. Ga gindin waƙar da ya fara yi masa, a inda yake cewa:

    Kana shirye baban ‘Yanruwa,

    Na Bello jikan Ɗanfodiyo.

     

    Gardaye zo ka yi man iso,

    Faɗa mashi murna niz zaka,

    Ɗan Sardauna jikan Hassan.

     

    Babban ɗa ga Baura Sarkin Kudu,

    Na Alƙali baban zagi,

    Mai ja ma ya bari ɗan Adamu.

     

    Na Sarkin Gobir Amadu,

    Ci fansa ga wan Sarkin Ƙaya.

     

    Waƙag ga da nim maka Muhammadu,

    Na ji daɗin ta Mamman Sarkin Kudu,

    Tun dak Kabi hak Kano ham Masar,

    Hab birnin Legas hab Bici,

    Kowa ya ji waƙar Sarkin Kudu.

    (Gusau, 1996 p. 120).

    Sa’idu Faru fasihin mawaƙin sarauta ne da ya naƙalci harshen Hausa ga baiwar da Allah ya yi masa ta fasahar ƙulla waƙa yadda za ta yi daɗi ta kuma yi armashi da ma’ana. Sakamakon haka ne ya kira kansa da Malamin waƙa, a inda yake cewa:

    Sa’idu Malamin waƙa,

    Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba×2

    Ban wuce gonata da irina ba,

    Inda Sarkin Kudu nat tsaya.

    Gindin Waƙa: Farin cikin Musulmin duniya.

    (Faru: Waƙar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo)

    Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talakka waƙa ba, komai tarin dukiyarsa. Hasali ma shi da kansa ya yi nuni da haka, a inda yake cewa:

    Ban zo gidan Ɗanbita niy yi roƙo ba,

    Ko ya raba lafiya ba ruwana.

    A wannan ɗiyan waƙar ya fito ƙarara ya tabbatar wa al’umma cewa shi bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Ya jaddada cewa ba zai yi haka ba ko da mutumin yana samar da kowane irin jin daɗi da ingancin jiki da kawar da ciwo daga jikin ɗan’adam. Shi bai damu da duk wannan ba, ballantana ya yi masa kiɗa da waƙa.

    Kalmar ɗanbita a nan tana nufin leburan da ke aikin gyaran hanyar mota. A daidai wancan lokacin, sarakuna ne ke bayar da waɗanda za su yi aikin hanya. Sukan zaɓo waɗanda suka dace da aikin hanyar daga cikin talakawansu. A daidai wancan lokacin akan ji tsofaffi na maganar aikin diga da ke nuni da aikin hanya. A sakamakon irin wannan aikin talakawa da dama sun tara abin duniya.

    Malamin waƙa ɗin ya bayyana dalilan da suka sa ba ya yi wa talaka waƙa da kiɗa kamar yadda Gusau (1996 p. 121) ya ruwaito su cewar:

    1. Ba wata hanya da zai bi ya ɓata wa talaka rai. A lokacin da talaka ya wulaƙanta makaɗi, to sai dai makaɗin ya yi na mai bara (haƙuri).
    2. Yayin da Sarki ko jinin sarauta ya yi wa makaɗi abin da ya ɓata masa rai, sai ya rama a cikin waƙa ta hanyar yi masa zambo ko habaici. Ba wani sarki ko jinin sarautar da yake son makaɗi ya yi masa su.

    Za a iya samun wasu rukunin al’umma su ce, idan haka ne wane dalili ne ya sa Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Shehu Kangiwa waƙa? Amsa a nan ita ce, an yi waƙar ne a shekarar 1976 bayan an naɗa shi Turakin Kangiwa. Sarauta ce da Masarautar Argungu ta ba shi, a ƙarƙashin Shugabancin Maimartaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Muhammadu Mera.

    Ya zama ɗaya daga cikin jigajigan masarautar. Don haka, an yi masa waƙar ne a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautun gargajiya a Msarautar Argungu. Idan aka yi la’akari da ma’anar makaɗan sarauta da lokacin da aka aiwatar da waƙar, za a iya tabbatar da cewa Makaɗa Sa’idu Faru bai taɓa yi wa talaka waƙa ba. Shi makaɗin sarauta ne tsantsa.

    4.3 Ƙananan Turakun Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

    4.3.1 Yabo

    Makaɗa Sa’idu Faru a cikin waƙoƙinsa yakan yabi ubangidansa ta haujin ambaton asalinsa. Yakan kuma danganta shi da asalinsa ta hanyar bayyana cewa ya gaji gidansu. Ta haka ne ya yabi Sarkin Kudu Macciɗo da irin wannan sigar a inda yake cewa:

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Alu Babba,

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah,

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Shehu, Amin.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙo Allah.

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Bello, Amin.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Bubakar na farko.

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar Bubakar na biyu,

    Ka gama lafiya da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Aliyu Babba,

    Ka gama da kyau da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah ya ba ka albarkar nan ta Alu ƙarami,

    Ka gama da kyau cikin sa’a mun yi roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar Abdullahi,

    Ka gama da lafiya da imani mun yi roƙon Allah.

    Allah shi ba ka albarkar nan ta Hassan Dattijo.

    Ka kammale, ka ɗibo jama’arka.

    Duk ka shirya mu gaban Ma’aikin Allah,

    Mu yi farin ciki,

    Mu ji daɗin da yaf fi daɗi daɗi na Annabi.

    Mu ji ƙamshin da yaf fi ƙamshi, ƙamshi na Bubakar,

    Allah shi sa ka samun martabar kakanka.

    Yayin da aka dubi waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga cewa, Sa’idu Faru na yi wa ubangidansa Sarkin Kudu Macciɗo fatan Allah ya ba shi albarkar waɗannan kakanni nasa ya kasance tamkarsu tare da samun martaba irin tasu.

    Ba nan kawai ya tsaya ba. Har ma ya yabi Sarkin Kudu Macciɗo ta haujin iya gudanar da mulki, a inda yake cewa:

    Shugaban duniya Alhaji Bello Sarkin Kudu,

    Jan damishi Shehu Sarkin Gabas,

    Baban su Alƙali.

    Gadangadan Shehu Sarkin duniya,

    Ba mai riƙo na ba.

    Ai! Ina ba magana ba ce yanzu gidan Bani,

    Ba mai kamar Macciɗon Hausa.

    Girmanka ya kai muƙaminka ya kai,

    Riƙon duniya wada Abubakar yak kai,

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).

    A nan mawaƙin ya bayyana cewa, Macciɗo zai iya gudanar da mulkin wannan duniya sakamakon ƙwarewarsa a fagen mulki.

    Ta fuskar addini ma, ya yabi ubangidansa a inda yake cewa:

    Gindin Waƙa: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,

    Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

    Jagora: Tsari gaskiya Bello kai Shefu yac ce,

    ‘Yan Amshi: Bari masu son dus su maishe ka yaro,

    Duk kyauta da ilmi da neman dalili,

    Da gode ma Allah da istingafari,

    Da su Bello ɓello ɗan Shehu yat tcarma kowa,

    Ka kai kamab Bello,

    Ka gadi Moyi,

    Saura ka kai inda mai Hausa yak kai.

    Yayin da aka dubi ɗiyan da suka gabata, za a ga yadda wannan turken ya ƙara tabbatar mana da kasancewar mawaƙin a gurbin makaɗin sarauta. Makaɗan fada ne suka yi fice wurin yabon uwayen gidansu ta fuskar addini. Hakan na faruwa ne kasancewar sarakunan ƙasar Hausa su ne shugabannin addinin Musulunci tun kafin jahadin Shehu. Jagorancin nasu ya ƙara bunƙasa ne bayan tabbatuwar jahadi. Da irin wannan yabon ne sarakuna suke alfahari da makaɗansu.

    A nan ya bayyana wasu siffofin da suka keɓanta ga sarakunan ƙasar Hausa, wato, kasancewarsu masu alheri ga al’ummarsu, da zamansu malamai masana dangogin ilmomin zaman rayuwar duniya, domin su ne tushen samun kyakkyawar makoma gobe kiyama. Ya kuma ƙara kawo abu da ya kasance tamkar ruwa da gishiri a fagen sarrafa abinci da sauran lamurran rayuwar duniya.

    A nan ya yi masa hannunka mai sanda ne da ya lizimci nuna godiya a kan ni’imomin da Allah ya yi masa da dagewa ga yin tuba game da kuskuren da yake aikatawa, domin ta haka magabatansa suka tsere tsara. Idan ya nace a kan haka, zai kai ga samun matsayin da Sarkin Musulmi Abubakar Sadik yake a kansa.

    4.3.2 Zuga

    A wannan haujin kuwa, Sa’idu Faru yakan harzuƙa ko tunzura sarkin da yake yi wa waƙa, ta hanyar kambama darajarsa. Dubi yadda yake cewa a waƙarsa da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo mai take:

    Gindin waƙa: Kana shire baban ‘yan ruwa.

    Jagora: Wani taro da an ka zo Ikko na bariyac can,

    Da Turawa da kuma ministoci had da kansiloli,

    Sarkin Musulmi da Amdu Bello sun zo wurin dus sun ziyar tai,

    Tafawa Ɓalewa ya sauka ga Lamiɗo Barno,

    Nan kudu Shehu Talba,

    Sarkin Bidda ya sauka ga Sarkin Ilori,

    Kulluhinsu sarakunan majalisa sun taru Ikko,

    Muhammadu Bello jikan Hassan kai sun ka zaɓa,

    Don ka hi su kyawon shirin kawo dalillai.

    Idan aka dubi kwayar turken wannan ɗan waƙar, za a ga ya fito ne ƙunshe da zuga Sarkin Kudu Macciɗo tare da fifita shi a kan waɗanda suka halarci taron. A ɗaya ɓangaren kuwa, ya taskace tarihin taron da aka aiwatar a Ikko tare da fito da maigidan nasa fili domin waɗanda ba su san shi ba su san shi. Irin wannan zugar ke ƙara tabbatar wa masu nazari gurbin da mawaƙin ya kasance.

    4.3.3 Habaici

    A cikin waƙoƙinsa akwai wuraren da yakan yi wa abokan adawar ubangidansa habaici ba tare da faɗa masa wata muguwar magana ba. Wannan kan iya kasancewa a cikin sigar jifa a kasuwa ko kuma ya san da wanda yake. Hasali ma makaɗan fada sun fi shahara ta fuskar amfani da habaici domin ƙasƙantar da abokin hamayyar sarkinsu ko muzanta shi a bainar jama’a a fakaice. Misali Sa’idu Faru yana cewa:

    Zaki mai zama ga hilin Allah ga shi ga hili,

    To wak ka san ya far mashi,

    Kafin maza su shirya Mamman na Ali ya shirya.

    Sun dai yi ɓaɓɓakar dutsi,

    Sun yi gyangyaɗar dutsi,

    ‘Yan hannuwansu sun gaza.

    Na Audu ko da ƙarfin Allah kana shiga gidan.

    Na ce mai kama da ƙot,

    Haka nij ji gun Badakkare.

    Dogon sarki yana da ban sha’awa,

    Ko da anka zo taro ya fi kyau da riguna,

    Duk wanda ag gajere a aje shi gun rabon dawo,

    Shi kai ma wanga dunƙule.

    Aw wurin da mata ciki,

    Har tuman gada yakai.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Tudun Falale).

    Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a fahimci Sa’idu Faru ya yi wa wasu ‘ya’yan sarki habaici ne a kaikaice, domin ya fahimci suna son su yi jayayya da ubangidansa.

    4.3.4 Zambo

    A nan ma akan samu inda yakan yi wa abokan hamayyar ubangidansa wata mugunyar magana. Misali a cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo yana cewa:

    Gindin Waƙa: Gogarman gidan Moyi ci fansa niƙatau,

    Mai babban rabo ginshiƙin Sarkin Shariffai.

    Jagora: Na ishe dale tai ƙawa ga jama’at ta ba ƙawa.

    ‘Yan Amshi: Ya murɗe su duy ya zuba dogon akwati,

    Rana ta kewayo ya naɗe ya kai Ilori,

    Dac can yas sawo man kishe,

    Ya sai tabarau.

    Yayin da aka nazarci wannan ɗiyar za a ga cewa, ya yi wa wani ɗan sarki zambo ne ta hanyar siffanta shi da wata tsuntsuwa da ake kira dale. Ita dale akan gan ta ne lokacin kaka. Ta kasance nau’i biyu. Akwai ja mai baƙi-baƙi ga kai, akwai kuma mai launin ɗorawa da baƙi-baƙi ga kai.

    Ita dalen ba a ganin ta sai lokacin da amfanin gona ya kai. Saboda halayyarta ne ya kamanta ɗan sarkin da ita, domin bai amfana wa kowa komai. Hasali ma idan wani abun alheri ya zo da ya kamata ya ba al’ummarsa, sai ya yi sama-da-faɗi da shi.

    4.3.5 Roƙo

    Akan sami wasu ɗiyan waƙoƙinsa da Sa’idu Faru yakan yi bara ko ya roƙi ubangidansa wani abu kai tsaye cikin hikima. Wannan wata azaliyya ce da ta keɓanta ga makaɗan sarauta, wato su bayyana abin da suke so daga ubangidansu kai tsaye ba tare da wani sakaye-sakaye ba. Shi ma Malamin Waƙa ya aiwatar da shigen wannan a inda yake cewa:

    Manyan ma’aikatan gwamnati,

    Manyan ma’aikatan N.A.,

    Almajirinku na aike,

    Don bisa gare ku Allah ya shiya mana asiri,

    Na roƙe ku in da hali,

    Ku zam shirya muna kujera mui Haji.

    Na yi mafarki nai sallah Makka nai ɗawafi,

    Kuma na rungumo hirami

    Da makaru a fuskoki,

    An ce mani Alhaji baitul fasali kake,

    Wanga mafarki ya Allah ya nufa a shirya shi,

    Ya zam haka.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kudu Macciɗo).

    A waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga mawaƙin ya fito ƙarara ya nuna buƙatarsa tare da ayyana dalilinsa wanda ya kasance mafarkin da ya yi da yake son a taimaka masa ya zama gaskiya. Za a iya cewa, ma’aikatan gwamnati da ya roƙa ai suna cikin rukunin talakawa. Lamarin a wancan lokacin ba haka yake ba. A daidai lokacin ‘ya’yan ahalul falala ake damƙa wa aikin hukumar En-e da na gwamnati.

    4.3.6 Koɗa Kai

    Sa’idu Faru fasihin makaɗan fada ne, musamman idan aka yi la’akari da wuraren da yakan wasa kansa ta hanyar nuna ƙwarewarsa wajen tsara waƙa fiye da sauran makaɗan fada. Kuma yakan yi hakan ne a ciki ɗiyan waƙoƙin da ya ƙulla wa maigidansa Sarkin Kudu Macciɗo. Kasancewar sa makaɗin fada, ya shahara wajen amfani da wasu halaye da siffofi na ɗan’adam, ya ƙaga su ga wani abu wanda ba mutun ba, wato abin da ake kira mutuntarwa. A waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu macciɗo cewa ya yi:

    Nan na bi Gusau sai niw wuce,

    Kuma nab bi Kwatarkwashi niw wuce,

    Kuma nib bi ta Tcahe ina gudu,

    Can na kusa kai wa Zariya,

    Sannan Daudu ni kau sai nit tsaya.

    Sai Sarkin Zazzau nig ga nay,

    Ya ce man Muhamman Sarkin Kudu.

    Sai nis saki hanya nig gabas.

    Can na taɓa ‘yar tafiya kaɗan,

    Sai ni ishe suda na kiwo,

    Tana barka Sarkin Kudu,

    Allah rai ya daɗe Sarkin Kudu,

    Allah sabbinane na Ahmadu,

    Allah shi ƙara mai nasara.

    Na ce suda waƙa akai,

    Ta ce lalle waƙa ni kai,

    Waƙar Mamman Sarkin Kudu,

    Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.

    Baicin uwar tsuntsaye nike,

    In da kamar mulkina nikai,

    Da nai mai wasiƙa ya yi min kiɗi,

    San nan ni kau sai niw wuce,

    Can na taɓa ‘yar tahiya kaɗan,

    Sai ni iske burtu na kiwo,

    Yana barka Sarkin Kudu,

    Rai ya daɗe Sarkin kudu,

    Allah sabbinane na Amadu,

    Allah shi ƙara mai nasara,

    Na ce burtu waƙa akai,

    Ya ce lalle waƙa nakai,

    Waƙar Mamman Sarkin Kudu,

    Waƙar nan da Ɗan’umma ya yi mashi.

    In na yi ta za ni wurin kiwo,

    In na so abinci sai na rufe.

    A cikin waɗannan ɗiyan waƙar, za a fahimci cewa mawaƙin ya yi amfani da adon harshe ne domin jaddada cewa ba ya yi wa kowa kiɗa da waƙa sai sarakuna da waɗanda ke da alaƙa da fada. Ga shi har da tsuntsaye sun san da haka. A ɗaya ɓangaren kuwa yana ɗaukaka waƙar da ya yi wa Sarkin Kudu, wadda sakamakon yadda ta tsaru ta yi armashi, har tsuntsaye na maganar waƙar.

    Waƙar da ya yi wa Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami, ita ma wata hujja ce mai ƙarfi da ke tabbatar da kasancewarsa makaɗin sarauta ne na gani-da-faɗa wanda sauyin zamani bai juya shi ba. A wasu ɗiyan waƙar, yana cewa:

    Gindin Waƙa: Muzakkarin sarki ɗan Audu,

    Abin biya Shehu na Ali.

    Jagora: Ɗan talakka komai yac cika huska,

    Sa’idu ni ba ni kiɗa mai, .

    Jagora: Ɗan talakka komai ya aje ƙarhe,

    Sa’idu ni ba ni kiɗa mai.

    Da duban waɗannan ɗiyan waƙar za a ga ya fito fili yana jaddada cewa shi ba makaɗin talakawa ba ne, kuma komai bajintarsu da ƙwazo da kuma uwa-uba mallakar tamani (jikkunan kuɗaɗe) ba zai yi musu kiɗa da waƙa ba.

    4.4 Sarrafa Harshe a Cikin Waƙoƙin Saidu Faru

    4.4.1 Ƙarangiya ko Gagara-gwari

    Makaɗan fada, musamman waɗanda suka fito daga yankin da ke cikin farfajiyar tsohuwar Daular Zamfara, wato yakin da ke cikin Masarautar Bakura da Zurmi da abin da ya gangara Sabon Birnin Gobir har zuwa Dacaɗi da sauransu, sun fi takwarorinsu da ba ‘yan asalin yankin ba ne wajen mallakar harshen Hausa da iya sarrafa shi.

    Sa’idu Faru ya yi wa takwarorinsa da suka yi zamani ɗaya da shi fintinƙau ta fannin sarrafa sautukan Hausa masu bugun juna ta hanyar maimaita su a cikin ɗiyan waƙa domin nuna ƙwarewarsa a harshen da yake waƙa da shi (Hausa). Ana kyautata zaton cewa, sukan yi amfani da wannan hikimar ne domin kawar da wani lamarin da ke ci wa sarki tuwo a ƙwarya ta yadda zai koma ga hayyacinsa har ya yi ƙoƙarin fahimtar yadda aka yi luguden kalmomin da fahimtar ƙunshiyarsu. A duba misalin inda Sa’idu Faru ke cewa:

    Yaro in taƙamar salon magana kaka yi,

    Ce tsare tsara,

    Ta hi tsantsamin tsantsara,

    Ko tsattsame tsari,

    Tsaf ga tsamiya.

    Tunkuɗa tunku cikin tukar rukuɓu,

    Tukuɗin Tumba yai tuɓus,

    Tumba taho yau da ke da taɓo,

    Da taɓo da’yat tuɓus..

    (Sa’idu Faru: Waƙar Sarkin Kiyawa na Ƙaura).

    Yayin da aka duba waɗannan ɗiyan waƙar za a tarar cewa Sa’idu Faru ya yi luguden sautukan Hausa kamar: tsa, tu, ɓa, ɓo, ɓu, ɗa, ɗi, da kuma ɗu, domin ya nuna ya naƙalci harshen Hausa da yake waƙa da shi. Mai nazari zai iya yin tambaya game da hujjar kawo wannan dalili?

    Hujja ita ce, tun lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa, a fada ya soma zama da kafa harsashe. Wannan ne ya sa Sarakunan ƙasar Hausa suka kasance malamai musamman bayan jahadin Shehu. Hasali ma sun kakkafa makaratun ilimi (zaure) inda ake koyar da fannonin addini da luggar Larabci da ake fassarawa cikin harshen Hausa. Wannan ne ya sa har gobe tsofaffin kalmomi da hikimomin Hausa sun yanke cibiya a makarantun zaure, ta la’akari da irin hikimomin da ke ƙunshe cikin Muƙamatul Hariyri.

    4.4.2 Dangantakar Kalmomi

    Ta wannan haujin za a ga cewa makaɗan sarauta sun sha bamban da na jama’a ta fuskar zaɓen kalmomin da suka dace da ke da dangantaka da juna tare da tsara su wuri ɗaya cikin waƙarsu. Makaɗa Sa’idu Faru shi ne kan gaba a wannan fagen. Allah ya ba shi basira da hikimar zaɓen kalmomi masu dangantaka da juna. Yakan kuma tsara su a wuri ɗaya cikin waƙarsa. Misali, yana cewa:

    Ihihiya da kunkuru shawara guda sukai.

    Bushiya da beguwa shawara guda sukai.

    Kurciya da hasbiya shawara guda sukai.

    Bubukuwa da jinjimi shawara guda sukai.

    (Sa’idu Faru: Waƙar Muhammadun Muhammadu).

    Ta la’akarida waɗannan ɗiyan waƙar za a ga cewa ya kawo jerin halittu da suke da dangantaka da juna ta siffofin yanayin halittarsu.

    5.1 Sakamakon Bincike

    Daga abin da ya gabata dangane da wannan nazari, ya fayyace mana tabbatuwar Makaɗa Sa’idu Faru a matsayin sahihantaccen makaɗin sarauta na gwadi da ya tsayu wajen kiɗan sarauta da sarakuna a manyan gidaje sarauta har ma da ƙananansu da ke farfajiyar ƙasar Hausa. Sauye-sauye zamani da ɓullowar siyasar dimokuraɗiyya da kwaɗayin neman tara abin duniya bai sa ya bar turbar iyaye da kakanni ba.

    Irin wannan dogiya tasa, da ra’ayin mazan jiya sun bambanta shi da takwarorinsa da suka yi zamani tare har ya zamanto bai taɓa yi wa wani mutun waƙa ba idan ba jinin sarauta ba ne. Hasali ma ko jinin sarauta sai wanda ke riƙe da wani muƙamin sarautar gargajiya. Ya bambanta da mawaƙa irin su Alhaji Musa Ɗanƙwairo da suka kasance cikin zango guda da shi, wanda ya koma yana karɓar gayyatar jama’a domin rera musu waƙoƙi.

    Haka kuma, an fahimci sarakuna na rungume da makaɗansu ne sakamakon yadda suke tsara musu waƙoƙi, wanda ke zama sanadin daɗa ɗaukakuwarsu a idon duniya. Wannan kan auku ne, ta hanyar yadda makaɗan ke ambaton su da kyawawan halaye da ɗabi’u, waɗanda kan fito da sunayensu fili fiye da kima. Da haka ne sukan sami ƙwarin guiwar gudanar da harkokinsu na mulki ba tare da kasala ko tsoro ba, sakamakon zuga da kirarin da mawaƙansu ke yi musu, tare da tunatar da su tarihin iyaye da kakanninsu, musamman dangane da kyawawan halayensu kamar kyauta, haƙuri, ƙwazo da juriya.

    5.2 Kammalawa

    Waƙoƙin fada sun kasance wata maƙerar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha. Haka kuma, suna mazaunin wata makaranta da ke koyarwa ko cusa waɗansu halayen ƙwarai da kuma ƙarfafa guiwa ga waɗanda ake yi wa waƙoƙin, da ma sauran masu sauraro. A ɓangare guda kuwa, suna da matsayin rumbun adana al’ada da tarihi. Makaɗa Sa’idu Faru ya shahara a waɗannan lamura a matsayinsa na makaɗin fada na yankan shakku. Hasali ma, shi ne babban misali lamba ta ɗaya idan ana batun kiɗan sarauta.

    Manazarta

    Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka Ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corpora-Tion LTD.

    Abubakar, A.T. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

    Ammani, M.C. (2019). Nazarin Awon Baka Da Aiwatarwa Da Harshen A waƙoƙin Nafi’u Yakubu

    Baba Katsina. Juzu’i Na Biyu. (Ratayen Matanonin Waƙoƙin Da Aka Yi Nazari A Kansu). Kundin Bincike Da Aka Gabatar Domin Cikasa wata Ƙa’ida Ta Neman Digiri Na Adabin Hausa, A Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero Kano.

    Bango, A. & King, A.B. (1986). “An Introduction to Life and Works of Abubakar Akwara (C. –1876-1962)”. Seminer Paper. Zaria: Ahmadu Bello University.

    Bello, G. (1976). “Yabo, Zuga da Zambo a WaƘoƙin Sarauta”. Harsunan Nijeriya, Vol. VI: 21-34.

    Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre LTD.

    Bunza, A.M. (2014). In Ba ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo. Cairo: Elkods Printing House.

    Ɗangambo, A. (1984 ). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Trimph.

    Funtuwa, A.I. da Gusau, S. M. (edt) (2011). Waƙoƙin Baka Na Hausa. Kano: Century Research And Publishing Limited.

    Gital, G. M. (1984). “Adabin Baka”. Maƙalar da aka gabatar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha, Bauchi.

    Gusau, S. M. (1988). “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Da Yanayinsu, Musamman A Ƙasar Sakkwato. Juzi’i Na Ɗaya Da Sharhi. Kundin Binciken Da Aka Gabatar Domin Samun Shaidar Digiri na Ɗaya.

    Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kaduna: Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa Na 1. Kaduna: Ɗab’in Fisbas Media Services.

    Gusau, S. M. (2002). Salihu JankiɗI Sarkin Taushi. Kaduna: Baraka Publishes Limited.

    Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na WaƙoƘin Baka na Hausa.Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M (2011). Adabin Hausa A Sauƙaƙe. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Biyu. Kano: Century Research and

    Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). Kano: Published for Bay-Ero University.

    Gusau, S. M. (2015). Audu Karen Gusau. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2016). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa. Littafi Na Biyu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2018). Diwanin Waƙoƙin Baka: Matanonin Wasu Waƙoƙin Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2019). Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Huɗu: Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa

    Ɗankwairo Maradun (1909-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin Maradun Jahar Zamfara. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2020). Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i Na Biyar: Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka. Kano: K.d.G.

    Ibrahim, M.S. (1983). Kowa Ya Sha Kiɗa. Ibadan: Longman Nigeria.

    Sa’id, B (edt) (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Yahaya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA SERVICE.

    Yahaya, A. B. (2001). Salo Asirin Waƙa. Kaduna: FISBAS MEDIA SERVICE.

     

    [1] Kotso abin kiɗa ne na makaɗan sarauta. Ya so ya yi kama da kalangu, amma shi fuska ɗaya kawai ake rufewa, a kuma kaɗa shi da hannu. Sa’idu Faru yana daga cikin sahun makaɗan da suka fi gwanancewa wajen kiɗan kotso. Ƙwararru kuwa sun haɗa da Ibrahim Narambaɗa da  Musa Ɗankwairo.

    [2] [Keɓantacciyar tattaunawa I. Muhammad, 14 ga watan Yuli, 2024] (A lokacin yana matsayin Ɗanmadamin Birnin Magaji)

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken: Zamani Abokin Tafiya: Tasirin Kafafen Sada Zumunta ga Tashin Tashinar Zamfara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Tatsuniyar Naƙuda A Daji

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata mai ciki. Sai wata rana ta shirya za ta yi balaguro. Tana tafiya a cikin daji, sai naƙuda ta kama ta. Sai ta raɓa a ɗan wani wuri ta haihu. Ta ɗauki jinjirin ta kama hanya tana tafiya, ko za ta tarar da wani gida ta huta. Sai ko ta tarar da wani gida a tsakar dokar daji ta shiga.

    Ashe gidan nan na Dodo ne. Sai ko mai jegon nan ta ga ruwa a gidan, ta ɗiba ta yi wanka da shi, ta wanke ɗanta, ta dafa abinci. Sai ta hau kan ɗakin Dodon, ta zauna ta ci abincin da ta dafa. Sai ta ga wata wuƙa a gidan Dodo, ta kuwa ɗauke ta, ta hau kan ɗakinsa ta zauna.

    Can Dodo ya dawo daga farauta, sai ko tsoro ya kama ta, sai ta tsunkuni jaririnta, har ya saki zawayi saboda jin zafi. Zawayin kuwa ya zubo a tafin hannun Dodo yayin da yake zaune a gindin ɗakin yana hutawa, sai ya lashe, ya ko yaba da daɗin abin da ya lasa, sai
    ya ce: “Wannan ai miya ce da gauta.”

    Da ya ɗaga kansa domin ganin daga inda wannan abin daɗi yake zo masa, sai ko suka yi arba da matar nan. Sai ta sake tsunkunin ɗanta, ya yi wata irin ƙara. Da Dodo ya ji, sai ya tsorata, ya shiga daji a guje, ya kira sauran dabbobin dawa domin su zo su ga wata irin halitta da bai saba ganin irinta ba, wai yana so su kore ta daga gidansa.

    Dabbobin suka cika gidan Dodo, to amma ba wanda ya shiga saboda tsoro. Suka ce Giwa ta shiga, ta ƙi; aka ce Raƙumin Dawa, ya ko yarda ya shiga. Da ya kunna kansa ya shiga sai ko matar ta riƙe kan. Da sauran dabbobin suka ga ya jima bai fito ba, sai suka tambaye shi abin da ya riƙe shi. Sai ya ce: “Dodo ne ya riƙe mini wuya.”

    Ita kuwa matar sai ta sa wuƙar ta fara yankan wuyan Raƙumi. Tun suna tambayar Raƙumin Dawa yana magana, har ya kasa magana. Jim kaɗan sai suka ga ya faɗi matacce, ba kai a jikinsa. Ganin haka fa duk suka tarwatse da gudu; Dodo mai gidan ne kuwa a kan gaba. Duk bishiyar da ya ci karo da ita sai ya tuge ta don gudu.

    Da matar ta ji ba sauran motsin dabbobin nan, sai ta sauƙo goye da ɗanta ta kama hanya, ba ta tsaya ko’ina ba sai gidan mijinta. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Banza ta kori wofi.
    • Taron tsintsiya ba shara.
    • Dabara ta fi ƙarfi.
    • Yuyu banza, ƙwaƙƙwara ɗaya ya fi amfani.
    • Dabara ɗaukar ɗaki.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani Sarki Kunkuru, wanda matarsa ta haifi ɗa namiji. Sai ya tara Kunkurayen garin ya sanar da su cewa matarsa ta haifi ɗa. Ya bayyana cewa duk wanda ya san sunan yaron, zai ba shi ’yarsa aure. Sai wani Kunkurun ya je bakin rafi ya ɓuya. Lokacin da ’yar Sarki da ƙawayenta da kuyangi suka je ɗaukar ruwa, sai Kunkurun ya faɗa cikin tukunya ɗaya daga cikin kuyangin, ya ɓuya.

    Bayan ’yar Sarki da jama’arta sun koma gida, kuma wadda ya shiga tukunyarta ta ajiye ruwan, sai Kunkurun nan ya fito, ya ɓuya a bayan ƙyauren ɗakin Sarki. Da Sarki ya shiga gida, sai ya kira matarsa mai jegon jaririn nan da aka haifa, ya ce: “Kin ba Kuturin nono ya sha?”

    Kunkurun da ke maƙe yana jin su, kuma ya ji sunan yaron Kuturin. Sai uwar ta ce da Sarki: “A a, ina dai shirin ba shi yanzu.”Can da Kunkurun da ke bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya ji ƙafa ta ɗauke, sai ya fito, ya gudu. Washe-gari sai Sarki ya tara Kunkuraye, ya tambaye su ko akwai wani da ya san sunan jaririn gidansa.

    Duk wurin aka mutu a ka, ba wanda ya yi magana, sai Kunkurun nan da ya yi dabararl aɓewa a bayan ƙyauren ɗakin Sarki ya nuna alamar yana da magana. Sai Sarki ya ba shi dama, ya tambaye shi sunan yaron. Nan take kuwa Kunkurun nan ya ce: “Ai sunansa Kuturin.” Sai Sarki ya ce: “Haka ne kuwa, ba shakka.”

    Ba tare da wani ɓata lokaci ba Sarki ya cika alkawari, watau aka ɗaura wa ’yarsa aure da wannan talakan Kunkuru da ya faɗi sunan jaririn gidansa daidai. To, amma kuma yarinyar ba ta son Kunkurun da aka ba ta, amma kuma ba ta nuna masa ba. Wata rana ’yar Sarki da mijinta suna hira, sai ya yi suɓur-da- baka ya gaya mata dabarar da ya yi har ta kai ya aure ta.

    Bayanin da ya yi mata ya ɓata mata rai, domin da ma ba ta son sa. Amma fa ba ta nuna masa tana cikin ɓacin rai ba. Washe-gari sai tace da mijinta tana son zuwa ganin gida. Sai mijinta Kunkuru ya amince, amma ya ce kar ta daɗe ta dawo da wuri. Da ta isa gida, sai ta gayawa mahaifinta yadda mijinta ya yi har ya ji sunan ƙanenta, wanda kuma a sakamakon haka ya aura masa ita.

    Da Sarki ya ji bayaninta, sai ya ce mata ta koma gidan mijinta, ya san abin da zai yi. Sai ta koma. Wata rana sai Sarki ya tara duk Kunkurayen da ke fadamu da yake iko da ita, ya ce musu ya yi baƙo, kuma duk wanda ya gaya masa sunan baƙon, to zai ba shi rabin garinsa. Bayan Sarki ya gama jawabi, jama’arsa duk sun koma gida, sai ya umarci dogarai da su shiga fakon duk wanda zai zo ya shiga gidansa, su kama shi.

    Da dare ya yi, sai ga Kunkuru surukin Sarki ya doshi ƙofar shiga gidan Sarki, yana sanɗa. Bai san ana ganin sa ba. Yana shiga zauren farko, sai ko dogaran Sarki suka yi wuf suka cafke shi, suka ɗaure.Da gari ya waye, sai aka kai shi gaban Sarki. Nan da nan labari ya bazu, duk gari aka shiga mamakinsa da jin haushinsa.

    Daga bisani Sarki ya sa aka yanke masa hannaye da ƙafafu, aka kai shi bayan gari aka jefar. Yana cikin halin azabar ciwo a daji, sai Ƙadangare ya zo wucewa. Da Kunkurun nan ya gan shi sai ya kira shi, ya roƙe shi ya ba shi aron ƙafafuwansa, domin ya je kasuwa. Sai Kadangare ya girgiza kai, ya ce: “A a, ba zan iya ba ka aron ƙafafuwana ba.”

    Can kuma Maciji ya zo wucewa, sai Kunkurun nan ya ce da shi: “Maciji, maciji ɗan’uwa, ka ba ni aron ƙafarka mana in je kasuwa, idan na dawo in ba ka kayanka.” Sai Maciji ya yarda ya ba shi, ya ce masa amma fa ya dawo da wuri. Kunkuru ya sa ƙafafuwa ya kama hanya, amma fa bai dawo da wuri ba kamar yadda ya yi wa Maciji alƙawari.

    To a kan haka shi ya sa duk sanda yake cikin tafiya, da ya ji motsi sai ya yi sauri ya maƙe ƙafafuwansa da hannayensa, saboda yana zato Maciji ne ya biyo sawun ƙafafunsa. Wannan rashin dawo masa da ƙafafun da Kunkuru ya ara ne ya sa kowa yanzu yake ganin Maciji yana jan ciki ba ƙafafu. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karya fure take ba ta ’ya’ya.
    • Kayan aro ba ya rufe katara.
    • Mayaudari ƙarshensa asara da nadama da jin kunya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata mata da mijinta, ba su taɓa haihuwa ba. Sai ’yan gaza gani a garinsu suka shiga cewa ita juya ce ba mai haihuwa ba. Irin waɗannan maganganu kuwa sukan dame ta. Wata rana tana dawowa daga gona, sai ta ga wani jariri a gindin gamji. Sai ta ɗauke shi, ta goya, ta tafi da shi gida. Da mijin ya shiga gida, sai ta gaya masa ta haihu a gona.

    Ya yi murna, amma fa da ’yar shakka. Bayan mako guda aka raɗa wa jariri suna Tabi. Daga nan sai ta shiga zaman jego a gida, ta yi kwana arba’in tana cin kaji. Bayanta cika arba’in, sai ta gaya wa mijinta tana buƙatar yarinyar da za ta taimaka mata wajen renon yaron. Mijin kuma ya nemo mata.

    Ashe yaron nan ba mutum ba ne, aljani ne, amma ba su sani ba. Kullum idan mai gidan da matar za su je gona, sai yaron yace: “Iya ki zo mini da ɓera; baba ka zo mini da fara.” Kuma da zarar sun fita daga gidan, sai yaron ya rikiɗa ya zama babban mutum. Tuni kuma ya ja kunnen yarinyar, ya ce mata: “Idan kika gaya wa mutanen nan abin da nakan yi bayan sun tafi gona, to zan kashe ki.”

    Shi ke nan, kullum sai ya sa ta shiga rumbu, ta ɗebo hatsi yasa ta shiga niƙawa, yana yi mata kiɗa da gurmi. Ga waƙar da yakan yi airin wannan lokaci: “Kai Ɗan Tabi, Kai Ɗan Tabi, Ɗan mai gajerar fuska, Wagga mata ba ta haifi ɗa ba, Sai ka sa ta sami Tabi. Tabi, Tabi na me ye?” Da zaran ya ƙintaci iyayen sun kusa komowa gida, sai ya rikiɗa ya koma yaro, kamar yadda suka san shi, ya sa yarinyar ta goya shi.

    Idan suka dawo sai su ba shi ɓeran da farar da suka kamo masa. Kowacce rana sai sun kawo masa ɓera da fara. Ana nan, a kwana a tashi, sai suka lura yarinyar tana ramewa, amma ba su san abin da ke damun ta ba. To, ashe wata tsohuwa maƙwabciyarsu tana ganin duk abin da yake faruwa tsakanin yarinyar nan da ɗan aljanin nan.

    Sai wata rana ta kasa jurewa, ta kira mijin da matar tace da su: “Ku yi kamar za ku gona, sai ku ɓuya a gidana, ku gaabindayaronku yakan yi.” Washe-gari da sassafe suka je gidan tsohuwa, suka sa idonsu a ƙafar danga, suka shiga jira. Jim kaɗan kuwa yaron ya rikiɗa, ya zama babban mutum. Suna gani ya ɗauki yarinya ya jefa ta cikin rumbu. Suna gani ta miƙo masa hatsi, ta fito ta fara niƙa masa.

    Sai ya bugi cikinsa, riga ta fito. Da ya sake bugawa, sai ga hula. Da ya buga a karo na uku, sai ga gurmi. Nan take ya fara kaɗa gurmi yashiga yin wannan waƙar: “Kai Tabi, Kai Ɗan Tabi, Ɗan mai gajerar fuska, Ka ga mata ba ta haifi ɗa ba, Sai ta sa ma ɗa suna Tabi, Tabi na meye.” Sai mijin ya tambayi tsohuwar yadda za su yi.

    Tsohuwar tace da su: “Yanzu ku koma gida; gobe za mu je gidan mai magani.” Washe-gari suka yi kamar sun je gona, suka nemo ɓera da fara suka kai wa yaron. Sai yaron ya ce: “Mama, yau ba ku je gona ba.” Sai ta ce masa sun je, sun gaji shi ya sa ba su samo masa ɓera da fara masu kyau ba. Sai yaron ya ce ba zai ci ba, amma gobe idan sun je gonar su zo masa da fara da ɓera masu kyau.

    Washe-gari suka je wurin tsohuwa ta raka su wurin mai duba. Suka gaya masa duk abin da ake ciki. Ya duba, ya gano cewa yaron nan fa ba mutum ba ne. Da suka tambayi mai duba yadda za su rabu da yaron nan, sai ya ce to su je su sami baƙin rago mai farar ƙafa da gyaɗa da riɗi a soye, da ƙwarya da garin dawa, sai su tafi da su bakin rafi.

    Duk wanda aka aika, to idan ya tafi kada ya sake dawowa, ya je ya hau wata bishiya. Sai suka je, suka nemo duk abin da aka ce, suka kai. Ɗan duba mai magani ya ce su je su ɗauko yaron, su je bakin rafi da shi. Suka sa yarinya mai goyonsa ta goya shi suka ce za su je bakin rafi kamun kifi. Sai ta goya shi, suka tafi.

    Da suka je bakin rafi, sai ɗan duban ya ce ya kamata a fara dafa abinci kafin a kama kifi. Ashe wai suna yi wa Tabi wayo ne, sai matar ta yi kamar za ta hura wuta sai ta ce: “Af, mun yi mantuwa. Mun manta auduga da dutsen hura wuta.” Sai suka cewa yarinyar ta sauke goyon, ta je ta ɗauko musu dutsen hura wutar.

    Sai ta sauke yaron, ta je, ta hau kan bishiya. Da suka ji shiru, sai suka ce tsohuwa ta bi sawun yarinyar ta duba ko lafiya. Ita ma ta je shiru. Sai mijin shi ma ya bi tsohuwa, shi ma shiru. Sai matarsa ta bi sawunsa. Daga ƙarshe dai kowa ya tafi, suka bar yaro da ɗan duba. Shi ma mai duba sai ya yi wa yaro dabara ya tafi ya bar shi. Da yaro ya ji shiru, sai ya yi ta kiran su, amma ina, sai ya ce: “Wato mutanen nan suna so su ci amanata ne.”

    Sai ya juye gyaɗa da riɗi a cikin aljihunsa. Idan ya ɗiba sai ya watsa a bakinsa, sai yace wannan ƙafar wane ne, yana ta bin sawunsu, har ya isa gindin bishiyar da suka hau. Yana ɗaga kansa, sai ga su gaba ɗaya kan bishiyar. Dukansu tsoro ya kama su. Sai ya ce: “Yanzu haka za ku yi min? Na kwanta a gindin bishiya ina hutawata kika zo kika ɗauke ni, kuma yanzu za ki ci amanata? Ki sani idan Allah bai ba ki ɗa ba, to ba wanda zai iya baki shi. Ku sauko ku tafi na yafe muku. Amma nan gaba kada ku ƙara tsintar ɗa, ku ce za ku riƙe.” Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Abin da Allah bai ba ka ba, babu wanda ya isa ya ba ka shi.
    • Zaƙin nema ba ya kawo samu.
    • Tsintattar kyanwa ba ta mage.
    • Idan za ka yi fatan samun ɗa, yi fatan samun nagari.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗankucaka

    Tatsuniyar Ɗankucaka

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana Ɗankucaka ya fita kiwon ragonsa a bayan gari. Ya yi wa rago talala don kada ya shiga gonakin mutane ya yi ɓarna. Bayan la’asar sai ya koma ya kunce ragon, ya hau ya kama tafiya. Da ya isa kusa da gidan Kura, sai rago ya yi kuka. Da Kura ta ji kukan rago sai ta fito da gudu ta kira Ɗankucaka. Da ya je sai tace: “Yaya sunanka ne?” To daman kuwa Ɗankucaka wani hatsabibin yaro ne.

    Wasu ma kan yi masa ganin aljani. Sai ya ce da Kura: “Sunana Ɗankucaka.” Kura ta tambaye shi: “To, Ragon na sayarwa ne?” Sai Ɗankucaka ya ce: “E, na sayarwa ne.” Sai Kura ta ce: “Nawa ne kuɗinsa?” Sai Ɗankucaka ya ce: “Ba da kuɗi za a saya ba; sai dai a yi kokowar kwana bakwai.

    Kuma kokowar a kan dutse nake yinta.” Jin haka sai Kura ta yi dariya ta ce: “Mutanen ƙwarai ma ba su ce za su yi kokowa ba, sai kai Ɗankucaka!” Tana gama faɗin haka sai kawai ta kama Rago ta kashe, ta ɗauki gangar jikinsa ta kai gida suka sha gara ita da ’ya’yanta.

    Washe-gari sai Ɗankucaka ya je wurin Kura suka tafi kokowa. Suka kama kokowa; can Kura ta kayar da Ɗankucaka. Lokacin da za su rabu kowa ya tafi gida, sai Kura ta ce: “Banda wawa, maimakon ka karɓi kuɗi sai ka zaɓi duka?” Ɗankucaka dai bai ce da ita uffan ba. Washe-gari ya sami Kura suka tafi dutsen da suke yin kokowa.

    Gaga-gaga, Kura ta sake kada Ɗankucaka. Da za su rabu kowa ya tafi gidansa sai Kura ta kalli Ɗankucaka ta ce: “Gara ka haƙura da kokowar nan haka, don za ka rasa ranka.” Ɗankucaka dai bai ce komai ba. A ranar kokowarsu ta ukun ma Kura ta kayar da shi. Amma a rana ta huɗu, sai Ɗankucaka ya ɗaga Kura ya doka ta a kan dutse.

    Kayen kuwa ya kiɗima ta. Sai ta ce da shi: “Kai aboki menene haka?” Ɗankucaka ya ce mata: “A lokacin da kika ƙwala ni da ƙasa na yi magana ne?” Kura ta ce: “A a, a gaskiya ba ka yi magana ba.” Da Kura ta isa gida daga fagen kokowarta da Ɗankucaka, sai tace da ’ya’yanta: “Duk wanda ya zo nema na gobe ku ce na yi tafiya, ba zan dawo ba sai bayan kwana biyar.”

    Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura domin ta fito su tafi kokowa. Ashe ta shiga rumbu ta ɓuya, amma ’ya’yanta suka ce tayi tafiya. Ɗankucaka ya ce: “Na ji ta yi tafiya; amma daman tace idan na zo in ɗauki rumbu in tafi da shi.” Sai ’ya’yan suka ce: “To, ɗauki mana.” Ba tare da ɓata lokaci ba, sai ya ɗauki rumbu.

    Sa’adda ya je bakin ƙofa, sai ya yi wurgi da rumbun. Kura ta buge ƙugunta; ba ta san sanda ta ce: “Wayyo!! Mene ne haka aboki?” ba. Da Ɗankucaka ya ji haka sai ya ce: “Na gaji ne saboda nauyinki; ina hutawa ne. Ashe kina nan, kika ƙi fitowa mu je kokowa?” Tun da an gane, kan dole ta yarda suka je fagen kokowar.

    Da suka kama kokowa kici-kici, sai ya ɗaga Kura sama, ya yi juyi da ita, sannan ya maka ta a kan doron dutsen nan. Kayen ya kai kaye, kuma jikinta ya yi tsami fiye da kullum. A rana ta shida sai Kura ta ɓuya a cikin zana. Da Ɗankucaka ya biya mata domin su tafi fagen fama, sai ya ce ya je ne ya ɗauki zana.

    Ba tare da wani musu ba ’ya’yan Kura suka ba shi zanar da uwarsu ta maƙe a ciki. Da ta lura ya je bakin ƙofa, sai ta ji tsoron kada ya yi jifa da ita. Sai tace: “Abokina daure ka ajiye ni a hankali, kada ka yi jifa da ni irin na jiya.”Da Ɗankucaka ya ji maganarta sai ya ce: “Ashe kina nan?” Ba su zame ba sai a wurin kokowarsu.

    Ɗankucaka ya sake yi wa Kura mummunan kayen da bai taɓa yi mata kamarsa ba; duk kanta ya farfashe. Da ta isa gida, sai ta gudu daga gidanta, ta tafi gidan kawunta. Tana isa sai ta tarar da ɗan kawunta mai suna Goshi. Ta tambaye shi: “Goshi, ina babanka?” Sai yaron ya ce: “Babana yana nan, amma kin san ba a tashinsa daga barci sai da wani babban dalili, kuma idan ana son ya tashi sai an nemi zugazugai an sa a ƙarƙashinsa, an haɗa wuta kamar ta maƙera.

    Zafin wannan wuta ne zai tayar da shi.” Yana gama yi mata bayani ta ce: “Goshi, abin da ya kawo ni fa babban abu ne.” Goshi ya dubi Kura ya ce: “Wane abu ne kuwa wannan?” Sai Kura ta gaya masa yadda suka yi da Ɗankucaka, kuma ta nuna masa kanta, duk ta ji ciwo. Sai Goshi ya ce: “Ai idan dai wannan ne, ai ko ni zan yi miki maganinsa.”

    Shiga gida a shafa miki magani.” Goshi ya koma bakin ƙofa ya zauna, yana jiran ya ga wanda zai zo. Washe-gari Ɗankucaka ya je gidan Kura, ya tambayi ’ya’yanta inda take; suka ce masa ta yi tafiya. Sai ya fita ya fara bin sawun Kura, har sawunta ya kai shi gidan kawunta.

    Da ya isa, sai ya tarar da Goshi a kofar gida. Sai ya tambaye shi: “Kura tana nan ne?” Goshi ya sanar da shi Kura tana nan, kuma ya tambaye shi: “Me ya faru ne?” Ɗankucaka ya ce masa: “Ina son ta zo mu je mu ƙarasa kokowarmu ne.” Ba tare da tunani ba, Goshi ya ce: “Na sayi kokowar. Mu je ka yi da ni.”

    Sai Ɗankucaka ya ce: “A kan dutse muke yi fa.” A cikin fushi Goshi ya ce da Ɗankucaka: “Ko a kan ƙarfe ne na karɓa.” Suka tafi. Da fara kokowa Ɗankucaka ya Ɗaga Goshi ya danƙara da ƙasa. Goshi ya ji zafin kayen nan ƙwarai. Shi ma ya zabura, ya ɗaga
    Ɗankucaka, ya maka shi da ƙasa kan dutsen nan. Kayen ya razana Ɗankucaka.

    To amma sai suka ci gaba da fafatawa. Can Ɗankucaka ya sake kayar da Goshi. Da ya ga Goshi a ƙasa, sai yace: “Dutse buɗe.” Dutse ya tsage, Goshi ya faɗa ciki.” Goshi ya yi wa dutse magana, wani hayaƙi ya turnuƙe, sai ga Goshi ya fito. Suka sake kama kokowa. Da Goshi ya yi wani gwauron numfashi, ya cicciɓi Ɗankucaka, ya yi sama da shi ya maka shi da ƙasa a kan dutsen nan, bai ko shura ba ya mutu.

    Goshi ya ɗauki Ɗankucaka ya je gida, ya feɗe shi, ya dafa suka cinye namansa, amma ya shanya fatarsa. Ba a ba Kura naman Ɗankucaka ba, saboda yaminsa ya fi nata ƙarfi. Bayan ’yan kwanaki sai kitsen fatar Ɗankucaka da ke rataye ya fara narkewa yana ɗiga ƙasa.

    Aka gaya wa Kura duk kwaɗayin da zai kama ta, kada ta kuskura ta taɓa fatar. Kwanci-tashi, wata rana Kura ta zo wucewa sai ta ga mai yana ɗiga daga jikin fatar nan, sai ta ce: “Ga daɗi, amma an ce kada in ci. Amma bari in taɓa kaɗan.” Sai ta sa harshe ta lashi man. Nan da nan wasu dogayen farata masu kaifi da tsini suka bayyana a jikin fatar, suka datse harshen Kura.

    Zafi ya kama ta. Sai ta ƙwala ihu. Da Goshi ya ji haka, sai ya fito ya ce: “Me ya faru?” Sai ta ce: “Fatar nan ce ta yi farata, ta kama ni za ta kashe.”Da ya ji haka sai ya gane Kura dai ta taɓa man da ke ɗiga ne. Daga baya sai Goshi ya ɗinka jaka da fatar Ɗankucaka.

    Wata rana zai fita farauta sai ya ba Kura jakar ta rataya domin ta raka shi. Suna cikin tafiya sai jaka ta yi farata. Faratan suka kama Kura. Sai ta ƙwala ihu. Sai Goshi ya karɓi abinsa ya riƙe, suka shiga daji. A cikin dajin, sai Goshi ya ce: “Wuta, wuta daji!” Daji ya kama da wuta.

    Ɓeraye da gafiyoyi da sauran ƙananan dabbobi suka fito. Sai Goshi ya dube su ya ce: “Duk ku gasu.” Nan da nan suka gasu. Ya ce: “Tuwo fito.” Sai ga tuwo masaki-masaki. Sai Goshi ya ce da Kura: “Fara ci.” Kura ta ce: “A a, kai dai fara. Ai kai ne babba.”
    Sai Goshi ya fara cin naman nan da tuwo. Kafin a ƙifta idanu, ya cinye komai. Mamaki ya kama Kura.

    Sai ta tambaye shi: “Yaya ka cinye duka ba ka rage mini ba?” Sai ya ce: “Ai ke ce ba ki yi magana ba.” Daga ƙarshe dai haka suka kama hanyar gida. Shi a ƙoshe, Kura na jin yunwa. A kan hanya ne suka je bakin wani rafi. Sai Goshi ya dubi ruwan ya ce: “Kifaye ku zo ku taru in kama.” Nan take kifaye suka taru.

    Ya ba Kura dama ta kwashi kifaye ta ci. Ta ƙi, wai shi ne babba. Shi kuwa sai ya kama kifayen ya cinye su baki ɗaya, ko ƙaya bai bari ba. Haka suka ci gaba da tafiya. Sannu a hankali suka isa daidai wata kuka mai ’ya’ya da yawa, amma ba abin kaɗo su. Sai Goshi ya ce da Kura ta ba shi cinyarta ɗaya ya kaɗo ’ya’yan kukar da ita.

    Tun kafin ta yi magana sai ya fizge mata cinya ɗaya, ya jefa, ’ya’yan kuka suka zubo birjik. Ya sha kukar nan ta yi masa karo. Ya ɗauki cinyar Kura ya maƙala mata, ta zauna kamar ba a taɓa cire ta ba. Mamaki da tsoro suka rufe Kura. Da haka dai suka isa gida. Washe-gari sai Kura ta je ta sami abokinta Kurege, ta ce da shi: “Yau za mu je farauta, amma kar ka ɗauki gayan tuwo.”

    Amma Kurege da wayonsa ya ɗauki gayan tuwo ya jefa a jakarsa. Sai Kura ta ce kar ya ɗauki fartanya. Amma sai Kurege yasa ƙaramin magirbi a cikin jakarsa. Ta ce ko dutsen hura wuta kada ya ɗauka. Amma duk abin da ta ce kada ya aikata, sai da ya yi. Suna isa daji Kura ta ce: “Wuta, wuta daji. Daji bai kama da wuta ba. Da ta yi ta gaji, sai ta ce da Kurege, “Mene ne abin da za mu yi?”

    Sai ya ce da ita: “Ko da yake kin hana in zo da dutsen wuta, na zo da wani da na gani a jakarki.” Ta yi murna. Suka yi ƙyastu da dutse, wuta ta tashi a daji. Kura ta ce da ɓeraye su fito, amma ko gashi ba su gani ba. Ta nemi shawarar Kurege. Shi kuwa ya tuna mata: “Ai kin ce kada in zo da magirbi.” Kura ta ce: “Je ka ɗauko mana.”

    Don kada ya wahala, sai ya fito da wanda ke cikin jakarsa. Kura ta amsa, ta yi ta tonon ramukan ɓeraye, amma ba su samu da yawa ba. Ta ce da ɓeraye su gasu, amma ba abin da ya faru. Ta rasa yadda za ta yi. Amma sai Kurege ya taƙaita musu wahala, ya fito da dutsen ƙyastu, ya buga shi, wuta ta kama. Da haka dai har duk abubuwan da ta ce kada ya ɗauko daga gida suka yi amfani.

    Ba tare da wata-wata ba, Kura ta kama nama da ci. Kurege dai bai ce komai ba. Amma idan ya faki idonta, sai ya ɗauki gasasshen ɓera ya jefa cikin jakarsa. Da haka ya tara abinda zai je gida da shi, ko da yake ba ta bari ya ci ba. Duka abubuwan da Goshi ya yi sanda ya fita farauta da Kura, sai da ta yi irinsu tare da Kurege. Amma shi yana fakar idonta ya ɓoye irin abubuwan da ta riƙa ci tana hana shi, har suka isa bishiyar kuka.

    Da suka je bishiyar kuka, sai Kura ta ce wa Kurege: “Ka kwanta in cire cinyarka in jeho mana kuka da ita.” Sai Kurege ya ce: “Haba Kura. Haka bai dace ba.” Sai Kura ta fusata ta ce: “Ka yarda da abin da na ce, in ka ƙi kuwa in kashe ka, in ciri cinyar in yi abin da nake so da ita.” A kan dole Kurege ya kwanta, ta tuge cinyarsa, ta jefi kuka da ita.

    Sai cinyar ta maƙale. Da Kurege ya ga haka sai ya fara ƙaraji, yana hargowa. Can dai ya yi sa’a, iska ta kaɗa cinyar ta faɗo. Kura ta ɗauko cinya wai za ta maƙala wa Kurege. Idan ta sa nan, sai ta ƙi zama, ta ce ta yi yawa ne. Sai ta riƙa cin naman cinyar da nufin rage mata girma, domin ta yi daidai.

    Da haka har cinyar tarage saura kaɗan; sai ga Goshi. Kukan Kurege ne ya jawo shi. Sai
    ya tambayi abin da ya sa Kurege kuka. Kurege ya yi masa bayani. Goshi ya tambayi Kura nata bayanin. Kura ta ce Kurege ya faɗi gaskiya. Sai Goshi ya yi wuf ya cafke Kura, ya kashe ya cinye. Daga nan kuma ya nemo wata cinya ya maƙala wa Kurege, ta zauna. Da
    aka sa wa Kurege cinya, sai ya tashi, ya ruga a guje bai sake komowa kusa da inda ya saba haɗuwa da Kura ba. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
    • Azzalumi a ƙarshensa jin kunya ko wahala.
    • Kura dirungu sha duka.
    • Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Furera Da Gungume

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya sunanta Furera. Wata rana ita da ƙawayenta suka je daji neman itace, sai ta ga wani gungume tace za ta ɗauka, amma suka hana ta. Ta kafe faufau ita sai ta ɗauka. Ta ɗauka, ta tafi da shi gidansu. Ya zamana a gidan suna dadabbobi da yawa, kamar shanu da tumaki da awaki da jakai, har ma da alfadari.

    Furera ta ajiye gungume a tsakar gida. Can sai gungume ya kama waƙa yana cewa:

    “Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci.”

    Wannan abu ya ba Furera mamaki, sai ta je ta yi wa babanta irin waƙar da gungume ke yi. Sai mahaifinta ya ce: “Ki ba shi kaza ya ci.”Furera ta kama kaza ta ba gungume. Da aka ɗan jima kuma gungume ya sake komawa kan waƙarsa:

    “Nama, Furera nama, in ci,

    Nama, Furera nama, in ci

    Nama, Furera nama, in ci.”

    Furera ta garzaya ga mahaifinta ta ce: “Baba, baba, ka ga gungumen nan ya sake cewa in ba shi nama.” Mahaifinta ya ce: “Ki ba shi akuya.” Furera ta ba shi, ya lankwame nan take. Da haka ɗaya bayan ɗaya har dabbobin gidan suka ƙare, iyayen Furera kuwa suka gudu don kada gungumen yace zai cinye su.

    Gungume kuma ya sake waƙar neman nama, amma ba sauran dabbobi a gidan, sai Furera. Ta rasa yadda za ta yi. Gungume kuwa maitarsa ta motsa, sai kawai ya mirgina inda Furera take, ya haɗe ta, ya cinye. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Wanda bai ji bari ba ya ji hoho.
    • Mai rabon shan duka, sai ya sha.
    • In ajali ya zo, ko babu ciwo sai a tafi.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Tatsuniyar Dawi Mai Turmi

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can wata ’yar unguwa da ke dab da wani tsauni, an yi wasu’yan biyu, Awa da Dawi. Tun suna yara mahaifiyarsu ta rasu, suka ci gaba da taimakon juna. To, amma shi Dawi hatsabibin yaro ne, kuma duk sanda ’yar’uwarsa Awa ta dafa abinci, sai ya cinye. Kullum ana haka har ta kai sai da ta tona rami domin ta riƙa ɓoye rabonta na abincin a ciki, amma sai ya tono ya cinye.

    Wata rana Dawi ya ce da Awa: “Ni fa na gaji da zaman garin nan. Ina so ki goya ni mu yi ƙaura mu je mu zauna a wani gari inda za mu sami kwanciyar rai.” Bayan Awa ta yi ɗan tunani, sai ta amince, ta goya shi, kuma ta ɗauki ’yan tarkarcensu a ka, suka kama hanya.

    Suna cikin tafiya sai Awa ta ce: “Na ga inda za mu tafi yana da nisa kuma ga shi ina jin yunwa.” Can sai Dawi ya hango wani ɗaki a gefen hanya, ya ce su shiga ciki. Da suka shiga, sai suka tarar da abinci a ciki. Dawi ya ce: “To ga shi Ubangiji ya ji kukanmu, ai sai mu ci.”

    Ba da wata-wata ba sai Awa ta yarda. Suka cinye abincin nan duka, duk da yake ba su san mai shi ba. Suka sha ruwa, suka sake kama hanya. Suna tafiya har suka isa wani
    gari. Dawi ya ce: “Albishirinki, ni fa ina da wata dabara.” Awa ta ce: “Kawo ta mu gani.” Sai kawai Dawi ya tara yaran garin nan ya ce shi fa ɗan dabo ne, kuma zai yi wasanni iri-iri domin ya ɗebe musu kewa.

    Daga nan sai ya ce a kawo turmi, domin ya yi musu wasan daka mutum irin yadda ake yi a garinsu. Dawi ya fara shiga turmi, yara suka daka shi, kuma ya fito jiki lafiya lau. Wani daga cikin yaran ma ya shiga, aka daka shi, amma sai ya fito da jikinsa jina-jina. Da yaran suka ga haka, sai wasu daga cikinsu suka tsere.

    Sauran da suka tsaya kuwa, sai suka riƙa shiga turmi ɗaya bayan ɗaya ana laƙada su, suna fita jiki a kumbure. Da mutanen garin suka ga abin da yake faruwa da yaransu, haushi ya kama su, suka yi ca a kan Awa da Dawi. Dawi ya ce da su: “Don Allah ku dakata.

    Idan kun yi haƙuri, za ku ga abin mamaki.” Mutanen suka tsaya, suna jira su ga abin da Dawi zai yi. Sai ya yi wani irin siddabaru na hatsabiban yara, nan take duk yaran da aka yi wa rauni a turmi suka warke sarai. Mamaki ya kama jama’a, suka ce sai shi da Awa su zauna a garin nan tun da suna da abin mamaki da asiri haka.

    Suka yarda. Suka zauna a garin. Dawi da Awa suka girma, ya zama sadaukin matashi. Awa kuma ta zama kyakkyawar mace, son kowa. Dawi ya kama noma da farauta. Ya tara dukiya mai yawa kamar ba maraya ba. Ita kuma ta zauna da shi suna cin duniyarsu.

    Mutanen gari suka yi wa Dawi laƙani: “Dawi Mai Turmi.” Shi kuma yakan ce: “In da mai son mu daka shi ya zo.” Duk sanda ya faɗi haka sai a bushe da dariya, labarinsa ya bazu a duniya. Shi yasa ma kuke jin duriyarsa a taskar tatsuniyoyi. Kurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.
    • Tausasa wa ɗan’uwa shi ma wani jari ne.
    • Kar a yi saurin yanke hukunci ga abin da ba a san haƙiƙaninsa ba.
    • Arziƙi a ƙafa yake.
    • Motsi ya fi zama

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano

    Edita@rumasau-kallamu