Tatsuniyar Jika Da Kaka

0
17

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can wani ɗan ƙauye da ke kusa da Gulbin Tattabaru, an yi wata yarinya da ke zaune tare da kakarta. Rannan yarinyar tana shara sai ta tsinci kurkunu ta bai wa kakarta ta ajiye mata. Da ta gama sharar sai ta je wurin kakar ta tambaye ta: “Kaka, ina kurkununa?” Kakar ta dubi jikarta ta mayar da jawabi: “Ai na cinye, jikalle.”

Da jin wannan amsa sai yarinya ta fusata; ta ƙura wa kakar ido tace: “A gaskiya kaka ban yarda ba.” Daga nan ta ɗauki buta, ta cika ta da ruwa; ta kama wata kuka ta haye; ta yi zamanta ba niyyar saukowa. Da kakarta ta ga ya kamata ta sauko ta ci abinci, sai ta je kiran ta.

Yarinya abu kamar da wasa, sai ta ƙi saukowa kakar ta kira maƙwabta da ƙawayen jikarta domin su sa ta ta sauko, ammaina, abu ya faskara. Sai ta ce da wasu samari: “Don Allah ku taimaka ku sare mini kukar nan tun da jikata ta ƙi saukowa.” Samari suka yarda suka debo gatura daga gidajensu.

Kowa ya yi ɗamara suka fara saran kuka. Suna waƙar gayya, wannan ya sara idan ya gaji wannan ya karɓa, da haka da haka har suka ci ƙarfin kaurin bishiyar. Can da kuka ta nuna layin faɗuwa, sai kawai aka ga yarinyar ta fara rikiɗa, har ta zama kurkunu. A halin haka sai ta haifi ’ya’ya da yawa.

Kuma nan take ta sake rikiɗa, ta koma mutum a kan bishiyar. Kowa ya buɗe baki sai kallon abin al’ajabi yake yi. Sai ta ce da kakarta da sauran mutanen: “Ga kurkunu nan da yawa ku ci ku ƙoshi, amma ki rage mini guda ɗaya kawai; daga nan sai ki koma gida, zan sauko.”

Da kowa ya bar wurin, sai yarinya ta sauko ta kama hanyar gida. Tana isa gida sai ta yi wa kakarta bayani cewa: “Ai aljanun da ke zaune a kukar nan ne suka hana a sare ta, saboda haka ne ma suka rikiɗar da ni har na haifi kurkunu domin ki dawo min da shi a ƙyale musu gidansu.

Kuma sun ce in gaya miki ki gaya wa Mai Gari kada a sake ƙoƙarin sare wannan kukar.” Kakar yarinya ta yi mamakin wannan bayani, kuma ba ta yi nawa ba ta je ta sanar da Mai Gari saƙon da aljanu suka aiko ta hannun jikarta. Shi kuma Mai Gari ya sa aka sanar da jama’arsa cewa kada wani ya kuskura ya sare kukar nan domin gidan mutanen ɓoye ne, abokan zaman lafiyarsu. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Wasa tsakanin jika da kaka ba abu ne mai kawo ɓacin rai ba.
  • Wasu mutan ɓoye abokan zama ne ba abokan faɗa ba.
  • Komai za ka yi ka yi tunani kafin ka aikata shi.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar ’Yan Matan Fangama

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMaƙala Mai Taken: Hoton Waibuwar Hausawa a Cikin Waƙoƙin Mamman Shata
Labarin na GabaTatsuniyar Zinari A Bakin Kwano
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.