Ga ta nan, ga ta nanku.
Tasalla mace ce wadda ke zaune a wani kauye mai suna Saladuna. Tana kiwon wani kifi babba. Ta daɗe da wannan kifin, har sun saba da juna. Tasalla tana ciyar da kifin a kullum gwargwadon ƙarfinta. Saboda sabon da suka yi da juna, har yakan riƙa yin tsalle cikin wasanni da ita.
Wata rana Tasalla ta yi tafiya, sai mutanen ƙauyen suka kama kifinnan suka cinye. Kowa ya ji daɗin naman kifin. Da Tasalla ta dawo sai ta nemi kifinta ko sama ko ƙasa, ya ɓace. Ta yi ta tambaya da cigiya ko ta ji wani abu game da kifin, amma ba ta sami bayani daga bakin kowa ba.
Nan take ta shiga kukan takaici. Wannan ya sa ta yi wani siddabaru da ya ƙarar da ruwan garin, kowa ya rasa ko da ruwan wanke ido, balle na wanka da girki. To amma akwai wani mutum ɗaya da Tasalla ke jin nauyi, kuma tana matuƙar ƙaunarsa.
Sai aka turo mata shi domin ya roƙe ta, ko za ta warware siddabarun da ta yi suka rasa ruwan sha. Ga irin abin da yake cewa da ya tunkari inda take:
“Tasalla, Tasalla, Ki ji tausayina,
Ki sam min ruwa in sha.
Ki ji tausayi na, Ki sam min ruwa in sha.”
Sai ta mayar da jawabi tana tambaya:
“Wane ne yake neman ruwa?
Wane ne yake neman ruwan sha?”
Sai mutumin ya ce: “Ni ne masoyinki, Ni ne nake roƙon ruwa in sha.” Tasalla ba ta amince ba. Tana fushi a kan cinye mata kifi, saboda haka ta hana mutumin ruwa. Sarkin garin da fadawansa suka ɗunguma suka je roƙon ta, amma ta ƙi sauraronsu. Ba yanda ba su yi ba, amma ta ƙi.
Sai can uwarta ta zo ita kaɗai ta roƙe ta ruwan sha. Saboda ƙaunar da take yi wa uwar, sai ta daina fushin da take yi. Nan take ta warware siddabarun da ta yi, ruwa ya samu kowa ya wadata da shi. Daga bisani mutanen garin suka zo suna ba Tasalla haƙuri, kuma suka amince lallai sun yi mata laifi da suka cinye mata kifi.
Duk mutanen garin suka ɗauki alƙawari za su nemo mata wani kifin. Bayan ‘yan watanni suka samo mata wani kifin. Sabon kifin yana da ruwan zinari, kamar dai wanda aka cinye; wannan yasa zaman lafiya tsakaninta da su ya tabbata. Kifin ya girma, kuma ya dinga hayayyafa. Daga ƙarshe dai har kifin ya zama ya wadaci mutanen garin.
Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Soyayya da tausayi a rayuwar duniya ya haɗa da zaman mutum da halittar Allah ga baki ɗaya.
- Soyayya tsakanin ɗa da iyaye tana da ƙarfi ƙwarai fiye da yadda mutum ke zato.
- Ɗaukar abin wani ba da izininsa ba zalunci ne.
- Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna na don karanta Tatsuniyar Kwaɗayi Mabuɗin Wahala
Edita@rumasau-kallamu










