Ɗan Kutungayya

0
6

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani mutum da ke zaune awani gari mai suna Raƙumawa tare da matarsa da ’ya’yansu su goma sha ɗaya. Rannan sai matar ta haifi ɗa namiji, ya zama na goma sha biyu. Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana ya ce wa uwarsa: “Kada ma a yi wahalar raɗa mini suna, domin sunana Ɗankutungayya.”

Ya ƙara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinƙa hawa. Iyayen suka yi haka, jama’ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana yayyen Ɗankutungayya suka shirya za su gidan wata mata da suka saba zuwa gidanta hira da ’ya’yanta su goma sha biyu.

Sai Ɗankutungayya ya ce zai bi su amma babban wansu ya hana shi bin su. Amma ya bari sai da yayyen suka tafi, sai ya bi su a baya. Da isarsu gidan, sai matar ta yi musu maraba; ta yi musu shimfiɗa, suka zauna; ta kawo musu abinci mai daɗi suka ci, suka fara hira. Amma fa duk zuwan da suke yi gidan ba su san cewa matar nan dodanniya ce ba.

Suka zauna suna ta hira kamar yadda suka saba kullum. Kuma duk sanda suka yi barci a gidan, Dodanniyar kan tashe su, su tafi gida. Ashe duk wannan dabara ce take yi don su saki jiki da ita, wata rana ta cinye su. Kuma tuni ta yi tanadin manyan tukwanen dafa su, ta sha romo.

To a daren da suka je tare da Ɗankutungayya ma, duk sauran sun yi barci in ban da shi. Can cikin dare sai ya ji ana wasa wuƙa sai ya ce a ransa: “A a, lafiya kuwa?” Sai ya kwanta ya yi kamar yana barci. Da aka ɗan jima sai ga Dodanniya tana sanɗa, har ta shiga wajen yara.

Ɗankutungayya yana kallon ta, tana riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙa sai ƙyalli take yi. Da ya ga lallai ta nufi yayyensa, sai ya yi tari da ƙarfi. Da ta ji tarinsa, sai ta koma da sauri. Da aka jima, sai ta sake dawowa; shi kuwa Ɗankutungayya ya ƙara yin tari, ta koma. A zuwanta na uku ne fa da ta ji tarin Ɗankutungayya, sai ta ɓoye wuƙa ta leƙo ta ce: “Kai ɗan samari ba ka barci ne?

”Sai ya ce: “Ai ni ba na barci in ba a kan rairayin ƙorama mai sanyi ba.” Da ta ji haka, sai ta ɗauki masaki ta tafi neman rairayin ƙorama. Kafin ta dawo sai Ɗankutungayya ya fito da wata ’yar batta, ya buɗe bakinta, ya zazzago wani magani, ya matsa kusa da wutar da ta hura, ya barbaɗa maganin nan a cikin wutar, sai wani hayaƙi ya tashi.

Da ’ya’yan Dodanniya da yayyensa suka shaƙi wannan hayaƙi, sai barcin da suke yi ya ƙara nauyi. Nan da nan Ɗankutungayya a cikin sauri irin na hatsabiban mutane ya bi ya tuɓe wa ’ya’yan Dodanniya kayan jikinsu, ya sanya wa yayyensa. Kuma ya tuɓe wa yayyensa nasu kayan, ya sanya wa ’ya’yan Dodanniya.

Da ya gama wannan aiki sarai, sai ya kwanta, ya shiga jira. Can sai Dodanniya ta dawo, ta kawo rairayi ta ba Ɗankutungayya. Sai ya ce: “Yawwa, iya; na gode. Yanzu zan yi barci.” Da aka jima sai Dodanniya ta dawo da wata sharɓeɓiyar wuƙarta a hannu, ta iske Ɗankutungayya ya yi barci.

Nan da nan cikin gaggawa da ƙeta ta bi duk ’ya’yanta ta yanke, tana zaton samarin da sukan je hira gidanta ne. Amma ba ta yanka Ɗankutungayya ba, saboda ta ga shi ƙarami ne. Ta ƙyale shi, da nufin ta kiwata shi ya yi ƙiba. Da Dodanniya ta fita za ta fara shirin kwashe naman da take zato ta samu, sai Ɗankutungayya ya zaro battar nan tasa ya sake barbaɗa garin maganin nasa a kan wuta.

Kafin kifta ido, hayaƙi ya murtuke ɗaki. Cikin gaggawa ya tashi yayyensa, ya gaya musu abin da ya faru, kuma ya ce su yi maza-maza su gudu gida. Ya ce shi zai bi su da gari ya waye, kada su jira shi. Take suka sulale, suka gudu. Da gari ya waye, sai Dodanniya ta zo za ta fara tattara waɗanda ta yanka, a zatonta ’yan’uwan Ɗankutungayya ne.

Yana ganin ta sai ya kaɗa battarsa, sai ga ragonsa ya zo ya harari Dodanniya, yana yi mata kallon raini ya ce: “To, waɗannan fa ’ya’yanki ne kika yanka. Ba ’yan’uwana ba.” Da ta lura da haka, sai ranta ya ɓaci ta yi wani ƙaraji, ta yi wuf ta kai masa bara za ta cafke shi, sai ya bauɗe.

Ta sake rarumo shi, amma sai ya ɗare bayan ragonsa. Rago kuwa kamar ya san zancen, sai ya kama sukuwa kamar walƙiya, ya tsere mata fintinkau ya bar ta sororo a cikin baƙin ciki. Dodanniya ta ɗauko ɗan magurjinta na tsafi ta bi ’ya’yanta tana buga wa kowannensu a kai.

Nan da nan namansu ya zama na tumakai, ta soye suka cinye ita da autarta. Daga nan ta yi alƙawari sai ta rama ƙetar da Dankutungayya ya yi mata. Bayan ’yan kwanaki, sai Dodanniya ta je bakin garin su Ɗankutungayya ta rikiɗe ta zama kanya kuma ta kwanta ’ya’ya da yawa, har sun kusa nuna.

Da yaran gari suka ga kanyar sai suka yi murna. Da ta nuna, sai wasu daga cikinsu suka dinga kaɗo ’ya’yan suna sha. Har dai wata rana yara da yawa suka hau kanta suna ɗiba. Da Dodanniya ta ga haka sai ta tashi sama da su, ba ta tsaya ba sai a gidanta. Nan da nan ta gaya wa autarta cewa nama ya samu.

Sai ta umarce ta da ta wanke tukwane. Tana kuwa cikin wanke tukwane sai Ɗankutungayya ya ji labarin abin da ya faru, sai ya rikiɗa, ya zama ɗanmaraki, ya je gidan Dodanniya. Da zuwansa sai ya fara cin shuke-shuken da ke gidan, watau dai yana yi mata ɓarna. Yana cikin wannan ɓarna sai Dodanniya ta ce wa yaran da ta sato, su je su kori ɗan marakin mai yi mata ɓarna.

Da ya ga sun doshe shi, sai ya ƙi gudu; amma da suka zo dab da shi, sai ya ɗan gudu ya ɗan matsa gaba kaɗan kuma ya ci gaba daɓarna. Yara kuma suka ɗan matsa kusa da shi, ya ɗan ƙara gaba kaɗan. Haka dai ya dinga jan su, har sai da suka yi wa Dodanniya nisa. Sai ya rikiɗa ya zama mutum, ya ce da yaran nan su hanzarta su gudu.

Ya jaddada musu cewa idan ba su gudu ba, Dodanniya za ta cinye su. Da suka ji haka, sai suka sheka da gudu, suka koma garinsu, suka gaya wa iyayensu abin da ya faru. Shi kuwa Ɗankutungayya sai ya hau ragonsa, ya koma gidan Dodanniya. Da ya tabbatar ta gan shi, sai ya yi mata gwalo ya ce mata: “Na kuɓutar da yara daga sharrinki, sun koma wurin iyayensu.

Ni ne Ɗankutungayya na yi miki gayyar tawa, wadda ba za ki iya ramawa ba har abada.” Wannan abu da Ɗankutungayya ya yi wa Dodanniya da maganar da ya gaya mata, suka sa ta shiga tunani da ƙulla yadda za ta ɗauki fansa a kansa. Ana nan, sai Dodanniya ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawar gaske, ta ɗauki wani adudu ta je cin kasuwa.

Masoya suka yi ta kanta, kowa yana so ya aure ta amma ta ce ba wanda za ta aura, sai wanda ya buɗe wannan adudun. Samari da yawa suka gwada, amma duka suka kasa. Bayan ’yan kwanaki, har samari sun fidda rai, sai ɗaya daga cikin yayyen Ɗankutungayya ya ji labari, ya bincika inda take a kasuwa ya je kuma ya gan ta, sai ya ji yana son ta.

Ita kuma Dodanniya ta gane shi, saboda haka sai ta yi tsafi ta yadda idan ya gwada buɗe adudun zai buɗe. Da zuwansa kuma ya gwada sai adudun ya buɗe, mutane suka yi ta mamaki, shi kuma ya yi murnar samun kyakkyawar mata. Aka ɗaura aure, ba ta jima ba ta tare a gidansa.

Amma bayan ’yan kwanaki sai ta ƙwakwale wa mijin ido ɗaya, ta tafi da shi ta bar shi da jinya. Ɗankutungayya da jin wannan aika-aikar ya tabbatar da cewa Dodanniya ce. Don haka ya ƙudiri aniyar sai ya ɗauko fansar abin da ta yi wa yayansa. Sai ya rikiɗa ya zama Bafulatana, ya ɗauki nono, ya je gidanta talla.

Da isarsa sai autar Dodanniya ta fito ta saya. Shi kuma ya yi mata araha. Kullum sai ya kai tallar nono, Dodanniya ba ta gane gogan ne ba. Da haka har Dodanniya ta saba da Bafulatana ƙwarai da gaske. Wata rana sai Bafulatana, watau Ɗankutungayya ya zo gidan Dodanniya a fusace.

Dodanniya ta tambayi Bafulatana dalilin fushinta, sai ta ce: “Wani mutumwai shi Ɗankumale yake zuwa yana kashe musu shanu. Ga shi yanzu duk sun kusa ƙarewa.” Dodanniya ta ce: “Ke ba sunansa Ɗankumale ba, sunansa Ɗankutungayya. Mugun mutum ne.

Ba shanunku kaɗai ba, ku kanku ma ku yi hankali da shi. Ni ’ya’yana goma sha ɗaya ya sa na kashe. Kwanan nan ma na kusa makantar da ɗan’uwansa. Kin ga idon yayansa da na ƙwakule.” Sai Bafulatana ta ce: “Tir, da ganin idon lalatacce.” Sai Dodanniya ta ce: “Yau saura kwana uku ma in ba kyanwata idon mugun ta cinye.”

Bafulatana ta ce: “Kash, da idon nan zai yi wa ƙanena daidai da kin ba ni shi. Shekaran jiya saniya ta harbi idonsa ɗaya ya fashe ya tsiyaye.” Cikin ɗoki da ƙeta Dodanniya ta ce: “Af, don wannan ai sai in ba ki.” Da jin haka sai Bafulatana ta yi farat ta ce: “Ai ko na gode.” Dodanniya ta ƙara yi wa Bafulatana gwaninta, sai ta gaya mata yadda za ta sa masaidon ta ce:

“A nemo ƙwaiƙwayen kifi guda bakwai da hantar baƙin kare, da ƙiyashi guda bakwai da ƙaucin maƙe, a shanya su bushe, sai a niƙa, a rinƙa sa masa a gurbin idon har kwana uku. A rana ta huɗu, sai a sa idon, zai zauna daram.” Bafulatana, watau Ɗankutungayya, ta amshi ido, ta yi godiya.

Da ta gusa kaɗan, sai ta tuɓe kayan Fulani, sai ga Ɗankutungayya ya bayyana. Sai ya yi wa Dodanniya gwalo, ya ce: “Kin ga, ni ne Ɗankutungayya.” Sai ya yi wani hatsabibanci ya ɓata, Dodanniya ta daina ganinsa. Bai tsaya a ko’ina ba sai gida. Da ya isa ya yi yadda Dodanniya ta kwatanta masa, idon yayansa kuma yazauna daram, kamar ba a taɓa ƙwakule shi ba.

Rannan kuma sai Dodanniya ta rikiɗa ta zama kyanwa. Ta kama hanya ba ta tsaya ko’ina ba sai a gidan su Ɗankutungayya. Da shigarta sai ta iske shi yana barci; sai ta lafaba, har ta kai kusa da shimfiɗarsa. Sai ta yi wani ƙaratu irin na tsafinta, ta tofa masa a fuska, sai ya zama ɓera sai ta ɗauke shi ta kai gidanta, ta sa shi a ƙuryar ɗaki.

Daga nan ta yi masa wani tofin, ya koma mutum.Ita kuma ta rikiɗa ta zama mutum. Sai ta harare shi, fuskarta murtuk, tana cike da fushi, ta ce: “Ɗankutungayya, yau fa ga ni ga ka, ƙaryarka ta ƙare.” Ɗankutungayya bai tsorata ba, kuma bai ce mata komai ba. Can da Dodanniya ta ɗan huta, sai ta sa autarta tsaron Dankutungayya, ita kuma ta kama hanyar kasuwa sayen kayan yaji wanda za ta dafa shi da shi.

Tafiyarta ke da wuya sai Ɗankutungayya ya yi wa ’yar auta dabara, ya karɓi kayan jikinta ya sa, ita kuma ya sanya mata nasa. Can sai ya ji motsin Dodanniya ta dawo, ya zabura, ya tarye ta yana ƙwaikwayon maganar ’yar auta, yana yi mata maraba. Bayan wani ɗan lokaci kuma sai ga ’yar a cikin kayan Ɗankutungayya, tana yi mata maraba.

Sai Ɗankutungayya ya dubi Dodanniya ya ce mata: “Ga munafukin nan Ɗankutungayya yana nuna wa wai shi ne ni ’yar autarki har da cewa, ‘Sannu da zuwa inna’. Yau dai ƙaryarsa ta ƙare.” Sai Dodanniya ta ce: “Lallai kam; bar ni da lalatacce!” Nan take ta yi wuf, ta shaƙo ’yarta, ta sa wuƙa ta yanka.

Tana gamayanke autarta, sai Ɗankutungayya ya buga tsalle gefe, ya kwance zannuwan da ya ɗaura, ya dubi Dodanniyar nan ya ce: “’Yar auta kika yanka, ni ko ni ne Ɗankutungayya, gwanin gayya. Na yi miki gayyar tawa!” Yana gama faɗa mata haka sai ya yi wal, ya ɓace. Dodanniya ta kama ’yarta ta tuɓe kayan jikinta, sai ta ga lallai kuwa autarta ce ta yanka. Nan take sai ta haɗiyi zuciya ta mutu.

Kurunkus.

Abubuwan DaLabarin Yake Koyarwa 

  • Kaunar juna da son ’yan’uwa kan ƙara danƙon zumunci. *
  • Mugunta fitsarin faƙo ce kan wanda ya yi take komawa.
  • Dan’uwa rabin jiki.
  • Kaiƙayi koma kan masheƙiya.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Musare Da Hodanego

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Musare Da Hodanego
Labarin na GabaTatsuniyar Kurege Da Kura
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.