Wane Ne Bahaushe?

0
572

Idan muka juya kan sanin wane ne Bahaushe kuwa? A iya cewa mafi yawancin mazauna Ƙasar Hausa su ne al’ummar Hausawa.

Amma akwai wasu ƙabilu waɗanda suka yi kaka-gida a wannan Ƙasa ta Hausa; har hakan ya sanya suka koma Hausawa a harshe da al’adu da kuma adabi.

Waɗannan ƙabilu kuwa sun haɗa da Fulani, Buzaye, Barebari, Nufawa, Yarbawa da sauransu. Amma Ibrahim (1981:1) ya bayyana cewa Hausawa su ne mutanen dake zaune a Ƙasar Hausa tuntuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa.

A ra’ayin Adamu (1983:3) kuwa, na ganin Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda ƙaura da magabantansu suka yi daga Ƙasar Hausa; zuwa wasu sassa dake maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa da Ƙasar Hausa; koda kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko yin al’adun Hausawa, sun ɗauka su Hausawa ne.

Misali, Abakwariga dake zaune a Jihar Taraba ta Nijeriya da kuma wasu dake ikirarin cewa su Hausawa ne; waɗanda ke zaune a ƙasashen Cote de Voire da Burkina Faso da Mali.

Magaji (1986:3), ya nuna Hausawa dai su ne mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa. Haka kuma dukkanin al’adunsu da ta’adunsu na Hausa.

Haka kuma addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu.

A ra’ayin Sallau (2000:71) kuwa, na ganin waɗanda saboda ƙaura da magabatansu suka yi zuwa Ƙasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun ɗauki na Hausawa. A taƙaice sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. Misalin ire-iren waɗannan mutane sun haɗa da Barebari, Kambarin Barebari, Barebarin Katsina da Buzaye da wasu Fulani.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo wanda Ibrahim Baba (Ibrahim Garba Nayaya (Baban Fauzan) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Aure A Ƙasar Hausa danna nan

Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Macaroni 2
Labarin na GabaTaƙaitaccen Tarihin Ƙasar Hausa