Hausar Gardawa

0
464

Kasancewar tsarin tsangaya wani fage ne mai faɗi, kuma wata wayewa ce ga ma’abotanta mai zaman kanta; tsarin ya haifar da samuwar wasu lafuza ko ƙarin yare wanda ya keɓanci waɗanda ke cikin wannan da’ira ta gardawa.

Kamar dai yadda sojoji ko wani rukuni na mutane ke da yaren da ya keɓance su, kuma ba mai gane shi, sai su ya su.

Akwai Hausar gardawa mai alaƙa da Alƙur’ani, wata Hausar tasu na da alaƙa da shi kansa harshen Hausa, wata kuma mai Alaƙa da harshen Turanci ko kuma Larabci.

Misalin mai Alaƙa da Alƙur’ani:-

– Tilka: baƙar mace
– tusuna: mummunar mace
– Udda: gajeren mutum
– Ƙala ƙato: malamin littafi
– Na gaban innaka: maye
– Wa hananan: an hana

A wani lokaci kuwa, su kan ƙirƙiri wata sabuwar ma’ana a cikin shi kansa harshen na Hausa; misali:

– Tashe:- tashi cikin dare don yin karatu maimakon tashe da ake yi da watan Azumi.
– Sauka:- kammala karatun Alƙur’ani
– Kasgi:- Jahili
– Badawai:- ƙauye
– Yankan baki:- raba kalma
– Yanka Alamina:- yin ɓarna ko yin zina
– Rani:- fita Neman karatu lokacin bazara
– Banda:- kayan tafiya almajiri
– Warat:- kiran gaggawa don cin abinci
– Wanke:- baƙin ruwan da ake tawada da shi
– Kwami:- karatu ko nacin karatu
– Ɗan bajire:- guntun tuwo
– Zaman sidi:- jiran abinci a wajen bara
– Mako:- yin itacen sati
– Gabza:- abincin maras daɗi
– Malam Shehu:- talaka
-Tsoma:- aljani a cikin gardawa
– Kara:- kuskure ko tsallake
– Buƙa:- gabatar da buƙata
– Datsi:- rabo ko gutsiren abinci
– Kantuga:- wasa ƙwaƙwalwa
– Alif na gaban wau:- mutum marar ra’ayi
– Shim mai ruwa Uku:- shashasha ko mara hankali
– Miya ba gishiri:- makarantar islamiyya
– Kaukau:- marowaci
– Bakaddike/Kadikko:- almajirin da ya daɗe a gari
– Kura:- matar gardi
– Jargi:- busasshen nama
– Bugu:- dafa tuwo
– Gaga:- rashin ji
– Bajancuri:- ba zato sai ya yi tilawa mai yawa
– Curinbaje:- ana sa rai kuma sai ya kasa tilawa mai kyau

Gardawa a tsarin tsangaya, ba su taƙaitu wajen ƙirƙiro sababbin ma’anoni cikin Alƙur’ani da harshen Hausa ba, har sai da suka kutsa cikin harshen Turanci. Misali:

– Boko:- ilmin boko ko ilmin gangan
– Ladan boko:- ƙaramar mota
– Coca-Cola :- ko ka kula giya ce?
-Chiyaman ko Shugaban cin amanar
Ƙaramar Hukuma:-

Tsokaci

Canza salon kalmomin Alƙur’ani ya zuwa wata ma’ana, abu ne da bai halarta ba. Domin zancen Ubangiji Maɗaukaki ne da ɓace, ko wasa baya zuwa bayansa ko gaba gare shi. Don haka ya zama wajibi ‘yan uwa gardawa su kiyaye, domin hakan zai iya kai mutum ga yin ridda.

Domin karanta cikakken bayani a kan Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Zubin Tsangaya Yake danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceƘa’idoji Da Laduban Neman Halal
Labarin na GabaShin Mene Ne Tsafi Ko Sihiri?