Yadda Zubin Tsangaya Yake

0
326

Tsangaya a Arewacin Najeriya wasu gidaje ne na ƙasa da ‘yan ɗakuna don kwanan almajirai. Lakkoki su ne a mafi yawan lokaci sunan da a ke kiran matsugunin samarin almajirai.

Lakka ɗaya kan ƙunshi almajirai huɗu zuwa sama; gwargwadon yalwar muhallin tsangaya da kuma yawan makaranta da ke karatu a cikinta.

A cikin farfajiya ko kuma harabar tsangaya a Arewacin Najeriya akan samu gargari. Gargari wata da’ira ce ta guman-guman itace da almajirai ke zama a yayin da aka haɗa wuta ganga-ganga a tsakiyar da’irar cikin dare, don yin karatu. Duk da yawaitar fitilu na gargajiya da na zamani, makaranta a tsangaya ba su daina amfani d gargari ba. Wannan ya sa samuwar gargari a tsangaya wata alama ce da ke nuna daɗewar tsangaya; ko kuma tsananin riƙon ta ga ta’adun makaranta tun kaka da kakanni.

Samarin makaranta Alƙur’ani da sauran almajirai kan tafi Ƙisƙali ko Ƙisƙadi musamnman ma bayan karatun safe.

Ƙisƙali ko Ƙisƙadi suna ne na ‘yan ƙananan ɗakuna na kara da darni cikin gonaki ko bayan gari; musamman nesa da wurin hayaniyar Jama’a.

Wani abin ban sha’awa game da al’adar makaranta idan sun tafi ƙisƙali shi ne, shagaltuwar kowanen su; da wani aiki da yake son cimma kafin komawa makaranta da yamma. Don haka ne ma wasu za ka gan su suna rubuta allunansu, wasu kuma suna Ƙwami; ma’ana suna ta biya allunansu, a lokaci guda kuma wasu suna taƙara.

Domin karanta cikakken bayani a kan Kayan Karatu A Tsangaya danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceMa’anar Tsangaya
Labarin na GabaKayan Karatu A Tsangaya