GABATARWA:
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai. Malamai na fiƙihu suna da saɓani a kan wannan mas’ ala kuma suna da ra’ ayi guda huɗu a kai wanda bayanin su zai zo kamar haka. Allah ya ba mu ikon faɗin gaskiya da kuma ikon aiki da ita.
RA’AYI NA FARKO:
Ra’ayi na farko a kan wannan mas’alar suna cewa idan ranar idi ta faɗo daidai da ranar Juma’a dole ne a yi Sallar Juma’ a kuma wajibi ne a yi ta a kan lokacin ta ko da kuwa mutum ya yi sallar idi ko bai yi ba. Kuma ba a ɗaukewa limami da masu salla ba. Wannan shi ne matsayar makarantar Hannafiyya, Malikiyya da Zahiriyya. Sannan ibni Kudama a littafinsa wato “Almughni” ya danganta wannan ra’ayi ga mafi yawan malaman fiƙihu.
Har Wala yau, ibni Rushd ya ambata a cikin littafin sa Bidayatul Mujtahidâ
cewa hujjar su a kan wannan ra’ayi ita ce faɗin Allah (SWT) a cikin suratul
Jumu’a:
Ya ku waɗanda suka yi imani idan an yi kira zuwa ga salla a ranar Juma’a to ku yi hanzari kuma ku bar harkar cinikayya, yin hakan shi ne mafi alkhairi a gare ku in kun kasance kun sani.
Haka kuma al’amarin wajibcin sallar Juma’ a yake a cikin littafin hadisin Bukhari da Muslim da ma wasu littattafan hadisai na sunnah. Suka ƙara da cewa sallar Juma’a wajibi ce saboda haka sallar idi kaɗai ba ta ɗauke ta kamar yadda ita ma Juma’ a ba ta ɗauke IDI. Malam Ibni Hazm acikin littaffinsa mai suna “al-Muhallaa” yana cewa idan ranar IDI ta yi karo da ranar Juma’ a to mutum zai fara yin sallar IDI ne farko sannan Juma’a.
Ya ƙara da cewa yin wannan dole ne kuma babu ƙwaƙƙwarar hujja na rashin aikata hakan. Ibni Hazm ya ƙara da cewa ita Sallar Juma’a wajibi ce amma ita kuma sallar IDI nafila ce saboda haka ba a barin wajibci don nafila. Daɗin daɗawa, ibni Hazm ya ƙara da cewa al’amarin Juma’a da IDI tamkar al’amarin IDI da sallar azahar ce a kowace rana bayan ranar Juma’a. Akan haka, idan dai har za a buƙaci yin sallar Azahar a ranar IDI, to haka ma sallar Juma’a wanda ta zama (sallar) farillar ranar Juma’a za a buƙaci
gudanar da ita.
RA’AYI NA BIYU:
Masu ra’ayi na biyu suna ganin cewa sallar Juma’a a wannan yanayi tana wajabta ne ga mazauna gari da kuma waɗanda ba su da nisa sosai da masallaci. Amma ga masu wucewa ko waɗanda ke nesa da masallaci(waɗanda suke tafiya mai yawa kafin su zo masallaci), idan suka sallaci IDI ya wadartar da su ba sai sun dawo sallar Juma’ a ba. Sai dai shi limami wajibi ne ya dawo ya yi sallar Juma’a. Wannan shi ne ra’ayin Imam ash-Shafi’ee.
Haka Imam An-Nawawi ya danganta wannan ga mafi yawan malaman musulunci a cikin littafin sa mai suna “AlMajmou”. Hujjar sa ita ce faɗin Sahabi Abu-Ubaid kamar yadda aka ruwaito a cikin Muwatta na Imam Malik (Allah ya ƙara masa yarda) cewa (Abu-Ubaid) na yi sallah a bayan Usman bin Affan wani lokaci a inda ya fara da gabatar da Salla sannan ya yi huɗuba a ciki yake cewa: “a wannan rana kuna da IDI guda biyu a rana ɗaya, saboda haka mutanen da suka zo daga yankin al-Awaali (wani ƙauye a cikin yankin Madina) duk mai so ya tsaya sallar Juma’a zai iya tsayawa. Wanda kuma yake so ya koma gida zai iya tafiya. Wannan umarni na ne”.
Haka Imam Annawawi ya dangata wannan ga Bukhari. Imam As-Shirazi yake cewa “ ana karɓar uzurin mutanen da zuwa sallar Juma’a ta tsananta a garesu, saboda haka buƙatar mutane su dawo zuwa sallar Juma’a daga ƙauyuka bayan sun halarci sallar IDI zai tsananta matuƙar tsanantawa a garesu.
RA’AYI NA UKU:
Masu ra’ayi na uku suna cewa duk wanda ya halarci sallar IDI to an yi masa afuwa daga halartar sallar Juma’a ba tare da la’akari da wurin zaman sa ba, haka yake ga limami da masu halarta. Amma duk da haka, shi limami zai gabatar da sallar Juma’ a ga waɗanda suke da buƙatar halarta da kuma waɗanda ba su sami halartar sallar IDI ba.
Karin bayani: A nan ba ana nufin an ɗauke sallar AZAHAR ba a saboda sallar Juma’a.
Wannan ra’ayi, saboda bayyana hujjoji a buɗe ya zama mafi ƙarfi a dukkanin ra’ayoyi a kan wannan mas’ala.
Haka kuma wannan shi ne ra’ayin Imam Ahmad ɗan Hambal kuma haka shaykhul Islam Ibn Taymiyyah yake danganta wannan ra’ayi ga wasu sahabbai irin su Umar ɗan khattab, Usman ɗan Affan, Abudllahi ɗan Mas’ud, Abdullahi ɗan Abbas da sauransu. Kuma ya ƙara da cewa babu wani ilimi na saɓani da suka yi a kan wannan mas’ala. Haka kuma wannan
shi ne ra’ayi na mafi akasarin malaman hadisi.
Hujja a kan wannan shi ne hadisin Zaid ɗan Arƙam wanda yace: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi sallar IDI a ranar Juma’a sai ya ba da dama ga halartar sallar Juma’a inda yace: “ duk mai son ya yi salla (ma’ana halartar sallar Juma’a) to ya yi”. Wannan hadisin an rawaito shi daga Imam Ahmad ɗan Hambal da kuma litattafan Sunani Dawud da Tirmizi kuma Ibn Khuzaima ya inganta shi.
Haka kuma, a cikin Sunan Abu Dawud, Abu Huraira ya rawaito cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce: “ a wannan rana kuna da IDI guda biyu saboda haka ga duk wanda ya so, sallar IDI ta wadatar masa amma mu kam za mu yi sallar Juma’a”.
Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah (rahimahullah) ya ƙara da cewa “ idan mutum ya sami halartar sallar IDI to ya riga ya samu manufar da ake so a samu ta jam’i a sallar Juma’a, saboda haka sallar Azahar kaɗai zai yi idan bai halarci sallar Juma’a ba. Sallar Azahar zai gabatar akan lokacin ta.
Sallar IDIn sa ta wadatar masa cimma manufar sallar Juma’a. Masu wannan ra’ayi suka ƙara da cewa farlanta sallar Juma’a a wannan yanayi zai sanya tsanani da takura ga mutane kuma zai rusa manufar IDI wanda dalilin yin sa shi ne don nuna farin ciki da nishaɗi. Haka, idan mutane aka tirke su daga jin daɗin lokutan su (domin halartar sallar
Juma’a) a nan IDI zai janyo ƙunci kuma ma’anar sa za ta kau.
RA’AYI NA HUƊU:
A wannan ra’ayi wanda shi ne fahimtar Ata’ ibn Abi Rabah da kuma ɗaya daga cikin sahabbai wato Ibn Zubair suna ganin cewa duk wanda ya hallarci sallar IDI to an yi masa rangwame ba ya buƙatar ya sallaci kowace salla har sai sallar La’asar, ma’ana ba zai yi sallar Juma’a da sallar Azahar ba. An ruwaito wannan cewa shi ne ra’ayin Imam Ahmad Ibn Hanbal.
An ruwaito Abdullah ibn az-Zubair radiyallahu anhu yana cewa “ IDI guda biyu (IDIn Sallar da IDIn Juma’a) sun zo a rana ɗaya, sai (Abdullah ibn Azzubair ) ya yi salla raka’a biyu da safe da wuri kuma bai ƙara yin salla ba har sai La’asar. Dangane da kore wannan ra’ayi na huɗu, Imam al-Khattabi rahimahullah ya ce: “irin wancanenka aiki na Ibn Zubair ba za a iya fahimtar sa ba sai dai ta hanyar fahimtar masu ra’ayin yin sallar Juma’a gabanin zawali (Zawali shi ne farkon lokacin Azahar yayin da rana ke fara matsawa daga tsakiya). Don haka Ibn az-Zubair sallar Juma’a kawai zai yi a maimakon IDI da Azahar”
Daɗin dadawa, shi Ata Ibn abi Raba wanda shi ne ya ruwaito aikin Ibn azzubair yace: a lokacin Juma’a mun taru domin salla amma shi (wato Ibn Azzubair) ya ƙi ya fito domin ya limance mu saboda haka sai muka yi salla daban-daban” wannan yana nuna cewa sallar Azahar suka yi kuma akwai yiyuwar Ibn az-zubair shi ma ya yi sallar Azahar a gidan sa. Allah shi ne masani
TAƘAITACCEN NAZARI MAI GAMSARWA NA MALAMAN FIƘIHU DA
MAZAHABOBI A KAN MAS’ALAR SALLAR JUMA’A DA SALLAR IDI IDAN
SUKA HAƊU A RANA GUDA WATO RANAR JUMA’A.
DAGA ALKALAMIN HUSAIN INUWA MAITAKARI
USAINISKIMA@GMAIL.COM
+2349042152353
Danna nan don karanta Yaushe Ne Kwanakin Layya Suke Ƙarewa?
Edita@rumasau-kallamu