HUKUNCIN YIN ASKI GA SABON JARIRI/JARIRIYA

0
802

Tambaya

Assalamu alaikum Mal inada tambaya
Shin in an haifi ‘ya mace wajibine sai anmata aski

Amsa

Wa’alaikumus Salam Warahmatullah, Gameda aske kan Jariri aranar 7 Hadisaine 2 sukazo
NAFARKO: Lokacinda FATIMA R/A tahaifi jaririnta AL-HASAN sai ANNABI SAW yace da ita “ki aske kansa” (MUSNAD-AHMAD)
NABIYU= ANNABI SAW yace “kowane yaro abin jinginawane da abin yankarsa, ayanka masa masa yinin 7, kuma arada masa suna kuma a aske masa kansa” (AHMD, ABU DWD, NASA’IY, IBN MAJAH)
Hadisin farkon yayinda aka haifi AL-HASAN ne shi kuma namijine,
Hadisi nabiyu kuma yazo da lafazin (غلام) shi kalmar (GULAM) yana nufin yaro namiji,
Don haka ba’a shar’anta aske kan jaririya ta maceba said in namijine, وبالله التوفيق
(FATAWAL LUJNAH- no-17,998)
ALLAHU A’ALAM.

Ansawa : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
13/10/2019