Na Sha Ruwa Bayan Tayar Da Iƙama A Kan Kuskure, Ya Hukuncin Azumina?

0
1290

Tambaya

Assalam MALAM ni ne lokacin azumi, sai na farka zan yi sahur, sai na ji ana kiran sallah, sai aka ce mun ai kiran assalatu ne, ni kuma sai nace bari ko ruwa na sha, sai aka ce kar ka sha, to ashe su suna nufin har an shiga sallah, sai da na fara shan ruwan, sannan na ji ai har an shiga sallah, sai na tsaya da shan ruwan, to yaya azumina na wannan ranar⁉

Amsa

Wa’alaikumus Salam Warahmatullah, Azuminka ya yi, babu biya a kanka, Hujja kuwa shi ne: A tsarorinda IBN JAREER ATDABARY ya kawo su a tafsirinsa cikin Tafsirin SURATUL BAQARA- ƙarƙashin aya ta (187)👉🏼

👉🏼(2873) ABU UMAMAH ya ce:
أقيمت الصلاة والإناء في يد عمر، قال أشربها يا رسول الله؟ قال “نعم” فشربها.
Wato= An tada iƙamar asuba, alhali akushi yana hannun UMAR (R.A), sai ya ce “In sha ne YA RASULALLAH? Sai ANNABI SAW ya ce “Ka sha” sai UMAR ya sha,”

👉🏼(2874)&(2875) BILAL (R.A) ya ce:
أتيت النبي (صلى) أذنه بالصلاة وهو يريد الصوم، فدعا بإناء فشرب، ثم ناولني فشربت، ثم خرج إلى الصلاة.
Wato= Bayan kiran sallah na shigo wurin ANNABI SAW na sanar da shi, yana da niyyan azumi, sai ya sa aka kawo abin sha, ya sha ya ba ni ni ma na sha,

👉🏼(2858)BARRA’U IBN AZIB ya ce:
تسحرت في شهر رمضان ثم خرجت فأتيت ابن مسعود فقال: اشرب،فقلت: إني قد تسحرت، فقال: اشرب! فشربنا ثم خرجنا والناس في الصلاة.
Wato= na kammala sahur a RAMADAN, na zo wurin Sahabi ABDLH BN MAS’UD R/A sai ya ba ni abin sha, na ce masa na kammala sahurfa! Sai ya ce= ka sha na ce, BARRA’U ya ce “Sai na sha, muna mutane na cikin sallar asuba,

👉🏼(2864) HIBBAN ya ce:
تسحرنا مع علي ثم خرجنا وقد أقيمت الصلاة فصلينا.
Wato= mun yi sahur tare da ALIY BN ABI DALIB (R.A) mun fito an riga an tayar da iƙamar sallah, sai muka yi sallah,
ALLAHU A’ALAM.

Domain sanin hukuncin yi wa mata kaciya danna kuren rubutu

Amsawa : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
22/10/2019

Daga : ZAUREN ISLAMIC SUNNAH

labarin da ya wuceƘARSHEN ALEWA
Labarin na GabaYadda Ake Tarbiyyar Yara
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.