Menene hukuncin yiwa mace kaciya?

0
1355

Kaciyar mata a musulce bata da wani hukunci na ayi ko kar ayi cikin shari’ar musulunci.

saboda duk hadisan dake cikin litattafai kamar su sunan na turmuzi da ragowar litattafai ba suyi magana kan wajibi ne yin kaciyar ko sunna ba. sunyi bayin al’adane na masu yi awadancan lokutan baya,tsari na kiwon lafiya kuma ya nuna hakan nayin lahani ga ‘ya mace, tunda hakane kuma musulunci na karewa duk wani musulmi abubuwa guda biyar (5) ciki harda lafiyar shi, “kaga bai halatta ayiba matsawar akwai cutuwa aciki”.

sassa bakwai (7) na jikin dan adam diyarsu daidai take da diyar rai, domin sune suke tafiyar da rai da Allah busa maka. Sassan sune kamar haka:

  1. Ido
  2. Kunne
  3. Hanci
  4. Harshe
  5. Wuya
  6. Baya
  7. Al’aura.
A likitance kuma:
Yiwa  yarinya mace kaciya kamar rage mata daraja ne, kuma ba wani amfanin yima
mace kaciyakuma yin haka yana sa a hukunta duk wanda yayi ma ‘yarsa mace kaciya.

 

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here