Yadda Ake Taimama

0
3023

Taimama hanyar da ake yin tsarkice idan an rasa ruwa tahanyar amfani da kasa, ana shafar fuska da hannaye biyu da qasa mai tsarki, da niyyar dahara. Ga bayani dalla-dalla yadda ake taimama:

1 – A doki qasa da hannayensa biyu bugu Daya.

2 – Sannan ya bushe su don ya rage qurar da take kansu

3 – Sannan sai ya shafi fuskarsa da hannayensa sau Daya

4 – sannan sai ya shafi bayan tafin hannunsa, ya shafi bayan tafin hannun dama da cikin hannun hagu, sannan bayan hagu da cikin hannun dama.

Dalilin wannan siffar ta taimama shi ne hadisin Ammar – Allah ya qara yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya doki Kasa da tafin Hannayensa biyu, ya busa a cikinsu, sannan ya shafi fuskarsa da hannayensa da su”[Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi].

Ga bidiyun yadda ake taimama domin kara fahimta sosai:

Domin karin bayni akan duk wani abun da ya shafi taimama Danna nan

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here