- Tambaya
As salamu alaykum wa rahmatul lahi wa barkatuhu. Malam barka da warhaka, Malam ina da tambaya, Ana kiran sallah Azahar sai mutum ya ga haila, in ya yi tsarki ya rama sallah ko baya rama sallah? Nagodé Allah ya saka da Alkhairi
Amsa
Wa’alaikumus Salam Warahmatullah. Irin wannan tambayar an yi wa SHEIKH SALEH UTHAIMEEN cewa, mace ce haila ta zo mata karfe 1:00 kafin ta yi sallar azahar, shin in jinin ya tsaya, za ta biya azahar ɗin ne⁉ Sai ya ce:
“Akwai saɓanin malamai a kan haka zuwa gida biyu:
1- suka ce, ba wajibi ba ne ta biya sallar, domin ba ta yi laifi ba, kuma ba ta yi sakaci ba, tunda ya halatta a jinkirta salla zuwa ƙarshen lokacinsa,
2- suka ce wajibi ne ta biya wannan sallar, don umarnin faɗin Annabi (S.A.W)
[عن أبي هريرة:] من أدرك ركعةً منَ الصلاةِ فقد أدركَ الصلاةَ
أبو داود (٢٧٥ هـ)، سنن أبي داود ١١٢١ • سكت عنه [وقد قال في رسالته لأهل مكة كل ما سكت عنه فهو صالح] • أخرجه البخاري (٥٨٠)، ومسلم (٦٠٧)
Wato, “Wanda ya riski raka’a guda a sallah, kafin fitar lokacinsa, to ya riski sallar,
Sai UTHAIMEEN ya ce, “Abin da ya fi a gare ta, ta biya tun da sallah ce ɗaya kacal babu takura wajen biya,
Dubi (MAJMU’U FATAWAL MAR’AH- tattarawan SHEIKH MUHD SALAH)
ALLAHU A’ALAM.
Amsawa : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
13/10/2019