Kamar yadda aka sani, aikin Hajji rukuni ne na musulunci ga wanda ya ke da iko.
Malamai sun yi saɓani dangane da matsayin Umara shin farilla ce ko nafila? Malaman Mazahabar Hanafiyya da Malikiyya suna ganin Umara ba wajibi ce; yayin da Malaman Mazahabobin Shafi’iyya da Hambaliyya da zahiriyya suna ganin Umara wajibi ce kamar aikin Hajji. Kowane ɓangare suna da hujjojinsu da suka dogara da su a ayoyin Ƙur’ani da hadisai; waɗanda suna nan cikin littattafan fiƙhu1.
Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce; “Ku jeranta hajji da Umara saboda jeranta su yana kore zunubai da talauci kamar yadda ƙira yake kawar da tsatsar ƙarfe.” (Tirmizi 738, Nasa’I 2585).
Wannan hadisin yana nuna cewa yin Umara bayan aikin hajji a kai-a kai yana maganin talauci, yana kankare zunubai.
Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Umra A Watan Ramadan danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.