Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim

0
496

Ismullahil A’azim – Ana so a karata wannan addu’ar a duk lokacin da mutum ya samu kansa cikin tsanani ko kuma damuwa.

An samu wani sahabi a zamanin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam); É—an kasuwa, wanda yana cikin tafiya daga Madina zuwa Makkah, domin kasuwanci sai ya gamu da wani É—an fashi, inda ya kama shi zai halaka shi; sai ya nemi izinin da ya bar shi ya yi alwala ya yi sallah raka’ah biyu, sannan duk abin da zai masa ya yi masa.

Sai ya ba shi dama, sai ya tashi ya yi alwala ya yi nafila raka’ah biyu (2); a sujjadar Æ™arshe sai ya karanta wannan addu’a ta Ismullahil A’azim

Ga addu’ar kamar haka:

Bismillahir Rahmanir Rahim; Allahumma inni as’aluka bil’izzati lati la taraam, wal mulkul lazhi la yadam, wal aynul lati la tanaam, wan nurul ladhi la yadfa’a, wabil wajhil lazhi la yubla, wabiddaymumatil lti la tafna, wabil hayatul lati la tamut, wabis samdiyyatul lati la taÆ™har, wabirrububiyyatul lati la tastazil an taj’al lana min umurina farjan wa makhrijan hatta la narju gairuka ya arhamur rahimin”.

Bayan da ya karanta wannan addu’a; ko da ya É—ago sama sai ya ga wata halitta a saman doki tana gudu É—auke da takobi a buÉ—e ya zo ya sare kan wannan É—an fashin. Bayan haka, sai ya tambaye shi; “Wane ne kai ka kawo mini É—auki daga inda ban yi tsammani ba?”

Sai yace da shi, “Ka kira Allah (Subahanahu Wata’ala) da sunaye cikin sunayensa zaÉ“aɓɓu; wanda ba wata buÆ™ata da za ka roÆ™i Allah (Subahanahu Wata’ala) bai biya maka ba; don haka Ubangiji ya umarce ni da na kawo maka É—auki”.

Saboda haka; duk halin da mutum yake ciki in har ya roÆ™i Allah (Subahanahu Wata’ala) da sunayen nan; Allah (Subahanahu Wata’ala) zai taimaka masa.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba danna nan.