Addu’o’in Kiran Sallah

0
379

Wanda ya ji kiran sallah zai faɗi dukkan abin da ladanin yake faɗi, sai dai idan ya ce:

“Hayya alas-salaati (da) Hayya alal falaahi”.

{Ku taho ga sallah; ku taho ga babban rabo}.

A maimakon haka sai shi ya ce:

“Laa haula walaa ƙuwwata illaa bil-laahi.

{Babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah}.

Bayan ladanin ya yi kalmar shahada, sai shi kuma (mai sauraron) ya ce:

“wa’ana Ashhadu an laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahuu wa’anna Muhammadan abduhu warasuuluhu, radhiitu bil-laahi Rabban, wabi Muhammadin Rasuulan wabil Islaami diinan”.

Bayan ya gama amsa kiran sallar, sai ya yi salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam). Sannan kuma sai ya ce:

“Allaahumma Rabba haazihid da’awatit tammati was-salaatil ƙaa’imati ati Muhammadan wasiilata wal fadhilata wab’as’hu maƙaaman mahmuudal lazii wa’adtahu innaka laa tukhliful mii’adi”.

{Ya Allah! Ubangijin wannan kira kammalalle, da wannan sallar da za a tsayar da ita, ka ba wa Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) wasila (matsayin kusanci a Aljanna), da Matsyin fifiko, kuma ka tashe shi a matsayin abin godewa, wannan wanda ka yi masa Alƙawarinsa. Lalle kai ba ka saɓa Alƙawari}.

Sannan ya yi wa kansa addu’a a tsakanin kiran sallah da tayar da iƙama, domin addu’a a wannan lokaci ba a ƙin karɓar ta.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a A Yayin Sujjada danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya Yi Bayan Ya Tafi Sujudah danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceJagoran Noman Waken Soya
Labarin na GabaAddu’o’in Tashi Daga Barci
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.