Addu’o’in Tashi Daga Barci

0
525

“Alhamdu lillaahil- lazii ahyaana ba’ada maa amaatanaa wa’ilaihin nushuuru”.

{Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya ɗauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi yake}.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare yace:

“Laa’ilaha illallahu wahdahu la shariikalahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun. Subhanallahi wal hamdu lillaahi walaa ilaaha illallahu Allahu akbaru walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil laahil aliiyil aziimi, Rabbigfirlii”.

{Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma shi Mai iko ne a bisa komai, Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, Maɗaukaki, mai girma Ya Ubangijina! Ka gafarta mini}.

Wanda ya faɗi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu’a za a amsa masa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karɓi sallarsa.

“Alhamdu lillaahil lazii afaani fii jasadii waradda alayya ruuhi wa’azina lii bi zikrihi”

{Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo min da raina, kuma ya ba ni izinin ambatonsa}.

“Inna fii khalƙis- saamaawati wal ardhi wakhtilaafil laili wannahari la ayaatil li ulil albaab allaziina yazkurunallaaha ƙiyaaman waƙu’udan wa alaa junuubihim wayata fakkaruuna fii khalƙis- samaawati wal ardhi rabbanaa maa khalaƙta hazaa baaɗilan subhaanaka faƙinaa azaban naari rabbanaa innaka man tudkhilun nara faƙad akhzaitahu wamaa liz zaalimiina min ansaari rabbanaa innanaa sami’ina munaadiyan yunadii lil imani an aminuu bi rabbikum fa’amanna rabbanaa fagfirlanaa zunuubanaa wa kaffir annaa sayyi’ atinaa watawaffanaa ma’al abraar rabbanaa wa atinaa maa wa’adtanaa alaa rusulika walaa tukhzina yaumal ƙiyaamati innaka laa tukliful mii’ada fastajaaba lahum rabbuhum annii laa udhi’u amala amilin minkum min zakarin au ansaa ba’adhukum min ba’adhin fallaziina haajaruu wa ukhrijuu min diyaarihim wa uzuu fii sabiili waƙaataluu wa ƙutiluu la’ukaffiranna anhum sayyi’ atihim wala udkhilannahum jannatin tajrii min tahtihal anhaaru laziina kafaruu fil bilaadi mataa’un ƙaliilun summa ma’awaahum jahannamu wa bi’isal mihaadu laakinil laziina taƙau rabbahum lahum jannatun tajrii min tahtihal anhaaru khaalidiina fiihaa nuzulan min indil laahi khairun lil abraar wa’inna min ahlil kitaabi laman yu’uminu bil laahi wamaa unzila ilaikum wamaa unzila ilaihim khaashi’ina lillaahi laa yashtaruuna bi ayaatil laahi samanan ƙaliilan ulaa’ika lahum ajruhum inda rabbihim innal laaha sari’ul hisaabi yaa ayyuhal laziina aamanuus biruu wa saabiruu wa raabuɗuu Wattaƙullaaha la’allakum tuflihuuna”.

(Ali imrana, aya ta 190 zuwa ƙarshen surar)

{Haƙiƙa a cikin halittar sammai da ƙassai, da saɓawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abota hankula. (su ne) waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingiɗe, suke kuma tunani a kan halittar sammai da ƙassai (suna cewa):

“Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa kai, duk wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu mataimaka. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa; ku yi imani da Ubangijinku. Sai muka yi imani.

To ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu, ka kuma karɓi rayukanmu tare da mutane nagari. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alƙawari da shi a kan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alƙiyama. Haƙiƙa, kai ba ka saɓa alƙawari.

Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa); Haƙiƙa, Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace sashinku daga sashi yake.

To, waɗanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaƙi, kuma aka kashe su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah.

Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai- koman waɗanda suka kafirta a cikin garuruwa ta ruɗe ka. Jin daɗi ne ɗan ƙanƙani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta.

Amma, waɗanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta, kuma haƙiƙa akwai daga ma’abota Littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar.

Zuwa gare su, suna masu ƙanƙan da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da ɗan tamanni ƙanƙani. Waɗancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Haƙiƙa Allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi haƙuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin haƙuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta}.

(Ali Imran, 190 zuwa ƙarshen surar).

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’o’in Kiran Sallah
Labarin na GabaYadda Ake Horon Masu Yi Maka Flashing A Waya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.