Category: Tsaftar maza

Wannan shafin yana koyar da yadda ake tsaftar maza , a cikin harshen Hausa a sauƙaƙe.

wikiHausa ta kowa ce. Kowa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara. Bugu da ƙari, kowa na iya amfani da wannan kafa Domin koya ko koyar da yadda ake tsaftar maza, wanda zai amfanar da jama’a

  • Dunƙulallun Matsaloli A Musulunci

    Dunƙulallun Matsaloli A Musulunci

    Bayan abin da aka faɗa a baya, na matsalar dake tattare da wasu nau’o’in kwalliyar mata wadda ta kaucewa hanya, to akwai kuma wasu matsalolin da za a iya faɗa a dunƙule kamar haka:

    (a) In tsarin kwalliyar zamani ya fi karkata ya zuwa tsiraici da mace. 

    (b) Haka kuma kwalliyar zamani tana jan kuɗi sosai, domin wadda ta zaƙe a cikinta za ta sami kanta a cikin ɓarnar dukiya da almubazzaranci, kuma wasu sukan fifita kashe kuɗaɗe maƙudai a kan kayan ado masu tsada, fiye da taimakawa faƙirai da mabuƙata. 

    (c) yana rage darajar mace, kamar dai ita wata abin sha’awa ce kawai ga maza, bayan kuma mace (kamar namiji) bayan harkar sha’awa tana da ayyuka da gudunmawa a rayuwa iri-iri idan ta martaba kanta. 

    Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

    (d) wasu kayan kwalliyar sukan zama isgili ga mace, maimakwan su ƙara mata kwarjini da muhimmanci, sai su mayar da ita abin abin dariya saboda wasu shafe-shafe da akan yi a leɓe da girar ido da sauransu, har canzawa mace kamanni na cikakkiyar mutum suke, wani dalili dake tabbatar da abin da na faɗa shi ne, da wuya ka ga mace mai ilmi ko mai wani matasayi na alafarma ta yi irin waccan kwalliyar, idan kuma ta yi, sai ka samu mutane duk suna raina ta. 

    (e) Yawaita yin amafani da kayan kwalliya na zamani sukan sanya wasu matan jin isa da fariya da girman-kai. 

    (f) kasancewar kullum mata suna bayyana adonsu barkatai, wannan yana illata maza ta fuskoki guda biyu: 

    (i) Wasu mazan sukan zama fitinannu, su faɗa cikin zinace-zinace da sauran miyagun ayyuka, kamar fyaɗe da kwartanci. 

    (ii) Wasu mazan kuma yawaita ganin mata barkatai cikin ado da tsiraici a koda yaushe, yana dakushe musu mazakuta, yadda ba su cika damuwa da iyalin su ba, sai da taimakawar ƙwayoyi ko kuma magugunan gargajiya, masu zaburar da sha’awa. 

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya

    Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya

    Abu ne mai kyau mu zayyana kaɗan daga wasu kayan kwalliya na tufafi da shafawa da sauransu, waɗanda za su iya zama illa ga mace don su nisance su, saboda ta yi amfani da nau’in kayan kwalliya da zabsu biya mata buƙatarta ta ado, ba ta kauce ƙa’idojin Mahaliccinta ba , kuma ba tare da ta cuci kanta da kanta ba. 

    Matsattsun Kaya

    Sanya matsattsun kaya ga wasu mata ya zama ruwan-dare gama duniya. Irin waɗannan mata sukan fifita kayan da za su matse jikin tamau! Yadda za a iya ganin ƙirar jikinsu. Sosai, masana da yawa sun yi tsokaci a kan irin waɗannan kaya, ta fuskokin ilmi daban- daban. 

    Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

    A ɓangaren kiwon lafiya, ana ganin irin waɗannan ɗamammun kaya suna tsananta matse jikin mace, haka kuma yana azabtar da ita sosai, ta hanyar takura ta, da rashin samun walwala, saboda haka yawan sanya irin waɗannan kayan zai sanya mace yawan jin damuwa a ranta. 

    Haka kuma matsewar da tufafi ke wa jiki zai takurawa tsarin zagayawar jini a jijiyoyinta, wannan kuma zai iya sabbaba mata cutar hauhawan jini. 

    Domin karanta bayani akan Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci Danna nan

    • A wani faɗin ma, wasu masana cewa suka yi; “Yawaita sanya matsattsun kaya, zai iya hana wa mace haihuwa, ko kuma ya yi sanadin samun tangarɗar haihuwar”. 

    Tufafi masu Bayyana Fatar jiki

    Ƙoƙarin kwaikwayon kangararrun Turawa, yasa wasu matan musulumi, suna sanya tufafi masu bayyana wasu sassa na jikinsu, yadda za a iya ganinsa ƙarara, kamar gadon baya ko faɗin ƙirji ko sha-raba, da dai sauransu.

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci

    Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya A Musulunci

    Wata aya ta tabbatar da cewa ado na Allah ne, don haka babu wanda zai haramta wa bayinsa kayan da ya fitar don amfaninsu. kuma shi ado da kayan daɗin duniya na halak, duk an fitar da su domin Musulmi su more su a duniya , haka kuma a lahira su kaɗai ne za su sha daɗin waɗannan ni’imomi. Ayar tana cewa: 

    “Ka ce wane ne ya haramta kayan Ubangiji na ado da kayan daɗi na halal wanda ya fitar da su ne, don amfanin bayinsa, ka ce wannan (duk) na musulmi ne duniya, kuma a lahira su kaɗai ne za su more su”.Al-A’raf:32. 

    A nan za mu ga cewa, Allah Ta’ala ya yi tsawa ga wanda ke ƙoƙari haramta wa musulmi more kayan ado da na halal, kuma ya jingina ado ya zuwa ga zatinsa saboda ya ce, (ado Ubangiji), sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa musulmi tun a duniya , ya 

    halatta su more waɗannan ni’imomi, bugu da ƙari a lahira su kaɗai ne ma za su amfana da su. 

    Domin karanta bayani akan Muhimmancin Ado Da Kwalliya A Musulunci Danna nan

    Allah Ta’ala mai Kyau ne, kuma yana son abu mai kyau. 

    Magana a kan matsayin ado da ƙaye a addinin Musulunci ba za ta cika ba, har sai an kawo Hadisin Manzo Allah (S. A.W) da ya ke cewa: 

    “Haƙiƙa Allah (Ta’ala) mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau”. (Hadisi ne ingantancce). 

    Saboda haka duk abin da za a faɗa an yi ne don a hana su kyautata jikinsu da ƙawata kansu ba ne, sai dai a faɗakar da su a kan abin da zai iya zame masu illa idan sun saɓawa ladubban ado da kwalliyar tasu a Musulunci. 

    Tabbas, a irin yadda kwalliyar mata ta zamani take, tana buƙatar mata Musulmi su yi mata gyare-gyare, akwai nau’o’i da yawa na kayan sawa da na kwalliya, waɗanɗa suna iya zama matsala gare su, a kan haka bai kamata garin kwalliya a jawo wa jiki illa ba, ko kuma a jawo wa aljihu ko jaka naƙasu ba! Ko Hausawa ma suna cewa: “kada garin gyaran gira a tsone ido”!

    Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
  • Allurar Tsarin Iyali Ta Maza (Male Family Planning)

    Allurar Tsarin Iyali Ta Maza (Male Family Planning)

    Wannan itace alluran danafadamuku ansamu ta maza kwanaki kuma cikin ikon Allah allurar ta samu amincewar hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO,wanda allurar an gama dukkan wani gwaje gwaje da za’a yi a kanta na ingancin ta da lafiyar ta.

    Bincike ya nuna cewa allurar tana da kashi 97.3 cikin 100 na nasara wajen cimma burin da ake so.

    A lokaci guda, tanada ingancin 99.02 wajen hana haihuwa,azoospermia shi ne toshewar fitar maniyyi daga da namiji.yayin saduwa.

    Da zarar an yi wa mutuma allurar, tasirinsa zai kasance har na kusan shekaru 13.

    Domin karanta Yadda Zaka Bada Agajin Gaggawa Ga Wanda Ya Sha Kananzir (Kerosene) Danna nan 

  • Saurin Inzali (Premature Ejaculation)

    Saurin Inzali (Premature Ejaculation)

    Menene Premature Ejaculation: Premature ejaculation is the inability to delay ejaculation for more than one minute after penetration.

    Ma’ana 

    Saurin inzali ko kuma saurin kawowa wanda bazai wuce minti daya ba.

     How Many Minutes Of Sex Are Enough, And How Many Are Too Few?
    •  Sex that is too short lasts one to two minutes

    (Mafi karancin jima’i shine wanda yake farawa kuma yake karewa iya minti daya zuwa biyu)

    • Adequate lasts three to seven minutes 

    (Gamsashe bai wuce mintuna uku zuwa hudu ba)

    • Desirable is seven to 13 minutes 

    (Mafi dogon lokoci shine mintuna goma zuwa goma sha uku)

    Me Yake Kawo Premature  Ejaculation

    Psychological Factors:

    • Early sexual experiences
    • Sexual abuse
    • Poor body image
    • Depression
    • Worrying about premature ejaculation
    • Guilty feelings that increase your tendency to rush through sexual encounters

    Biological Factors:

    • Abnormal hormone levels
    • Abnormal levels of brain chemicals called neurotransmitters
    • Inflammation and infection of the prostate or urethra
    • Inherited traits

    Others Factors:

    • Erectile dysfunction
    • Stress / Anxiety
    • Relationship problems
    Treatment:

    The pause squeeze technique

    Begin sexual activity as usual,including stimulation of the penis,until you feel almost ready to ejaculate repeat as many times as necessary at least for 3 days in a week.

    Ma’ana

    Kayi ƙoƙarin shafa gabanka in kaji zaka kawo sai ka bari,ka sakeyi gwargwadon yadda zaka iya akalla zuwa kwana uku cikin mako guda.

    Domin karanta Dalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace Shiga nan 

    Have your partner squeeze the end of your penis,at the point where the head (glans) joins the shaft and maintain the squeeze for several seconds,until the urge to ejaculate passes,have your partner repeat the squeeze process as necessary.

    Ma’ana 

    Idan sha’awa tafara motsawa saika zarota,matarka tadora babban yatsarta a bisa kan azzakarin na ka manuniyarta a ƙasa saita matse da dan ƙarfi ta ci gaba da matsawa,zaka danji zafi,nan take sha’awar za ta kintse,saika mayar a dinga maimata haka har sai tagamsu .

    Condom 

    Condoms might decrease penis sensitivity,which can help delay ejaculation. “Climax control” condoms are available over the counter. These condoms contain numbing agents such as benzocaine or lidocaine or are made of thicker latex to delay ejaculation.

    Ma’ana

    Amfani da condom yana rage susar azzakari wanda yana taimakawa wajen kara inzali da yake yana dauke da mai nauyin zolacain,idan za’ayi amfani da shi sai a dan huda gaban yadda ruwanka zai fita,kana iya hada biyu in har kana jin susarta.

     Kegel Exercise

    Learn to control your ejaculation by doing an exercise called the Kegel,named after Dr. Arnold Kegel,this exercise helps your pubococcygeus or pc muscle get stronger. The pc muscle goes from the pubic bone to the tailbone along the floor of pelvic cavity. To strengthen this muscle,you can squeeze the pc muscle,you can do this by restricting your urine flow. Stop in midstream and then relax the muscle to allow the urine to flow,that is the pc muscle,you can squeeze this muscle at various times to strengthen it,not just during the urination process,if you do this 10 times a day,you may see positive results in two to four weeks.

    Domin karanta bayani akan Hyperstimulated Nervous System Danna nan 

    Ma’ana

    Wannan wata hanya ce ake kiranta kegel exercise ta samo asali daga wani bature mai suna Dr Almond kagel,wannan hanya ta samarwa da daruruwan mutane mafita daga saurin inzali.

    wannan hanya ta kunshi wasu jijiyoyi da ake kira pelvic muscles da suke cikin kashin kunkuru,yadda zaka gane su cikin sauki shi ne yayin da kake cikin fitsari sai ka yanke fitsarin nan take ya tsaya ba tare da ka gama fitsarin ba,ya zamanto kana yanke zuwan fitsarin maimakon ka sake fitasarin,jijiyoyin da suke wannan aiki su ake so ka kiyaye yanayin aikin su,kuma su ne dai suke ba mutun damar matse bayan gida ko bahaya,to wannan jijiyoyin su ake kira pelvic muscles,in ka fahimci hakan to da su ake kegel exercise.

    Yadda zakai kagel exercise wancan  hanyar da ka bi wajen tsaida ko yanke fitsari nan take ita za kai amfani da ita,za ka rike wannan jijiyoyin na tsawon sakan uku sai ka saki,sai ka kara maimaitawa ka rike sakan uku ka saki har sau goma shabiyar,haka za kai da safe da rana da kuma daddare,sau uku kenan a rana,insha Allah cikin dan kankanin lokaci sati 2 zuwa 4 za’aga canji sosai .

    Karanta cikekken bayani akan HIV/AIDS 

    Changes Position 

    Masu irin wannan matsalar amfiso iyalinsu ta kasance a sama domin idan iyalin ne a kasa  akwai saurin kawowa da wuri saboda saurin zuwan jini gaban ka.

    Food For Premature Ejaculation:

    Wadannan abincin suna taimaka sosai :

    • Eggs (Ƙwai)
    • Onions (Albasa)
    • Garlic (Tafarnuwa)
    • Carrots (Karas)
    • Banana (Ayaba)
    • Beans (Wake)
    • Green Vegetables (Salat,Cabbage)
    • Ginger & Honey (Citta da Zuma)
    • Watermelon (Kankana)
    • Orange,Mango etc.

    Medication

    Topical Anaesthetics

    Anaesthetic creams and sprays that contain a numbing agent,such as benzocaine, lidocaine or prilocaine are sometimes used to treat premature ejaculation. These products are applied to the penis 10 to 15 minutes before sex to reduce sensation and help delay ejaculation.

    Anesthetic cream ana amfani da shine wajen magance saurin inzali,wajen rage jin susar fatan namiji kuma ana amfani da shine mintina 10 zuwa 15 kafin lokacin jima’i,sai dai yana rage dadin jima’i ga namiji.

    Oral Medication 

    Hakanan akwai magunguna da dama wanda ake amfani da shi idan angane matsalar kamar nau’in magunguna

    • Antidepressants
    • Phosphodiesterase-5 inhibitors 

    (Wannan kam yazama ruwan dare wanda daya daga cikin mazaje suna amfani dashi ba bisaga ka’ida ba)

    Wasu Shawarware:

    • Acire yawan tunani da damuwa akan matsalar 
    • Adinga cin abinci masu amfani kamar su fruits  da vegetables
    • Adinga ziyaratar asibity domin neman shawarwari.

    Karanta Abubuwan Dake Haddasawa Mace Ganin Ruwa Clear Ko Ruwan Nono Na Zuba Daga Nonuwanta

  • Likita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penis]

    Likita Ina Neman Taimako Haɗe Da Shawara Game Da Matsalar Ƙanƙantar Azzakari [Micro Penis]

    Wannan na daga tarin tambayoyin gami da ƙorafin da a ko yaushe nake samu daga wasu cikin maza na sha kau da kai garesu, tare da ɗan tsaga bayani kaɗan cikin wasu rubuce-rubuce na, amma dai a yanzu abin ya yi yawan da dole na fito na yi bayani a iya kan wannan matsalar kurum. 

    Haƙiƙa daga sanda mutum ya fara jin cewa an rage shi ta wannan ɓangaren to mataki ne da zai kai mutum ga rasa self confidence ɗinsa na namiji, yana kuma iya kai mutum ga damuwa da fargaba na ba gaira babu dalili wanda za su dabaibaye shi haka kurum. 

    Sai dai kaso sama da 80% na masu irin wannan tunanin azzakarinsu ya kai tsaikon da ake so wanda ya dace da halittar su, zubin su da halaiyarsu dai-dai da na kowa kurum kallon kitse suke wa rogo! Amma a zahiri ƙalau suke.

    Azzakari na fara girma ne jikin namiji daga shekara 11 sannan ya kammala girmansa zuwa 18yrs daga nan ya cika girman sa, don haka galibi daga shekara 20 shi kenan kurum abinda ka ganka da shi shi ne abunda Allah ya ba ka na tsayi ba za ka ƙara ba, domin kamar tsayi ne, daga shekara 21 shi ma ka gama tsayin da duk za ka yi. 

    Kwata-kwata adadin masu fuskantar ƙanƙantar gaba a duniya wato Micro penis shi ne 0.015% cikin 100, wanda ke nuna kaso 99.85% duk azzakarinsu ya kai tsaiko sai de rashin godiyar Allah

    Ina So Baki Ɗaya  Ku sani

    A jima’i, binkicen masana game da azzakari an tabbatar da:

    • Mafi ƙanƙantar azzakari da in kana da shi shi ne za ka zargi kanka da matsalar ƙanƙantar gaba shi ne in ya gaza kai wa 3.6 inches kwatankwacin 9.16 centimeter sanda sha’awa ta kama mutum ya miƙe. 
    • Yayin da average wato tsayin da Allah a ƙallah kusan kowa inde ya kai toh babu zancen matsala shi ne: wanda yake (3.66 Inches wato 9.3centimeter) Idan an auna tsayin a sanda yake kwance wato flaccid kafin Erection, da kuma kai  wa tsawon 5.16 inches wato 13.12cm centimeters a sanda ya mike…. Wato Erection yayin sha’awa. 

    Sharaɗin Kiyayewa 

    Kafin gwajin ya kamata kowa ya sani yanayin wheather musamman lokacin sanyi ko yanayin zafi a inda yake da na’urar sanyaya ɗaki (AC) suna da tasiri wajen sanya shi ya kuɗe ciki don haka yanayin ɗumi shi ne zai sa a sami awo me kyau. 

    Hakan tasa wasu kan ga gabansu ƙarami amma ba a nan abun yake ba domin galibi in ya miƙe su kansu suna ganinsa da girma musamman a masu masturbation saboda takurarku ce tasa fata ɓoye shi… don haka wannan normal ne babu buƙatar damuwa don ya kasance ƙarami amma in sha’awa ta taso kai achieving Erection ka gansa ya kai girman sa, ba ka da buƙatar ka dami kanka… 

    Kamar yadda nace lokuta musamman na sanyi azzakari yakan ɓoye kansa ciki saboda canjin temperature.

    Ba Ƙasa Da Ido Ake A Kalli Azzakari Ba

    Idan kana so ka gane tsayin azzakarinka ba wai yadda kake ganinsa da ido ba ne, a a ka bari sai ka fito wanka ko kuwa yanayi me kyau sai ka sami irin ƙaton Mirror ɗin nan wato madubi sai ka tsaya ka ɗora hannuwanka a ƙugunka kai poster a sannan ne za ka gane zahirin tsayin azzakarinka sanda ya zamto kansa na pointing din ƙasa. 

    A sannan ne in za ka auna sai ka sa ruler ɗinka ko tape ɗinka irin na awon teloli ka ɗora daga tushenta na gashin gabanka (BASE) zuwa ƙarshen penis glands ɗin wato wajen fitar fitsari (TIPS) sai ka ga numba nawa ka samu shi ne zai zamto tsayin azzakarinka 

    Kuma an fi son gwajin ne sanda azzakari yake a miƙe wato aka sami Erection fiye da in yana kwance in ka ga ya miƙe ya yi ƙasa da 9.1centimeter (cm) Toh sannan ne za ka ce kana da ƙanƙantar azzakari wanda kuma galibi ɗan Nigeria ya wuce hakan. 

    Idan Muka Duba Ƙididdigar Duniya Gaba Ɗaya

    A kwai bayanai da shafin bayanai (WORLD DATA) suka fitar bisa survey da suka yi na jerin ƙasashen duniya tun daga ƙasar da mazajenta suka fi tsayin azzakari zuwa mafi ƙanƙanta, inda ƙasar ECUADOR  ita ce ƙasar da mazajenta suka fi ko ina tsayin jela da murabba’in AVERAGE tsayin da yakai 17.61 centimeters, sai ƙasar CAMEROON, BOLIVIA da SUDAN matsayin na 2, na 3 da na huɗu, yayin da ƙasar CAMBODIA ita ce average na tsayin jelar ‘yan ƙasarta 10.04centimeter, yayin da ƙasar Nigeria  ke matsayin ta 43 a duniya da mazajenta ke da AVERAGE na tsayin azzakari da ya kai 14.38cm centimeter. Wanda a hakan ma na san muna da mazaje masu yawa da azzakarinsu ya kai tsayin na wasu yan ƙasar Ecuador ɗin wato 17cm +

    Sannan binkice ya nuna fiye da kaso 85% sun nuna gamsuwarsu da yadda duk azzakarin namiji yake matsayinsa na Average, in fact tsayin azzakari ba shi ne jima’i ba, iya sanin kalar mace da yadda za ka sarrafa ta ka tattabata Shi ne ke ba da gamsashhen jima’i, wasu magana a kunne yayin jima’i shi ke gamsar da su.

    Don haka babu buƙatar ku je kuna kashe kanku, kuna sa kai a damuwa ba gaira babu dalili, ko ku yi ta shaye-shayen magungunan da ba za su amfane ku da komai ba.

    Mu dai  likitoci ba mu da wani magani da sunan na ƙara tsayin azzakari, ko surgery shi ma babu, sai dai a yi wanda za a katsewa mutum majanyen da ke riƙe da azzakarin a can tushensa wato ligament domin ta zazzago shi ne ma wasu suke samun abu me ɗan nauyi su ɗaura a kanta suna tafiya yana lilo wai duk don ta zazzago…

    Haka ko advance surgery sai dai ya zamo cosmetic kurum ka ga ina lafiya a ce azzakari sai an saka masa roba da sunan implant an tsai da shi kullum a haka duk da ba kowa ma ake wa hakan ba sai wanda rashin tsayin ya amsa rashin tsayi. 

    Yana da kyau ku shiga nan domin karanta Dalilan Da Suke Sanya Mace Rashin Daukar Ciki

    Fina Finan Batsa Da Maganganun Batsa Ba sa Komai Sai Lalata Tunani 

    Kamar yadda na sha faɗa sau tari kalle-kallene na fina-finan batsa ke jawowa, wanda kuma na faɗa muku duk wannan ba azzakarin gaskiya ba ne, hatta abunda za ku ga ana fitarwa matsayin maniyyi wallahi ba maniyyi ba ne artificial cream ne aka haɗa shi… Wanda yake turo shi da syringe yake amfani, ɓoye kansa yake bayan camera man. A ƙalla ka sami mutum 12 a cikin ɗakin da ake shooting na porn, shi yasa komai za ka ga perfect…

    Yau zan tabbatar muku da hakan a link ɗin da na sa muku ƙarshen wannan post ɗin, zai kai ku YouTube ku ga yadda suke haɗa pornographic scene ɗin.

    Sai kuma lalacewar tarbiya da ƙarancin kunya domin mata a yanzu su ne kan gaba wajen ƴaɗa batsa a ko ina, za kai takaici ka ga irin abunda ‘ƴa’ƴan mu, ƙannen mu ke videos a kai suna ɗorawa a YouTube da sunan koya jima’i don neman kuɗi, ko kuma ka ga an ƙirƙiri group a Facebook da WhatsApp ana mata zalla amma ɓarnar da suke kare ma ba zai ci ba.

    A haka duk sai su zo su yi ta tattauna hatta abinda ke faruwa a shimfiɗa saboda rashin mutunci na wasu matan, ka ji abubuwan ƙarya da gaskiya wasu su ji kuma su hau kai su zauna, daga ranar ta fara ganin gazawar mijin ta, ko ta kalli porn ta ɗauka duk gaskiya ne, mijin ta da ba shi da kaza ko ba ya iya minti kaza suna jima’i ba lafiyar sa ƙalau ba. 

    Wani Abu Da Ba ku Sani Ba Shi ne 

    Shi fa farjin mace baki ɗayansa FLEXIBLE ne, babu wata mace wai ita dunduɓus kurum sai dai in infection gare ta, amma Allah ya tsara shi ne ya sa masa transitional epithelium da duk yadda namiji yake zai dai-dai da shi in ya sanya gabansa, kamar roba ne, yana talewa, ya tsuke, ko ɗame,

    Average na zurfin farji wanda galibi bai wuce wa shi ne 10centimeter fiye 90% na mata haka suke, kai me average 14cm Ka gayan ina za ka shigar da ragowar 4cm ɗin cikin 10cm?

    Ni’imar Allah sakamakon can gaba bakin mahaifa ne shi yasa ko da ka kai 17cm ɗin ma kana iya jin ka shige baki ɗaya domin hakan zai kusata tips din penis dinka ga bakin mahaifa shi yasa in da rabon ciki kana yin release shi kenan maniyyinka zai nemi hanya ya shige cikin mahaifar cikin sauki.

    Wannan bayanin zai zamto mabuɗin idanu ya zamto a dena ruɗarku da porn ko zantukan shirme, lafiya ƙalau kuke, ku mance da masu karanta muku wani ya ake kwanciya… duk su ma a finafinan batsa suke kawo muku wanda duk ƙarya ne galibi ba abunda kuke gani ba ne.

    Allah ya taimake mu, ya shirya mana zuri’a baki ɗaya amin.

    Domin karanta Me yasa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Yana Fitowa  Kafin Ko Bayan Sanin Period Din Su? Danna nan

  • Amfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements )

    Amfani da Kuma Illar Magungunan Kara Karfin Maza (Male Sex Enhancement Supplements )

    Tabbas saduwar aure a tsakanin namiji da mace tana da matuƙar muhimmanci a zamantakewar aure. Duk da kasancewar ba ita kadai bace take samar da morewar zaman aure, saduwa itace akan gaba.

    Wannan yana nufin cewa koda mace tana da ladabi da biyayya,iya magana, iya girki, iya ƙwarƙwasa,iya ƙwalliya,tsabta da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure,to dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin mijinta. Haka nan kuma koda namiji yana da ƙoƙarin samar ma matarsa da abinci da abin sha, sutura, wurin zama, kiwon lafiya, tsare mutunci, tausayawa, kyautatawa da sauran abubuwan ƙayatarwa na zaman aure, to, dukkansu basu kai muhimmancin saduwa ba a wurin matarsa. Bisa wannan dalilin ne maza suke jajircewa wajen ganin cewa sun gamsar da matansu ta fuskar jima’i.

    Abinda Ake Nufi da Gamsar da Juna Wajen Saduwar Aure (Sexul Satisfaction )

    Masana a fannin lafiya (medical health), da na addinin musulunci (Islamic clerics), da na halayyar dan-adam (psychologists) sunkai sun komo game da ma’anar gamsarda juna a wurin saduwar aure. Amma duk bayanansu sun tattara ne akan cewa ma’anarsa itace a samu natsuwar da zata gusar da duk wata sha’awa bayan an gama saduwar, sai kuma wani lokaci idan bukatar hakan ta taso.

    Da Wannan Ne Wasu Da Yawa Daga Cikin Mazajenmu Suke Ɗaukar Cewa Mutum Ba Zai Iya Gamsar Da Iyalinsa Ba:
    • Idan yana da al’aura mai kauri,ko tsawo, ko kuma duka biyun.
    • Idan yana dadewa wajen saduwa

    Hakan ne ya baiwa wasu kamfannoi masu sarrafa magungunan bature, da kuma masu maganin gargajiya damar samarda magunguna iri-iri wadanda aka ce suna baiwa namiji karfin gamsar da iyalinsa yadda ya kamata. Abin yayi yawa sosai, ta yadda masu wadannan magunguna suka cika chemists, da kasuwanni, tituna, da tashoshin mota suna cin karensu babu babbaka.

    Rabe-Raben Magungunan Bature Na Kara Karfin Namiji 
    • Ƙwayoyi (drugs): wadannan sune magungunan da ake sha da baki, kuma suna da yawa. Sun hada da Viagra, VigRX Nitric Oxide , TestRX, GenF20 Plus, Semenax, ProSolution Plus, VigRX Plus, Extenze, da sauransu. 
    • Mayuka (creams): wadannan sune magungunan da ake shafawa. Suma suna da yawa, kamar Maxman Delay Sex Cream, Viamax Maximum Gel, TITAN Gel, Doc Johnson Power Plus Delay Cream, Man1 Oil Penile Health Cream, Lavenda Massage Oil, da sauransu.
    • Allura (injection): wadannan sune magungunan da ake yin allura dasu. Suma suna da yawa, kamar Papaverine, Prostaglandin E1 (PGE1), Phentolamine, Alprostadil, Trimix, da sauransu.
    • Tiyata (surgery): wannan shine aikin yanka mazakuta da ake yi a dakin tiyata domin a kara mata tsawo ko kauri (penile augmentation surgery) ta hanyar sanya wata roba mai kama da jijiyoyin mazakuta (medical grade silicone). Anfi yinta a kasashen turawa, kuma tana da tsada sosai.
    • Jike-jiken magungunan gargajiya (herbal concoctions): wannan shi yafi yawa a cikin al’umarmu. Suma akwai na sha akwai kuma na shafawa. Masu ilimin kimiyya basu cika yarda da tsabtar wadannan magungunan ba, haka kuma basu yarda da sahihancin ka’idar amfani da su ba (dosage).

    Masu amfani da wadannan magunguna suna ganin tasirinsu. Hakan baya rasa nasaba da abubuwan da ake hada su da shi, kamar ginkgo biloba, ginseng, DHEA, horny goat weed, fenugreek, maca da sauransu. Wasu chemicals ne wasu kuma ana tatso su ne daga tsirrai, sa’annan suna sanya karuwar zubar sinadarai (hormones) a cikin jiki ne. Amma a gaskiya sakamakon binciken kimiyya da yawa ya tabbatar da cewa dadewa ana amfani da su yana haifar da illa ga lafiyar mutum. Bayan wannan kuma, idan jikin mutum ya saba da su, to, zai yi wahala ya iya saduwa da matarsa in baiyi amfani dasu ba. Assha! Kaga kenan matsala ta auku.

    Sirrin Gamsar Da Mace Wajen Saduwar Aure 

    Alqur’ani mai girma ya gama mana komai, domin ya sanar damu yadda za’a gamsar da mata wurin saduwa:

    نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأْتُوا حَرْثَكُمْ أَنَّىٰ شِئْتُمْ ۖ وَقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ وَاعْلَمُوا أَنَّكُمْ مُلَاقُوهُ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ 

    “matanku gonakinku ne, ku shiga gonakinku ta yadda kuke bukata, kuma kuyi wasanni dasu (a lokacinda zaku sadu dasu)”, Baqarah: 223. 

    Kenan idan mutum yayi wasaanin motsa sha’awa sosai kafin ya fara saduwa da iyalinsa, to, insha-Allahu zai gamsar da ita. Wasu suna yin kuskuren fahimtar cewa dadewa ana saduwa shine ƙwazo da burgewa. A likitance wannan ba gaskiya bane, domin ana so ne saduwa ta zama daga minti 3 zuwa 17. Idan ta kai minti 20, to, tayi yawa domin zata iya sanya ni’imar matar ta dauke, daga nan sai ta fara jin zafi, kila ma ayi mata rauni. Amma a lura ba wai ina nufin dole kada a wuce abinda na fada bane, domin wani yana iya yin minti 60 ma ba tare da matar ta tsawwala ba. Domin karanta bayani akan Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i shiga nan

    Menene Abun Yi?
    • Matsalar ƙanƙanacewar gaba gaskiya ce. Idan mutum yana da ita, to ya kamata ya tuntubi likita domin a dora shi akan maganin da ya dace, maimakon saye da kuma amfani da magunguna barkatai, wadanda idan illarsu ta taso bai san yadda zai magance ta ba.
    • Idan bai  zama dole ba, kada ka saba ma madam da dadewa ana saduwa, domin idan ka daina dadewa daga baya, to, akwai matsala fa.
    • Ka karfafa wasanni kafin ka fara, kamar yadda qur’ani yayi umurni.

    Domin karanta Kadan Daga Cikin Matsalolin da Mata Kan Fuskanta A Lokacin Zuwan Al’ada Danna nan

  • Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure)

    Ciwan Farfadiya (Epilepsy/Seizure)

    Wasu suna sakata daya daga cikin psychiatric disoders domin ciwone dayake shafar ƙwaƙwalwa 

    Ciwon farfadiya cuwo ne wandda yake zuwa da yawan jijjiga sakamakon excesive electrical discharge daga kwakwalwa yawancin jijjigar takan faru tsakanin sakanni 30 zuwa mintina 2.

    yayinda mai fama da wannan ciwo ya taso masa yana buƙatar abasa agajin gaggawa

    Yadda za’a taimakawa mai wannan ciwon wanda zai bada agaji ya nutsu sannan yatabbatarwa da mutane zai iya bayar da agajin

    A cire duk wani abu wanda yakan iya matsewa mara lafiya wuya ya tare mishi numfashi irinsu maballin riga na wuya,neck tie ko sarqar wuya,velt da sauransu 

    Kada a riƙe mara lafiyar da niyyar tsayar da jijjigar,hakan ka iya haifar da babbar matsala

    Kada a saka komai a bakin mara lafiyar,ko ayi ƙoƙarin riƙe mishi harshe ko kuma bude bakinshi,idan hakan bazai yuwuba a samu dai a dafe masa baki domin taimakawa karya daddatsa harshensa 

    A saka wani abu mara tudu sosai kuma mai taushi a kasan kansa domin gujewa fasa kai saboda jijjigar dayakeyi 

    Bayan jijjigar ta tsaya a ƙwantar da mara lafiyar a barin jikinshi na dama ko na hagu

    saboda ya samu sararin yin numfashi.

    Kada a rabu da mara lafiyar bayan jijjigar ta tsaya har saiya dawo cikin hankalinsa domin rashin hakan zai iya sakashi cikin dimuwa

    Domin karanta maganin Larurar Sanyin Gaba  (Genital Infaction) Dan nan ko kuma bayani akan lalura shanyewar barin jiki shiga nan

  • Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i

    Sanyi (Infection) Wanda Ake Ɗauka Ta Hanyar Jima’i

    Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa da shi ne ta hanyar jima’i wato. Mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu’amala da wasu mazan.  Haka shima zai iya shafawa matar sa idan yana da mata sama da ɗaya ko kuma idan yana neman mata.

    Namiji ba kasaifai yake ganewa yana da wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane shima yana dashi.

    Amma Idan Anyi Sa’a Ya bayannana Cikin Namiji Akwai Alamomin Kamar Haka;

    1. Jin zafi wajen fitsari
    2. Jin zafi bayan fitan maniyyi
    3. Fitar farin ruwa kaɗan
    4. Ƙaiƙayin gaba
    Alamomin a Jikin Mata
    1. Ƙaiƙayin gaba
    2. Jin zafi wajen fitsari
    3. Warin gaba
    4. Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass.
    5. Kwailewar farji

    Amma akwai wasu ɗabi’un da mata keyi hakan na jawo shi wannan ciwo na sanyi wato (infection)

    1. Yanayin tsaftace farji:

    Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu,  a ganinsu hakan shi ne dai dai. Kaninfari da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami,medicated soaps da sauransu.

    Wanann ba tsaftaceki za suyi ba, hasalima kina ƙara ɓata halittar farjinki. Kaman yadda mukayi bayani a baya ga me da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka er uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

    1. Yanayin wanke dubura bayan:

    kinyi bayan gida: Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shi ne ki fara daga gaba zuwa baya, ma’ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka suke yi. Wannan ɗabi’ar sam bata da ce ba. Idan kika fara daga baya kina ɗebo ƙwayoyin cutar da ke cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba. Shi farji baya san baƙon abu a tattare dashi.

    Domin karanta Larurar Sanyin Gaba Wato Genital Infaction  Ko Ciwon Hanta  danna koren rubutun nan

  • Yadda Ake Tsaftace Baki

    Yadda Ake Tsaftace Baki

    Baki na da buƙatar kulawa ta musamman, domin kawar da wari, da cututtuka, da zubewar haƙora.

    Rashin tsaftace baki na haifar da matsala a tsakanin ma’aurata sosai. Shi ne abin dake sa ƙiyayya. Har ma wannan matsala tai sanadin rabuwar ma’aurata da yawa.

    A dinga yin aswaki a duk Lokacin da aka ci wani abu mai sa baki ya yi wari. Yawan aswaki na da muhimmanci.

    Muna da abin koyi daga Annabi (S.A.W) . Assayida A’isha (RA) tana cewa: Annabi salallahu Alaihi Wasallam yana yin aswaki a duk lokacin da zai shiga gida.

    In muka duba Wannan hadisi, za mu ga lallai akwai bukatar mu dinga yawaita aswaki.
    Annabi (S.A.W) ya ce: “Ba don ina jiye wa al’ummta tsoro ba, da na umarce su da yin aswaki a kowacce sallah.”
    ( Bukhari da Muslim)

    Cikar kyawu da gayu shi ne, bakin mutum ya kasance fes-fes. Ta yadda a ko’ina mutane za su yi magana da kai cikin daɗin rai.

    HANYOYIN DA AKE TSAFTACE BAKI

    Wanke baki aƙalla sau biyu a rana. Kafin ƙarin kumallo da bayan cin abincin dare.

    Wanke kowanne sako na baki, da lungu, da saman harshe.

    Yin amfani da mai na wanke baki. Da amfani da ruwan kuskura baki .

    Sanya kwayoyin kaninfari kamar 5 a baki. A tauna sai a rike ruwan. Tsawon mintuna aƙalla 3. Sai a zubar dashi. Safe da yamma na kwana uku. Acikin kowanne wata. Zai kawar da warin baki, har ma da wasu cututtuka na haƙori.

    A ƙarshe a kula da canja abin goge haƙori a kowanne wata biyu. Da kuma ganin likitan hakori sau biyu a shekara.

    Littafin da aka duba:
    Umdatul ahkam -babu Asiwak.