Yadda Ake Tsaftace Baki

0
2770

Baki na da buƙatar kulawa ta musamman, domin kawar da wari, da cututtuka, da zubewar haƙora.

Rashin tsaftace baki na haifar da matsala a tsakanin ma’aurata sosai. Shi ne abin dake sa ƙiyayya. Har ma wannan matsala tai sanadin rabuwar ma’aurata da yawa.

A dinga yin aswaki a duk Lokacin da aka ci wani abu mai sa baki ya yi wari. Yawan aswaki na da muhimmanci.

Muna da abin koyi daga Annabi (S.A.W) . Assayida A’isha (RA) tana cewa: Annabi salallahu Alaihi Wasallam yana yin aswaki a duk lokacin da zai shiga gida.

In muka duba Wannan hadisi, za mu ga lallai akwai bukatar mu dinga yawaita aswaki.
Annabi (S.A.W) ya ce: “Ba don ina jiye wa al’ummta tsoro ba, da na umarce su da yin aswaki a kowacce sallah.”
( Bukhari da Muslim)

Cikar kyawu da gayu shi ne, bakin mutum ya kasance fes-fes. Ta yadda a ko’ina mutane za su yi magana da kai cikin daɗin rai.

HANYOYIN DA AKE TSAFTACE BAKI

Wanke baki aƙalla sau biyu a rana. Kafin ƙarin kumallo da bayan cin abincin dare.

Wanke kowanne sako na baki, da lungu, da saman harshe.

Yin amfani da mai na wanke baki. Da amfani da ruwan kuskura baki .

Sanya kwayoyin kaninfari kamar 5 a baki. A tauna sai a rike ruwan. Tsawon mintuna aƙalla 3. Sai a zubar dashi. Safe da yamma na kwana uku. Acikin kowanne wata. Zai kawar da warin baki, har ma da wasu cututtuka na haƙori.

A ƙarshe a kula da canja abin goge haƙori a kowanne wata biyu. Da kuma ganin likitan hakori sau biyu a shekara.

Littafin da aka duba:
Umdatul ahkam -babu Asiwak.

labarin da ya wuceTarihin Samuwar Shafukan Sada Zumunta
Labarin na GabaYadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.