Tag: tsafta

  • Yadda Za Ki Gyara Kanki

    Yadda Za Ki Gyara Kanki

    Yadda Za ki Gyara Kanki. Akan so mace ta zauna kamar shinkafa a gidan mijinta; kar ki bari ya daina yinki, kar ki bari ya ƙosa dake.

    Kin san shinkafa za a iya sarrafata ta kowace irin launi. Misali; za a iya yin tuwon shinkafa, jellof, farar shinkafa, dambun shinkafa, fried rice dadai sauransu.

    Shinkafa ce za a shekara da shekaru ana cin ta a gida ba a gaji da ita ba, da zarar an yi sati ɗaya babu ita, ranar hankali ya tashi. Yara da kansu za ka ga suna cewa Daddy ba shinkafa.

    Don haka ki zama kina da dabarar iya kwanciya da mijinki, kullum da irin kwanciyar da za ki yi masa, ta yau daban ta gobe daban.

    Sai ki ga kin daɗe kina zamani a gidan mijinki, sai ki gan ki kullum amarya kike.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Daya Kamata A Sani Game Da Ciwon Sanyi danna nan.

  • Yadda Ake Tsaftace Baki

    Yadda Ake Tsaftace Baki

    Baki na da buƙatar kulawa ta musamman, domin kawar da wari, da cututtuka, da zubewar haƙora.

    Rashin tsaftace baki na haifar da matsala a tsakanin ma’aurata sosai. Shi ne abin dake sa ƙiyayya. Har ma wannan matsala tai sanadin rabuwar ma’aurata da yawa.

    A dinga yin aswaki a duk Lokacin da aka ci wani abu mai sa baki ya yi wari. Yawan aswaki na da muhimmanci.

    Muna da abin koyi daga Annabi (S.A.W) . Assayida A’isha (RA) tana cewa: Annabi salallahu Alaihi Wasallam yana yin aswaki a duk lokacin da zai shiga gida.

    In muka duba Wannan hadisi, za mu ga lallai akwai bukatar mu dinga yawaita aswaki.
    Annabi (S.A.W) ya ce: “Ba don ina jiye wa al’ummta tsoro ba, da na umarce su da yin aswaki a kowacce sallah.”
    ( Bukhari da Muslim)

    Cikar kyawu da gayu shi ne, bakin mutum ya kasance fes-fes. Ta yadda a ko’ina mutane za su yi magana da kai cikin daɗin rai.

    HANYOYIN DA AKE TSAFTACE BAKI

    Wanke baki aƙalla sau biyu a rana. Kafin ƙarin kumallo da bayan cin abincin dare.

    Wanke kowanne sako na baki, da lungu, da saman harshe.

    Yin amfani da mai na wanke baki. Da amfani da ruwan kuskura baki .

    Sanya kwayoyin kaninfari kamar 5 a baki. A tauna sai a rike ruwan. Tsawon mintuna aƙalla 3. Sai a zubar dashi. Safe da yamma na kwana uku. Acikin kowanne wata. Zai kawar da warin baki, har ma da wasu cututtuka na haƙori.

    A ƙarshe a kula da canja abin goge haƙori a kowanne wata biyu. Da kuma ganin likitan hakori sau biyu a shekara.

    Littafin da aka duba:
    Umdatul ahkam -babu Asiwak.

  • Yadda Ake Turaren Ɗaki Na Musamman

    Yadda Ake Turaren Ɗaki Na Musamman

    Turaren ɗaki na ruwa mai daɗin ƙamshi, yana sa ɗakunanmu su zama na Musamman.

    Babu shakka ɗakunanmu na da buƙatar kulawa ta Musamman, Domin su zama wajen hutawarmu tare da mazajenmu. Mu dinga tsaftace su, kuma mu dinga yawan sa turaren ɗaki na Musamman akai-akai.
    Haɗin wannan turare, yana da sauƙin haɗawa. Kuma da kuɗinki ɗan kaɗan za ki haɗa shi.

    KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA BAKHUR :

    Ruwan Bakhur
    Ambur
    Turaruka Madarori: Sk, Nasis , Sultan.

    Za ki juye ambur a roba. Sai ki dake ambur shi ma ki zuba a ciki. Sai ki juye madarorin turaren Sk , Nasis , sultan. A dinga yarfashi a kafet , dardumar sallah da shimfidar gado.

    KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA RUWAN SS:

    Turaren ruwa na SS
    Turaren kafi-kafi
    Madarar ambur
    Ambur dakakke
    Itacen Demask niƙaƙƙe
    Kafur

    Idan kika haɗa su, sauran sai ki zuba cikin ruwan turaren SS. Ki juya su haɗe sosai. Sai ki zuba madarar ambur. Sai ki rufe su cikin mazubi. Ki dinga yarfawa a shimfidun falonki da ɗaki. Dardumar sallah, harma da jikin kujerunki.

    Domin karanta yadda ake turaren wuta danna koren rubutu nan

  • Yadda Ake Gyaran Kafa Na Musamman (kaushi ko faso)

    Yadda Ake Gyaran Kafa Na Musamman (kaushi ko faso)

    Mafi yawan tafin ƙafar mutane na bushewa,  Fatar ƙafa ta yi ƙarfi,  har ma ta dinga tsattsagewa. Ga shi tana yawan kwasar datti.

    Wannan yasa ƙafafuwanmu na da buƙatar gyara na musamman.

    HANYOYIN GYARAN KAUSHIN ƘAFA:

    1 – Wanke Ƙafa a duk lokacin da mutum yai wanka. Koda kuwa da dutsen goge kaushi ne.

    2 – Wankin ƙafa da kayayyakin wankin ƙafa na zamani. Wannan ya zama kowane sati.

    3 – Shafa mai basilin a tafin kafarmu kullum.

    4 – Sanya safa na matuƙar gyara kafa. Ya hana ta lalacewa.

    5 – Shafa man kaɗanya a dinga kwana da shi.

    YADDA AKE GYARAN KAUSHIN ƘAFA :

    MaN kaƊanya
    Spirit hydrogen
    Ruwan sabulu

    Za ki haɗe man kaɗanya da spirit kaɗan waje ɗaya. Sai ki zuba su cikin roba. Ki dinga shafawa a ƙafa, duk lokacin wanka. A ba shi kamar daƙiƙa 10 sannan a sa ruwan sabulu a wanke ƙafar da soso na kaba.

    A taƙaice dai waɗannan hanyoyi za su sa, ka ji daɗin ƙafarka. Za ta yi laushi , ta yi fes , kuma abin sha’awa. domain karanta yadda ake gyaran gashi na Musamman ko gyaran jiki na musamman danna koren rubuntu nan.

  • Yadda Ake Gyaran Jiki Ya Yi Laushi Kuma Ya Yi Kyau

    Yadda Ake Gyaran Jiki Ya Yi Laushi Kuma Ya Yi Kyau

    Gyaran jiki yana taimaka wa Namiji ko Mace ta daɗe tana more jikinta. Fatar mutum ta zama lafiyayya, kuma abin sha’awa. Shi ne za ka ga mace komai yawan shekarunta, haka komai yawan haihuwarta, Tana da kyakkyawan jiki.

    Gyaran jiki ya samo asali ne daga wajen Larabawa. Sai Barebari wato daga Maiduguri, a nan Ƙasar NIjeriya. Haka ma Turawa sun yi mayuka kala-kala domin gyara fata.
    Sai dai duk Sanda mutum yake so zai dinga gyara jiki. To ya zama tilas ya kula da mafi muhimmanci, wato ya bi matakai na gyara jiki.

    MATAKAN GYARAN JIKI:

    1 – Cin lafiyyen abinci.
    2 – Yawan Shan ruwa .
    3 – Yawan Cin ‘ya’yan itatuwa.
    4 – Atitsaye ( motsa jiki) .
    5 – Amfani da kayan gyaran jiki ( Dilka).

    GYARAN JIKI NA DILKA:

    Za a zuba Dilka a cikin mazubi. Sai a zuba masa ruwan zafi. Bayan jimawa sai a zuba kurkum, da mai zaitun , da ƙwai .
    Sai a ƙara ruwa ɗan dai-dai. A shafe dukkan jiki har fuska. Idan ya bushe sai a murje jiki da shi.

    GYARAN JIKI NA ALKAMA:

    Za a niƙa Alkama ne, a tankaɗe ta, tai luƙwui. Sai a soya ta kamar yadda ake idan za a yi kunun alkama.
    Za a zuba wa soyayyiyar alkama yis. A zuba ruwa a kwaɓa ta. A shafe duk jiki da ita. Bayan ɗan lokaci, sai a dinga murje jiki ko’ina.

    GYARAN JIKI NA KHALDA ( OATS):

    Za a zuba wa khalda (Oats) madara. Sai kuma a matsa lemon tsami kaɗan. A juya shi a kwaɓa sosai. Sai a shafa amma shi duk jiki. Bayan ɗan lokaci sai a murje duk jiki.
    A ƙarshe, lallai akwai buƙatar mu dinga waiwayar gyaran jikinmu, duk sati in da hali. Ko kuma duk Wata. Ya danganta da yadda ake da hali, lokaci da himma.
    Duba yadda ake ado da kwalliya ta Musamman.
    Litattafai da aka duba
    Amina Mar’atussaliha
  • Yadda Ake Wanke Flask Ɗin Ruwan zafin Da Ya Dafe Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Wanke Flask Ɗin Ruwan zafin Da Ya Dafe Cikin Sauƙi

    Yadda za a wanke flask ɗin ruwan zafin da ya dafe cikin sauƙi

    matakai 3 kacal sun isa.

    1. A sami baking soda,
    sai a zuba kamar cokali 4 ko 6 sai a zuba veniger wato ma’u khal, sannan a zuba ruwan zafi a duk a cikun flask ɗin.

    2. Sai a bar shi tsawon mintuna 8-10 amma fa kar a rufe shi da murfin don zai iya ɓaci, sai a saka shi a ciki faranti ko (sink). Don in an bar shi haka, zai taso sama.

    3. A sami burushin wanke kwalba a gurje shi tas, sai kuma a sa ruwa a ɗauraye.