Yadda Ake Turaren Ɗaki Na Musamman

0
4669

Turaren ɗaki na ruwa mai daɗin ƙamshi, yana sa ɗakunanmu su zama na Musamman.

Babu shakka ɗakunanmu na da buƙatar kulawa ta Musamman, Domin su zama wajen hutawarmu tare da mazajenmu. Mu dinga tsaftace su, kuma mu dinga yawan sa turaren ɗaki na Musamman akai-akai.
Haɗin wannan turare, yana da sauƙin haɗawa. Kuma da kuɗinki ɗan kaɗan za ki haɗa shi.

KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA BAKHUR :

Ruwan Bakhur
Ambur
Turaruka Madarori: Sk, Nasis , Sultan.

Za ki juye ambur a roba. Sai ki dake ambur shi ma ki zuba a ciki. Sai ki juye madarorin turaren Sk , Nasis , sultan. A dinga yarfashi a kafet , dardumar sallah da shimfidar gado.

KAYAN HAƊA TURAREN ƊAKI NA RUWAN SS:

Turaren ruwa na SS
Turaren kafi-kafi
Madarar ambur
Ambur dakakke
Itacen Demask niƙaƙƙe
Kafur

Idan kika haɗa su, sauran sai ki zuba cikin ruwan turaren SS. Ki juya su haɗe sosai. Sai ki zuba madarar ambur. Sai ki rufe su cikin mazubi. Ki dinga yarfawa a shimfidun falonki da ɗaki. Dardumar sallah, harma da jikin kujerunki.

Domin karanta yadda ake turaren wuta danna koren rubutu nan

labarin da ya wuceYadda Ake Gyaran Kafa Na Musamman (kaushi ko faso)
Labarin na GabaYadda Ake Special Cincin
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.