Yadda Ake Gyaran Gashi Da Sanya Shi Yayi Tsawo

0
14

Gyaran Gashi Da Tsawo: Zaki samu shinkafa kowace iri ce rabin kofi; ki wanke ta sai ki zuba mata ruwa kofi biyu; sannan ki samu mazubi mai murfi ki rufe kibarshi har tsawon awa 24.

Sai ki ɗauka ki riƙa murzawa kamar yadda kikeyi in zaki wanke, har tsawon minti goma. Sai ki tace ruwan kisamu costor oil kizuba ƙaramin cokali huɗu aciki sai ki ɗauka ki rinƙa shafawa akan ki.

Ki tabbatar kin raba kan gida huɗu; sai ki shafa a kowanne bangare; sannan ki ɗaure ki barshi har zuwa safe ki wanke.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Gyaran Gashi danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita
Labarin na GabaKaratun Surah A Cikin Sallah