Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

0
71

A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa, zaɓar abubuwan da za su taimakawa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kika San yanayin fatarki Sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum. misali:

  1. GOGE KWALLIYA KAFIN BACCI

Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani to yana da kyau ki samu abinda za ki goge ta tas kafin ki kwanta bacci. Ko da wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa amma Idanuwa  da laɓɓa suna buƙatar kula ta mussamman saboda haka sai ki samu abun goge kwalliya (wiper)jiƙaƙƙe ki sake gogewa a hankali.

Domin karanta Yadda Za Ki Inganta Halayyarki Da Ɗabi’u Masu Kyau Danna nan

2. WANKE FUSKA

Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya Sai Kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi ba mai zafi ba sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska sannan a sake ɗaurayewa.

3. AMFANI DA TONER

Bayan an wanke fuska ana so a shafa toner a samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan sai a dinga shafawa a hankali banda gurin ido sannan ba a wankewa.

Domin karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki danna koren rubutun nan

4. AMFANI DA MOISTURIZER

Bayan toner ta bushe akan fuskarki yana da kyau a yi amfani da moisturizer akan fuska har da tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido Sai ki samu wani mai na musamman.

5.YIN MURZA (SCRUBBING)

Ana iya yin murza ta musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa sai kina dangwala da hannunki kina murzawa a hankali akan fuskarki. Bayan wasu mintuna sai a wanke da ruwan ɗumi.

6.YIN AMFANI DA (SUNSCREEN)

Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

Domin karanta Yadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki Danna nan

labarin da ya wuceYadda Zaki Inganta Hallayarki Da Ɗabi’u Masu Kyau
Labarin na GabaYadda Za Ki Nunawa Mijinki Tsantsar Kula
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.