Yadda Za Ki Yi Mu’amala Da Uwar Mijinki

0
768

Mahaifiyar Namiji ita ce Mace mafi kima da daraja awajensa. Kuma ita ce mafi kusanci da shi .

Ita ce dan mukullin arzikinsa , daukakarsa , da albarkarsa. Allah Ta’ala ya bawa Annabinsa ( SAW) Labarin Uwaisul Qarni. Manzon Allah (S.A.W) ya ba da labarin sa a wajen sahabbansa. Duk da girman Matsayi irin na sayyadina Umar(R.A) . Amma yai masa wasiyya da in ya gamu da shi Uwaisul Qarni. Ya nemi yai masa addu’a, hakan kuma aka yi.

Halaka ce Babba ki bar mijinki ya na sabawa iyayensa.

Cikin suratu Baqara: 73.
:”… Kuma ku kyautatawa iyayenku ku zama masu biyayya a gare su”.

A duk lokacin da Uwa ta sawa danta Namiji albarka. Wannan Albarka tana bibiyarsa da kuma’ya’yansa. Wato daya daga cikin hanyar da ‘yayanki za su yi albarka. Shine ta wajen Uwar mijinki.

Ya zama dole ne ga kowacce mace. Ki san yadda za ki yi mu’amala da Uwar mijinki.

Mu'amala Da Uwar Mijinki

 

HANYOYIN MU’AMALA DA UWAR MIJI

1 HAKURI: Yin hakuri da ita , ko da ta fadi bakar magana . Ka da ki mayar ma ta. Yin hakuri da yawan bukatunta. Shi hakuri dukkaninsa alkhairi ne.

2 – KARANTA TA: Akwai bukatar ki karanta uwar mijinki sosai. Kuma ki koyi irin yadda ake ma mai irin halayenta. Domin kuwa ana samun wasu masu kaushin Hali, da sa ido , da kishi , da rowa , da mita da dai sauransu.

3 – GIRMAMATA: Amsawa da yin abin da tai umarni. Yin waya ki gaishe ta. Ziyararta domin ku dan zanta. Aika ma ta da jikokinta su gaishe ta.

4 – TAIMAKONTA : Duk sanda ki ka kai ma ta ziyara. Ki tayata aikin da kika tarar ta na yi. Shara , girki , ….

5 – KYAUTA : Kyauta ta na faranta rai. Kuma alama ce ta ka na son wanda ka baiwa. Ta na nuna ka na tunawa dashi.
Daga lokaci zuwa lokaci. Dai-dai karfinki ki dinga aikawa da Uwar mijinki. Sabulu, turare, Goro , lalle , da kudi .

Da kuma yi ma ta kyauta alokuta na Musamman. Kamar da azumi , da sallah , da dai sauransu.

6 – KUNYA : Ki dinga jin kunyar iyayen mijinki.

A Duk lokacinda mijinki ya ga kina bawa mahaifiyarsa kulawa. To zai fahimci irin kaunar da ki ke masa. Zai kara kaunarki , ya ba ki Matsayi na Musamman a Zuciyarsa. Ga wani labarin Wata Mata da Mijinta.

Ma’aikaciya ce ni mai himma sosai, da bana son wasa da aikina. Sai mu ka wayi gari surukata ta rasu ( Uwar Mijina) . Na roki a bani lokaci ,domin ayi janaizarta da zaman ta’aziyya. Amma fir Shugabana da na ke karkashinsa ya ki amincewa. Sai dai ya bani awa biyu rak. Na ce masa gaskiya mijina na tsananin bukatata . Domin bashi da tamkar mahaifiyarsa. Shugabana ya ce: Ni dai awa biyu na ce . Muddin ki kai zamanki kuwa to zai zama kin sallami kanki.

Nai tafiyata kawai, cike da tsoron ma na rasa aikina. Domin gaskiya Mijina ya fi min aikina. Nai zama na ina lallashi da tausayawa mijina har akai uku. Bashakka mijina yai farin ciki da irin kulawata. Na samu karin soyayyarsa da daraja awajensa. Ya kance min:” Matata ba zan manta da irin abin da ki ka min ba. A lokacin da na rasa mahaifiyata”.

Allah Mai iko sai gashi ban rasa aikina ba. Shugabana ya bar wajen aikinmu. Ni kuma aka min shugabanci.

A karshe dai taimakawa mijinki ya kula da iyayensa. Zai za me miki alkhairi cikin rayuwarki.
Wani Bature ma ya ce ,ana iya gane irin son da mace ke ma. Idan aka ga yadda ta ke son iyayenka.

Domin karanta yadda zaki mayar da gidanki masarautar ki danna koren rubutun nan

Litattafai da aka duba:

1 – Qur’an
2 – Riyadu Salihin.

3 – 101 Amazing ways to say”I LOVE YOU !”. By Cucan Pemo.