Awon Juna Biyu

0
59

Awon ciki shi ne gwaji wanda ake yi a lokacin da mace take jin alamu a jikinta kamar ta sami juna biyu. Sakamakon awon shi ne yake tabbatar da gaskiya ko akasin abinda take hasashe. Idan sakamakon ya nuna tabbaci (positive), to, shikenan juna biyu ya tabbata. Idan kuma ya nuna rashin tabbaci (negative), to, juna biyu bai tabbata ba.

RABE-RABEN AWON JUNA BIYU 

Awon juna biyu ya rabu zuwa manyan gidaje guda biyu:

  1. Na fitsari (urine test)
  1. Na jini (blood test)

Amma bayan waɗannan gwaje-gwajen, ana yin wasu, sai dai su ba na tattabatar da shigar juna biyu ba ne, a a na bibiyar halin da juna biyun yake ciki ne bayan an tabbatar da shi. Waɗannan sun haɗa da gwajin hoto na ciki (ultrasound scan) da kuma na jini kamar rhesus factor domin gane ko akwai protein a ƙwayoyin jinin mace, chorionic villus sampling (CVS) da amniocentesis domin gane ko jariri yana da nakasa, glucose test domin gane yiwuwar ciwon sugar, group B streptococcus test domin gane ko uwa tana ɗauke da ƙwayoyin cutar da zata iya sanya ma jaririnta a lokacin haihuwa, da sauransu.

AWON JUNA BIYU NA FITSARI

Ana amfani ne da wani tsinke wanda ake kira “strip”, kuma akwai shi na kamfanoni da yawa kamar First Response Early Result, Clinical Guard GCH Pregnancy Test Strip, Clear Blue Rapid Detection, Early@Home Pregnancy Test Strip, Wondfo Pregnancy Test Strip, da sauransu.

A jikin tsinken akwai sinadarai da ake kira “immunochemical reagents” masu tantance ko akwai sinadaran human chorionic gonadotropin (hCG) a cikin fitsarin. Jikin mace zai fara samar da sinadarin hCG a cikin jininta da zarar ’ya’yan maniyyin namiji (sperm cells) sun ƙyanƙyashe ƙwan haihuwarta (ovum) kuma ƙwanƙyasasshen ƙwan ya maƙale a cikin mahaifa. Don haka idan aka tsoma tsinken strip a fitsarinta zai canza launi, ko ya nuna layi biyu, ko ya nuna alamar tarawa (+).

Domin samun kyakkyawan sakamako, ana buƙatar a yi amfani da fitsarin farko na safe. Sa’annan kada a sha ruwa da yawa domin fitsarin ya yi kauri (concentrated). Idan akwai hCG a fitsarin, to, zai nuna sakamako cikin minti 5 zuwa 10, ya danganta da kamfanin da ya yi tsinken. Kuma an fi buƙatar yin test ɗin kwana 7 zuwa 14 da gama al’ada. Idan kuma tsinken bai canza ba, to, babu juna biyu kenan.

Abubuwan da suke sanya a yi awon fitsari kuma a rasa ganin sakamako mai kyau duk da mace tana jin alamun ciki sun haɗa da lalacewar tsinken strip ɗin (expired strip), rashin isasshen fitsari a lokacin da aka yi test ɗin, ko fitsarin da ya haɗu da ruwa (diluted urine). Yawancin mata sun fi son awon juna biyu na fitsari saboda sauƙin kuɗinsa da kuma rashin ɗaukar lokaci kafin a ga sakamako.

AWON JUNA BIYU NA JINI

Ana yin sa ne a ɗakin bincike na kimiyya (laboratory). Shi ma abinda ake dubawa a cikin jinin shi ne sinadarin hCG. Wannan awon ya fi tabbas saboda komi ƙanƙantar sinadarin ana iya ganinsa.

SHIN SAKAMAKON AWON FITSARI DA NA JINI ZA SU IYA NUNA ƘARYA?

Allah (SwT) da Manzonsa (SAW) su kaɗai ne ba su kuskure. Don haka mai yiwuwa ne shi ma sakamakon awon juna biyu ya nuna kuskure. Amma kashi 99 bisa ɗari (99%) na awon juna biyu, fitsari ko jini, suna ba da sakamako daidai. Sai dai idan an yi kuskure wajen yinsu, ko kuma wanda ya yi bai fahimci yadda ake yi ba. 

SHAWARA

Idan kina shakkun  sakamakon awon fitsari, to, a sake yi bayan wani lokaci, haka kuma idan na jini ne, ko kuma a canza wurin awon. Allah yasa mu gama haife-haife lafiya, Allah ya ba mu zuriyya ɗayyiba, amin. 

Danna nan don karanta yanda ake amfani da na’urar gwajin ciki (juna biyu)

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceKafar Sadarwar Zamani, Amfani Da Ƙalubalenta
Labarin na GabaNasiha