Wannan Shi Ne Miji Nagari

0
1759

Duk wani miji a duniya yana so da neman mace tagari wacce a idonta akwai tausayawa, a wajenta akwai hutu da nutsuwa, a zuciyarta akwai so da ƙauna, kamar yadda shi ma yake siffantuwa da siffofin nagarta.

  • Miji nagari shi ne mai tsoron Allah a cikin maganganunsa da ayyukansa, yana taimaka wa iyalansa wajen samar da asalin tushen ƙauna, nutsuwa da girmamawa, wanda a kansu Musulunci ya gina zamantakewar aure.
  • Miji nagari shi ne wanda ya ɗauki Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam abin koyin sa wajen kyautata mu’amala da iyalai, taya su aikin gida, ɗebe musu kewa, sanya farin ciki da annashuwa a zuciyarsu tare da kauda kai daga rauni da rangwamen tunaninsu.
  • Miji nagari yana sauraron matarsa, ya fahimci damuwa da buƙatunta ya kuma baza tunani da ƙwarewarsa wajen magance matsaloli da damuwar farin cikin ransa.
  • Miji nagari yana riƙon matarsa a matsayin abokiyar rayuwarsa, rabin addininsa, mahaifiyar ‘ya’yansa, yana nuna mata ƙauna, kulawa da girmamawa, tare da ƙarfafa mata gwuiwa wajen ayyukan alkhairi.
  • Miji nagari yana bai wa matarsa lokaci, tare da tantance tsakanin haƙƙoƙin mahaifiya da na matarsa. Mahaifiya: ƙauna, girmamawa da biyayya. Mata: ƙauna, girmamawa da tausayawa.
  •     Matuƙar an samu mace tagari a gidan miji nagari, hakan zai ba su damar zama da rayuwa tagari, tare da samar da zuri’a tagari wacce Annabin Rahma sallallahu alaihi wa sallam zai yi alfahari da ita. Allah Jalla wa Alaa yana cewa:

Wal baladud dayyibu yakhruju nabaatuhu bi izni Rabbihi wallazi khabutha laa yakhruju illa nakida…” 6

RUFEWA

Kiyaye ladubban zamantakewar aure shi zai bai wa auren armashi da sakamako mafi inganci, wanda wannan sakamakon, shi zai sanya al’umma ta zama a kan saiti, da ci gaba wanda akasin haka, zai jefa al’umma cikin mummunar makoma, Allah Jalla wa Alaa ya kiyaye. Dr. Muhammad Sani Umar yana cewa:“Masu miyagun tunani sun ɗago kai, suna aiki dare da rana, domin ganin cewa sun rushe ginin wannan al’umma wanda farkon tubalinsa an gina shi ne daga gida.

Idan miji da mata suka sami haɗa kansu bisa turba ta Musulunci, to sai ka samu ‘ya’yansu sun taso cikin kyakkyawar tarbiyya, To amma da zarar aka samu kishiyar haka, wato miji da mata suka gina rayuwa ba a kan turba ba, to lamarin ‘ya’yansu ba zai yi kyau ba”.

Rabbana hab lana min azwaajina wa zurriyyatina qurrata a’ayunin waj’alna lil muttaqina imaama. Wa antal musta’aan wa alaikal balaagh wala haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem. Wa sallallahu wa sallam alaa nabiyyina Muhammad wa aalihi wa sahb ihi ajma’in.

Subhanakallahumma wa  bihamdika asshahadu an laa ilaha illa anta astaghfiruka wa atuubu ilaika.

karanta yadda za ki mayar da gidanki masarautarki  ko ladubban tarewa a gidan miji ko Muhimmancin Aure a rayuwa domin sauke cikakken littafin ladubban zamantakewar aure danna koren rubutu

labarin da ya wuceWannan Ita Ce Mace Tagari
Labarin na GabaLadubba Zaman Ma’aurata