Tatsuniyar Kyawawa Matuƙa

0
3

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can ƙasar Turu, an yi wani mutum mai ’ya’ya mata biyu. Allah ya yi su kyawawa. Ga haske, in ka gan su kamar taurari. Ɗaya daga cikin ’yammatan ba ta fita ko da ƙofar gida. Amma ɗayar takan zauna a ƙofar gida, kuma duk wani saurayi da ya zo, sai ta ce za ta kira masa ’yar’ uwarta.

Ana nan, ana nan, sai wata rana wani dodo ya rikiɗa ya koma saurayi, ya je gidansu. Sai ya tarar da yarinyar nan da kan zauna a ƙofar gida, ya yi mata sannu; ita kuma ta mayar masa. Sai ya ce: “Kai amma yarinyar nan na yaba da kyaunki.” Sai ita ko ta ce masa: “Ai da ka ga ’yar’uwata da ba za ka yi mini magana ba, balle ma ka ce ina da kyau.”

Dodo ya sami gangara, sai ya ce: “To, ko za ki kira mini ita?” Sai yarinyar ta shiga ta yi wa ’yar uwarta magana. Ita kuma ta tambaye ta: “Da wa ya yi kama?” Sai ta ce: “Ya yi kama da mahaifiyarmu.” Da ta ji haka sai ta ce: “A a, ai babu wani saurayi da ya isa ya gwada kansa da mahaifiyata. Ba zan je ba.”

Daga nan mai zama a bakin ƙofa ta je ta ba mutumin haƙuri. Ba tare da ya nuna fushi ba, ya kama hanya ya yi tafiyarsa. Amma saboda nacinsa, kullum sai ya je gidan, yana ƙoƙarin ganin yarinyar. Sannu a hankali har yarinyar nan mai tsayawa a waje ta gayawa mahaifinsu halin da mutumin nan yake ciki na tsananin ƙaunar da yake yi wa ‘yaruwarta.

Da mahaifinsu ya ji bayaninta, sai yace: “Duk sanda ya zo ki shigo ki gaya mini. Can kuwa sai ga mutumin. Nan da nan ta yi masa bayani cewa: “ka jira in yi wa sanar da mahaifinmu cewa ka iso. Mahaifin yaran ya fito, suka gaisa da baƙon, ya kuma sanar da shi cewa yana so ne ya auri ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, wato wadda take cikin gida.

Sai baban yaran yace masa ya jira yana zuwa. Ya shiga gida. Da shigarsa, sai ya ɗauki yarinya ya sa ta a cikin rumbu. Sai ya kira mutumin yace: Ga wannan rumbu ka kai wa kakannin yarinyar a garinsu. mutumin nan ya ɗauki rumbu, ya kama hanya. Yana cikin tafiya sai ya yi tun tuntuɓe ya faɗi; yarinyar da ke cikin rumbun ma ta faɗo.

Da yarinyar ta ga mutumin sai tace: “sannu kawu” Sai mutumin ya ce: “Ashe ke ce a ciki?” Da ta lura a daji suke, sai ta gudu ta tasamma gida. Washe-gari sai mutumin ya koma gidansu yarinyar, ya tambayi labarinta, to amma kafin ya je, mahaifinta ya tambaye ta abin da ya farutsakaninta da mutumin, ta kuma gaya masa yadda mutumin ya yi tuntuɓe ya faɗi, da yadda ta yi masa sannu bayan ta faɗo daga rumbu.

Da mahaifinta ya ji haka sai ya ce: “Ai ko nai kamata ki yi masa sannu ba da ya faɗi. “Sai ya sake sa ta a cikin rumbu, ya sake ɗora wa mutumin. Mutumin ya kama hanya, sai ya sake yin tuntuɓe a cikin daji, ya faɗi. Yarinya ta mance da abin da mahaifinta ya gaya mata, sai ta yi masa sannu.

Shi kuwa ya kama ta, ya fyaɗa da ƙasa, ya mueɗe mata wuya, nan take ko haurawa ba ta yi ba. Daga nan sai ya ɗauki gawar ya jefa a cikin jakarsa. Ya ajiye jakar a gindin wata bishiya, ya tafi neman itacen da zai yi tsire da gawar, ya gasa. Ashe duk abin da suke yi wata tsohuwa tana ganinsu, sai ta yi sauri ta cire gawar yarinyar ta jidi duwatsu ta zuba masa a cikin jakar, ta gudu da gawar, ba ta tsaya ko ina ba sai gidan mahaifin yarinyar nan.

Ta kai masa gawar ‘yarsa. Da dodo ya samo itacen, ya ɗauki jakarsa ya je inda zai gasa yarinyar nan ya ci nama, sai ya juye duwatsu a tukunya ya hura wuta, ba tare da ya san duwatsu yake dafawa ba. Can da ya ji dutse ya fashe sai ya ce: “Yawwa wannan ƙwaƙwalwarta ce ta fashe. Sai ya ɗebi fasasshen dutse ya cinye.

Da tsohuwa ta kai gawar sai ta ce da iyayenta: Ku duba abinda kuka sa aka yi wa ‘yarku.

Mahaifin yarinyar ya yi wa tsohuwa godiya, suka yi sallama ta tafi. Tsohuwa na tafiya, sai uban ya ƙone gawar yarinyar, ya zuba tokarta a cikin mararaki, ya zuba ruwa, sai ya rataye mararakin nan; sannu a hankali ruwan tokar ya fara ɗigowa daga mararaki. Da ya ɗigo, sai yace: “Wannan hannun Sirandi ne.” Can kuma idan ruwa ya sake ɗiga sai yace: “Wannan kuma ƙafarta ce.”

Da haka dai, kafin wani lokaci yarinyar nan ta haɗu tsaf ta miƙe. Washe-gari kuma sai Dodon nan ya sake zuwa ƙofar gidansu yarinyar. Da mai zama a ƙofar gida ta gan shi, sai ta shiga gida da gudu ta gaya wa mahaifinta cewa ga fa mutumin nan ya sake zuwa. Sai mai gidan ya fito. Da suka gaisa sai ya tambayi baƙon wa kuma ya zo nema.

Shi kuwa ya ce ya zo ne yana neman wannan yarinyar da ta gudu ta shiga gida, wai ya aura. Sai mahaifinta ya gaya wa baƙon nan cewa ai yarinyar ta yi miji tuntuni. Sai bai komai ba ya tafi abinsa. Bayan ’yan kwanaki aka ɗaura wa yarinyar aure ta tare. Da mutumin ya sake dawowa sai aka ce masa yarinyar ta bar gidan.

A nan take sai ya kife. Can cikin dare kuma sai ya rikiɗa, ya je inda yarinyar take ya ce zai kashe ta. Sai yarinyar ta nemi mijinta da ya kuɓutar da ita daga hannun wannan azzalumi. Amma sai mijinta yace ai shi ba ya ganin komai. Washe-gari sai ya je ya sami mahaifin yarinyar nan ya ce masa ya lura dai matarsa tana ganin aljanu, saboda haka ya dawo da ita, ba ya auren, ya sake ta.

Da uban ya ji haka, sai ya tambaye ta abin da ta gani. Ta gaya masa duk yadda suka yi da Dodo. Sai baban yarinyar ya ba ta wata kyanwa, ya ce: “Idan har mutumin nan ya sake zuwa zan ce masa zan haɗa shi da ke ku je gidansa. Idan har ya rikiɗa ya zama wani abu, sai ki ce masa idan da gaske yake to ya rikiɗa ya koma wani ƙaramin abu, kamar ɓera.

Idan ya zama ɓera, sai kawai ki cinna masa kyanwar nan ta cinye shi. ”Rannan da mutumin ya dawo, sai uban yarinyar nan yace: “Zan ba ka ɗiyata, amma sai ta je da kai ta ga gidanka.” Sai mutumin ya ce: “Ta fito mu tafi.” Nan da nan yarinya ta naɗe tabarmarta, ta saka kyanwa a ciki yadda ba zai gan ta ba, ta fito suka tafi.

Suna isa kusa da gidansa, sai ya zama Giwa, sai ya ɗauki yarinyar ya kawo ta kusa da tukunya, amma ba ta tsorata ba, sai yarinyar ta ce: “In da gaske kake kana rikiɗa, to ka rikiɗa ka koma wani abu ƙaramin gani.” Nan da nan ya zama bushiya. Da ta ga haka sai ta yi tsaki ta ce: “Wannan ai ka yi rikiɗar kaya ce kurum. Ina so ka rikiɗa ka zama abin da ba shi da kaya.”

Yana jin abin da ta faɗa, sai ya rikiɗa ya zama ɓera. Kamar walkiya, sai yarinyar nan ta saki kyanwa. Nan take kuma kyanwa ta kama ɓerar nan ta lanƙwame. Jim kaɗan sai kawai dawaki da jakuna da raƙuma da sauran kayayyakin alatu masu ɗimbin yawa suka bayyana.

Nan da nan ta kwashe su ta ɗora wa raƙuman nan da shanu da jakuna da ta mallaka, ta zaɓi wata taguwa ta haɗa mata sirdi, ta hau, ta kora sauran dabbobin da ta yi wa laftun dukiya, ba ta tsaya ko’ina ba sai a gidansu. Da babanta ya gan ta da wannan dukiya mai tarin yawa, ga shi ta durƙusa ta gaishe shi, ta kuma yi godiya ga Allah saboda ya raba ta da wannan bala’i, sai ya yi matuƙar murna. Ita da mahaifanta da ’yan’uwanta suka ci gaba da morar wannan dukiyar hankali kwance. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Girman kai rawanin tsiya.
  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
  • Abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai iya hango shi ba.
  • Karen bana, maganin zomon bana

Danna nan don karanta Tatsuniyar Kare Da Kura

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Kare Da Kura
Labarin na GabaTatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.