Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Biri da kullum yakan je rafi wanka, bayan ya gama yawon cin ‘ya’yan itatuwa da tsalle-tsallensa ya gaji. Wata rana ya je wanka rafin da ya saba zuwa, sai ya haɗu da wani Kifi a cikin ruwa. Sai Kifin ya nemi su ƙulla abota da Birin. Biri ya amince, kuma suka yi wa juna alƙawari ba za su ci amanar junansu ba.
Suna nan, abotarsu ta yi ƙarfi. Wata rana sai Biri ya ce zai je ganin gida, watau a can wani daji da danginsa suke. Da Kifi ya ji haka, sai ya shirya wa Biri kayan tsaraba, ya ba shi; suka yi ban kwana, Biri ya kama hanya, ya tafi. Bayan ya tafi, sai sauran kifayen da suke cikin ruwa suka fara gunaguni wai su ba su son abokinsa Biri.
Har ma dai sauran kifayen suka shirya taro a ɓoye. A wurin taron waɗansu kifaye suka ce a kashe Biri, ko a kashe Kifin da ke abota da Biri. Sai babban kifayen ya ce: “A a, ba maganar kisa, domin kisan kai zai jawo gaba mara amfani tsakaninmu kifaye, ko kuma tsakaninmu da Birai.”
Haka dai suka ci gaba da shawarwari, har wani ya kawo shawarar cewa a kira Kifi a gaya masa za a ba shi sarauta a fadar Sarkin Kifaye, amma sai ya zo da zuciyar abokinsa Biri kafin a naɗa shi. Duk suka amince da wannan shawara. Aka kira Kifi abokin Biri, aka yi masa bayani.
Da ya ji bayanin da kifaye suka yi masa, sai ya ce da su: “Amma fa ni da Biri mun yi alƙawari ba za mu ci amanar juna ba. Kuma ni ba zan iya cin mutuncinsa ba idan aka ba ni sarautar.” Sai Kifi abokin Biri ya ce da danginsa kifaye su bari Biri ya dawo daga ganin gida, ya san zai yi duk yadda ya nemi ya yi.
Suna nan, sai Biri ya dawo daga tafiya, sai ya je wajen Kifi kamar yadda ya saba, ya kai masa tsarabar da ya zo da ita daga gida. Suka gaisa sosai, kuma suka shiga hira. Can sai Kifi ya sanar da Biri cewa bayan ya yi tafiya ‘yan’uwansa kifaye sun ce za su ba shi sarauta, ya zama Sarkin Kifaye.
Da Biri ya ji haka sai ya ce: “Kai, amma wannan labari da daɗi yake.” Sai Kifi ya ce: “To amma fa za ka raka ni cikin ruwa don ka gaishe su.” Biri ya ce: “To, ai sai mu je.” Suka yi nutso, har wajen taron kifaye. Sai abokin Biri ya ce: “Amma fa abokina, an ce sai na kawo wani abu kafin su ba ni sarautar.”
Da Biri ya ji haka, sai ya dubi Kifi ya tambaye shi: “To mene ne suke so? Ka ba su mana.” Kifi kuma ya ce da Biri: “Ai abin da suke so a jikinka yake.” Biri ya ce: “Mene ne, fadi zan ba ka.” Sai Kifi ya ce: “Sun ce in kai musu zuciyarka ne.” Sai Biri ya ce: “Ai don wannan babu komai, zan ba ka.
Amma ka san ba na yawo da zuciyata; tana can a kan bishiya na rataye ta. Bari in je in ɗauko maka.” A cikin murna Kifi ya ce: “To.” Ya raka Biri har bakin ruwa domin ya je kan bishiya ya ɗauko zuciyarsa ya kawo wa Kifi a nada shi sarauta.
Da Biri ya samu ya fita daga cikin ruwan, sai ya hau bishiya ya ceda Kifi: “Daga yau ba zan sake abokantaka da kai ba. Kuma ba zan sake shiga ruwa ba.” Da wannan dabara Biri ya gudu. Shi ya sa har yau din nan Birai ke tsoron shiga ruwa. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kowa ya ɗauki amana ya kamata ya riƙe ta da gaskiya.
- Hassada ga mai rabo taki ce.
- Kafin ka ga biri, biri ya ganka.
- Dabara kashin kwance.
- Iya ruwa, fidda kai.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan’uwa
Edita@rumasau-kallamu










