Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan’uwa

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani mutum da ‘ya’yansa guda biyu. Suna nan, suna nan, sai wata rana babansu ya tura su neman furannin ƙawa. An ɗauka cewa duk wanda nasa ya fi kyau, to mahaifinsu zai fi nuna masa soyayya a gidan, kuma za a yi masa aure. Shi ke nan, sai suka je. Da suka je, sai ƙaramin ya tsinki fure mai kyau.

Da yayansa ya gani, sai ya ƙwace, sannan kuma ya kashe shi. Sai ya kai furen nan gida. Sai babansa ya yi masa aure. Daga baya sai babansa ya tambaye shi inda ƙanensa yake, sai ya yi wa uban ƙarya, ya ce masa ya bar shi a baya, kuma zai ƙaraso gida ba da jimawa ba. Ana nan, ana nan, har wuni biyu, yaro bai dawo ba, Mahaifinsu ya jure ya kau da kai.

Wata rana wani boka ya zo wucewa, sai ya ci karo da ƙashin yaron da aka kashe, ya ɗauka yana hurawa. Sai ƙashin ya fara rera wa bokan nan wannan waƙa: “

Kai bokan nan kai bokan nan;

Ƙashina ne kake hurawa.

Baba ya aike mu daji, Mu samo furannin ƙawa,

Nawa sun fi na ɗan’uwana kyau,

Sai ya ƙwace nawan, Ya kashe ni.”

Da boka ya ji haka, sai ya kai wa Sarki wannan ƙashi. Da Sarki ya hura sai ya ce:“Kai Sarkin nan, kai Sarkin nan, Ƙashina ne kake hurawa. Baba ya aike mu daji, Mu samo furanni, ni da yayana, Nawa sun fi na wana kyau, Sai ya ƙwace nawan, Ya kashe ni.”

Sai Sarki ya sa a yi shela a sanar da mutanen garin cewa washegari gaba ɗayansu su zo ƙofar fadarsa, domin a tambaye su wanda ya yi wannan ɗanyen aiki. Da suka taru washe-garin, sai kowa ya ce ba shi ba ne. Sai Sarki ya ce, to za a sa duk wanda ke garin ya hura wuta, domin ƙashin zai faɗi wanda ya yi kisan kan.

Sai aka fara ta kan mahaifin yaron da aka kashe. Da ya hura, sai ƙashi ya ce: “Kai babana, kai babana, Ƙashina ne kake hurawa, Kai ka aike mu daji, Ni da wana, mu samo furanni, Nawa sun fi nasa kyau, Sai ya ɗauke nawan, Ya kashe ni.” Sai Sarki ya ce to ya kira yaron, watau yayan wanda aka kashe.

Ya zo, aka ba shi ƙashin ƙanensa, da ya fara hurawa, sai ƙashi ya ce: “Kai yayana, kai yayana, Ƙashina ne kake hurawa, Baba ya aike mu daji, Mu samo furanni, Nawa sun fi naka kyau, Sai ka ɗauke nawan, Ka kashe ni.” Sai Sarki ya ce to a kama yaron shi ma a kashe shi. Aka kama shi, aka kashe. Shi ke nan, an yi maganin wanda ya ci amana. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Cin amana kan jawo wulaƙanci.
  • Zafin nema ba shi ke kawo samu ba.
  • Idan Allah ya nufi mutum da arziki ba wanda ya isa ya hana.
  • Alhaki kare ne, mai shi yake bi.
  • Abin da ka shuka, shi za ka girba.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.