Tatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wasu yara su uku abokan juna. Wata rana sun je farauta sai suka kama maciji, suka aiki ƙaramin cikinsu ya nemo wuta domin su babbaka macijin, su ci; ya ce da su ba zai iya ba. Suka ba shi riƙon macijin, suka tafi neman wutar da kansu. Kafin su dawo ya saki macijin.

Da suka dawo suka ce ina macijin, ya ce maciji ya fi ƙarfinsa, wai sun yi kokawa ya ka da shi a cikin toka, kuma ya gudu. Sai suka ce ba su yarda ba, sai ya biya su. Baki ɗaya suka shiga gari, ba su tsaya ko’ina ba sai a gidan su wannan yaron. Bayan sun yi wa iyayensa bayani, sai mahaifansa suka kori yaron daga gidansu domin a hore shi.

Ya rasa inda zai zauna, sai ya shiga dajin da sukan je farauta da abokan nan nasa. Yaro ya gina gida a dajin nan, kuma ya faɗa a ransa cewa gara da bai kashe macijin nan ba. Can sai ga macijin nan ya fito, yaro ya gaya masa abin da ya faru. Sai ya ce da yaron ya bi shi gidansu domin su ci abinci.

Yaro bai yi musu ba; suka kama hanya. To, ashe macijin nan ba maciji ba ne, wani ɗan sarki ne da yakan rikida ya zama maciji idan ya yi nishaɗi. Suna zuwa gidan aka kawo musu tuwo a kwanon tagulla, irin na gidajen manyan tajirai da sarakuna. Yaro bai saba ba, ya ce ba zai ci tuwo a kwanon tagulla ba, sai a cikin ƙwarya.

Sai aka kawo masa abinci a ƙwaryar, ya kuma cinye shi duka; bai saba da rage abinci ba, kamar yadda akan yi a gidajen sarauta. Da zai kwanta sai aka yi masa shimfiɗa da buzun Sarki, sai ya yi fitsarin kwance a kai. Aka ce masa ya je ya wanke buzun. Yaro ya kama hanyar rafi domin wanke buzun Sarki.

Amma sai ya faɗa wani gida haka kwatsam, ba tare da ya sani ba. Sai masu gidan suka ce masa in yana jin yunwa tun da sun ga shi baƙo ne, kuma ba su san irin nisan tafiyar da ya yi ba, ya ɗauki shinkafa ƙwaya ɗaya ya dafa; sai ya ɗauka, ya wanke, ya jefa a tukunya, ya ɗora sanwar shinkafa; sai ya ga ta cika tukunya; ya ci, har ya ƙoshi, kuma ya bar saura.

Bayan ya yi wa masu gidan godiya, sai ya ce da su zai tafi gida. Sai suka ce ya ɗebi ƙwaiƙwaye guda uku, idan ya kama hanya ya fasa ɗaya. Da ya kama hanya ya ɗan yi nisa da gidan nan, sai ya fasa ƙwai ɗaya. Yana fasawa sai ya ga fatu masu yawa masu launi iri daban-daban.

Sai ya kwasa, bai zame ko’ina ba sai gaban Sarki, da nufin Sarki ya zaɓi wadda yake so, Sarki ya zaɓa. Bayan yaron ya ƙara hutawa, sai ya ce da abokinsa ɗan Sarki, zai tafi. Sai abokin ya ce in babansa, watau Sarki, ya ba yaron kyauta, to kar ya karɓa, kuma ya ce masa ba ya son komai sai zoben da ke hannun Sarkin na hagu.

Yaro ya matsa kusa da Sarki ya sanar da shi zai tafi. Da Sarki ya ji bayanin yaro, sai ya ce da shi ya faɗi duk abin da yake so zai ba shi. Sai yaro ya dubi Sarki ya ce ba ya son komai sai zoben da ke hannun Sarki na hagun. Sai ko Sarki ya ba shi; ya yi godiya, ya fita waje suka haɗu da abokinsa ɗan Sarki.

Sai ɗan Sarki ya ce wa yaron nan abokinsa: “A duk sanda ka ji yunwa, sai ka ce zobe-zobe, mai shekara tamanin da takwas, zai ba ka duk abin da kake so.” Shi ke nan, yaro ya yi ban kwana da abokinsa, ya kama hanya.Yana cikin tafiya sai ya fara jin yunwa, kuma ba abin da zai ci. Sai ya zauna a gindin wata bishiya.

Sai abokinsa ɗan Sarki ya zama maciji, ya same shi ya ce da shi: “Ka manta abin da na gaya maka ka faɗa wa zoben idan kana jin yunwa?” Sai ya tuna masa. Sai yaron ya ce: “Zobe, zoben shekara tamanin da takwas”. Zoben ya ce: “Me kake so?” Ya ce: “Ina son tuwo.” Sai ko ya ga tuwo; ya zauna ya ci har ya ƙoshi.

Da ya tafi gidansa na ciyawa, sai ya ce: “Zobe, zobe mai shekara tamanin da takwas.” Sai zoben ya ce: “Me kake so?” Sai ya ce: “Ina so gidana ya zama mai kyau kamar na samarin da ke tashe a gari.” Sai ya ga gidansa da ɗakinsa sun yi kyau. Sai ya je gidan babansa ya ce ya zo ya kai su su ga gidansa.

Sai suka bi shi, suka gano gidan. A gaban iyayensa ya kirawo sunan zobe mai shekara tamanin da takwas, ya sa zoben nan ya mayar da shi saurayi kyakkyawa. Daga bisani a wannan hali na kyau ya je neman aure gidan Sarki. Sarki ya sa masa sharuɗa, watau lallai sai ya kawo shanu masu yawan da ba a taɓa ganin yawansu ba a garin, tare da zannuwan da kamar ba za su ƙare ba saboda yawa.

Nan da nan yaron nan ya sa zobe mai shekara tamanin da takwas ya kawo duk abin da aka nema. Sarki ya aura masa ‘yarsa. Suna nan, suna nan, sai wata rana yana wurin wanka, sai matar ta sace zoben, ta kai wa babanta. Sai aka kama yaron aka ɗaure. Sai yaron ya aiki kare da kyanwa da ɓera su je gidan Sarki su ɗauko masa zoben nan.

Da suka je, kare ya ja Sarki da taɗi, kyanwa tana yi wa Sarki wasa, ɓera kuma ya shiga wajen da Sarki ya ajiye zoben, ya sato shi. Daga bisani suka yi sallama da Sarki, suka kama hanya domin su kai wa yaron nan zobe. Suna cikin tafiya, sai suka tarar da wani kogi, wanda dole sai sun haye shi kafin su kai gidan yaro.

Sai kare ya goya ɓera da kyanwa domin su ƙetare ruwan. A garin tsallaka ruwan, sai zoben ya sulluɓe, ya faɗa cikin ruwa. Bayan sun isa gidan yaro sun gaya masa, sai ya ce su je bakin ruwa su ce da masu kamun kifi suna son hanjin kifayen da suka kama, suka feda. Aka yi ta kawo musu hanjin kifi, har aka ba su wanda zoben ke ciki.

Sai suka kai wa yaron nan zoben. Da ya kira zobe mai shekara tamanin da takwas ya amsa masa, sai ya tambaye shi abin da yake so. Yaro ya ce ya na so zoben nan ya fitar da shi daga gidan maza, watau kurkukun da aka ɗaure shi a ciki. Nan take ko sai ya gan shi a gidansa. Can kuma sai ya lura da ɓera da kyanwa da kare ma suna nan.

Sai ya tambayi ɓera abin da yake so. Ɓera ya ce daddawa yake so. Yaro ya tambayi kare abin da yake so ya ci. Kare ya ce yana so ya ci ɗanyen nama. Daga nan kuma yaro ya tambayi kyanwa abin da take son ci; ta ce ƙadangare take muradi. Sai yaron ya ce: “Zobe, zobe.” Kafin ma ya kai ga cewa mai shekara tamanin da takwas a duniya, tuni zoben ya tambaye shi abin da yake so.

Sai ya ce yana son ɗanyen nama da daddawa da ƙadangare. Kafinya gama rufe baki har ya kawo masa su. Ba tare da jinkiri ba kowa ya ɗauki nasa, ya tafi. Sai yaron ya ce wa zoben yana son ya ga Sarki da matarsa ‘yar Sarki a gabansa suna rawa. Sai ko ya gan su suna rawa. Sai ya ce yana so ya ga sun mutu. Sai suka faɗa wuta, suka mutu. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Alheri ɗanƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
  • In za ka haƙa ramin mugunta, haƙa shi gajere.
  • Kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau.
  • Kowa ya tausayawa wani, shi ma sai Allah ya tausaya masa.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗan Agwai Da Kura

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ɗan Agwai Da Kura
Labarin na GabaTatsuniyar Cin Amanar Ɗan’uwa
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.