Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum yana da ’ya’ya biyu mace da namiji. Macen ce babba, namijin ne ƙarami. Ita sunanta ’Yar Gwaggo, shi kuma sunansa Ɗan’auta. Da iyayensu za su rasu sai suka kira ’Yar Gwaggon suka ce: “Za mu bar miki ƙaninki Ɗan’auta. Kada ki ba shi wahala, duk abin da yake so ki ba shi; kuma duk abin da ya ce zai yi, kada ki hana shi; ki bar shi ya yi.”
’Yar Gwaggo ta ce: “To na ji.” Sai iyayen suka kwanta, suka rasu. To da ma iyayen sun bar musu dukiyar abinci da kadarori. Bayan ’yan kwanaki da rasuwarsu sai Ɗan’auta yace su tattara dukiyar da abincin da gidan baki ɗaya su ƙona. Sai ’Yar Gwaggo ta ce: “Haba Ɗan’auta, idan muka ƙona kuma me za mu ci, kuma a ina za mu zauna?” Sai Ɗan’auta ya ce: “Ba su baba sun ce idan ina son komai ki ba ni ba, kuma duk abin da zan yi kada ki hana ni?”
Sai ta ce: “To shi ke nan, ka tashi mu tara kayan a ƙona.” Suka tara kayan da abincinsu rumbu-rumbu, suka ƙona. Da yunwa ta fara damun su sai ’Yar Gwaggo ta ce to su tafi bara. Suka kama hanya har gidan Sarki sai suka tarar da ’ya’yan Sarki suna wasan kirbe-kirbe, sai yace shi ma sai ya yi.
Sai ’Yar Gwaggo ta ce: “Haba Ɗan’auta, wannan fa gidan Sarki ne, kuma ’ya’yan Sarki suna wasa. Idan aka kama mu fa?” Sai ya ce: “Ba su iya da baba sun ce duk abin da na ce zan yi ki ƙyaleni ba?” Sai ta bar shi ya shiga wasan ’ya’yan Sarki. A cikin wasan ya ɗaga ɗaya daga cikinsu, ya ƙwala da kasa sai cinyarsa ta karye.
Sai Sarki ya sa fadawa su kama shi. Ganin haka sai ’Yar Gwaggo ta kama hannun ƙanenta suka kama gudu, har cikin jeji, dogarai suna bin su. Can sai suka hau kan wata bishiya, suka ɓuya. Da dogarai suka zo sai suka rasa hanyar da suka bi, sai suka ce bari su huta a gindin bishiyar nan. Su Ɗan’auta na kan bishiyar.
Da ɗaya daga cikin dogaran ya kwance rawaninsa domin ya sha iska, ga shi ya aske kansa ƙwal-ƙwal yana ƙyalli, sai ɗan’auta ya auna kan dogarin sosai, sai kawai yace wa ’Yar Gwaggo: “Zan yi kashi.” Tsoro ya kama ’Yar Gwaggo, domin idan dogaran nan suka ji motsi za su kama su. Sai ta ce: “Haba Ɗan’auta, idan ka yi kashi za su gan mu, su kama mu fa.”
Sai ya ce: “Ba iya da baba sun ce duk abin da zan yi ki ƙyale ni ba?” Sai ta ce: “To shi ke nan yi kashinka.” Sai ya tuɓe wandonsa ya auna daidai kan dogari sai ya ɓarke da kashi. Da kashi ya zuba kan dogari sai ya ce: “Wannan wane ɗan iskan tsuntsu ne ya yi mini kashi?”
Da suka ɗaga kai sama sai ga su Ɗan’auta da ’Yar Gwaggo, sai suka fara sarar bishiya, saura kaɗan ta faɗi, sai ga wata ’yar tsuntsuwa za ta wuce, sai ’Yar Gwaggo ta ce: “‘Yar tsuntsuwa ki taimake mu mana.” Sai tsuntsuwar ta ce: “To ku hau bayana.” Suka hau bayan ’yar tsuntsuwa, ta tashi da su sama suka fara tafiya.
Bayan sun fara nisa a can sama, sai Ɗan’auta ya ga gindin tsuntsuwa na ta motsi, yana budewa ya rufe. Sai kawai ya ce zai tsokale gindin tsuntsuwa. Yayarsa ta ce: “Haba Ɗan’auta, ita da ta taimake mu. Da an kama mu an kashe. Ka yi haƙuri mana.” Sai ya ce: “Ba inna da baba sun ce idan na ce zan yi abu kada ki hana ni ba?”
Sai ta ce: “To ka yi.” Sai ya sa kara ya tsokale gindin tsuntsuwa. Sai ta juyar da su, suka faɗa cikin wani babban rafi. Suka yi ta iwo har suka kai bakin ruwa. Sai suka fita a daidai wani ɗan ƙauye. Da suka shiga ƙauyen sai suka fara neman masauki. Sai suka haɗu da wata ’yar tsohuwa suka gaya mata su baƙi ne masu neman masauki.
Sai tace: “To zan ba ku masauki, amma fa a garin nan ba a fita da daddare don akwai wani dodo da yake cin mutane; har sarki ya yi alƙawari zai ba duk wanda ya kashe dodon rabin gari kuma ya aura masa ’yarsa.” Sai suka ce: “To shi ke nan.” Da dare ya yi sai Ɗan’auta ya ce shi fa sai ya ga dodon da yake hana mutane fita.
Yayarsa ta yi, ta yi da shi kada ya fita waje, ya hura wuta a gefensa. Da wuta ta ruru, sai ya saka duwatsu bakwai a cikinta, har suka yi jawur. Sai ya zauna a tabarmarsa, ’yar tsohuwa kuma don tsoro sai ta shiga randarta ta buya a ciki. Da dodo ya iso gari ya shiga waƙa yana cewa: “Wa ya yi da ni a garin nan, Wa ya yi da ni, ni dodo in cinye shi?”
Sai Ɗan’auta ya mayar masa yana cewa: “Na yi da kai a garin nan, Na yi da kai ni Ɗan’auta.” Da tsohuwa ta ji sai ta fara zawo a cikin randar don tsoro. Sai dodo ya nufo inda Ɗan’auta yake. Da Ɗan’auta ya ga ya buɗe baki, sai ya ɗauki dutsen nan da ya yi jawur da wuta, ya jefa a cikin bakin dodo.
Sai dodon nan ya hadiye. Ya ci gaba da matsowa, shi kuma Ɗan’auta ya ci gaba da jefa duwatsun nan, har ya zo kan na ƙarshe. Da ya jefa na bakwai, sai kawai dodon ya faɗi matacce. Da Ɗan’auta ya ga haka, sai kawai ya koma ya kwanciyarsa. Da gari ya waye sai aka aika wa Sarki cewa an kashe dodon da ke damun mutanen gari.
Sarki kuwa ya ce duk wanda ya kashe dodon za a ba shi rabin gari, kuma a aura masa ’yar Sarki. To da ma shi Ɗan’auta ya manta takalmansa a inda ya yi faɗa da dodo. Da aka tara mutane suka zo suka yi ta gwada takalma amma bai yi ba, sai da suka nemi baƙin da suke garin.
Da Ɗan’auta ya gwada takalma sai suka yi daidai da shi. Nan take aka ba shi rabin gari, Sarki kuma ya cika alƙawari, wato ya ba shi auren ’yarsa. Ƙurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Wauta ne a sakar wa yaro linzami ya yi abin da ya ga dama.
- Mai wayo ya fi mai zafin nama cin nasara.
- Ya kamata a karɓi bako da hannu bibbiyu don ba a san alhairindazai kawo ba.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Sarki
Edita@rumasau-kallamu










