ASALIN ƘASAR HAUSAWA

0
3648

Masana tarihi sun ambaci cewa, akwai mutane tun lokaci mai tsawo da ya shuɗe a waɗannan garuruwa na Kasar Hausa, kuma babu wanda zai bugi ƙirji ya ambaci daga inda suke,

koda yake dai wasu kuma sun ambaci cewa ana kyautata zaton asalin Hausawa barbarar yanyawa ne, tsakanin mazauna kasar da baƙi da suka yiwo ƙaura daga ƙasashen Asiya zuwa ƙasashen Afirka.

Dalilin wannan ƙaurar kuwa, an ce wai juyin mulkin da ya faru ne a tsakanin Banu Abbas da Banu Umayyah a Bagadaza, shi ya sanya wasu suka yiwo ƙaura, daga nan ne suka bazu cikin Afirka ta Yamma, musamman ta fuskar kasuwanci.

Sai dai kuma an ce, yayin da suke yin waɗannan kaurace-kauracen ne, kamanninsu da harshensu da al’adunsu suka canja saboda auratayya da canjin yanayin rayuwa.

Har ila yau, an ƙara da cewa, ana zaton mutanen sun fi daɗewa a Daura da Kano, ba don komai ba kuwa, sai don su ne aka gwada kuma aka ga akwai daɗaɗɗen tarihinsu da yadda mutanen suka rayu a waɗannan wurare. (Adamu, M.T. 1997:21 – 22).

  Akwai masu ra’ayin cewa, tun asali Hausawa a garuruwansu na Ƙasar Hausa Allah ya yi su, ba wai sun yiwo hijira ba ne daga wani wuri suka zo nan ɗin.

Malaman suna da hujjoji masu yawa a kan hakan, daga ciki suna kafa hujja da maganar babban Malamin nan Sheikh Nasiru Kabara, kamar yadda yake cewa jirgin kwale-kwalen

Annabi Nuhu (AS) yayin da ruwan Dufana ya dauke, ya tsaya ne a wani gari mai suna ‘Yandoto, wanda yanzu garin yana cikin Jihar Zamfara ta nan Ƙasar Hausa.

A wajen masu wannan ra’ayi, wannan nahiya tun asali ana kiran ta da shi wannan suna ne da aka santa da shi wato “Hausa”.

Yawan ƙare-ƙare a wasu shiyyoyi na Kasar Hausa, da ƙarancinsu a wasu wuraren shi ne babban dalilin da za a jinginu da shi.

A cewar masu wannan ra’ayin, duk inda ƙare-ƙaren suka tattaru a ɗan ƙanƙanen wuri, to a nan aka haifi harshen.

Idan kuma ka ga harshe ya yaɗu, bai daya a kasa mai fadi, to ba a nan aka haife shi ba, ya zo ne daga wata kasa.

(T/Wazirchi, 2009:17 – 18). Bunza, yana da irin wannan ra’ayi cewa “Hausa ba daga wani wuri ta zo ba, Nahiyar Gobir nan ce mahaifar Hausa”.

(T/Wazirchi, 2009): 18). Sannan su ma mafi yawan mawakan baka, musamman waɗanda suka fito daga yankin Sakkwato, Zamfara da Kabbi suna ambaton wannan nahiya “Hausa”.

Idan muka koma ga gurbin ƙasar Hausa, wato taswirarta ta faro ne daga yammacin Afirka, yankin kudancin Sahara kuma arewa da Kurmi inda Larabawa ke kira Biladul Sudan, wato kasar baƙar fata.

Yanki ne da ya ƙunshi ƙasashe da dauloli da dama a cikin su har da Ƙasar Hausa.

Wadda ta kafu a Yammacin Sudan, tsakanin Tafkin Cadi daga Gabas, da guiwar Kogin Kwara daga Yamma, da hamadar Sahara daga Arewa, da kuma dazuzzukan gabar Tekun Atilantika daga Kudu.

Dangane da Ƙasashe da Ƙabilu da Ƙasar Hausa ta yi iyaka da su kuwa, a Gabas ta yi iyaka da Kanem-Borno, a shiyyar Kudu, kuma ta yi iyaka da Kwararrafa (Kasar Tibi, Nufe, Gwari, da sauran tsirarun Ƙabilu).

A yamma kuma ta yi iyaka da tsohuwar Daular Songhai, daga shiyyar Arewa kuma Ƙasar Hausa ta yi gaɓa da garuruwan Buzaye (Agadas) na cikin kasar Nijar.
(T/Wazirchi, 2009: 11 – 12). A yanzu haka idan muka duba taswira, za mu ga Kasar Hausa tana Arewacin Nijeriya ne da kuma wani sashi na Jamhuriyar Nijar (T/Wazirchi, 2009: 12).

A cikin ƙabilu mazauna yankin Savannah, wato ƙasa mai karancin itatuwa, ko mai itatuwa jefi-jefi, Hausawa su ne suka fi mamayar wurin zama mai fadin gaske.

Wannan wuri shi ne aka fi sani da ƙasar Hausa. (Gusau, 2008: 2).

Domin karanta cikakken bayani a kan Hausawa da al’adunsu ko kuma asalin kalmar Hausa da ma’anarta danna koren rubutu nan

labarin da ya wuceHausawa Da Al’adunsu
Labarin na GabaASALIN KALMAR HAUSA DA MA’ANARTA