Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana ’yan matan Fangama suka shirya za su biki a wani gari da ke kusa da su. Dabarar zuwan ita ce ko za su yi dace kowaccensu ta sami manemi, wata rana a yi nata bikin. Kowacce dai ta ci ado, abin gwanin ban sha’awa. Amma kafin su tafi sai da suka fita bayan gari domin kowacce ta tsinko wa mahaifiyarta goriba.
Dukkanninsu sun samo goriba, in ban da ɗaya daga cikinsu. Ita ta nema, ta rasa. Shi ne bayan sun koma gida, sai mahaifiyarta ta ce lallai ta koma sai ta samo, in ba haka ba kuwa, ita babu tafiya biki. Ta rasa yadda za ta yi don ƙawayenta sun shirya za su tafi su bar ta.
Haka dai ta jure ta koma wurin bishiyar goriba, ta roƙe ta. Da bishiyar ta ji bayaninta, sai ta tambaye ta: “Me za ki yi da goribar idan na ba ki?” Yarinya ta ce: “Zan kai wa mahaifiyata saboda ta ba ni kayan da zan sa mu je wani biki aure tare da ƙawayena.” Da jin haka bishiyar ta ce: “Ba zan iya taimakon ki ba, sai in kin roƙi girgije ya sako ruwa in sha.
Idan na sha sai in zuba ’ya’yan da zan ba ki.” Yarinya ta durƙusa ta roƙi Ubangiji ya sauko da ruwa. Bayan wani ɗan lokaci kuwa sai aka kece da ruwa mai ɗimbin yawa. Goriba ta yi ’ya’ya, yarinya ta tsinka ta kai wa gyatumarta. Nan da nan uwar ta kawo kayan kwalliya da na alatu, masu kyan gaske ta ba ’yarta.
Amma kuma tuni ƙawayenta cikin gaggawa sun tafi, sun bar ta a baya.Da yake tana cikin ɗoki, ba tare da kasala ba ta kama hanya ita kaɗai, har ta isa wurin bikin. Ta tarar ƙawayen ba su jima da zuwa ba. Samari kuwa sun cika wurin, saboda iyayen ma’auratan sun gayyato mutane da yawa.
Aka yi ta shagali, suka ɗirki rawa, har suka gaji. Can a lokacin tsarince, sai wani saurayi kyakkyawa wanda ke tashen samu ya kira ta. Suka yi taɗi, ya yaba hankalinta. Daga nan suka shirya aure, da ta koma gida ta sanar da iyayenta, shi maya tura magabatansa gidansu.
A takaice dai, aka ba shi ita, suka yi aure. Sauran ƙawayenta ma daga baya Allah ya ji kukansu, ɗaya bayan ɗaya suka sami maza, kowacce ta shiga ɗakin miji. Yanzu haka suna can har sun fara hayayyafa, kowacce na zaune lafiya da mijinta. Kuma wani abin ban sha’awa shi ne, har yanzu suna ƙawance da junansu. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Mai nema yana tare da samu.
- Ka so wa ɗan’uwanka abin da kake so ga kanka.
- Biyayya ga iyaye takan kawo wa mutum buɗi da cimma burinsa na rayuwa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata
Edita@rumasau-kallamu









