Tatsuniyar Gizo Da Sarki

0
35

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wata tsohuwa a wani ɗan ƙauye; tana da ɗan maraƙinta kyakkyawan gaske; ga shi ƙosasshe. Ana nan wata rana Gizo ya je gidan wannan tsohuwa bara sai ya ga wannan maraƙi. Sai ya fasa bara ya fita daga gidan, ya sheƙa a guje sai gidan Sarki.

Ya faɗi a gaban Sarki, ya ce: “Ko kunnuwan Sarki nawa ne?” Sarki ya ce: “Biyu.” Sai ya ce wa Sarki: “Ƙara biyu, a kan biyu ka sha labari.” Sarki ya ce: “Na ƙara.” Sai Gizo ya ce: “Akwai wani kyakkyawan sa a gidan wata tsohuwa, in ba gidanka ba, to sai gidana.” Sai Sarki ya ce: “To shi ke nan.”

Sai Sarki ya tura dogarai don a kamo kuma a kawo masa wannan san. Da dogarai suka kama hanya ba su tsaya a ko ina ba sai a gidan tsohuwa. Suka same ta, suka isar da saƙon Sarki. Da ta ji bayanin dogaran Sarki sai ta ce: “To yaya zan yi yau.” Dalilin tsohuwa na faɗin haka shi ne wannan sa ba ya yin komai sai dai zninta.

Dogaran Sarki suka yi, suka yi su kwance sa daga turkensa su tafi da shi amma abin ya gagara. Can dai sai tsohuwa ta saka san a gaba tana yi masa waƙa tana cewa:

“Tafi tafiye tirke,

Sarakan bana kwaɗayi gare su,

Abu kadan a kai ka fada,

Abu kadan a kai ka fada, Har gaban Sarki.”

Haka ta rinƙa rera wannan waƙa san yana yi mata biyayya har suka isa gidan Sarki. Da suka isa fada Sarki ya ga sa sai ya ce za a yanka shi. Sai ya tambayi tsohuwa abin da take so daga jikin san. Sai ta ce ita abin da take so kawai shi ne kayan ciki. Sarki ya ba da umarni aka yanka sa, aka feɗe aka ɗebi kayan ciki aka ba tsohuwa.

Da tsohuwa ta koma gidanta sai ta shanya kayan cikin nan, ta mai da hankalinta a kan aikinta na gona. Wata rana ta dawo daga gona sai ta tarar an yi mata shara a gida da sauran aikace-aikacen gida. Sai abin ya ba ta mamaki tana tunanin ba ta da kowa, kuma wanene zai zo ya yi mata wannan aiki.

Kashe-gari ma aka sake yi mata aikin. Ashe da ma kayan cikin nan da tsohuwa ta shanya su ke rikiɗa su koma ’yan mata kyawawa guda biyar. Kullum idan ta tafi gona, sai su fito daga ƙarƙashin gadonta inda suke kwana su yi mata hidima. Wata rana sai tsohuwa ta ce tun da ba ta san mai taimaka mata ba, za ta shirya kamar za ta gona sai ta ɓuya a bayan danga domin ta ga mai yi mata wannan hidima.

Haka kuwa aka yi. Ta ɓuya a bayan danga, can sai ga ’yanmata kyawawa sun fito daga ƙarƙashin gadonta. Nan da nan suka fara aikace-aikacen gida, suka buɗe randunanta suka cika da ruwa, suka yi share-share da duk sauran ayyukan da suka kamata. Can sai kwatsam tsohuwa ta faɗo tsakar gida suka gan ta.

Ta yi musu magana. Daga wannan rana sai ’yan matan nan suka daina ɓuya, suka zauna da tsohuwa suna taya ta aikace-aikacen gida. Bayan wasu ’yan kwanaki sai tasa wa kowacce budurwa suna. Akwai Ta-kitse da Ta-hanji da Ta-tumbi da Ta-hanta da Ta-huhu.
Ana nan, ana nan wata rana Gizo ya sake komawa bara gidan tsohuwa, sai ya hango waɗannan ’yan mata kyawawa a gidan tsohuwa.

Ya fita da gudu sai gidan Sarki. Da ya isa sai ya ce: “Sarki, Sarki kunnenka nawa?” Sai Sarki ya ce: “Biyu.” Sai Gizo ya ce: “Ka ƙara biyu ka sha labari.” Sai Sarki ya ce: “Na ƙara.” Daga nan sai Gizo ya kwashe labarin ’yan matan da ya gani ya gayawa Sarki. Nan take sai Sarki ya tura fadawa a kawo masa guda ɗaya daga cikinsu.

Sai dogarai suka je gidan tsohuwa suka yi sallama da ita. Da ta fito sai ta ga fadawan sarki ne. Sai ta koma gida ta fara waƙa tana cewa: “Ta-hanta, Ta-hanta, Ɗebo ruwa ki kai wa baƙon da ke waje.” Sai Ta-hanta ta ce: “Tabɗi, in ɗebo ruwa Ta-huhu tana nan.”

Sai tsohuwa ta sake rera waƙa ta ce: “Ta-huhu, Ta-huhu, Ɗebo ruwa ki kai wa baƙon da ke waje.” Sai ta ce: “Tabɗi, in ɗebo ruwa in kai wa baƙon da ke waje, ga Ta-hanji
tana nan?” Da haka, da haka har tsohuwa ta gama zagaya ’yan matan nan, har ta kai
kan Ta-kitse. Ita ce ta ƙarshe.

Sai ta ɗauko ƙoƙo, ta ɗebi ruwa ta kai wa baƙon da ke waje. Tana fita da ruwan nan sai fadawa suka kama ta, sai gaban Sarki. Da Sarki ya gan ta sai ya ce zai aure ta. Nan da nan kuwa ya aure ta ya sa ta cikin matansa. Amma ba ta fita rana, kuma ba ta zuwa kusa da wuta domin ita kitse ce, idan ta sha rana ko zafin wuta ya buge ta sai ta narke.

Wata rana Sarki ya tafi yaƙi, sai kishiyoyin Ta-kitse suka ce sai ta fito ta yi girki, tun da ita ma auro ta aka yi kamar su. Da suka matsanta sai ta yi girki, sai ta je bakin murhu. Tana zuwa sai ta narke. Da tsuntsun Sarki ya ga abin da ya faru sai ya yi tsalle ya tashi sai filin daga inda su Sarki suke fafatawa da abokan gaba.

Sai tsuntsun nanyafara waka yana cewa: “Sarki, Sarki, Ka mai da yaƙi baya, Ta-kitse ta narke, Ta narke ta zama ruwa.” Da Sarki ya ji waƙar tsuntsun nan sai ya bar yaƙi ya komo gida. Sai ya tarar har Ta-kitse ta gama narkewa. Saboda laifin da matansa suka yi masa na sa Ta-kitse girki a kan dole, sai ya kore su gaba ɗaya ya yi zamansa shi kaɗai. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Son zuciya ɓacin zuciya.
  • Abin da ka shuka shi za ka girba

Karanta Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceRiya Da Tasirin Social Media
Labarin na GabaTatsuniyar ƊanAuta Da ’Yar Gwaggo
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.