Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

Wata rana Kurege yana farauta a daji sai ya ga mushen Kurciya, sai ya ɗauka ya ajiye a kan itace. Ya ci gaba da tafiya sai kuma ya ga mushen Giwa, ya matsa kusa, ya dubi mushen da kyau, ya yi dariya. Daga nan sai ya kai wa Kura ziyara.

Ya same ta tana saka zana sai yace: “Ki bari in kwanta a kan zanar nan taki.” Sai Kura ta ce: “To, kwanta mana.” Da Kurege ya kwanta sai ya lumshe idanunsa. Jim kaɗan kuma ya buɗe; sai ya ce da Kura: “Na yi mafarki wai mun je yawo da ke sai muka sami kan Kurciya mai kyau.”

Kura na jin haka sai ta ce: “Kai-kai, ai gara ka sake kwanciya ko ka ƙara yi mana mafarki mai daɗi fiye da wannan.” Kurege ya rufe ido, ya buɗe sai ya ce: “Kai na sake yin mafarki wai kin sami mushen Giwa ke kaɗai.” Kura na jin haka sai ta ce da Kurege: “To mu tafi mu bi sawu.”

Da ya ji sai ya ce: “Yanzu dare ya yi, sai dai can idan gari ya kusa wayewa.”Bayan zakara ya yi cara sai Kura ta sake cewa da Kurege su tafi, shi ko yace ta bari sai da hantsi. Kura ta kasa haƙura, sai ta hura wuta a kan ɗakinta wai hantsi kenan. Amma Kurege sai ya gane, ya ce da ita: “Ai wannan wuta ce kika hura a kan ɗakinki.”

Daga ƙarshe dai da gari ya waye hantsi ya ɗaga, sai suka kama hanyar bin sawun mafarki. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura Kura wajen kan Kurciya. Da ta gani ta kirawo shi suka raba. Suna cikin tafiya sai Kurege ya tura ta wajen mushen Giwa. Da ta gani sai ta je ta yi kashi domin ta kasayar da abin da ke cikinta, domin ta sami damar cin naman mushen Giwa sosai, tun da ga nama kamar ba iyaka.

Kurege da Kura suka shiga gyara nama. Suna cikin wannan aiki kenan sai ga ‘ya’yan Giwa sun bi sawun uwarsu. Sai tsoro ya kama Kurege da Kura. Sai Kurege ya ce: “Zan shiga cikinta in buya.” Sai Kura ta ce: “Kai yaro ne, ni babba ce zan shiga ciki.” Da Kura ta dage sai ta shiga cikin Giwa, shi sai ya shiga mafitsarar mushen Giwar.

Da ‘ya’yan Giwa suka je kan mushen uwarsu, sai suka fitar da mafitsarar suka yar da Kurege a ciki. Da Kurege ya fita daga cikin mafitsarar, sai ya ga wata ƙarama daga cikin ‘ya’yan Giwar tana yankan ciyawa sai yace: “Wayyo, wa ye ya zuba mini ruwa?” Sai ‘ya’yan suka ce: “Ayya sannu ba mu san kana nan ba.”

Sai ya ce: “A a, me ya sami kakata?” Sai baki ɗayansu suka ce: “Ba mu sani ba.” Sai Kurege ya ce: “Ku kawo jar dawa in zuba a ruwa in yi muku duba.” Da suka ba shi jar dawa sai ya ce: “Abin da ya kashe kakar nan tawa yana cikinta. Abin da za ku yi sai ku ɗauko sanduna ku yi ta dukan cikin.” Sai ko ‘ya’yan Giwa suka yi kamar yadda Kurege ya faɗa.

Da duka ya ishi Kura sai ta ce: “Ba ni kaɗai ba ce, ni da Kurege ne.” Kurege ya ce: “Kada ku saurari maganarta, ku bugi wajen gefen bakinta.” Haka suka yi ta jibgar Kura, ta fito daga cikin Giwa jina-jina, ta gudu ta tsira da ƙyar. Sai ‘ya’yan Giwa suka ɗauki sauran mushen uwarsu suka kai gida domin su binne. Sai Kurege ya roki su ba shi kan kakarsa dominwai yabinne a gidansa. Sai suka yarda suka ba shi.

Niyyarsa yana so ya dafa ne. Da zuwansa gida sai ya sa a tukunya aka hura wuta, aka sa tukunya akan murhu, kuma ya ce wa ‘yarsa: “In wuta ta mutu sai ki zo ki faɗa mini cewa ciyawa ta kare a gaban doki.” ‘Yar Kurege ta ce: “To baba, na ji.” Shi kuwa Kurege ya sa kai ya koma wurin ‘ya’yan Giwa zaman makoki.

Da wuta ta cinye icen, sai ‘yar ta je gidan Giwa inda ubanta ke zaman makoki tace masa: “Baba ciyawa ta kare a gaban doki.” Kurege na jin haka ya ɗauki hannu, kuma ya tashi ya bi ‘yarsa suka tafi gida. Ya tarar naman kan Giwa bai gama dahuwa ba, sai ya ƙara ice, ya koma gidan makoki. Bayan wani dan lokaci da kan Giwa ya gama ɓararraka, sai yarinyar ta koma gidan Giwa inda ake zaman makoki ta ce masa: “Baba ai kan kaka kamar ya nuna.”

Da ‘ya’yan Giwa suka ji haka, sai suka ce: “Ashe ba binne kan ka yi ba, dafawa kake yi? To sai a kama shi a kashe nan take.” Da ya ji haka sai ya falle da gudu tal-tal-tal ana bin sa, sai ya tarar da wani Kurege yana saƙa. Sai Kurege mai saƙa ya ce da Kurege mai gudu: “Me ya koro ka?” Sai Kurege mai gudu ya ce da Kurege mai saka: “Ai Sarki ne ke son wutsiyar Kurege dubu, sai mu gudu.”

Da jin haka sai Kurege mai saƙa ya falle da gudu shi kuwa Kurege mai laifi
ya yi zamansa ya kama saƙa. Da ‘ya’yan Giwa da masu taya su bin sawun Kurege mai laifi suka ga wancan Kurege yana gudu, sai suka bi shi, har suka kama shi, suka kashe. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Zafin nema ba ya kawo samu.
  • Kwaɗayi mabuɗin wahala.
  • Dabara ta fi ƙarfi.

Karanta Tatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar ‘Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.