Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani Sarki yana da ‘ya’ya maza da mata da yawa. Wata rana an kawo masa ɗinya sai ya ajiye ta a dakinsa. Rannan sai tafiya ta kama shi. Sai ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ta ɗauki dinyar ta cinye. Da Sarki ya dawo sai ya tarar an cinye masa ɗinya. Sai ya tara matansa da ‘ya’yansa ya tambaye su ko waye ya cinye masa ɗinya.
Sai suka shiga yi masa rantsuwa cewa ba su suka ɗauka ba. Bayan an yi, an yi babu wanda ya amsa cewa shi ne ya ɗauka, sai Sarki ya ce da fadawansa su tara matan da ‘ya’yan a kai su Kogin Rantsuwa su rantse, kuma duk wanda ya ɗauka to ruwa ya cinye shi, ya tafi da shi.
Suka yarda aka kama hanyar kogi. Da aka isa sai aka fara rantsuwar da matan Sarki. Duk wadda ta shiga cikin ruwan sai ta fara waka tana cewa: “Kogi, kogi, In ni ce na ci ɗinyar Sarki, Ka tafi da ni, Kuma ka dawo da ni. Kada ka hadiye ni.” Matar farko ta fita ruwa bai tafi da ita ba.
Ta biyu ma ta shiga ruwan bai tafi da ita ba, har matar ƙarshe ta shiga ita ma ruwa bai tafi da ita ba. Daga nan sai aka shiga kan ‘ya’yan Sarki maza. Aka zuba su gaba ɗaya suka rantse, su ma ruwa bai cinye ko ɗaya daga cikinsu ba. Shi ke nan aka zo kan ‘ya’yan matan.
Su ma aka shigar da su, ba wadda ruwa ya ci har aka zo kan ta ƙarshe wadda ta cinye ɗinyar. Sai ta shiga ta fara waƙa tana cewa: “Kogi, kogi, Idan ni ce na ci ɗinyar baba, Ka tafi da ni, Kuma ka dawo da ni, Kada ka haɗiye ni.” Sai Kogin Rantsuwa ya tafi da ita. Sai matan Sarki da sauran ‘ya’yansa suka juya, suka koma gida, aka je aka gaya wa Sarki abin da ya faru.
To ashe duk jama’ar gidan Sarki ba su san cewa wannan yarinya da ruwa ya tafi da ita Sarki na matuƙar son ta ba. Dalili kuwa ita ce ‘yar autarsa, sai ya yi ta kuka. Ruwa kuwa da ya tafi da ita sai ya kai ta wani baƙin jeji. Tana nan a rufe, can sai ta ga wata tsohuwa tana kama kwaɗi.
Da tsohuwa ta ƙyallara ido ta ga yarinya, sai ta ɗauke ta, ta kai ta gidanta. Yarinya ta shari barcin gajiya. Da ta farka sai tsohuwa ta tambaye ta labarin abin daya faru. Sai ta kwashe labari ta gaya wa tsohuwa. Da tsohuwa ta ji labari sai ta ce wa yarinya: “Zan taimake ki, in sauya miki kamanni.
Amma da sharaɗi, idan kin sami mijin aure zai kawo mini buhunan tsutsa biyu.” ‘Yar Sarki ta yarda. Nan take tsohuwa ta haɗiye ta sau bakwai. Da ta yi amanta ta haɗiye ta sau bakwai sai ga yarinya ta sauya kamanni baki ɗaya, ta zama fara jawur kamar ‘yar Sarkin aljanu.
Bayan wasu shekaru, wata rana sai yarinya ta je cin kasuwa, sai ta haɗu da wani ɗan Sarki. Shi kuwa ɗan’uwanta ne na jini, to amma ba ta sani ba, don sun girma ba za ta gane shi ba. Shi kuma da ma ba zai gane ta ba saboda tsohuwa ta sauya mata kamanni. Shi ke nan sai ɗan Sarki yace zai aure ta. Sai ta ce sai dai ya je wurin kakarta su yi magana.
Sai ya amince, suka je wurin tsohuwa. Da tsohuwa ta ji bayanin ɗan Sarki sai ta ce ya je ya kawo mata buhunan tsutsa biyu. Ɗan Sarki ya tashi cikin mamaki. Ya je ya nemo buhunan tsutsa biyu, ya kawo wa tsohuwa. Daga nan sai aka ɗaura masu aure. Ya ɗauki matarsa ya kai ta garinsu.
Bayan ya kai ta gidansu, sai ta ga ashe gidan babanta ne. Sai kawai ta shiga cikin gida gayar da surukanta. Sai ta ga ai wadda ta haife ta ce surukarta. Shi kuma mijin yayanta ne, ubansu ɗaya. Da ta gane sai hankalinta ya tashi, amma babu yadda za ta bayyana wannan al’amari a gamsu tun da tsohuwa ta sauya mata kamanni.
Kullum idan za ta yi daka sai ta fitar da turmi a tsakar gida tana daka tana waƙa tana cewa: “Babana da ya haife ni ya zama surukina, Innata da ta haife ni ta zama surukata
Yayana da nake binsa ya zama mijin aurena, Kannena da suke bi na sun zama abokan wasana, Zan daki turmin gidanmu, Zan daki turmin gidanmu timkwalan-kwalan.
Ana cikin haka kullum, sai wata tsohuwa ta kasa kunne ta ji abinda amarya take cewa. Rannan dai sai tsohuwar nan ta kira yaron ta gaya masa idan ya fita kamar za shi zaman fadanci, to ya laɓe a cikin gida ya saurari waƙar da matarsa take yi idan tana daka, ya ji abin da take cewa. Rannan sai ɗan Sarki ya fita, kamar ya tafi, sai ya laɓe.
Jim kaɗan da amarya ta fara daka sai ta kama waƙar tana maimaita abin da take cewa kullum. Da ya ji waƙar matarsa sai ya fahimci abin da take faɗa, kuma ya gane cewa ƙanwarsa ce. Sai ya ruga da gudu, ya kama ta, yana kuka ya ce: “Ashe ke ce ‘yar autar baba, amma kika ki faɗa?”
Ya ɗauke ta sai wurin babansa. Da ya yi gaisuwa, ita ma ta gai da Sarki, yace ta ba mahaifinta labarin abin da ya faru. Sai ta kwashe labari yadda ta cinye ɗinyar babanta, har ruwa ya tafi da ita. Ta faɗi yadda tsohuwa ta ɗauke ta, da yadda ta haɗiye ta ta sauya mata kamanni.
Bayan ta kammala ba su labari, sai baki ɗayansu suka yi ta kukan murna, ‘yarsu ta dawo. Daga nan sai aka raba wannan aure, domin mutum ba ya auren ‘yar uwarsa. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Ba a tausaya wa ɓarawon da aka kama.
- A kowane jinsin mutane auren zumunta yana da ƙa’ida
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Rimi Da ‘Yar Amana
Edita@rumasau-kallamu










