Har yanzu ba a tabbatar da asalin Hausawa ko harshensu ba, amma akwai hasashe da dama da ake yi game da asalin Hausawa ko harshen Hausa. Mafi yawan manazarta suna ganin harshen Hausa ya malalo ne daga Arewa maso gabas daga gurbin da yake a yanzu, wato ƙasar Hausa.
MA’ANAR KALMAR HAUSA
Ma’anar kalmar Hausa ba ta tsaya ga sunan harshe kaɗai ba, akwai wasu ma’anoni da Hausawa suke danganta kalmar da su. A ƙamusoshi kamar: Bargery (1933) da Abraham (1962) da Garba (1999) da kuma Ƙamusun Hausa (2006), kalmar tana da ma’anoni da aka rege kamar haka:
1. Kalmar tana nufin harshe ko yare kowane iri. Misali, Ba na jin Hausa tasa. Wato ba na jin harshensa ko yarensa.
2. Kalmar tana nufin harshen da Hausawa suke magana da shi.
3. Kalmar tana nufin ƙasar Sakkwato, wadda yanzu ta haɗa da jihohin Zamfara da Kebbi.
4. Hausa na nufin azancin magana.
5. Ana amfani da kalmar a ma’anar hikima ko kan gado.
6. Haka kuma yankin da Hausawa suke zaune ana kiransa da Hausa ko ƙasar Hausa.
7. Kalmar Hausa tana nufin abin da mutum yake nufi.
ASALINTA
Dangane da asali kuwa, har yanzu ba a tabbatar da asalin kalmar Hausa ba saboda saɓanin ra’ayoyi da ake samu dangane da asalin kalmar, kuma ga alama kalmar ba ta daɗe samuwa ba saboda rashin samunta a wasu daɗaɗɗun rubuce-rubuce da aka samu game da Hausawa, da wasu larabawa suka yi, irin su Ibni Sa’id da Ibni Batuta da Almaƙrizi da kuma Leo Afircanus.
Amma wasu masana sun yi ƙoƙarin bayyana ra’ayinsu game da asalin kalmar kamar haka:
1. Ra’ayin Skinner (1968) wanda ya ce an samo kalmar HAUSA ne daga Songhai, wai su ne suke kiran mutanen da suke zaune a gabas da ƙasar Songhai da suna ‘AUSSA’ daga nan kalmar ta zama ‘HAUSA’ saboda Hausawa ne suke zaune a gabas da ƙasar Songhai. Haka kuma mutanen gabashin tafkin cadi suke kira mazauna yammacin Tafkin Cadi, ba mamaki kasancewar harshen ya malalo daga wannan waje.
2. Ra’ayin C. R. Niven (1971) wanda ya ce an samo kalmar ne daga Buzaye, domin suna kira mutane da suke zaune a arewacin kogin Kwara da suna Hausa.
3. Muhammad U. Adamu (2011) ya ce an samo kalmar ne daga sunan Fir’auna Hausal, wanda yake ganin daga zuriyarsa ne aka sami Hausawa.
4. Ra’ayin Malam Aminu Kano da Yusif Maitama Sule Ɗanmasanin Kano, waɗanda suka ce an samo kalmar ne daga HABASHA, domin Hausawa daga Habasha suke, kuma kalmar ta sauya daga HABASHA ta koma HABSA sannan ta zama HAUSA.
5. Ra’ayin sarkin Ningi Haruna, wanda yace an samo kalmar ne sakamakon zuwan Bayajidda Daura, domin ya je ne a kan doki, ita kuma tsohuwar da ya sauka a gidanta ba ta san doki ba, sai ta bayyana shi da wanda ya hau sa, wai daga kalmar ‘HAU SA’ (hawa sa) aka sami ‘HAUSA’.
Domin karanta Aure A Ƙasar Hausa danna nan
Edita; Rumasa’u M. Kallamu