Bahaushe yana tsohon tsarin kwantar da tarzo ma (peace and conflict resolution). A kowacce masarauta akwai sarki, sarki yana da alqali domin zartar da hukunci da masu laifi ko daidaito tsakanin ma’aurata, ‘yan kasuwa da sauransu.
A matakin qasa kuma, uba shi ne ke sasanto (sulhu) a tsakanin ‘ya’yansa, ko matansa, ko ‘ya’yansa da ‘ya’yan makwafta. Dattijan unguwa ko mai unguwa kan iya sasanta makwafta da suke savani.
Kafin zuwan addinin na amfani da tsafi, layoyin sagau, layar zana, buduhu domin tsarin jiki. Bahaushe na amfani makamai kamar takobi, mashi, majaujawa, sanda, qolo, qele, qotar wuqa, adda, gitta da tarko. Sai bingida barudu bayan zuwan Larabawa.
Domin karanta bayani akan Addinin Bahaushe Danna nan
A tsaron gari kuma, Bahaushe yana gina ganuwa da qofofin shiga gari don samun kariya daga hari. Sannan akwai tsarin dogarai da ‘yandoka (police) masu kula da shige da fice, kama mai laifi, hukunta mai laifi da sauransu.