Sana’o’in Bahaushe

0
30

Bahaushe tun asali ba cima-zaune ba ne, yana da  sana’o’i domin samar da abinci, sutura, muhalli da  dogaro da kai. Sana’o’in Bahaushe na da rassa huxu;  noma (yawaituwa), kasuwanci (sayarwa), aiwatarwa  (skills) da sana’o’in bixa.

Yahaya da wasu (1992) sun raba sana’o’i gida uku, a kasan kowanne ya samar musu  ‘ya’ya, a qasan noma, akwai qira, saqa, dukanci. A  kasuwanci, akwai dillanci da fatauci da sauransu. Kaso  na uku su ne, qunshi, soye-soye, gyare-gyare, gashe gashe. 

Noma, shi ne xaxxanar sana’ar Bahaushe ce da ma  mutanen duniya baki xaya (Alhassan da wasu 1982), sai  farautar dabbobin daji da harbin tsuntsaye. Bahaushe na  fatauci, kasuwanci, su (kamun kifi), shiqa, farauta, harbi, gini, sassaka, jima, qira, gini, saqa, dukkanci, rini,  wamzanci, fawa, sarrafa abinci (shiqa, daka, niqa, dafe dafe, soye-soye da gashe-gashe). 

Domin karanta bayani akan Addinin Bahaushe Danna nan

Wani abu game da sana’o’in Hausawa, a da, mutum  yana gadon sana’ar gidansu ne (xan gado), wanda kuma  ya kama sana’ar da ba ta gidansu ba, ana ce ma  ‘shaye’(shigege) (Niang, 2005). Misali, a garin Haxejia,  akwai unguwannin masu sana’o’i, kamar unguwar  Masaqa, inda ake saqa; akwai Unguwar dukawa,  Majema, Maqera, unguwar Sarkin Ruwa, Unguwar  Sanqira da sauransu. 

Yadda Bahaushe ke koyon sana’a kuma, ana koyo ne a  barance, saboda babu rubutu. Idan yaro ya kai shekara  bakwai (7) da haihuwa, bayan an yi masa shayi, za a kai  shi yana kallo yadda ake yin sana’a. Daga shekara sha uku (13) za a fara sa shi qananan aiyuka. Daga shekara  sha takwas (18) zai fara manyan aiyuka, shekara 20  kuma za a barin sa yana aiyuka, ko ba dubawa, shekara  25 – 27, za a ‘yanta shi.

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceHukunci Da Sulhun Da Tsaro Agun Bahaushe
Labarin na GabaFasahar Bahaushe